Showing 15001 words to 18000 words out of 94923 words

Chapter 6 - WA ZAI FURTA complete

04 Sep 2026

10

da tsageranci idan nayi la'akari da yanda kike datsa mun magana many times.

Ya nuna ta

da yatsa wallahi ki taka a sannu......Amira dai juyawa tayi abinta.

Ya kirata Amira tana juyowa tace abinda ya kawo ni kenan idan itama tana da nata korafin Ina jiranta.....tayi ficewarta.

Amma ke wallahi Baki da wayau Ummi. Da kin San Hali irin na Amira

da kin lallabata Kun zauna lafiya. Kin Aure mata miji Kuma kin dawo kina wani hauka...... Gori zaka mun? Ai ba ni na kawo kaina ba....... An Miki gorin.

Wallahi matukar kina son Zama Dani cikin Jin dadi sai kinbi Amira Kun zauna lafiya.....fuuuuu ya tash

i ya shige daki ji kake gammmmm.

Kwalla suka zubo mata, zuciyarta tayi mata kunci wanna masifa dame tayi Kama?

******************

*Federal University dutsinma*

Sun fito lecture 9-11 kenan aka aiko registration officer dinsu na kiranta.

B

abban mutum ne ana yawan Kira mishi kirki da mutunci.

Tana ta faman tunani ko lafiya?

Bayan sun gaisa ya mata fatan alkhairi sannan yace yaji dadin gajin result dinta da Kuma yanda ta Sami shaida a department na tare mutunci amatsayin ta na budurwa Kuma

ita kadai mace musulma a ajin.

Sannan idan har tana da wata matsala kada tayi kasa da guiwa ta je ta sanar dashi in shaa Allah zai taimaka.

Tayi godiya sosai, ta koma aji dayake suna da wata lecture ta 11-1 sannan suyi test 2-4.

Sadeeq babban abokin Anw

ar, Wanda kowa yasansu tare tun aji daya, ya hangota yace mutumen ga fa bilky can .

Yayi kamar baiji Shi ba miskilin........

*Zainab wowo*..

πŸ’–

✍

🏼

ayi hakuri da kadan pls

🀐

*WA ZAI FURTA?*

🀐

0

⃣

5

⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Ra

bi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

*Kinfi Alawiyya farin jini unex ta han

nun damata ( Hussaina Nasir )* Allah yaba kauna. *Alawiyya*

πŸ‘‰πŸΌπŸ˜

*********************

*Federal University dutsinma*

Tana isowa ya tashi yabar gurin.

Haushi ya kamata ganin zai dizga ta bayan Kuma yasan cewa wurin Shi tazo.

Sai Shan kamshi yakeyi y

au ta rasa dalili.

Ta kalli sadeeq yau me akayi wa abokin ka ko Yan wulakancin ne bisa Kai.?

Yayi murmushi to wa ya sani.?

Sadeeq Yana da kokari Shima sosai musamman bangaren calculation ya iya Math sosai da sosai.

Tayi murmushi kyaleshi don nace zamu

zauna test tare ne yake faman hade rai.

Murmushi kawai sadeeq yayi.

Suleiman na zaune gefen ta, tace sadeeq kara nuna mun nan please ta bude littafi ( Bilkisu kenan ba girman Kai indai maganar karatu ne ), ya danyi Yar dariya bari in Kira Miki mutumen ki

kada.......bana so kyaleshi kawai nunan.

Tare da Suleiman ya nuna musu sai ma ta ga cewa yafi Anwar iya koya lissafi Shi Kuma yafi iya theory ( labaran banza ).

Yana shigowa ajin ya gansu tare da sadeeq ya Kara hade rai, wani haushi ya turnukeshi ji yak

eyi kamar ya rufesu da duka su biyun.

Zai gitta sadeeq ya rikoshi malam zo ka koya mata.....kyaleshi banso ta fada a hasale.

Baka ga sai wani Shan mur yakeyi ba simply don nace Zan zauna test kusa dashi? Mtsew ta balla mishi harara.

Duk kunya ta kamash

i, saboda Shima fa bai San dalilin fushin nasa ba,

Gaban sa ya fadi kaddai fa kishin yarinyar nan yakeyi. Yayi saurin kawar da tunanin yadanyi tsaki a hankali.....

