Showing 21001 words to 24000 words out of 94923 words

Chapter 8 - WA ZAI FURTA complete

04 Sep 2026

8

da ita Shima me yasa baya iyawa?

Yaja wani dogon tsoki....... Ya wuce a fusace.

*******************

*KADUNA RIGASA*

Wannan ba shawara bace, kasan su mata shaidanin su babba ne, Basu da

hankali ko kadan.

Idan nayi haka mun Zama daya dasu kenan.

Abinda nake gani ka dawo gobe da safe kawai Bari na shiga masallaci na kwanta.

Amma yarinyar nan akwai Yar iska..... Ya dafa kafadar idanun sa kamar garwashi kada ka damu, mu zauna da safen.....

. shikenan Zan taho dasu hajia......noooo kada ka Kira kowa please.

Dole ya hakura ya tafi ba don ya so hakan ba ..... Abin Babu dadi hakan yake ta nanatawa a cikin Rai domin yasan kawaici ne yakeyi mishi saboda kada abotar su tayi rauni.

Ya girgiza Kai.

.....zata ci ubanta goben.

Ina Kai Yara school 7:30 gidan Zan yi ma tsinke.

Hakan kuwa akayi,

Kamar kullum karfe bakwai Yara suka fito Yana hangosu ya fito masallacin saboda Babu Wanda ya gane a can ya kwana daga cikin masu aikin gidan sai Mai gadi.

Y

a ce Ahmad je ka karbo mun mukullin motar mamar ka.

Da gudu ya juya, tana kitchen tana gyaggyara inda tayi aikin kayan break din yaran domin ( Amira tana da masifar tsafta Sam da yawa Bata jiran masu aiki musamman bangaren da ya shafi dahuwar abinci).....

Kai lafiya ko jakar ce ka manta?

Abba yace ki bashi makullin mota.

Ta kalleshi sosai Ina Abban?

Gashi can ya fito daga masallaci....gabanta ya Fadi. Kamar zata Kuma tambayar Shi sai ta fasa ta tafi daki don dauko mishi.

Ya kura ma kofar ido ya kalli ag

ogon wayar sa har da kwata tayi Yana mamakin dadewar da Ahmad din yayi sai gashi ya fito da gudu.

Ya Dan saki ajiyar zuciya har Almustapha ya Dan kalleshi abinka ga yaro bai hasaso komai ba saboda Babu kwalwar tunanin.

Duk abin nan tana tsaye jikin taga

tana kallon su, Yana fita da motar ko layin bai shanye ba ta fito da sauri don komawa bangarenta, maimakon tabi ta hanyar baya kamar kullum sai ta fito ta kofar gaba, abinka ga babban gida kuwa tana mikewa zata Sha kwana Yana shigowa da mota.

Gabanta yay

i mummunan faduwa ta tsorata ainun sim...sim ...sim ...zata wuce ya fito. Wurinki nazo daman.

Ta yi zuru zuru da ido alamar rashin gaskiya Yaya Ina kwana ta Dan rusuna, ya wuce gaba muje daga ciki.......

Mai aikinta har tazo tana ta goge goge, saboda tan

a da nata makullin.

Yana shiga yace ke fita ki jira a waje..... Tayi saurin ajiye mop kuwa.

Tana bayan sa zugum tayi tsuru tsuru tsaye....waigowar nan da zaiyi kuwa sai kauuuuu ya wanka mata Mari ta gigice kafin ta saka hannu ya Kara wanka mata......sa

i kawai ta zukunne don girman Allah Yaya na tuba......ta fada cikin karaji tana kuka....

Dan ubanki kina tunanin kin wuce duka har Yanzu? Ke har Zaki rufe ma miji kofa Kuma nazo nayi magana kinji muryata saboda ki nuna bamu Baki tarbiyya ba shine Kika yi

shiru. Ya daga hannu zai Kara Kai mata bugu yaji an rike hannun........Kana da hankali zaka Dakar mun Mata?....... Ya fincike hannun cikin bacin Rai....Dan ubanta ta wuce a dake ta ne?

