Showing 54001 words to 57000 words out of 94923 words

Chapter 19 - WA ZAI FURTA complete

04 Sep 2026

22

kwada Mata Kira.....

Bilkisu.... Ta waiga da sauri saboda yanayin yanda ya daga murya duk ya janyo hankalin wadanda Basu Kai ga fita ba.

Zo ki zauna anan ya nuna Mata kujerar dake gefensa ..

... Kowa ya tsareta da ido Yana jiran response dinta,

Me Zan maka? Ta fada tare da tsuke fuska.

Kawo mun note dinki zanyi using ...... Bai rufe baki ba ta jefa mishi littafin har ya daki fuskar sa, gashi nan idan ka gama gobe Zan karba Ina sauri ta yi h

anyar waje.....da gudu ya fito har ya ba wasu tsoro.

Ita kanta sai da gabanta ya Fadi lokacin da ta wurga mishi book din saboda tasan cewa ta debo ma kanta wutar dafa kanta.

Ta yi sauri ta tsaya tare da rike kugu....... Ni Kika jefa?

Ya fada Yana za

ro ido.

Ta mishi kallon up and down kafin tace idan kaji haushi ka maido mun littafi na Mana.... Jeki dauka bana so ya fada Rai bace .

Fine , ta fada tare da wuce Shi ta koma class din.

Duk aka kawar da fuska ganin ya biyo bayanta, samm bata lura ba Bat

a Kuma ji takunsa ba.

Littafin ya fada can karkashin desk ta kutsa can ciki ta Kuma duka tana kokarin dauko Shi, ya shigo sit din ya zauna, ita kuma tana ciki.

Dagowar da zatayi taji ta fada bisa kafar mutum ta mike da sauri innalillahi.... Wai kanka

daya Anwar??? Ta daka mishi tsawa.

Idan baki so na Miki abinda Kika tsana ki zauna silently muyi magana wallahi idan Kika kuskura anan zan Miki abinda...... Bazan zauna ba bani wuri in wuce.

Naki na bayar ko Zaki daukeni da tsiya ki fitar? Me yasa kike d

a gardama Bilkisu???

Kai Kuma me yasa baka da zuciya?.

Yayi murmushi nima Ina neman amsar nan wallahi..... Ta ja tsoki kanka akeji bani wuri.

Ya kalleta alamar ba wasa yayi baya da hular sa , kin san Allah idan Baki zauna ba Zan daura ki a bisa cinyata

ki zauna in kuma rikeki har sai na gama maganar da zanyi ko bazan iya ba?

Tayi shiruuuuu, sai Kuma ta zauna saboda tasan karamin aikin sa ne sai dai idan ya aiwatar daga baya ya bada hakuri.

Ya bita da ido Yana murmushi..... Ta Kara tsuke fuska Ina sa

uraron ka ba ka tsareni da ido ba......

Me yasa Kika tafi Kika barni jiya?

Saboda ka gane baka gabana bana son wannan shisshigin, Kuma na Kara fahimtar fakai bana son kana taba ni na tsani hakan .

Kin tabbatar bana gabanki?

Ta kalleshi shekeke Zan ma k

arya ne don Ina tsoronka ko kana nufin...... Ina nufin mufeeda ce ta Kara Bata Miki Rai ko?

Mufeeda? Mtseww a'a ka manta.

Idan ba ita bace me yasa Kika hasala sosai Kika tafi Kika barni?

Saboda ka rike ni na kuma fada maka bana so..... Me yasa ke bazaki

daina abinda nima bana so ba?

Ajiyeni kayi? Ko kana iko dani da zaka Sanya mun doka kace kuma dole sai na bi?

Kiyi hakuri, ya fada a hankali.

Tayi sokoko ta kasa ci gaba da masifar.

Ya tsareta da ido, Dan Allah kiyi hakuri naji nayi kuskure baz

an Kara ba I'm sorry please.

Tayi shiru,

Bana son fadan nan wallahi, bana son kina wannan tada jijiyoyin kina fushi dani bana so ko kadan please kiyi hakuri shikenan ko?.... Ba shikenan ba, sai ka mun alkawarin bazaka Kuma taba ni ba sannan.

Yayi sh

iruuuu, gaskiya ban yi alkawari ba amma Zan kiyaye.