Ke bana son Sheri, yaushe ma na ganki da har Zaki mun wannan shaidar.

Eh Mana, Ina ma k

a ganni ai baka so ko ido mu hada kana ta wani muzurai......mtseew ya finciko sadeeq tashi munafuki. Ya zauna kusa da ita kamar ya ingije Suleiman yakeji , kawai baya son raini ya shiga tsakanin su.

Zaka karya nine?

Ya mishi banza..., Ita ma bai Kara ma

ta magana ba.

Suleiman dai na gefe ta juya tana mishi magana......idan na wanko ga Anwar ka wanka kada kayi kasa da guiywa....ya kyalkyace da dariya ita ma dariyar tayi.

Ya Kara hade Rai....yarinyar nan ma ta daukeni Dan iska Amma ba laifin ta bane Sulei

man zanci ma uwa......akan me? Wata zuciyar ta bukata. Yayi saurin kawar da zancen ya maida Air piece dinsa a kunne. Ya ajiye littafin sa ya fita waje.

Kowa nata karatu Amma Shi ba yanda zaka ganshi da littafi.

Handsome and intelligence guy amma girman K

ai da wulakanci sun bata Shi. Vivion dake zaune gaba na ta fada tare da kallon uchechi.

Ai ya Raina kowa don Yana da kokari.

Ga kyau Kuma ko?

Eh, Amma baya birgeni saboda gadarar sa, jiya munyi ta kiransa yaki daukar waya nida su faith.

Hmmm mu samun s

a mukayi dazun after lecture muna son ya koya Mana Amma kowa ya kasa Masa magana........ Maganar ta makale ganin Yana dawowa.

Ashe malamin nee gani ya taho.

Ko Zama baiyi ba ta nuna su uchechi gasu Nan suna son ka koya musu amma sun kasa tambayar ka.....

.sai ke Mai Baki Zaki tambayeni?

Idan abun ya damesu ki bari su fada Mana.

Zata Kuma magana ya nuna mata hannu alamar ta duba ga malamin nan ya shigo.

Sadeeq na bayansa.

Ta fiddo paper zata rubuta suna yayi saurin daukewa ya rattaba nasa sunan ya wani

hade Rai.

Ta kura mishi ido Baki bude.....gashi Bata da wata.

Ko wa ya dauke jakar sa....malamin ya fada.

Ya dauko jakar ta ya saka littafinsa Suleiman ya Miko nasa a saka mishi da wayar sa kawai ya Mike ya saka tashi wayar yakai jakar can gaban malamin

.

Ita Bata San me yayi ba, Amma Shi Suleiman din yaji haushi sai dai Yana uchechi ta saka mishi a tata jakar.

Sadeeq kuwa dukewa yayi Yana sumke dariya.

Bilkisu tayi zugum tana zare ido Anwar ya kwace takarda.

Tana tsoron tayi magana ya canza mata wuri

n Zama.

Ko ajikin Anwar tuni ya Fara rattaba number sa bayan ya rubuta suna da course code.

Suleiman ya Ankara Ashe biyu gareshi. Ya Miko mata.

Wani sanyi taji ta balla ma Anwar harara sosai sannan ta Fara rubuta suna.

Gaba daya ajin yayi tsit!

Tana r

ubuta suna taga Anwar ya fiddo wata takardar ashe daman Yana da ita.

Haushi ya Kara kamata shin me take nufi da akoreta sit din ko meye? Nan da nan ta Kara kulewa.

Har malamin ya gama raba question paper Bata gama duminiyar Jan layi da rubuta suna ba.

L

okacin da ya bada umarnin a Fara kowa ya bude takardar Amma sai wutar kowa ta dauke saboda yanda ya mako muguwar tambaya Mai sarkakkiya.

Sadeeq taji na magana a hankali, Anwar wannan 35 din zamuyi amfani da ita kuwa?

Ya kada Kai alamar a'a.

Yawwa na god

e.

Bilkisu tayi zugum, Suleiman ya zungurota alamar ta iya?

Ta girgiza Kai ya ce to kawai tayi ta kwafo musu na Anwar.

Ganin ya Fara rubutun tayi saurin maida hankali don samun abinda zata tsira.