Ya janye Shi, malam ba haka ake sasanci ba....Ni kiranka nayi ka sasan

ta ni da matata ba ka rikita man ita ba........ Sasanci? Kishin nata na hauka shine zaisa a sasanta ku? Sai dai in Mata rauni in karairayata Dan ubanta...kizo ki iske Shi da matar Shi da yaranshi ki nuna Baki kaunar su don Kina mahaukaciya har kiyi tunanin

zakiyi daraja da kima?

Duk suka zauna lokaci guda...... Saurara malam.

Matsalar Ummi daya tsageranchi da wannan mugun kishin na kwatanta Mata Amira Bata da matsala......ko tana da matsala ba dole tayi hakuri ba tunda ta Aure Mata miji don ubanta.....



Dan Allah ka daina hargitsa lamarin nan.

Ummi koma can ki zauna.....ya nuna Mata kujera...ba gardama ta tashi fuskar har tayi fushi.

Wallahi tallahi ban auri Ummi don in mayar da ita zawara ba. Amma Ina Mai tabbatar maka da cewa muddin ta Kara kuskur

en da tayi jiya na rantse da Allah sai na rabu da ita Koda zata kawo karshen alakar mu......saboda tun farko ita ce ta hada mu?

Noooo....

Then, what do you mean, wannan idiot din ta Isa ta rabamu ne? Daga alfarmar Dan ubanta?......Dan Allah ya Isa.

Ummi

.....Ummi...ummi.

Ya Kira sunanta sau uku.

Ga Dan uwanki zan maki magana ta karshe daga yau.

Kina son Zama Dani?

Tayi shiruuuuuuuuu,

Ki bude Baki kiyi magana yau zanyi wa tubkar hanci.

Kin shirya Zama Dani?

Da kyar ta daga Kai alamar eh.

Good, to

saurara.

Muddin kina son Zama dani sai kinbi wadannan dokokin wallahi tallahi inba haka ba Zan sawwake Miki Yanzu matukar kikaji sunyi Miki tsauri.

Idan kuwa Zaki iya to ki sani Koda wasa Kika kuskure Nan gaba daga gone har shekara dari Nan gaba kada ki

taba tunanin ban iya rabuwa da mace don na haihu da ita ba wallahi ko duniyar Kika safke mun sai na sallameki.

Na farko Amira wacce ta zame Miki damuwa tun kafin ki shigo gidan Nan. Matukar kina son Zama Dani sai kin Mata biyayya da kyautatawa, na biyu ma

ganar abinci ya Zama wajibi kiba kowa hakkin sa lokacin da kike da dama. Na karshe Yan aikin gidan nan ki sani ba bauta suka zo ba neman abinci suka zo yi to ya Zama wajibi a kyautata ma nemansa ta ko wace hanya. Cin fuska ,izza da gadara bazan Kara dauka

ba.

Allah ya gani naso in biki ta ruwan sanyi to maganar gaskiya yau na kafa shaida da yayanki akan kadan daga cikin wautar da kikeyi gidan Nan. Maganar iyaye na Kuma ko na Amira kice ma Baki sansu ba wannan kanki kikayi mawa domin duk Wanda ya kashe uwar

shi to Shima baza 'a mishi kani ba.....

Wannan kenan shawara Kuma Yanzu ta rage daga wurin ki.............

*************

*Federal University dutsinma*

Idanun sa jawur kamar garwashi ....dakin a cike Amma ana ganin yanayin sa kowa ya Fara z

arewa one by one. Ko takalmi bai cire ba ya fada bisa katifa ruf da ciki.

Anas ma fita yayi sadeeq kadai ya rage.

Anwar......ya Kira sunan sa.

Bai amsa ba Amma ya dago Kai.

Lafiya dai ko?

Kamar jira yakeyi...... sadeeq bana tsoron yarinyar nan wannan

Zan biye Mata fa.

Bilkisu?

Ya buga tsoki who else?

Me Kuma ya hada ku?

Simply useless girl din nan mufeeda tazo muna karatu she couldn't even understand abinda nake undergoing a wurin yarinyar nan ta fito a fusace, nayi Kiran duniya tayi burus Dani na

bita Ina Bata hakuri shine ta barni a wurin ta wuce abinta, Kuma tana fada mun Bata ji haushi ba idan bataji haushi ba zata ce in daina binta?