Ya wuce ko?

Eh, ta fada a hankali.

Mun shirya?

Ta dan harareshi.

Yayi Yar dariya. Mun shirya ko?

Um, ta ce tana murmushi.

Hmmm, Bilkisu kenan kina yarda Kika ga dama.

Karfe nawa Zaki kawon tuwo

?

5, ta ce .

Lokacin na gama mutuwa da yunwa ko?

Ba abinci dare zakaci ba?

Waya fada Miki?

Shi zanci a matsayin lunch..... Tuwon???

Yayi Yar dariya yes!

Hmmm,

Zaki kawon irin two din nan?

I'll try. Ta fada a hankali.

Waye Zaki Aiko ko nine Zan t

uro?

Zan kiraka idan na gama dai.

Ya Mike tashi muje.

Ga book din ta Mika mishi .

Yayi Yar dariya daman ke nake bukata ba Shi ba...... Ta zaro ido what?

Ya Kara yin dariya ya ce Ina nufin ke nake so kizo inyi magana dake ba littafin ne a gaba na ba.

Tace hmmmm.

Suka jera suna tafiya..... Tana tsallaka titi sadeeq ya karaso suka wuce.

Ta zagaya can baya wurin Mai nama ta siyo tsoka Mai kyau ta Shani kilo daya.

Tana shiga ta cire hijab ta Fara hada Miya...( Duk kudi irin nasu Bilkisu baisa anyi sak

e da koya Mata girki ba ) har catering school tayi ga karance karance da tambaye tambaye saboda girki na daya daga cikin abinda take so a rayuwarta.

Ta shirya miyar kuka Mai Rai da lafiya, naman yayi ruguf a ciki wurin Aisha ta Samo kukar da daudawa sab

oda bata dasu Kuma Bata Kai ga ta siya ba, anan daman take siye.

Duk wacce taji kamshin sai ta leko. Tana gamawa ta daura tuwon bai wani dauki lokaci ba, karfe daya da kwata ta kullashi a leda, ta janyo sabbin coolers manya cikin kwali Wanda batayi amfa

ni dasu ba daya kawai take amfani da ita karamar tana zuba Miya.

Ta jera tuwon guda Sha biyar aciki.

Ta zuba Miya ga Mai bi Mata duk naman ta kwashe musu kaf! Ta bi da manshanu saboda bata rabo dashi ita ma'abociyar taliyar hausa ce dahuwar daudawa Tasha

manshanu.

Ta kwalala mishi ta rufe.

Ta jera a basket ta Sanya mishi gwangwanin biscuit biyu cikin wadanda ya siya Mata da lemuka kala kala, ta dauki basket din da 200 ta fita.

Napep ta tsaida tare da mishi kwatancen hostel..... Zan kirashi ya fito sa

i ya karba sunan sa Anwar..... Anwar? Ya zaro ido... Anwar din zai fito ya karba? Ta banka mishi harara ka San sa ne?

Ni kuwa na sanshi an bani abinci na Kai mishi kwanaki nafi awa banga kowa ba na Kira abokin sa da aka bani number sa Koda yaji zancen naw

a ya kashe waya bai Kara..... Malam zaka Kai mun sakon Nan ko na nemi wani?

Zan Kai Hajiya Amma idan bai karba ba Ina Zan ganki saboda wadancan kayan har Yanzu suna gidan mu...... Kaga compound gashi can??? Ka ce Bilkisu kake nema ta ajiye mishi basket di

n ta bashi 200 ta juya kawai.... Ya kalleta a yamutse wahalallu.....

Ta kanga waya a kunne tana Kiran sa..... Barci yakeyi kasa rika Kuma yanajin dadin barcin.

A hankali wakar *Because you love me* ta Fara tashi ta cylindion.

Yayi firgigi saboda Bilk

isu kadai keda ring tone din.....

Hello ya fada cikin muryar barci.

Ina hanya Zan kawo maka tuwon na kusa karasowa na sameka bakin gate din ku kada ka barni Ina jira......ta kashe wayar.

Idanun sa suka bude tangaran ya bi fuskar wayar da kallo..... Ya

Mike zumbur ya zura jallabiya ya fice da silifas kafarsa.

