Showing 90001 words to 93000 words out of 122467 words

Chapter 31 - Buzu Book 2 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

17

sunan Imam, lokaci lokaci su na haWa wa da Hausa, sai dai ta manta a inda ta taSa jin Imam Win.

Babban abin da ya Waurewa Imam kai, bai wuce yadda a faransa yake jin sa garau, ba shi da wata damuwa ko wani ciwo da yake ji ba. Amma tun da ya sanya ?afarsa a Agadez tsawon kwanaki huWu, ko sau Waya zuciyarsa ba ta saurara da bugun da take yi cikin sauri babu ?a??autawa ba.

Nana na ta kai komo a kitchen, ta kammala duk wani aiki da ya shafe ta, tana shirin tafiya ta je ta kwanta. Balaraba ta ce "Saurin me ki ke yi ne Nana?"

"Ina son na je na yi wanka na kwanta ne"

"Ki je ki yi wankan, nan da mintuna talatin za ki kai wa Gimbiya Asal bunu da madara sashinta"

Har Nana za ta yi magana, dan ba ta shiga sashin Asal sai sau Waya, ta taSa zuwa idan sun yi girki akwai waWanda suke kaWai suke iya zuwa sashen su kai. Ta fasa maganar ta ce "To"

A gurguje Nana ta kintsa, ta koma ta Wauki kayan za ta yi gaba, Balaraba ta ce "Ai ba sashinta za a kai ba, Ramata raka ta"

Ramata ta kalli Nana ta yi mata kallon banza, ta Wan kwaSe baki sannan ta yi gaba Nana ta bi bayanta.
Duk yadda Nana ta so sarrafa kanta ta kasa, ta Waga kai ta din ga kallon ?awataccen gurin tare da jinjina yadda masu gidan suka ?ware a iya almubazzaranci. Dan ba za ta kira shi ado ba kawai sai dai almubazzaranci.

Tana saka ?afarta a cikin falon, ta ji tamkar an jona mata shocking, saboda rawar da jikinta ya yi, sai da farantin hannunta ma ya girgiza tamkar zai Sare. Ramata ta kalle ta, ta yi tsaki kawai.
Nana ta ajiye kayan a hankali a kan carfet Win Wakin.
Bayan ta ajiye ta yi taku huWu zuwa biyar, ta ji yadda adadin sanyin da take ji yana ?ara yawa. Ta sauke idanunta a kan ?aton frame da hotonsa a jiki. Dan?arewa ta yi a guri Waya, ta kasa motsa ko da ?afarta.
Taku ta fara ji a bayanta, ana tahowa, muryar Asal ta ji tana magana da faransanci cikin shagwaSa.
?an ja ya yi ya tsaya, jin yadda jikinsa ya yi wata girgiza.

"Lafiya dai ko?"

Ya jinjina mata kai alamar eh.

"Amm me ku ke yi a tsaye a gurin nan ne?"

Ramata ta ce "Abinci muka kawo"

"Waye ya yi?"

Ta nuna Nana da ba ta juyo ba.

"Zo" ta kira Nana sai dai Nanan ta ?ame ba ta juyo ba. A wula?ance Ramata ta taSa ta ta ce "Ana yi miki magana"
"Tana ji na rainin hankalin za ta yi mini"
Sannu a hankali Nana ta juyo, idonsa na kan wayar hannunsa.
Yanzu ta tabattar da mafarki ta yi ba, Sayyid ta gani, sai dai ganinsa bai razana ta ya kiWimata ba, kamar yadda alamu suka nuna Asal matarsa ce ba.
Ta sunkuyar da kanta ?asa, tana jan ?afafuwanta a hankali.

"Me ya same ki ne?"

Ta girgiza kai alamar ba komai.

"Ki yi mini magana kina girgiza kai kawai"

"Ba ni da lafiya"

Asal ta ja tsaki ta ce "Je ki kar ki Sata mini rai"

Ta zuba masa shayin a kofi, ta zuba masa madara, ya Wauka a hankali ya kai bakinsa yana sha.

