Showing 81001 words to 84000 words out of 122467 words

Chapter 28 - Buzu Book 2 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

37

za ki je kuma ga ayyukan kitchen fal?"

Nana ta numfasa ta ce "Ki yi ha?uri, Hasna ce ta saka ni aiki, ta ce idan na gama, na je na huta"

"A'a ba zai yiwu ba, ni ce mini a aka yi kawai za ki yi mata aiki, dan hakan idan kin gama ki saka hannu ku ci gaba da aikinmu, wa za ki bar wa wannan aikin?"

"To ki yi ha?uri, na gaji gaskiya ba na jin daWi" kawai ta fice, tattaunawa suka shiga yi a tsakanin su, yadda za su kawo ?arshen Nana a gurin baki Waya.
A ?arshe suka yanke shawarar, su ?ara ?aimi su Sata ta a gurin Hasna, ganin yadda ita ma ta sako Nana a gaba da tsangwama.

Bayan sallar isha'i, Nana ta daWe a zaune tana tasbihi, tunanin gidansu da 'yan uwanta ya addabi zuciyarta, ga shi abin da ta fito neman har yau babu labari. Ta daWe tana addu'a kafin ta nemi guri ta kwanta.

Washegari ma su na ta aiki tun safe har Yamma, sai ga Hasna ta shigo.

Duk yadda Hasna take da kyau, ita da Al Hussain, wannan da suka shigo ta fita kyau, tamkar balarabiya, jawur da doguwa sai dai siririya ce sosai. Fuskarta ta sha make up, sai zuba ?amshi take yi.
Ta yafa Wan siririn mayafin abayarta a kanta. Sai kallonsu take Waya bayan Waya tana yatsuna fuska su na yare ita da Hasna.
Duk suka gaishe su, Nana kuma ta yi burus.
Hasna ta nuna mata Nana ta ce "Kin ganta nan"

Asal ta yamutsa fuska ta ce "Ya na ganta ba?a ?irin haka, ina fatan ba na ?azanta ba ne?" Nana ta yi mamakin jin Hausa raWau a bakinta.

"Ke ina ruwanki da ba?inta, ba dai Abinci ya yi ba?"

"Eh kin san ba na son ?azanta ne"

Hasna ta ce "Sauran ma'aikatan namu ma ai akwai ba?a?e, kuma kema kin san da ba ta da tsafta, ba zan saka ta yi miki girki ba.Ke Nana ba ki ganni da ba?uwa ba ne?" Nana ta Waga kai ta kalle su, ta yi shiru tana wasa da wu?ar hannunta, saboda ciwon da maganganun da suke yi ya yi mata, na cin zarafin ba?ar fatarta da danganta ta da ?azanta, duk ba wai duhu ne da ita sosai ba.

Shiru Hasna ta yi ta kamo wata hirar, ganin alamun idan ta matsa Nana za ta yarfa ta ne a gaban ba?uwarta. Ba a taSa ma'aikacin da ba ya shakkar ta ba sai Nana. Duk abin da ta saka ta na aiki za ta yi, amma ba ta son rainin hankali.

Bayan sun fito Asal ta tsaya ta kalli Hasna ta ce "Hasna"

"Na'am"

"Ina ga yarinyar nan ta yi dai-dai da abin da nake nema"

"Wace yarinyar?"

Asal ta ce "Wannan 'yar Nigeriar, ina bu?atar za ki ba ni ita"

Ayshercool
08081012143

70

Sai da Nene ta tabattar Nana ta Wan nutsu, sannan suka kwanta.

Washegari Nene ta fita, ta bar Nana a gidan tare da Muhsin. Bayan ta dawo daga gurin sama'arta ta cewa Nana, yakamata ta je ta Wan sai abubuwan da za ta bu?ata saboda tafiyar da za ta yi da nisa, kuma ba su san yaya tsarin aikin can Win yake ba.
Nana ta ce "Ni babu abin da nake bu?ata, ki bani wani abin na ri?e a hannuna, sauran kuWin kuma ki ri?e saboda kula da Muhsin na s...

"Biyana za ki yi kenan dan na ri?e miki Muhsin?" Nene ta katse ta.