Dai dai tsayuwar Mai napep din Yana hango napep yanufe ta da sauri Yana lekawa..... Kai ne Anwar?

Sai kawai yayi murmushi watau yarinyar nan dabara tayi mishi don ya fito?

Ya kalleshi eh, tare

da Mika hannu ya karbi basket din.

Yasa hannu aljihun jallabiya ya fiddo 500 ya Mika mishi.... Ta biya yallabai.

Yayi Yar dariya to in mayar kenan baxaka Kara ba tunda na fiddo?..... Yayi charaf ya karbe Yana fadin wazai mayar da alheri?.

Na gode yaba

napep wuta Shi Kuma ya nufi hostel Yana murmushi.

Ya bishi da kallo Yana jinjina Kai. Yanda suke fama da student wurin neman ragi da amsar chanji amma ga wani na kyautar 500, ita Kuma ta biya 200 zuwa kawai..... Wurin Nan akwai magana ya ce kafin ya chil

la keken titi.

Sadeeq nata barci bai motsa ba. Yasa kafa ya Kai mishi harbi.... Tashi Dan ubanka Bilkisu ta Mana girki..... Zumbur ya Mike Yana kallon basket din.... Yayi dariya wallahi tuwon ne ta kawo .



Yunwa sukeji Daman, sadeeq ya Fara kwashe l

emukan Yana ajiyewa kasa, sannan ya fiddo coolers din, kamshin manshanu ya buge dakin Anwar ya hadiye wani tsinkakken miyau ya gyara Zama .

Baiwar Allah hada biscuit ta debo da lemuka...... Tana so ta rage su ne sun Mata yasa Anwar ya katse Shi Yana mu

rmushi.

Sun kwashi tuwon sosai musamman Anwar kulli hudu suka Bari.

Amma fa yarinyar ta iya girki in har itace tayi.... Ita tayi nasan bazata ba kowa yamun ba ya janyo waya .

Hello ta fada tana Yar dariya..... Ni Kika mayar gaki nan zuwa ko?

Ta kyal

kyace da dariya.... Tuwon nan yayi dadi fa ga Sadeeq nan Yana lasar kwano.... Shi na Bari Yana lashewa karya yakeyi ya fada da karfi.

Ta tuntsure da dariya..... Na gode sai na maido kwanonin Allah ya biya thank you so much Bilkisu Mai gadon zinari...

Ya

fada Yana dariya.

Ta ce hmmm.

You and this your hmmm. Bye wanna baf. Ya kashe wayar.

Haka kawai taji ranar ta Mata dadi tana nishadi. Wunin ranar wani nishadi takeji.

Akan hanyarsu ta dawowa daga masallaci isha'i take ba Aisha labarin wayar da sukay

i cewar yaci tuwon.

Kamar daga sama suka ga mutane gewaye dasu hada maza..... Gabansu ya Fadi suka tsarata ainun Aisha tayi karfin hali tace lafiya?

Mufeeda suka gani ta fado gabansu tana taunar chingam.

Ta kalli Bilkisu ke karamar Yar iska ce wallahi

.... Ni zakiyi ma karuwanci?

Akan Anwar har kisan Kai Ina iyayi na rantse da Allah ta daga hannu zata kwada Mata Mari akayi charaf da hannun aka rike Shi ta baya.... Kowa yabi hannun da kallo zuwa inda aka Kama don suga waye?

Anwar ne yasha boyel fari ka

nsa da hula kube ya murzata irin sa hular kanawa sai kamshi ke tashi, hannunsa dayan rike da basket........

✍

🏼

*ZAINAB DAHIRU WOWO DUTSINMA*

πŸ’–

*KAUNAR KI AZIMUN CE Ina yinki over RUKAYYA BAKO DANBATTA* *ZAINAB WOWO NA JIN JINA MIKI ALALH YA SHIRYA ZU

RI'A AMIN*

A ringa mun uzuri, Ina zuwa aiki, Ina da miji Ina da Yara kafin na Fara rubutun na fada I won't be able to post all the time na Fadi haka saboda Ina da hidindimu.