Nana kuwa a Wakinta, gaba Waya ta burkice, tamkar za ta yi hauka ta ce "Dama abin da ka ke gargaWina a kai kenan ?aisar? Sayyid me yasa za ka yi mini haka, dama ka na da wata matar ka aure ni? Yanzu ka na nufin ka manta ni, Sayyid anya al?awari ya ce haka? Na ha?ura zan Wauki Wa na na koma gida, ganinka da wata kawai ya isa ya yi ajalina. Wata?ila alhakin iyayena ne ma da na taho ba da izininsu ba. Yadda ka ke a cikin daular nan, yaya za a yi na ce ina da ala?a da kai ma a yarda da ni?" Ka ce Ruhina da naka su na rayuwa a tare, kowannenmu yana Wauke da ruhin Wan uwansa, ni na yi dakon soyayyarka ashe ka na da matar da ta fi ni komai" Ta yi maganar cikin matsanancin kuka tamkar za ta fita daga hayyacinta.

Yana tsaye yana jin yadda ruwan yake ratsa shi daga cikin gashin kansa zuwa jikinsa.
Wani irin zafi yake ji a cikin ?wa?walwarsa, tamkar kansa zai tarwatse.
Karo biyu yana jin jikinsa ya yi girgiza.
Ya yi wankan ya lulluSo jikinsa da towel.
Asal ta sha kwalliya cikin ba?a?en kaya na bacci.
Ta nufo shi tana rangwaWa, ta cire towel Win da ya lulluSa da shi. Ya Wan lumshe idanunsa saboda ?amshin turaren da Asal take yi mai jan hankali.
Ta shige jikinsa ta rungume shi, ta ce "Na yi kewarka sosai Imam"
"Nima ina jin kewar abin da ban san mene ba, bayan kewarki da na yi"

"Akwai abin da ya fi ni muhimmanci dama, da har ka ke kewarsa fiye da ni?"

"A'a ban ma san mene ba, kawai dai ina jin akwai wani abu da ba daidai ba"

Ya yi maganar yana shafa gefen wuyanta, yana son tambayarta wace ce yarinyar nan, amma ya haWiye ya fasa.
Ya fara ?o?arin sumbatar ta, sai dai ya ja da baya da sauri yana dafe kansa, da yake jin wani sauti mara daWin ji a cikin sa.

"Imam jikin ne dai?"

Bai yi magana ba, ya hau kan gadon ya kwanta ya lumshe idanunsa.

Washegari da safe, idanun Nana sun kumbura suntum, saboda ba ta rintsa ba ko kaWan.
Ta saba da wuri take tashi, ta fara gudanar da aikinta, amma sai da aka zo aka kira ta, ta ce ba za ta yi aikin ba.

Bayan mintuna talatin sai ga Asal a Wakin, ta kalli Nana a wula?ance cikin isa da gadara ta ce "Ki ka ce ba za ki yi aiki ba yau? Saboda gidanki ne ko zaman kan ki ki ke yi a gidan? An kai wa Imam shayi ya ?i sha ya ce ba irin na jiya ba ne"

"Eh ba zan yi girki ba, kuma barin gidan nan zan yi, na gaji da wannan aikin, zan je na ga yarona"

Asal ta yi dariya ta ce "Ai kuma ?arya ki ke yi. Na Waukko ki gidan nan saboda nesanta mijin da waWanann munafukan hadiman, na kawo bare da baki san komai a kan harkar gidan mulki ba. Kuma ba kya cikin kalar matan da za su iya Waukar hankalinsa. Dan haka na kawo ki ne dan ki din ga kula da abin da Imam zai ci aikin da ki ka zo yi gidan nan kenan.
Nana ta yi wa Asal wani irin kallo mai cike da tsana, ji take tamkar ta kama Asal ta yi ta jibgarta har sai ta ji ta huce.

"Gimbiya Asal, ai an bar kari tun ran tubani. Ba zan yi girki ba sai dai yunwa ta kashe Imam Win, ke da yake aure idan ba za ki girka masa ba, to kar Allah ya sa ci, sai na bar gidan nan ba zan zauna ba" Ta yi maganar cikin Waga murya da zazzaro ido.

