Showing 60001 words to 63000 words out of 94923 words

Chapter 21 - WA ZAI FURTA complete

04 Sep 2026

31

Kam kin bani zuciyar ta saka Miki?

Ta zaro ido... A'a.

To fadan me ta ayyano Miki.?

Cewa tayi eight din is okay..... Yayi Yar dariya are you sure???

Yes. Ta fada tana ci gaba da murmushi.

Shikenan sai nazo. Kin hada kayanki ko?

Sai anjima.

Ya zaro ido kinji labarin Coronan ne?

Eh, m

ommy ta fada mun da mukayi waya.

Yaushe Zaki tafi?

To gani dai.... Ban gane gaki dai ba.

Ka bari idan kazo anjima zamuyi magana.... Shikenan sai nazo.

Ashe yayi waya yace a kawo mishi mota da maganin. Ko da aka kawo sai driver ya juya gata haya yabar

musu motar.

Katuwar mota kirar Jeep Amma Honda baka, Kai da kaga motar kasan lallai Mai ita *Don* ne.

Ta Sami Aisha daki, sai na jiki shiru.

Eh, wallahi Ina parking ne.

To Wai strike din ne ko Corona?

Duka fa, Anwar ya fada Miki?

Mommy, Ina tas

hi naga ta kira nabi Kiran,shine take fada mun, kema gobe Zaki wuce?

In shaa Allah, sai gida....Kare yasha taba. Duk suka bushe da dariya.

Ke sai jibi ko goben zaku wuce?...... Har na ma driver waya gobe in shaa Allah na fada mishi ana gama sallar asubah

zamu bar garin nan six da izinin Allah..... Anwar din fa, ba dashi zaku tafi this Time ba????

Noooo, bama zai sani ba..... Gaskiya bazai ji dadi ba....kada Allah yasa yaji so what?

Ta kura Mata ido, wannan Jan ajin naki fa ya Fara yawa ki zauna idan zar

en ya tsinke zakiyi wa kanki.

Tayi murmushi, sai dai ya tsinke Amma ko Zan rasa Anwar bazan taba binsa kamar rakumi da akala...... Yanzu me Zaki fada mishi? Ko kunyi maganar?

Bamuyi ba, sai anjima ya ce zaizo kawai Zan nuna mishi banyi deciding ba....

Bilkisu....

Aisha please mubar maganar Nan.

Dan Allah idan ya kawo Miki maganin ki dibar mun saboda Hafsa ( kanwarta ) ita ma the same problem with you.

In shaa Allah.....ohhh Wai carton, komai Shi sai yayi hauka..... Ba hauka bane kulawa ce.

Gasu m

ufeeda can time dinsa kawai suke so Amma sun kasa samu..... Haka ne .

Ai shu'umi ne wallahi. Nake ga kamar duk abun Nan Yana Axergurating ne don ya Sami sauki Yan mata.... Yanayi bil hakki da gaskiya.

Ko?

Allah kuwa.

Ta ce hmmm. Kawai.

Suleiman ya kir

ata, da sauri ta daga hello, Suleiman Ina wuni.

Bilkisu ya karfin jiki?

Na zo dazun har Kun fita da Anwar halan asibiti kuka je.

Eh wallahi. Jikin ma Alhamdulillah.

Mashaa Allah, sai Kika ji Kuma hutu ko?

Bari Kai dai.

Wallahi naji haushi da na Kara

jinkirtawa Kinga da ban wahala a banza ba.

Ai kuwa. Ta fada.

Shikenan Allah ya say ya zamo alkhairi garemu duka ya kawo Mana karshen wannan fitina.

Amin ya Allah.

Sai nazo Allah ya Kara lafuya.....ta ce Ai.... Amma tuni ya latse Kiran Sam bai ji cewar

zatayi wata magana ba.

Ta kalli Aisha naji Yana sai yazo kada yazo gobe na tafi ko in Kuma kiransa Kinga babu dadi.

Kyaleshi goben sai ki Kira. Yanzu kada ya zargi wani abu kin San maza..... Eh Kuma fa. Ta fada.

Ta dafa mishi indomie da kifin gwangwa

ni, ta Sanya tarugu da albasa Mai lawashi sai kuwa spices dinta.