Alawiyya ciwon ciki

πŸ—£πŸ—£πŸ—£πŸ—£πŸ™„πŸ™„

🀐

*WA ZAI FURTA?*

🀐

1

⃣

8

⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray

*

πŸ‘‰πŸΌπŸ’žπŸ’•πŸ’•

*RUKAYYA BAKO DAN BATTA i love you so much, remember this always*

πŸ₯°

😍😘

.

***************

*Federal University dutsinma*

```Ya juya hannun da karfi, wallahi duk ranar da wannan hannun ya yi gigin taba Bilkisu sai na karya shi, n

ima akanta Zan iya kisa```......... Ya wurgar da hannun. Sannan ya kalli wadanda ke tsaye *What the hell are you doing here?* Ya daka musu tsawa...... Suka Fara darewa, mufeeda ta juya zata tafi ya fizgota..... ``` Bata hakuri```....... Tayi saurin kallon

sa, Jin haka yasa kawayenta Suma suka Fara yin baya,

Bakiji abinda na fada ba?

```ki Bata hakuri ko Kuma wallahi....```

Ta fizge hannunta, bazan bayar ba..... Ta wuce da sauri kamar zata tashi sama.....

Aisha ta rike hannun Bilkisu tamau.

Ita kuwa kan

ta a kasa kawai tayi shiru......

Ya kalli Aisha, me ya hada su ne?

Me kuwa zai hada su inba kaiba??? Ita har Yanzu tana zargin akwai wani abu tsakanin ka da Bilkisu shine fa suka tare mu Yanzu mun dawo sallah..... Mtseww ya doka tsoki.

Ya Mika ma Aisha

basket ungo je Mata dashi ciki..... Ta juya kawai zata tafi ya yi saurin fizgota ta fada jikinsa kanta ya daki kirjinshi........ Yaushe Zaki fahimci da gaske bana so ki ringa tafiya idan nazo wurinki ko muna tare?

Ya hakuri sakeni please..... Ya Kara mann

eta jikinsa..... Aisha jeki tana zuwa.

Ta wuce tana dariya da mamakin wannan rigimammiyar soyayya.

Wai Anwar Kan ka qalau? Na shiga uku ni Bilkisu ka dubi Allah ka sakeni..... Yana rungume da ita ya Fara tafiya a hankali ..... Na shiga uku Anwar..... Ya

sunkuyo Yana kokarin hada fuskar sa da tata tayi saurin sunnewa jikinsa tana Kara fadin na shiga uku ni Bilkisu..... Ya manna bayan ta da Bango sannan ya matsa baya kadan ya rabu da jikin ta yasa hannuwa biyu ya tokare bango tare da Dan sunkuyawa fuskar sa

daidai tata suna shakar numfashin juna ya kafa Mata idanu.......

Innalillahi Anwar Wai meye haka? Ta fada tana faman yin kasa da Kai.......Haka zamuyi firar tunda ita Kika zaba..... Na zabi meye? Ka gyara Mana dan Allah ka matsa..... Allah ba inda zanje,

ba dai taurin Kai gareki ba? Wallahi zanci gaba da binki yanda kike so, ke me yasa baki da tausayi?...... Tausayin me Wai? Ta fada tana kallonsa kamar zatayi kuka.

Gashi yauma saboda mufeeda zaki Kara guduwa kibar ni anan Kuma kin san zuwan naki ne......

. Nayi Alkawarin Zan tsaya I'll give you the time you...... Never mind, I'm okay like this.....Anwar am not okay please shift back na tuba kayi hakuri Dan ...... Ke nafiki wuyar lallashi fa ki natsu muyi magana nafi Jin dadin hakan ma..... Tayi kwal kwal,

ya kamata..... Na rantse da Allah kina mun kuka Zan mayar dake Nan... Ya nuna kirjin sa.

Ta hadiye kwallan ba shiri , kayi hakuri Anwar bazan Kara ba I promised.

Yayi murmushi naji but next time.

Kina da sauran tuwon nan?

Babu.

Yayi Yar dariya Yana ka

llon Dan karamin bakin ta da take ta faman turowa.

Duk kin cinye?, Amma fa yayi dadi. Zuwa nayi godiya waccen useless din ta Bata mun plan.... Ba komai nidai jeka sai da safe.

Ya kyalkyace da dariya kina korata ne?.