Asal ta yi taku biyu, ta hankaWa Nana baya ta ce "Ki kiyaye harshenki a kan abin da zai din ga fitowa daga bakinki, a kan mijina. Biyan bu?atata ce kawai ta sanya nake ?yale ki, ki daina ?o?arin ?etare iyaka. Tafiya kuma ga hanya nan maza ki tafi mu gani, idan kina tunanin da ka na kawo ki gidan nan na ajiye"

Ayshercool
08081012143
Littafin kuWi ne, 1k ne via 0069685771
Aisha Adam stanbic bank ku tura mini hakkina kan ku karanta.
72


Sai da Nene ta tabattar Nana ta Wan nutsu, sannan suka kwanta.

Washegari Nene ta fita, ta bar Nana a gidan tare da Muhsin. Bayan ta dawo daga gurin sama'arta ta cewa Nana, yakamata ta je ta Wan sai abubuwan da za ta bu?ata saboda tafiyar da za ta yi da nisa, kuma ba su san yaya tsarin aikin can Win yake ba.
Nana ta ce "Ni babu abin da nake bu?ata, ki bani wani abin na ri?e a hannuna, sauran kuWin kuma ki ri?e saboda kula da Muhsin na s...

"Biyana za ki yi kenan dan na ri?e miki Muhsin?" Nene ta katse ta.

"Allah ya baki ha?uri, ba haka nake nufi na, na ga dole Wan abubuwan bu?atunsa duk ke ki ke yi masa Nene, tun da ga kuWi sun"

"KuWinki ba su isa su saka na ri?e miki Wa ba ko?"

Nana ta ce "Na sani, ai shi ya sanya na ce ki yi ha?uri.

Nene ta ce "Ba zan yi ha?urin ba sai na gama, kin iya kunna ni da na fara faWa ki hau bani ha?uri, wato in ci kaina to sai na idar"
Nana ta yi mata shiru ta yi faWanta ta gama.
Washegari Nene ta saka Nana a gaba suka je kasuwa, ta sata ta yi sayayyar kayan sakawa da na Wan shafe-shafe, ta yi wa Muhsin sayayyar kayan sakawa da pampers. Babu yadda ba ta yi da Nene ba ta Wauki wani abin ta ce ba za ta Wauka na.
Nana ta haWe rai ta ce "Eh dama ba ki Wauke ni 'yarki ba, shi ya sanya duk abin da zan yi miki ba kya karSa"

"Ni za ki yi wa wayo, na ji ban Wauke ki 'yar ba, ni ga Wana nan" tayi maganar tana shafo Muhsin da ke bayanta. Da ?yar sai da suka kai ruwan rana Sannan Nene ta karSi abin da Nana ta saya mata.
Sai dai kan su bar kasuwar har sun shirya. Nana ta ce "Nene kin ce mini ki na da Wa, amma ban taSa ganinsa ya zo ba, ba ya zuwa ya gan ki ne?"

Nene ta ce "Kamar ban damu da shi ba ko?"

"A'a kawai dai tambaya na yi "

"Yana can Nigeria"

"To me yake yi a Nigeria ba ya zuwa inda ki ke?"

"Sana'a yake yi, ai ya zo ki na can gurin aiki"
Duk da Nana ba ta gamsu da amsoshin da Nene ta ba ta ba, amma ta basar ta ce "Allah sarki, Allah bai yi zamu haWu ba".

Haka suka ci gaba da hira suka koma gida, Nana ji take yi tamkar ta Wauke Wanta ta tafi da shi.

Gidansu Ashura Nana ta je, ta samu keke ta WiWWinka kayan da ta sayo, ta sake haWa jakarta ta Wauki muhimman abubuwa a kayanta.
Duk da a Waki Nene take rufe mata su, ba ta taSa ganin alamar Nenen tana yi? bincike a cikin kayan ba.