"Allah ya baki ha?uri, ba haka nake nufi na, na ga dole Wan abubuwan bu?atunsa duk ke ki ke yi masa Nene, tun da ga kuWi sun"

"KuWinki ba su isa su saka na ri?e miki Wa ba ko?"

Nana ta ce "Na sani, ai shi ya sanya na ce ki yi ha?uri.

Nene ta ce "Ba zan yi ha?urin ba sai na gama, kin iya kunna ni da na fara faWa ki hau bani ha?uri, wato in ci kaina to sai na idar"
Nana ta yi mata shiru ta yi faWanta ta gama.
Washegari Nene ta saka Nana a gaba suka je kasuwa, ta sata ta yi sayayyar kayan sakawa da na Wan shafe-shafe, ta yi wa Muhsin sayayyar kayan sakawa da pampers. Babu yadda ba ta yi da Nene ba ta Wauki wani abin ta ce ba za ta Wauka na.
Nana ta haWe rai ta ce "Eh dama ba ki Wauke ni 'yarki ba, shi ya sanya duk abin da zan yi miki ba kya karSa"

"Ni za ki yi wa wayo, na ji ban Wauke ki 'yar ba, ni ga Wana nan" tayi maganar tana shafo Muhsin da ke bayanta. Da ?yar sai da suka kai ruwan rana Sannan Nene ta karSi abin da Nana ta saya mata.
Sai dai kan su bar kasuwar har sun shirya. Nana ta ce "Nene kin ce mini ki na da Wa, amma ban taSa ganinsa ya zo ba, ba ya zuwa ya gan ki ne?"

Nene ta ce "Kamar ban damu da shi ba ko?"

"A'a kawai dai tambaya na yi "

"Yana can Nigeria"

"To me yake yi a Nigeria ba ya zuwa inda ki ke?"

"Sana'a yake yi, ai ya zo ki na can gurin aiki"
Duk da Nana ba ta gamsu da amsoshin da Nene ta ba ta ba, amma ta basar ta ce "Allah sarki, Allah bai yi zamu haWu ba".

Haka suka ci gaba da hira suka koma gida, Nana ji take yi tamkar ta Wauke Wanta ta tafi da shi.

Gidansu Ashura Nana ta je, ta samu keke ta WiWWinka kayan da ta sayo, ta sake haWa jakarta ta Wauki muhimman abubuwa a kayanta.
Duk da a Waki Nene take rufe mata su, ba ta taSa ganin alamar Nenen tana yi? bincike a cikin kayan ba.

*****
Ko da Jamila suka dawo Kano, fakar ido ta yi ta jefar da wannan tarkacen da aka ba ta aka ce da su za ta kai jini.
Gaba Waya da ta tuna abin tsigar jikinta take tashi, ta ji ciwon kanta da zazzaSi ya ?aru.
Gefe guda kuma hankalinta yana kan yadda ta ji Hajiya Sa'a tana faWin za ta sake bayar da Wan Alhaji Fatuhu. Ta jinjina rashin imaninta mutumin da yake fama da karayar arziki ga ciwo, ya rasa wancan Wan kuma a sake bayar da wannan kamar ba a yi masa adalci ba. Sai dai gaba Waya ba ta san ta ina za ta fara ba, tana jin a ranta kamar yakamata ta tseratar da yaron.
A gida ta tarar da Gaddafi, ta sha jinin jikinta da irin mugun kallon da ya yi mata, amma bai ce mata uffan ba. Suwaiba ma ?ura mata ido ta yi tana bin ta da kallo.
Ta tsuke fuska ta harsri Suwaiba, sai dai Suwaiba ta tuntsure da dariya, kamar za ta shiWe. Jamila ta yi tsaki ta shige Wakinsu.
Ba ta tarar da Mama a gida ba, haka ma Baba.

*****

Shiru Alhaji Zailani ya yi yana kallon Doctor Sharif yana sauraren shi, har ya gama karanta masa abin da Shukura ta je ta same shi ta yi masa.
Ya ja numfashi ya ce "Shikenan, aikinka ya yi kyau Sharif, na kuma gode sosai da sosai da ka ke sanar da ni wannan abubuwan, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Ka je za ka ga sa?o" Sharif ya yin?ura ya tashi ya tafi.