In don Bilkisu zuwa safe za'a ga tana ma magana....... A da ko? Yanzu fa ko itace tamun laifi sai nine Zan Bata

hakuri I called her on ma way here for more than seven times she refused to pick up the call.

Nawaoooo....sadeeq ya fada Yana murmushi.

To Wai meye ke kawo yawan fadan Nan naku? Ya kamata ku zauna ku gano Shi ......itace keda problem din buh I'll soon l

eave her and rest.

Are you sure?

Mtsew abeg leave me alone. Ya juya abinsa.

Waje sadeeq ya fita Yana kyalkyatar dariya. Zai so yaga ranar da ko wane zai ajiye girman Kai ya bayyana zuciyar sa, sun tsaya sai ba juna wahala sukeyi.

Bilkisu kuwa harda Yan

kwallanta. Ko da mommy ta kirata ma bayan isha'i maganar batayi tsayi ba karyar kanta ke Mata ciwo.

Washe gari sai 11 suke da lecture.

Ta riga Shi zuwa, tasan cewa ya tsani Zama gaba sai Sami gefe kusa da Ruth ta zauna.

Lokacin da ya shigo har an Fara

lecture.

Idanunsa na kanta har aka gama, malamin na juyawa zai fita ya Mike don yau lecture daya garesu gobe ma free ce idan ta fita shida ita sai jibi.

Can karshe take jikin bango Yana zuwa yace masu Ruth duk su fito zai zauna yasha bakin glass Yana san

ye da shirt Fara Mai ratsin light blue haka da blue jeans.

Ta Kara tsuke fuska ta Mike itama zata fita kawai ya hawo bisa table din ya tsallaka ya zauna. Dole ta koma ta zauna. Sadeeq na can baya Yana kallon drama.

Ina zakije bayan kin San don in zauna n

ace su tashi?

Ina da aikin yi ne.

Yayi murmushi na sani. Har Yanzu fushi akeyi dani?

Fushi ta kalleshi up and down ta watsar kallon da ya gwammace duka dashi kafin tace fushi akan meye? Kamun laifi ne?

A'a ya girgiza Kai.

To bani wuri in wuce ta mike

tsaye, ya daga Kai me yasa kike son mun wulakanci gaban jama'a?

Kamar ta kurma ihu don takaici, ta dalla mishi idanu wulakanci? Simply don nace kabani wuri in wuce shine na maka wulakanci?

To jiya fa da........ Anwar na tsani tariyo duk abinda ya wuce a

rayuwata kullum Ina hangen abinda gaba zatayi. Ban wuri in wuce jiya Kuma Kai ta shafa bani ba.

Amma ai na Baki hakuri ko?

Ikon Allah nace ban hakura bane? To idan kin hakura ki zauna mu Kara abinda muka Fara jiyan.....tayi murmushi Mai Kama da kuka All

ah ya albarkaci abinda mukayi din ya wadatar wallahi bana so na yafe.

Ya kife Kai bisa table....shikai yasan yanda zuciyar sa ke mishi.

Kai nake jira.

Ya dago Kai har Yanzu taki yarda su hada ido, me kike so Yanzu in Miki?

Ka bani wuri in wuce. Ta fada

fuska chunkushe.

Anya yarinyar ba zafin kishi ke addabar ta ba? Me yasa bazata fito tace tana sonsa ba kamar yanda sauran Yan Mata keyi Masa?.

Zan Baki wuri ki wuce Amma sai kin mun alkawari Zaki dauki wayata anjima.....banyi ba Kuma bazanyi ba ka b

ani wuri in wuce Wai Ina dalili?.

Ya Mike tare da say hannu duka biyu aljihu Yana gaba tana bite kamar zata tureshi Yana fita sit din tayi hanyar waje da sauri ya bita da ido har ta yi nisa ta taga.

Sadeeq na can baya kansa bisa littafi kamar Mai karatun

gaskiya. Ya ce su tafi library din.

Ita kuwa daki ta koma.

Tana sallar azahar barci yayi awon gaba da ita, sai biyar ma ta wuce ta tashi. Ga wayarta silent missed calls kusan goma shaa biyu. Khausar biyu, mommy biyu, hudu sabuwar lamba sauran Anwar.