*****
Ko da Jamila suka dawo Kano, fakar ido ta yi ta jefar da wannan tarkacen da aka ba ta aka ce da su za ta kai jini.
Gaba Waya da ta tuna abin tsigar jikinta take tashi, ta ji ciwon kanta da zazzaSi ya ?aru.
Gefe guda kuma hankalinta yana kan yadda ta ji Hajiya Sa'a tana faWin za ta sake bayar da Wan Alhaji Fatuhu. Ta jinjina rashin imaninta mutumin da yake fama da karayar arziki ga ciwo, ya rasa wancan Wan kuma a sake bayar da wannan kamar ba a yi masa adalci ba. Sai dai gaba Waya ba ta san ta ina za ta fara ba, tana jin a ranta kamar yakamata ta tseratar da yaron.
A gida ta tarar da Gaddafi, ta sha jinin jikinta da irin mugun kallon da ya yi mata, amma bai ce mata uffan ba. Suwaiba ma ?ura mata ido ta yi tana bin ta da kallo.
Ta tsuke fuska ta harsri Suwaiba, sai dai Suwaiba ta tuntsure da dariya, kamar za ta shiWe. Jamila ta yi tsaki ta shige Wakinsu.
Ba ta tarar da Mama a gida ba, haka ma Baba.

*****

Shiru Alhaji Zailani ya yi yana kallon Doctor Sharif yana sauraren shi, har ya gama karanta masa abin da Shukura ta je ta same shi ta yi masa.
Ya ja numfashi ya ce "Shikenan, aikinka ya yi kyau Sharif, na kuma gode sosai da sosai da ka ke sanar da ni wannan abubuwan, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Ka je za ka ga sa?o" Sharif ya yin?ura ya tashi ya tafi.

Alhaji Zailani ya numfasa a fili ya ce "Duk da kasancewar ki 'ya mafi soyuwa a cikin zuciyata, an zo gaSar da ki ka ?etare layin da bai kamata ki ?etare ba, kina ?o?arin tono abin da zai wargaza zaman lafiya da kwanciyar hankali, dan haka ki yi ha?uri da duk matakin da zan Wauka a kan ki.

*****
Nana ta jingina da jikin gilashin motar, tana kallon tulin yashin saharar da ya mamaye gurin. Fili fetal hagu da dama duk yashi ne. Cikin yanayi mai kama da bacci take ganin abubuwan da ta din ga gani a bacci cikin saharar.
Ko a yanzun ma su na tafe Sayyid kawai take gani a kan ra?umi yana biye da su a cikin saharar.
Kamar an taSa ta ta Wan yi firgigit ta kalli gurin, haryanzu a titin da ya ratsa saharar suke tafiya, zuciyarta ta yi wani irin bugu da sai da ta dafe ?irjinta.
Sanyi ta fara yana ratsa ta har cikin ?ashinta, ta Waga ido tana Wan waige-waige ta ga ta ina za ta gano ?aisar ko wata ba?uwar halittar da ba jinsin mutane ba, sai dai ba ta ga komai ba.
Ta sake jingina da jikin motar tana ta karanto duk addu'ar da ta zo bakinta. A haka har suka shigo cikin gari sosai da sosai.
Nana na son karanta Symbols Win da take gani, amma ba komai take iya fahimta ba saboda rubutun French. Babbar hanya mai Wauke da ?aton gate ta ciki suka wuce.
Ba ?aramar gajiya Nana ta yi ba, saboda azabar nisan tafiyar da suka shawo ba, ba su ?arasa ba sai bayan magariba. Kewar Wan ta ta addabi zuciyarta, tunaninta yadda za ta din ga sintirin tsakanin Agadez da MaraWi a wannan uwar tafiyar kamar ta ya da shege.

Wasu irin gidaje ne manya-manya na alfarma da ?asaita a cikin gurin.
A ?ofar wani gida direban ya tsaya, ya cewa Nana ta fito sun zo. Haka ta saukko ?afafuwanta duk sun yi tsami saboda azabar gajiya.
Ya buWe bayan motar ya Waukko ?atuwar jakar Nana, ya rufe motar, ya yi gaba Nana ta bi shi a baya tana karanto addu'oin da suka sauwwa?a.
Cikin wani matsakaicin gida suka shiga, gidan ya ?awatu ya yi kyau sosai da sosai.
A falon gidan ya ajiye wa Nana kayanta ya ce "Ki zauna ki jira a nan"

Nana ta ce "Amma wa zan jira a nan Win, ban ga alamar akwai mutane a gidan nan ba"

"Za ki gan su, ni a nan aka yi mini umarnin na kawo ki kawai"