Tayi masifar dadi sai kamshi ke tashi..... Kafin ta sauke ya kirata.

Ta dauka hello...

Ina waje. Yana fadin haka ya kashe.

Gabanta ya Fadi,jikinta ya Dan dauki rawa, ( Wai me yasa Yanzu

ko waya sukeyi takejin wannan yanayin? ).

Doguwar Riga ce jikinta blue, tana da duwatsu yayyabe jikinta.

Ta dauko hijab maroon har kasa ta saka, ko kwalliya batayi ba turaren da ya siyo Mata ne ta fesa kawai ta juye indomie a plate ta rufe ta dauki roba

r ruwa da maltina ta fita.

Yana hangota da Kaya ya fito daga motar..... Gabanta ya Fadi. Anwar a irin motar uncle? ( Wani kanin mommy ne Mai masifar kudi ) wurin Shi suka Fara ganin motar Shi bama Nigeria yake zaune ba Soja ne a America.

....... Ya kar

bi plate din Yana Yar dariya, kawo na taimaka Miki.

Ya shiga motar ya zauna wurin Mai tuki ita Kuma tana tsaye ta rike murfin kofar tana son ya karbi ruwan da maltina.

Ya Dan kalleta zagayo Mana ki zauna....um um Nan ma ya Isa.

Ya Kara kafa Mata ido , s

ai Kuma yaki cewa komai ya Mika hannu ya karbi ruwan.

Zaman kujera yayi ya sako kafafunsa waje duka biyun Yan facing dinta. Ta Dan ja baya ,yayi kamar bai lura ba .

Riga round neck navy blue ya saka da jeans dark blue. Kansa yau ba hula, ya kwantar da

gashin sa inda ya bada kusurwa kusurwa ( waves ).

Yayi kyau matuka.

Ya bude plate din sama, kamshi ya daki hancin sa ya Dan lumshe ido waww.... Daga ji zatayi dadi fa.

Tayi murmushi kawai.

Ina folk din ko hannu Zan saka????

Ta Dan bude idanu innalilla

hi...Bari na dauko na manta..... Ta juya da sauri.

Kinga dawo ga wani Nan ...

Ya fada .

Ta dawo ya gyara fuska alamar seriousness yace duba aljihun kujera a baya akwai spoons dauko mun ciki.

Ba gardama ta ce toh.... Ta bude ta shiga lalube takeyi sosai

tun kafar ta na waje har ta shiga motar ciki tana tura hannu kawai taji kofa ta rufe wani Abu yayi Kara Nan da Nan ta gane locking yayi.

Ta dago Kai da sauri sai taga Yana ta cin indomie din a hankali..... Au dama da spoon dinka a aljihu kana son na shig

o motar ne...... Kina baya Ina gaba hakan ai ba matsala bane unless Zaki takura na dawo bayan..... Karka dawo ta fada da sauri.

Motar ta dau sanyi da wani da dadden kamshi..... Kamshin ya Mata dadi Amma hankalin ta duk ba a kwance yake ba.

........ Amma

indomie din nan tamun dadi kin ci?

Eh, ta fada da sauri.

Kice wallahi na ci.... Ba sai na rantse ba.

To idan ma bakici ba nidai na cinye tas!

Ta ce hmm.

Ya bude maltinar ya kafa Kai.... Yana shanyewa ya kalleta kina da fridge ne?

A'a.

Yanaji da sany

i ko siyo mun kikayi?

Ina ruwanka Kai dai kasha maltina.

Ya kyalkyace da dariya. Wallahi ke Bilkisun nan kin iya gwasale mutum..... Ta harareshi kawai.

Ya dafa kujerar say ta baya ya juyo sosai Yana kallonta..... Dan Allah in dawo Nan....a'a wallahi ta

fada da sauri. Yayi murmushi shikenan.

Yanzu yaushe Zamu tafi gida?

Kai da wa?

Da ke!

Tayi murmushi, tare muka zo?

A'a Amma tare zamu koma.

Shikenan mu jira gobe muga abinda Hali ya bada ko?

Ya rungumi kujera okay as you wish...

Ya Miko Mata ballin

magani ungo Kisha ga ragowar can a boot ance kullum daya zakisha har kwana hudu.