Kamar injin haka yake rubutun zu..zu..zuu kafin tayi lay

i hudu har ya juya , haushi ya turnuketa bai jira ta gama? Wannan wace irin mugunta ce?

Nan da Nan ta zuciya kawai sai ta ci gaba da rubuta shirme.

Gara naci zero da in yi naka ....ta fada cikin zuciya.

Kafin kace kwabo har ya gama ya janyo wata sabuwar

takardar, ya canza biro black ya ci gaba da rubutu, sakamakon ta farkon da ya Fara da blue biro.

Tana kallon sa ta wutsiyar ido ko ya Turo mata wacce ya Gama da ita ta rubuta sai ma ya sanyata kasan tashi , idanun ta har ruwa ruwa sukeyi saboda fushi .

Wallahi Ni da Anwar har abada au Ni zai ma rashin mutunci?

Duk inda ka waiga kowa sai mazurai yakeyi an kasa rubuta abin kirki.

Tana kallon sa ya gama kawai yasa hannu biyu a kirji.

Kamar tayi ta tsunkulinsa takeji don takaici.

*stop writing*, ya Fara

karbar wadanda ke gaba layi layi........ai kamar jira akeyi ajin yau dauki gungunai.

Jin haka kawai taga ya dauro mata takarda bisa tata.

Sunanta, number, course code.....da komai da komai.

Ta zaro ido Wai Daman biyu yayi tawa da tasa?

Tayi saurin kall

on sa, ki soke wannan shirmen da kikayi kisa mistake. Ta kalli takardar ita ce ya Fara solving da blue biro.

Suleiman ya Fara kunno Kai zai Fara kwafa , malamin har ya zo wurin su, duk suka Mika.

Shiru Suleiman din yayi yama rasa meye zaiyi don takaici,

Tabbas yasan don Shi Anwar yayi haka.

Ta kalli Suleiman din cike da damuwa ka gama kuwa?

Wallahi banyi komai ba ya fada Yana kakaro murmushi,

Innalillahi..... Ta juya zata ma Anwar magana Ashe har ya bar class din.

Ta waiga ta Kara waigawa Amma Ina tu

ni yabar shiyyar class din ma.

Kayi hakuri , ta juya tana ma Suleiman magana.

Nima wallahi har na sadakas, ashe rubuta mun yayi. Kai Anwar karshe ne wallahi.

Murmushi kawai yayi.

Ai kaga da ya barni na kwafa har kaima kayi.....kayi hakuri Suleiman.

Ha

ba ba komai wallahi. Ya fada Yana Yar dariya.

Haka suka fito duk jikinta wani iri.

Kai Anwar case ne. Watan Shi dole inba wulakanci yayi ba baya taba Jin dadi.

A bakin kofa sadeeq ya karaso Bilkisu ya test din....yawwa sadeeq zo kaji Dan Allah. Ta yi ga

ba Yana binta.

Sun danyi nisa kadan inda ba mutane sosai ta tsaya.

Ka ringa yi ma Anwar fada Dan Allah Shi me ya dauki rayuwa?

Me yayi ba dai tashi yayi ba ya bada ba tare da ya baku ba?

Hmmm , kusan haka.

Kaga yasan tare nake da Suleiman na Kuma fada

mishi Amma sai ya hana in copying Yana ta sauri sauri Ashe so yakeyi yaci lokaci yayi nawa yayi nashi Kuma don mugunta bai bani ba har sai da za'ayi submitting saboda Allah ya kyauta?

Tun tsirewa yayi da dariya, Dan iska, abinda yayi kenan?

Wallahi kuwa

, kaga ai Babu dadi.

Gaskiya ba dadi.

Kiyi hakuri Dan Allah Yana Ina yanzu?

Kasan halinsa ai, har ya gudu ya tafi.

Kiyi hakuri Zan mishi magana.

Ka kyaleshi Daman idan ka lura bai niyyar Zama Dani ba yau tun safe yake ta wani Shan kunu..... Baki tunan

in ko kin Masa laifi? ...Laifin meye?

Jiya ne mukayi Zan kirashi a waya na manta inaga kilan shine ......shine ma kawai.

Mtseww.....to kyaleshi .