Sai da ta Dan watsa ruwa tayi sallah sannan ta bi Kiran, khausar abinci zata Mata tayi, mommy Kuma zata fada Mata gobe zasu shigo Murna tsalle.

Alamar shigowar sako ta gani tana budewa taga wata number.

```i'm guilty I knew, please accept my apologies i

t will never happen again I promised```

Hmmm, tace kafin ta ci gaba da magana a fili.

Bana iyawa Yan matanka nesa nesan zaifi gaskiya don haka ka gaji ka kyaleni.

Washe gari karfe biyu su daddy sunka iso. Cikin wata Hummer Jeep bullet proof. Duk inda

motar ta gitta binta akeyi da kallo. A bakin hanya ta taro su tunda sukayi waya ita da khausar, su Aisha sunje test. Murna, tsalle, da ihu kawai takeyi.

Hankalin Yan compound din ya dawo kansu *lallai Bilkisu ba diyar kananan mutane bace* Nan da Nan kall

o ya dawo gunsu musamman lokacin da sukaga irin kayan da ake shiga dasu ciki.

Har dakinta Shima daddy.

Ta rasa inda zata sa kanta tana makale jikin kafar mommy ana shagwaba. Kayan ciye ciye baje na gani na fada. Daman sunce ko ruwan zafi kada ta dafa.



Kawaye aka Fara shigowa da makwabta ana gaisuwa abin ya birge kowa......

Daddy ya kalleta Ina *Anwar* ki kirashi mu gaisa da abokin fadan naki......mutanen dake cikin dakin duk aka Kama dariya.

Gabanta ya Fadi.

Wannan karon fa fadan na gaskene ......m

ommy tayi karaf, ai dole mu ga Anwar yau Kam maza kirashi a waya kice gamu munzo...........

Ayi hakuri da kadan. Wallahi nayi typing 7 dinnan kawai mistakenly na gogeshi Shi yasa na rasa ta inda Kuma Zan Fara .

Afuwan

πŸ˜„πŸ˜„πŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌ

zainab wowo ce

πŸ’–

✍

🏼

🀐

*WA ZAI FURTA?*

🀐

0

⃣

8

⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*

```wallahi tallahi ban taba ganin maiyi don Allah ba irin ki

ya Allah ya Kara Miki lafiya da tsawancin kwana kina Raina Koda yaushe Kuma addu'ar mu in shaa Allah muna rokon Allah ya karba alfarmar fiyayyen halitta SAW```

🀲🏼

*Abinda mutane suka kasa ganewa shine, ba daukar kudi ko wata kaddara kaba mutum kadai ne k

yautatawa ba, a'a..... Mutuntawa, girmamawa, magana Mai dadi da sakin fuska na daya daga cikin abinda ke saka soyayya, shakuwa da Kuma girmamawa, Amma sai kaga wasu jakkan sun maida mutane banzaye basa daratta kowa kuma suna tunanin dole ayi musu biyayya s

aboda suna da hannu da shuni....sammmm ba haka abin yake ba, ga Wanda ya San ciwon kansa ka Zama bola daga ranar.* Ya Allah ka wanke Mana zuciyar mu

irin ta *Aunty Rabi* ya hana mu kyama da wulakanta Wanda bashi dashi amin.

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

*Ke ce uwar gida Kuma Amarya in shaa Allah Alawiyya Nasir, matar Daddy uwar maamah da sofy, aminyar gaje Abu kawar Yar hareez Ina godiya ga namjij kokarin Samar mini Yar aiki na g