Sannan every month da kin Fara expecting Zaki Sha sau biyu a Rana safe da yamma har ki ganshi ...... Ta mishi banza.

Kin fahimta. Eh. Ta ce a kagare.

Ya sumke dariya ganin

tana ta faman kasa da Kai.

.....Wayarta tayi Kara, Suleiman ne. Ta Dan zaro ido a hankali ta daga tare da kangawa a kunne yayi fit! Ya fizge. *Suleiman eco* yaga an Sanya.

Nan da Nan annurin fuskarsa ya bace ya sa handsfree hello kana magana da Anwar.

.... Kawai sai Suleiman din ya latse wayar...... Ya kalleta kutumar uba ni zaima hanging phone???

Ta mishi banza.

Ya daka Mata tsawa meke tsakanin ki da Dan iskan yaron nan?

Akan me zaka Kira Shi Dan iska???

Ya zaro ido.

What?

Ai kaji abinda nace.

Kai ya Kira? Akan meye zaka dauki wayar da ba taka...... Ya wurga Mata wayar ta daki kirjin ta yace get out of my car.....

Ta dago da sauri ta kalleshi ... Ke kurma ce? I said get out ya Kara daka Mata tsawa......

✍

🏼

✍

🏼

✍

🏼

✍

🏼

Ayi hakuri da kadan yau ba

n zauna ba wlh

*Zainab wowo ce*

πŸ’–

*ALAWIYYA NASIR MY FAVORITE THANK YOU SO MUCH TAWAJENA*

πŸ₯°

🀐

*WA ZAI FURTA?*

🀐

2

⃣

0

⃣

*Gargadi* Bana son ana rubuta mun komai a page din dana tura. Naga 1

⃣

9

⃣

wat t rubuta *Anzo wurin* bana so. Duk

wacce ta Kara taba mun page daga ranar *Wallahi wazai furta ya Kare*

Labarin Nan saboda soyayyar makarantar ne nake rubuta tashi na fada don ku nakeyi to a daure a karbi iya abinda aka gani.

Sannan masu cewa na Sanya sunan su a page ku sani cewa wall

ahi idan dambu yayi yawa bayajin Mai. Duk yanda kuke Sona wallahi nafiku. Akan KU nakan hana kaina abubuwa da yawa don kada na Bata muku. Dan Allah a bani uzuri. Ina kaunar duk Wanda ke Sona ko wanene wallahi bana Raina masoya.

πŸ’–πŸ’žπŸ’•πŸ˜˜πŸ˜

πŸ₯°

πŸ’—

Tsoron Coro

na yasa har yau na kasa lekawa RIGASA KADUNA

πŸ€ͺ



*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... belov

ed sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

πŸ‘‰πŸΌπŸ’žπŸ’•πŸ’•

*RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*

πŸ₯°

😍😘

.

****************

*Federal University dutsinma*

........Ta rude ta kidime Ni kake Kora..... Ya bude mo

ta da karfi ya fita ya zagayo ya bude kofar bayan....get out I said are you dumb?

Kwalla suka zubo Mata sharrrr...... Ta sauko a hankali. Suleiman na gefe yaga ta fito.

Ya koma gefe ya tsaya, tana fita ya maida kofar da karfi gammmm. Ta kalleshi d

a sauri, ya banka mata harara am I safe now??? Idanun sa sunyi jawur duk sun kawo ruwan masifa.

Ta kawar da Kai ta nufi wurin driver ya finciko ta da karfi kada ki shigar mun mota...... Zan dauki plate ne ta fada kwallah naci gaba da shatatowa.....ya i

ngijeta ya kwaso plates din watso kasa....ya kalleta Yana zare ido you can go now!!!!!!........ Anwar duk akan Suleiman....... Ya doka tsoki ya juya zai fada mota, wata zuciya ta debeta Bata San lokacin da ta fizgo rigarsa ba ya dawo da karfi...... Kai har

ka iya kamun irin wannan wulakancin in kyaleka??........ Ya zaro ido. Suleiman dake kallon su shima fiddo nashi....... Ya daskare ya sankame tare da tsareta da jajayen idanun sa.....Wai me yasa yarinyar nan bata tsoro na.????