Alhaji Zailani ya numfasa a fili ya ce "Duk da kasancewar ki 'ya mafi soyuwa a cikin zuciyata, an zo gaSar da ki ka ?etare layin da bai kamata ki ?etare ba, kina ?o?arin tono abin da zai wargaza zaman lafiya da kwanciyar hankali, dan haka ki yi ha?uri da duk matakin da zan Wauka a kan ki.

*****
Nana ta jingina da jikin gilashin motar, tana kallon tulin yashin saharar da ya mamaye gurin. Fili fetal hagu da dama duk yashi ne. Cikin yanayi mai kama da bacci take ganin abubuwan da ta din ga gani a bacci cikin saharar.
Ko a yanzun ma su na tafe Sayyid kawai take gani a kan ra?umi yana biye da su a cikin saharar.
Kamar an taSa ta ta Wan yi firgigit ta kalli gurin, haryanzu a titin da ya ratsa saharar suke tafiya, zuciyarta ta yi wani irin bugu da sai da ta dafe ?irjinta.
Sanyi ta fara yana ratsa ta har cikin ?ashinta, ta Waga ido tana Wan waige-waige ta ga ta ina za ta gano ?aisar ko wata ba?uwar halittar da ba jinsin mutane ba, sai dai ba ta ga komai ba.
Ta sake jingina da jikin motar tana ta karanto duk addu'ar da ta zo bakinta. A haka har suka shigo cikin gari sosai da sosai.
Nana na son karanta Symbols Win da take gani, amma ba komai take iya fahimta ba saboda rubutun French. Babbar hanya mai Wauke da ?aton gate ta ciki suka wuce.
Ba ?aramar gajiya Nana ta yi ba, saboda azabar nisan tafiyar da suka shawo ba, ba su ?arasa ba sai bayan magariba. Kewar Wan ta ta addabi zuciyarta, tunaninta yadda za ta din ga sintirin tsakanin Agadez da MaraWi a wannan uwar tafiyar kamar ta ya da shege.

Wasu irin gidaje ne manya-manya na alfarma da ?asaita a cikin gurin.
A ?ofar wani gida direban ya tsaya, ya cewa Nana ta fito sun?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? zo. Haka ta saukko ?afafuwanta duk sun yi tsami saboda azabar gajiya.
Ya buWe bayan motar ya Waukko ?atuwar jakar Nana, ya rufe motar, ya yi gaba Nana ta bi shi a baya tana karanto addu'oin da suka sauwwa?a.
Cikin wani matsakaicin gida suka shiga, gidan ya ?awatu ya yi kyau sosai da sosai.
A falon gidan ya ajiye wa Nana kayanta ya ce "Ki zauna ki jira a nan"

Nana ta ce "Amma wa zan jira a nan Win, ban ga alamar akwai mutane a gidan nan ba"

"Za ki gan su, ni a nan aka yi mini umarnin na kawo ki kawai"

Nana ta yi shiru tana nazari, shi kuma ya juya ya fice.
Nana ta din ga rarraba ido, tana son ta yi salla amma babu wanda za ta tambaya. Harabar gidan ta fita saboda ta ga famfo ta yi alwala, ta dawo falon ta yi salla.
Gajiya ta yi ta koma harabar gidan da kayanta, ta zauna tana rarraba ido.
Can ta ji ?arar mota, aka buWe ?ofar wani jami'in tsaro ya shigo ya buWe gate Win, aka shigo da wata haWaWWiyar mota aka yi parking Win ta.
Aka buWe ?ofar motar, sai ga Asal ta fito sanye cikin doguwar riga, ta Waura mayafin a wuyanta, kanta babu Wankwali. Har bakin ?ofar shiga suka rakata, ta wuce Nana ta shige ciki kamar ba ta gan ta ba. Nanan ma ta yi zamanta ba ta shiga ba, ta jingina da jikin kayanta taka addu'a saboda a gajiye take matu?a, ga uwar yunwa tana ji ga tulin damuwa.
Sannu a hankali take tuna yadda ta shigo ?asar Nijar ba ta san kowa ba, da yadda ta din ga raragefe har zuwa kan zamanta da Nene. Sai ta tsinci kanta da tattara su baki Waya tana yi musu addu'a, da fatan dacewa a Duniya da lahira.
Ba ta san iya adadin lokacin da ta Wauka a gurin ba, ta ji muryar Asal a kanta.
"Wai ke wace irin bagidajiya ce, a Nigeria daga wani ?auyen ki ke ne?" Nana ta Waga kai ta kalle ta.