ode my disturber

πŸ™„

. Gaje Abu ga taki

πŸ‘‰πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ’–

na gode Allah yabar tare*

*****************

*KADUNA RIGASA*

```Wuya makarantar kare``` sunan wani littafin ```ZeeDee```

Ummi ta bala'in shiga hankalinta.

Ranar yabar gidanta, tun la'asar

ya mata sallama kagare yake magariba tayi don Yana son Zama da Amira itama.

Gidan ya dauki kamshi tana ta soye soye da gashe/gashe,

Sai dai taga mutum bayan ta. Zabura tayi cikin tsoro.

Ta turbune fuska wallahi ka bani tsoro.

Ai gara haka, Ni jiya ba

korata kikayi ba na kwana masallaci......Kai kajiyo. Ta katseshi.

Eh nasan cewa kishi ne yasa kikayi mun haka ....Ni na jiyo tunda na Kara Aure ko?........

Bana son irin wadannan maganganun ya kamata zuwa yanzu ka fahimceni.......naji...naji, shikenan.

Yanzu dai kawon abinda ya samu yunwa nake ji ....ya juya zuwa falo.

Dambun naman kaji, meat pie, doughnuts, da lemun kwakwa ta Fara kawo mishi. Yana Gama ci ya tafi isha'i, lokacin da ya dawo ya tarar da farfesun hanta, hunhu, Koda da tunbi.

Yana son sa

sosai, saboda yanayin yanda takeyin sa:

*Farfesun hanta,hunhu,Koda da tumbi*

Bayan ta wanke su da kyau ta zuba a tukunya sai ta kawo albasa Mai yawa (musamman Mai lawashi), tafarnuwa,da citta sannan ta Dan zuba Maggi onga na sachet ( gari ) Shi kadai.

Bata zuba ruwa sai ta dora Kan wuta low Yana heating a hankali kamshin kayan zai dakesu sosai ya danyi dry sannan sai ta zuba jajjagen tarugu da albasa again ta tsaida ruwa ta rufe.

Lokacin da ya dauko dahuwa ne ta zuba sauran Maggi da Dan gishiri to tast

e tare da curry kadan. Idan ya hade sai maganar ci.

Tana zaune gefen sa, suna ci tare, Ahmad ne ya shigo da gudu anyo mishi wanka,

Kai lafiya?

Abba gobe Aunty tace kowa yaci gayu zamuyi class picture.....

Shine zaka fado haka ba sallama daga Kai sai b

oxers? Ta fada tare da balla mishi harara....sim sim sim ya juya zai koma.

Ya kalleshi naji Ahmad in shaa Allah gobe gayu zakuci je hassu ta baku abinci kaji ko?

Yace toh ya juya.

Kin cika zafi yaran nan yanda suke tsoron ki koni basa tsoro haka meye ab

in fada ga shekaru irin nasa ma abinda yafi haka yi zaiyi.

Hmmm, kawai tace.

Ya finciko ta......zo in koya Miki yanda ake ba miji amsa idan yayi magana ba hmmm ake cewa ba.........dai dai ita Kuma ta turo kofa ashe bude yabarta lokacin da ya shigo.

Yana

kokarin Kai bakinsa ga nata sukaji an turo kofa itace tayi saurin zamewa tunanin ta ma ko Yan aiki ne.

Tuni idanun ta sun gane Mata.....me ya kawo ni?

Wace kaddara ta aikeni?

Na gano ma kaina Ni Ummi........gabanta ya dinga halbawa da karfi da karfi.

Ita Bata karaso ba, Bata Kuma juya ta koma ba.

Gashi ya rike Amirar gammmm yaki saki, sai kichiniya takeyi amma ya riketa tamau . Dole ta hakura ta kalleta, ki karaso daga ciki Mana Kika yi tsaye bakin kofa.

Bai dago Kai ba Yana ta wasa da hannun Amirar

yace idan wani abu kike bukata me zai hana ki Kira waya?

Shiru dai tayi har ta zauna bisa kujera tana facing dinsu amma ta kasa Kara maida idanu ta kalli takaici.

Tayi shiruuuuuuuuu, sai Kuma kwallah sharrrr, duk motsin da takeyi idon Amira na kanta sa

boda tana ta mamakin zuwan nata.

Ganin zubowar kwallah yasa ta zunguro shi,

Ya maida Kai gefe Ummi lafiya dai ko?

Ita kanta tasan kukan da biyu takeyin sa, kasa ta sauko ta Fara magana a hankali,

Aunty Amira kiyi hakuri Dan Allah Akan abubuwan da suka

faru sharrin shaidan ne, in shaa Allah hakan bazai Kuma faruwa ba......Ayya Ummi ba komai ya wuce.

Ta fizge hannun ta bari in zubo Miki abinci......um um na gode ta mike.

Ina zakije toh? Ki zauna muyi fira.......ya Kara hade fuska ya tsuke.

Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login