......... Kwallah kwance cik

in idanun ta, ta turashi da karfi bayanta ya daki murfin mota tayi kansa kamar zata matseshi duk ta fita hayyacinta......... Na rokeka kazo Nan????

Ya yunkura zai dawo ta mayar dashi da karfi wasu zasu wuce suka Dan tsaya kamar zasu fahimci wani Abu, haka

n yasa Shi kasa biye Mata kada su Tara jama'a........ Na ce kiranka nayi kazo??????

Matsa Bilkisu in wuce..... Ta galla mishi harara sannan ta juya kadan ta kalli inda ya watsar plates din ta ce ```dauko su day hanmunka``` ...... Ya kalleta da sauri.....

Wallahi tallahi ka dauko su ka Miko mun da hannunka ko Kuma nida Kai har abada mun rabu daga Nan...... Gabansa ya Fadi... Ya Kara kallonta.

Ta matsa nesa dashi ta tsaya tare da rungume hannuwa..... Kaka kara Kaka...ya yi shiruuuu..... Ban tilasta maka b

a, kana iya shiga mota ka tafi, wacce ka koreni cikinta kana ikirarin *motar ka*........ Ya runtse ido, taci gaba da cewa Amma ka sani na fita motarka salin alin wallahi Alan plates din nan Zan rabu dakai rabuwa ta har abada........ Ya Kara runtse ido tama

u.

In ba rainin wayo ba, Kai har yau baka ganin kowa da mutunci kana iya cin mutuncin kowa baka shakkar......kawai taga ya dauko plates din ya Miko mata. Fuskar sa murtuk....... Ta karba ta juya...... Kizo ki dauki maganin...... Bana so *jikan karuna*..

... Ka hada da maganin da motar ka cinye nafi karfin dukiyarka da wulakancin ka Anwar...... Ya fizgota da karfi, Ni kike gayawa magana????........ Ta fincike an fada maka ta nuna Shi da yatsa wallahi Ka Kuma taba ni Zan sharara maka Mari....... Ya zaro ido

what?????

Ta kalleshi shekeke....kafi karfin hakan ne? To idan kana musu ka jaraba... mtsewww ta buga tsoki ta juya.....ya tari gabanta da sauri....

Wai ke da me kike takama ne? Ya fada da karfi..... Lokacin ne Suleiman ya karaso.

...... Anwar meke fa

ruwa ne...... Ji kakeyi tasssssssss ya ramtse Shi da Mari..... Ya kidime ya gigice..... Bilkisu ta ja baya da sauri tare da daura hannu aka...... Yana dagowa ya daga hannu zai Rama ya Kara wanka mishi biyu double one after another.....sai jini ta hanci...

...... Bilkisu ta kwada ihu zata ruga ya janyota da karfi ta dawo kanta ya daki kirjinta........ Gashi na taba ki , Kuma na Mari wannan Dan iskan sai ki Rama mishi Kuma ki hukuntani da wani Marin Wanda Kika mun...... Ta zukunna kasa ta fashe da kuka .... Y

a kalli Suleiman ko bar nan ko na halaka ka....... Suleiman Dan Allah tafi..... Dan girman Allah Suleiman tafi..... Sai nanatawa takeyi tana kuka, yasa habar rigarsa ya toshe hancin ya wuce kawai Yana huci,... ya fizgi Wayarta ya Kira Aisha..... Anwar ne

fito ina waje......

Cikin hanzari ta fito, ganin Bilkisu duke tana kuka yasa ta rikice wata kila ya Mata halin nasa..

Ya fiddo kwalin maganin ungo kije Mata dashi ciki, ko soke soken wuka mukayi hakan bazai shafi neman lafiyarta ba........ Bana

so Ina ruwanka da lafiyata??? Aisha bar mishi tsiyarsa bana so, ta rushe da kuka........ Kin dai ga halin kawarki ko? Kiyi Mata fada........ Haihuwata tayi da zata mun fada?