"Na saka an kawo ki guri, ki shiga ki jira ni kin zauna a waje, na dawo ma kin nemi guri kin zauna ba za ki shigo ba?"

"Ta yaya zan shiga gurin da babu kowa na zauna, ni da ban san ma aikin da ki ka kawo ni na yi miki ba?"

Haushi ya kama Asal, ta ce "To idan kin ga dama ki shigo, idan kuma ba ki ga dama ba, ki yi ta zama a gurin" Ta shige ciki Nana ta bi ta da harara, kamar ba za ta tashi ba, sai kuma ta tashi ta ja kayanta, ta shiga falon ta nemi guri ta zauna a kan kujera. Asal ta saci kallon Nana, da yadda take gudanar da lamarinta cike da ?arfin hali.

Nana ba ta kula ta ba, ita ma ba ta kula ta ba, Nana ta gaji da zama, ta saukko ?asa ta mi?e ta kwanta.
Can Asal ta ce mata "Ga kitchen can, akwai abinci"
Daga haka ta tashi ta bar falon.
Nana ta tashi ta shiga kitchen Win, ta tarar da Abinci, ta Wauka ta ci sannan ta Wan dawo hayyacinta.
A nan falon Nana ta kwana, da Asuba ta yi alwala a harabar gidan, ta koma falon ta yi salla.
Duk wannan abin zuciyarta a cike da zullumin aikin da za ta yi wa Asal.
Da gari ya yi haske, Asal ta fito Nana ta gaishe ta, amma ta yi kamar ba ta ji ba, ta fice ta bar gidan ta bar Nana.
Nana tana nan zaune, aka zo aka ?wan?wasa ?ofar falon, ta tashi a Wan tsorace ta buWe, wani mutum ya mi?o mata takeaway ya ce "Ga shi nan, aka ce a kawo miki" daga haka ya juya ya tafi.
Nana ba ta sake ganin Asal ba sai dare, ba ta saurari Nana ba still. Ta cika gidan ita da ?awayenta, suka hau saman bene, suka kunna kaWe-kaWe har kusan Waya na dare su na abu Waya, suka hana Nana bacci.
Sai gefin Asuba suka daina wannan shirirtar, Nana ta din ga mamakin ita Asal zaman kanta take yi ne, ba ta da magabata ko kuwa?
Sai washegari sannan ta saukko ?asa, a lokacin ?awayen nata duk sun tafi.
Ta kalli Nana ta ce "Daga yau kar ki ?ara kwanar mini a falo, ga Waki can kusa da kitchen, a nan za ki din ga kwana. Na kawo ki ne duk da ba yanzu ne za ki yi aikin naki gaba Waya ba, amma za ki din ga yi mini girkin Abinci da ni da ?awayena, da sauran aikace-aikacen gida.
Abu na farko dalilin da ya sanya na Waukko ki, ke ba ?abilarmu ba ce ba, ba na son saka ido, ba na son surutu
Duk wani abu da za ki ga na yi, ko ina yi babu ruwanki, aikin duk da na saka ki shikaWai za ki yi mini"
Nana ta yi shiru tana tunani, dama duk wannan abin ba wani branch Win za a kai ta aiki ba, wannan zu?a??iyar za ta yi wa bauta, shi ne har da ci mata mutuncin cewa an yi amfani da kuWi sai ta yi abin da ake so. Kuma me yasa ba ta zaSi kowa ba sai ita?.
"Ba kya ji na ne?"

"Na ji"

"Ban gane kin ji ba? Haka zan din ga yi miki magana ki na amsa mini, ke ni fa ba Hasna ba ce ba, dole ki yi mini biyayya ki yi duk abin da nake so".