Nana ta yi shiru tana nazari, shi kuma ya juya ya fice.
Nana ta din ga rarraba ido, tana son ta yi salla amma babu wanda za ta tambaya. Harabar gidan ta fita saboda ta ga famfo ta yi alwala, ta dawo falon ta yi salla.
Gajiya ta yi ta koma harabar gidan da kayanta, ta zauna tana rarraba ido.
Can ta ji ?arar mota, aka buWe ?ofar wani jami'in tsaro ya shigo ya buWe gate Win, aka shigo da wata haWaWWiyar mota aka yi parking Win ta.
Aka buWe ?ofar motar, sai ga Asal ta fito sanye cikin doguwar riga, ta Waura mayafin a wuyanta, kanta babu Wankwali. Har bakin ?ofar shiga suka rakata, ta wuce Nana ta shige ciki kamar ba ta gan ta ba. Nanan ma ta yi zamanta ba ta shiga ba, ta jingina da jikin kayanta taka addu'a saboda a gajiye take matu?a, ga uwar yunwa tana ji ga tulin damuwa.
Sannu a hankali take tuna yadda ta shigo ?asar Nijar ba ta san kowa ba, da yadda ta din ga raragefe har zuwa kan zamanta da Nene. Sai ta tsinci kanta da tattara su baki Waya tana yi musu addu'a, da fatan dacewa a Duniya da lahira.
Ba ta san iya adadin lokacin da ta Wauka a gurin ba, ta ji muryar Asal a kanta.
"Wai ke wace irin bagidajiya ce, a Nigeria daga wani ?auyen ki ke ne?" Nana ta Waga kai ta kalle ta.

"Na saka an kawo ki guri, ki shiga ki jira ni kin zauna a waje, na dawo ma kin nemi guri kin zauna ba za ki shigo ba?"

"Ta yaya zan shiga gurin da babu kowa na zauna, ni da ban san ma aikin da ki ka kawo ni na yi miki ba?"

Haushi ya kama Asal, ta ce "To idan kin ga dama ki shigo, idan kuma ba ki ga dama ba, ki yi ta zama a gurin" Ta shige ciki Nana ta bi ta da harara, kamar ba za ta tashi ba, sai kuma ta tashi ta ja kayanta, ta shiga falon ta nemi guri ta zauna a kan kujera. Asal ta saci kallon Nana, da yadda take gudanar da lamarinta cike da ?arfin hali.

Nana ba ta kula ta ba, ita ma ba ta kula ta ba, Nana ta gaji da zama, ta saukko ?asa ta mi?e ta kwanta.
Can Asal ta ce mata "Ga kitchen can, akwai abinci"
Daga haka ta tashi ta bar falon.
Nana ta tashi ta shiga kitchen Win, ta tarar da Abinci, ta Wauka ta ci sannan ta Wan dawo hayyacinta.
A nan falon Nana ta kwana, da Asuba ta yi alwala a harabar gidan, ta koma falon ta yi salla.
Duk wannan abin zuciyarta a cike da zullumin aikin da za ta yi wa Asal.
Da gari ya yi haske, Asal ta fito Nana ta gaishe ta, amma ta yi kamar ba ta ji ba, ta fice ta bar gidan ta bar Nana.
Nana tana nan zaune, aka zo aka ?wan?wasa ?ofar falon, ta tashi a Wan tsorace ta buWe, wani mutum ya mi?o mata takeaway ya ce "Ga shi nan, aka ce a kawo miki" daga haka ya juya ya tafi.
Nana ba ta sake ganin Asal ba sai dare, ba ta saurari Nana ba still. Ta cika gidan ita da ?awayenta, suka hau saman bene, suka kunna kaWe-kaWe har kusan Waya na dare su na abu Waya, suka hana Nana bacci.
Sai gefin Asuba suka daina wannan shirirtar, Nana ta din ga mamakin ita Asal zaman kanta take yi ne, ba ta da magabata ko kuwa?
Sai washegari sannan ta saukko ?asa, a lokacin ?awayen nata duk sun tafi.
Ta kalli Nana ta ce "Daga yau kar ki ?ara kwanar mini a falo, ga Waki can kusa da kitchen, a nan za ki din ga kwana. Na kawo ki ne duk da ba yanzu ne za ki yi aikin naki gaba Waya ba, amma za ki din ga yi mini

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login