Wai me ya faru Bilkisu??? Aisha ta bukata cikin damuwa....... Wai daga Suleim

an ya kirani a waya fa, Ina abinda ya dameshi da wayata Ashe Yana son yace mun yazo ne ...... Uban me yazo yi?........ Kai me ya kawo ka? Ta daka mishi tsawa..... Ta kalli Aisha Kinga Marin da yayi mishi ya fasa mishi hanci........ Innalillahi yaushe? Aish

a ta fada a rude. Yanzu Mana,

Ya buga tsoki, idan Baki ja mishi kunne yayi nesa da ke ba wallahi Zaki janyo mishi nasifa da bala'in....... Kai a wa? Ta Mike tare da rike kugu..... Ya kalli Aisha Kinga irin action dinta da mood ko? To a duk lokacin da wan

cen Dan iskan..... Ka daina zagin sa wallahi..... na ce mishi Dan iska ko Zaki Rama mishi?........ Don darajar Allah kuyi hakuri......... Bilkisu ta buga tsoki ta juya kawai ya fincikota da karfi........ Ta kuwa Kama hannunsa ta gantsara mishi cizo da karf

i.....ya saketa da sauri Yana fadin Kai Kai Kai Kai, ta kwashi kasa ta watsa mishi a jiki sannan ta kwasa da gudu tayi ciki........ Tana shiga daki ta Sanya sakata ta ciki....... Ya biyota a guje, kafin ya karaso ta garkame........Aisha ta rude ta rikice g

idan ya harmutse Jin irin hargagin da yakeyi akan ta bude..... Wallahi zan karya kofar nan ki bude kizo ki fada mun dalilin watsan kasa...... Ban budewa.......har daya yayi ma kofar ta fada ciki tayi tsalle ta Haye katifa ganin zata bigeta........ Aisha ta

Fara rokonsa yayi hakuri ita Kuma ta makure ta Fara ihu tana kuka........ Ni Zaki watsa ma kasa saboda wancen Dan iskan........ Wallahi ba saboda Shi ba....... Ya sungumeta a kafada yayo waje Aisha da sauran mutane suka biyo su....... Ya juya duk shegiyar

data fito sai na karya ta. Aisha zo muje........ Ko wace tayi dakinta tana surutai......... Kafin kace kwabo magana har kunnen mufeeda.

Ya direta jikin mota ya kalli Aisha tambaye mun ita dalilin watsan kasa.......Dan Allah kayi hakuri Anwar.

Kika kawai

Bilkisu keyi......

Ya kalleta ke kina da gadara da taurin Kai ko? Kina tunanin duk wannan abun ba shine Kika janyo wa fitina ba?...... Dan Allah kayi hakuri Anwar. Aisha ta Kara fada.

Aisha na fadawa Yarinyar Nan bana son yaron can me yasa bazata kyale

shi ba?.......Akan wane dalili Zan kyaleshi Kai meye naka aciki da zaka hanani mu'a mala da wani?.....saboda..... Sai Kuma yayi shiru.

Saboda me?

To baka Isa ba, Yanzu na Fara kula Suleiman...... Kinji ko Aysha? Kinji abinda take fada ko?

Dan Allah

kayi hakuri Anwar zata daina kulashi........ Yaudarar ka zatayi, ba Wanda ya Isa ya rabani da Suleiman Kuma ka sani daga yau bani bakai, bana son abotar kaje ka nemi wata idan na Kara ganin ka anan ko kamun waya Kai ko tunani na kayi a zuciya ban yafe.....

..... Ya buge Mata Baki.

Ke kin Isa ki yanka mun doka?

Ta rike bakin tare da runtse ido...... Ya kalli Aisha kina Jin halin kawarki ko? Duk garin nan akwai yarinyar dake mun haka?

Ta girgiza Kai da sauri Babu kayi hakuri.....

Idan kin lura ta na nem

ana da rigima sosai......

Kayi zuciya ka kyaleni daga yau a fita harkar Bilkisu..... It's alright take care, Kawai ya fada mota yaja ya tafi .... Gabanta yayi mummunan faduwa, ta yi shiruuuuu kafin Ta figi hannun Aisha zo muje.

Suna zuwa daki ta fad

a katifa ta saki kuka.... Ai kinyi kuskure me yasa zakiyi mishi irin wannan wulakancin Bilkisu...... Ta dago fuska jage jage da hawaye.... Aisha na rasa gane inda Anwar ya dosa, masifar nan tashi ta isheni gara ya kyaleni na huta.... Wallahi bazaki huta ba

. Ta Kara kallon ta da sauri, yes bazaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login