Nana ji ta yi tamkar ta yi tsaki, ta ce "Amma yanzu fisabilillahi duk faWin ?asar nan ki rasa wanda za ki Waukko ya yi miki aikatau sai ni. Ni harkar dafa abinci nake yi, amma kin kawo ni nan in din ga yi miki girki da boyi-boyi ba tare da an yi mini bayanin haka ba, ni gaskiya ba a kyauta mini ba"

"Da hakan ki ka dace ai, ko kina ganin kin cancanci wani abin bayan bauta? Idan ba za ki zauna ba ga hanya nan za ki iya tafiya" Ta yi maganar tana mi?ewa tsaye.
Har ta yi gaba sai kuma ta tsaya ta ce "Duk wani abu da za ki bu?ata akwai shi a kitchen, kina iya dubawa, wanda babu kuma ki sanar mini, shi ma idan ba ki ga dama ba kar ki yi aikin" ta yi gaba ta bar Nana da ta gama ?ulewa.

*****

Gaba Waya Shukura ta burkicewa Sagir, ba Waga masa hankali ta yi da rigima ba, tattara shi ta yi ta watsar gaja Waya take harkokinta, da gaske take ?o?arin gano abin da mahaifinta yake Soyewa tsawon wannan lokacin da har ya hana Hajiya Amina bincike a kan lafiyarta.
Ga shirin tariyar Yusra Sagir na yi, ga damuwar rashin sakin jiki da shi da Shukura ta yi, ta tattara shi ta watsar.
?angarensa ya saka aka gyarawa Yusra, dama ba amfani yake yi da shi ba, aka ?ara gyara shi, aka haWa gidan gaba Waya aka sake yi masa fenti. Daga gaya mata batun dawo da Yusra zuwa gyaran gidan da kawo kayanta, ba a yi sati guda ba, gida ya Wau harama.
Duk yadda ya so ya lallaSa Shukura, ta saukko ta din ga saurararsa ta yi burus da shi.

Nana ta shafe sati guda tana gidan Asal, tana yi mata hidima, ta hantare ta ta kyare ta, dandazon ?awayen da take tarawa ma, su hana ta sukuni da aiki. Nana ta din ga iya ?o?arinta, gurin kai zuciyarta nesa, amma abin ya fara isarta.
Tana tsaka da nazarin yadda za ta Sullowa lamarin, da safe Asal za ta fita ta kalli Nana ta ce "Ki shirya nan da sati Waya zamu bar nan, zamu je asalin inda na Wauke ki ki yi mini aiki a gurin"

Nana ta ce "Ina kenan? Kuma aikin me?

"Idan mun je za ki gani" Ta ba wa Nana amsar a ta?aice.

*****
Jamila tana kwance tana chatting da Abba, bikinsa saura sati biyu.
Hajiya Sa'a tana ta zaginsa da yi masa bala'i, a kan yadda yarinyar take ta ?orafin ba ya kula ta, waya ma sai dai ita ta kira shi, babu abin da ya yi masa zafi da ita.
Yanzun ma kamar ya yi wa Jamila kuka.
Ita take ta rarrashinsa tana nuna masa babu komai ya yi aurensa kawai.

"?anwata ko na yi aure hankalina ba zai kwanta ba, kar ki manta da Sarnar da ta faru tsakanina da ke, ya zan yi da shi"

Ta ce "Na san kai mutumin kirki ne yayana, hakan ne ya sanya ka ke jin damuwa a kan abin da ya faru, amma ka yi ha?uri ka yi aurenka kawai, ina ro?on Ubangiji Allah ya kawo mini wani mijin"

"A'a ki daina faWa mini haka, zuciyata tana sosuwa, baki da wani miji sai ni in sha Allah" haka suka kasance tana ?arfafa masa gwiwa, shi kuma yana rarrashinta.
Ta gama wayar ta ajiye, ta ga Suwaiba ta ?uro mata ido tamkar ba ta taSa ganinta ba.

"Meye ki ke kallona, lafiya?" Suwaiba ta yi shiru ba ta bata amsa ba, kuma ba ta yi magana ba.

Jamila ta ja tsaki, tana ?o?arin kwanciya, Suwaiba ta ce "Jamila"

"Na'am mene ne?"

"Ki Wauki sa?onki mana"

Cikin rashin fahimta ta ce "Wane sa?on?"

"Na cikin jakarki"

"Cikin jakata kuma? Mene ne a jakar tawa? Wato bincike ki ke yi mini a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login