Anwar na Bilkisu.... Bilkisu ta Anwar ai in ba keba Shi.

Kai ai kyaleshi zanyi don ban iya hakurin wannan

mugun halin nasa.

Dariya sadeeq keyi sosai.

Ta wuce fuuuu.

Waya ta dauka, ta kirashi.

Yana tsaye zai siyi *Pepsi* yaga Kira.

True caller ta bayyana sunanta a screen din wayar sa *Balky gada*

Kawai sai yaji gabansa ya Fadi ras!

Ya danyi murmushi.....

.. Hello

Kana Ina?, Ta fada?

Cikin dakewa kamar bai San wake magana ba yace Ina Ina?

Eh kana Ina?

Wake magana ne?

Bilkisu.....kana Ina Wai?

Wace Bilkisu ? Ya Kara bukata.... Dariya ta kusa kubuce mishi Jin har ta Fara hasala.

Bilkisu Gada ....... Oh

ya fada tare da yin shiru.

Au shine kayi shiru mtseww.....ta katse waya.

Yabi fuskar wayar da kallo Yana kyalkyatar dariya ohh ni Hamza tawa ta sameni.

Wai yarinyar nan idan Sona takeyi haka zata shigar da kanta da tsiya ba da ARZIKI ba?

Ni wallahi na

Fara tsarguwa da tambayoyin da nake faman amasawa kullum akanta .

Ya kirawo ta......kamar bazata dauka ba har ta fito cikin makarantar sun rabu da Suleiman tun a bakin gate.

Ai naji kana ta wani rainan wayo saboda nice na kiraka ba credit Dinka ba. ....

...Allah ya bada hakuri. Kina Ina ne?

Ni na Fara maka wannan tambayar baka bani amsa ba don haka........ohhhhh na ma hangoki. Kawai ya kashe wayar.

Ta Fara waige waige....

**************

*KADUNA RIGASA*

Kutumar bala'i .....Kai Wai me aka daukeni gid

an nan?

To bafa Zan Dauka ba.

Daman some somen hauka zubda miyau, Ni fa ko lallashin da akeyi ma Amarya ban samu ba, bani da wata kima sai ta bisa gado ya iya lallaba da lallashi bisa gado....yau za ayi ta takare.

Ta tashi Yana kwance rubda ciki, ta ban

ka kofar da karfi har ya Dan razana....kace nan ba gidan mu bane daman na ce Nan din gidan mu ne?

Ya dago Kai da sauri ....kada ki kawo man hauka....an kawo ma hauka kayi maganina Mana mijin tace?

Nine mijin tace?

Kaine......kana da wani sunan da yafi w

annan shanyayye?

To Bari kaji in fada maka idan an shanye ka ni ba'a shanye Ni ba, ba malam ba boka amma dole ka maidani gidan ubana bani wannan wahalallen auren naka marar fa'ida..... Ke ba a Isa a Gaya miki gaskiya ba ko? Duk lokacin da kikayi kuskure a

ka nemi a Miki gyara......haka ake gyara a wulakance da cin fuska?

Ai Daman kallon ka nakeyi tun kafin in zo gidannan kake nuna mun bani da wani matsayi sai matarka..... Shut up.....ya daka mata tsawa......bazanyi Shurin ba......ita ma ta daka mishi tsawa

....ka sake Ni a yau Mana idan kana ganin Kai ke iko da kanka ba wat ke juya ka ba. Idan Kuma baka iyawa .....ta bude kofa kazo ka wuce ka tambayo ta idan ta amince yau ka bani takarda ta ita wacce ke auren naka.

Kai Bari kaji in fada ma Bashir.....wallah

i wallahi baka cikin tsarin mazan da nake so in aura saboda Ni duk Mai mata baya gabana musamman Wanda bai da gabata irinka sai abinda aka gindaya mishi.....Ummi Ashe Baki da kunya?.... Yau ne kasan haka?

Kai baka iya maganin rashin kunya ba?

Ka je ka ta

mbayo ta ya ake maganin marar kunya sai kazo kayi hakan Dani mijin tace....fuuuuu ya tashi yabar dakin ta bishi tana balbala bala'i ta inda take shiga Bata Nan take fita ba....idan hankalinsa tayi dubu yau a tashi yake, yayi hanyar dakin Amirar....ta daga

murya....Arrrrrr Ni nasan baka da idea din kanka sai wacce aka saka maka.......nesa nesa yake Jin maganar.