Ya Mike ya tsaya daidai ta saki wata

ajiyar zuciya Mai karfi ya bita da ido Yana murmushi...... Matsoraciya kina motsawa Zan.... Ba inda zanje ta fada tare da makurewa jikin bango.

Kiyi hakuri ya fada a hankali, wallahi Nima fa bana son Ina taba ki Bilkisu ki daina mun gardama kinji?

To, ta

fada a kagare.

Sadeeq ma yaji dadin tuwon nan. Ina Kika Sami manshanu?

Ina dashi. Ta fada a hankali. Duk jikinta yayi sanyi....ya Kara tsareta da ido sai ta bashi tausayi.

Bilkisu.....ya kirata a hankali.

Taji wani Yarrrr, tsikar jikinta duk ta tashi,

ta kasa amsawa.

Ya Kara cewa Bilkisu......

Na'am ta fada tana murza yatsunta.

Dan Allah kiyi hakuri kinji ko?

Ba komi ta ce a hankali.

Da komai. Gashi naga duk kinyi relax, please I'm sorry.

Ba Kya so Ina taba ki ko?

Ta daga Kai alamar eh, yayi mur

mushi to duk laifin da nayi Miki idan muna magana ko Ina a wajen don't leave me, kinji ko?

Ta Kara daga Kai .....yayi murmushi Baki magana?

Ta ce hmmm.

Dan Allah ki daina bana so kinji?

To Wai me yasa baka iya kyaleni in tafi?...... Saboda.. sai Kuma y

ayi shiru Yana murmushi.

Saboda me? Ta tsare shi da ido.

Bazaki gane ba, yace Yana Yar dariya.

Zata Kara magana ya yi saurin cewa na saka Miki turaruka a basket din da na maido Allah yasa kamshin suyi miki.

Biyana kayi kenan?

Ya zaro ido na Isa in biy

aki? Allah kadai zai iya biyan ki Bilkisu.

Na zo dasu ne tun daga gida ban dai kawo Miki bane ....... Turaruwanka Zan saka ajikina?

Nope, na Mata ne musamman na siyo Miki.

Hmm, na gode sosai.

Yaushe Zaki Kara mun tuwo?

Sai an kwana biyu kuma .

Gobe m

e Zaki dafa?

Ina ruwanka, Kai fa abinci ne damuwanka ni kuma ba girki nazo yi ba karatu..... Dariya yakeyi har Yana dukewa...... Wannan tsiwar taki na bir.... Sai yayi saurin canza magana yace tana bani dariya.

Ta ce hmmm, ai gara na fada maka na lura K

ai baka san ayi abu Dan marmari ba.

Dan Allah kiyi abinci dani gobe.... Indomie Zan dafa malam..... Zanci indomie din please ki taimaka.

Mtsew taja guntun tsoki.

Amma ki bari Zan Miki waya ten minutes before yanda Ina zuwa kin karasa naci da zafi..... K

aci a Ina? Ka Bari Zan Aiko maka.... Bana cin indomie idan ta shiga wani kwano ba plate ba daga tukunya..... Kiyi hakuri zanzo nan in ci..... Anwar! Ta Kira sunan sa.

Ya kalleta Bilkisu!

Shima ya fadi nata .

Idan na tambayeka zaka bani amsa saboda Allah

?

Ya danyi Yar dariya in shaa Allah.

```me yasa yake son takura mun bayan ga wadanda keson attention dinka kaki basu sai ni da ban nema ba?```

Ya fada murmushin fuskar sa ya zuki iska ya hurar..... Saboda kece best friend Dita. I'm More comfortable wi

th you than any other girl in this school.

Tayi shiruuuuu, ya kalleta ko ba wannan amsar kike son ji ba ya karasa maganar Yana dariya.

Ta galla mishi harara.

Kin San fa a tarihi abincin ki daya na taba ci duk school din Nan apart from sadeeq da ke Mana

girki sometimes da Abdul Mai indomie...

Yanzu kuwa I don't think ko na sadeeq zan Kara ci....... Ta zaro ido sai nawa?

Naki zanci. Gaskiya gara na fada Miki Zaki ringa Mana girki once in a day ko twice idan kina da lokaci...... Amma ka debo dala ba gammo

..... Ya kwashe da dariya.

You

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login