Da karfi yake buga mata kofa.....a rude tazo cikin tsoro take magana...wanene?

....ke bude nine....da sauri ta bude....lafiya baban Ahmed?

Waccen

yarinyar Bata da tarbiyya Amira wallahi wallahi ban tunanin Zan iya Zama da ita.....Nan da Nan tamu ta mata ta motsa ( kishi )....to Yanzu me kake nufi?

Zan kwanta anan ne saboda........saboda ita tafi karfin ka?

To ba anan ba wallahi.

Ta barshi tsaye t

a shige dakinta kawai tasa key........

Ya zaro ido

😳😳😳😳



Nima na zaro nawa

😳

........

✍

🏼

Ayi hakuri da kadan.......

✍

🏼

*ZAINAB WOWO*

*Maman Abdallah*

πŸ’–

🀐

*WA ZAI FURTA?*

🀐

0

⃣

6

⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kan

o maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

*Masoyana ku sani cewa Ina alfahari da ku 100% a ko

'ina kuke. Na gode da kauna*

πŸ‘πŸΌ

****************

*Federal University dutsinma*

Duk dube dubenta bata hango ta inda zai bullo ba, juyawa tayi don tafiyar ta..... Saura kadan suyi karo.

Ta razana ainun, hazbunallah! Ta fada da sauri tare da yin

baya kadan ........harara ta banka mishi kafin tace. Wallahi ka tsoratani.

Ya danyi murmushi matsoraciya kawai meye zai kamaki Yanzu da rana gatsal cikin wannan bainar jama'ar?

Mtseww...... Ta gittashi zata wuce.

Ina zakije Kuma Ina ce nemana kikeyi.

Barshi kawai , ta fada tana Kara yin gaba.

Ikon Allah, ya fada tare da rufa mata baya..... Wai ke me yasa kin cika nemana da rigima?

Ta Dan harareshi, ni nake nemanka da rigima ko kuwa Kaine ke nemana da rigima?

Me nayi?

Saboda me yau kayi wa Suleiman

wulakanci ni kuma ka kunyata ni?

Kunya ta ki Kuma?

Eh, ai kasan tare muke dashi sannan ka tabbatar idan na copy naka zai Sami damar yi shine ka rufe kayi biyu Kuma don mugunta baka tashi bani ba sai da aka ce submit.

Shine laifin da nayi?

Ban sani ba.

Allah ya Baki hakuri what next?

Kaje kaba Suleiman din hakuri......you are not well wallahi nine Zan ba Shi hakuri? Da na mishi me?

Shi ko kunya baya ji zai zauna mace na goya Shi Kuma......ai baya ganewa.

Please Bilkisu come to your senses Mana. Me y

asa kike kawo fada marar amfani tsakanin mu.

Ya ja ya tsaya Bari kiji na fada Miki, tunda Kika ajiye girman Kai Kika nuna kina son ki karu dani toba abinda bazan miki ba don naga kinyi passing no matter how, Amma duk masu zagi na suna mun shaidar banza a

class kallonsa kawai nakeyi.

A gabanki ake cewa Ina da girman Kai, bani da kirki....this and that..Amma Ina so in tambayeki lokacin da Kika nuna Zan koya Miki karatu Kinga negative response a wurina?

Akwai Wanda Kika taba Jin yazo wurina da sunan Zan koy

a mishi karatu na koreshi ko Kuma nace bazanyi ba?

Ko kuwa saboda kawai Ina son a yaba mun sai nayi ta yake baki Ina shelar ku taho kutaho Zan muku karatu imagine for God sake.

Eh na fahimceka amma ai baka sakin fuskar ma da za a tambayeka.....ke me yas

a Kika tambayeni?

Tayi murmushi ai ni kace.

Ke Bilkisu ko?

Ashe ka gane ....ta fada tana Yar dariya.

Mtseww......ya kamata ki daina mun wannan rigimar gaskiya bana so........ Sai kayi kokari ka canza Hali?

Nayi meye?

Na farko, Idan ka shigo class ka

danyi wa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login