Showing 51001 words to 54000 words out of 94923 words
kamfuna manya manya irin su *Gucci, M&S, C&K* ke gasu nan. Ji takalmomin da yake sawa..... Haba mutane, Ni
wallahi nasan karya ne ace duk sadeeq ke musu sai dai na yarda shikeyi ma sadeeq saboda ko dressing yanayin dauka a jiki ma ba daya ba Koda kuwa ir
i daya suka saka .
Ji lokacin zuwan su daddy ke baki lura bane Amma wallahi wani taku da Anwar keyi nasan yaron yaji bariki wallahi.....
Ke ni al'amarin sa ya Fara bani tsoro Aisha...... Hakuri zakiyi sonki yakeyi Kuma ya kasa *FURTAWA* kawai idan ya M
iki kina sonsa Ina Baki shawarar kada ki Bari wata tayi Miki shigar kutse sannan kada ki yarda ki nuna kin San inda ya dosa ki barshi har ya gaji ya *FURTA* idan da gaske yakeyi.
Koda yake wannan hauka haukan da ya Fara tabbas saura kiris ya *FURTA*......
. Aisha bana iya wa Anwar har ga Allah..... Ba Kya son sa?
Ta tsare ta da ido...... Tayi shiru ta kasa magana.
Kinji?
Idan bai Miki ba ki fada mishi ya rabu da ke, naga dai yanda Yan Mata ke neman kashe kansu saboda Shi Amma ke ya zabe ki kamar tumun da
re Zaki..... Understand me please.
I'll never understand you. Namiji kowa da kalar soyayyar sa, Anwar miskili, gadararre, Wanda ya Raina kowa kije kina bada labarin da kike bani Yanzu wani sai ya mare ki saboda cewa zasuyi karya kike yi amma Ni ganau ce b
a jiyau ba.
Amma ji yanda yake Miki rawar kafa.
Wallahi Yanzu dan ana farkon dawowa ba mutane Amma tabbas ni nasan wannan semester din akwai daru za 'ayi kallo. Sai ki dage..... Abinda ke tayar mun da hankali kenan wallahi.
Tayi dariya zai tare Miki na
san dole ya..... Wani abun ba agaban sa zai faru ba Aisha.... Yanzu ni ya zanyi da wadannan Kaya ni Bilkisu.... Ci zamuyi. Yanzu fa aka dawo.
Ai wallahi mun gode......... Wayarta ta Fara Kara.
Ta kalli Aisha Anya Anwar zai barni nayi abin kirki wannan se
mester din?..
Tayi dariya ta kwashi biscuits da wasu tarkace tace keni sai da safe...... Taja Mata kofa.
Ta kanga wayar a kunne ba tare da tace komai ba...
Ko har wayar ma an Sanya Mata doka?.
Ya fada Yana Yar dariya.
Hmmm, kawai tace.
Ke na gaji
da hmm, dinnan da kike neman ki ringa kawoshi bana son sa ki bude Baki kiyi mun magana kinji ko?.
Toh, tace a hankali tana murmushi.
Da gaske ba Kya so Ina zuwa wurinki?
Eh, tace da sauri.
Saboda me?
Ta runtse ido anya mutane sun San Anwar kuwa da
ake mishi shaidar baya magana?... Kinyi shiru. Ya katseta.
Haka Nan,
Baiyiwuwa ki fada mun dalili ko Kuma gobe ki ganni...... Dokar daddy ce, sannan zuwan naka zai rinka haddasa mun fitina tsakanina da Yan matanka, idan Kuma aiki yayi nisa Zan Sami ra
unin karatu...... Zuwa gidan naku?
Eh,
Fine. Zan daina zuwa shikenan ko?
Eh, ta ce tana murmushi.
Idan Zan ganki muyi magana Kuma fa?
Sai na sameka class....fine, gobe mu hadu new lecture rooms by four. Yana fadin haka ya kashe wayar.
Ta bi way
ar da kallo tace ikon Allah..... Allah ya kawoni ni Bilkisu.....
Tayi shiri daga sallar la'sar, a hankali take tafiya ga nisa daga masallaci zuwa classes din, kanta a kasa kadan kadan take gaisawa da mutane.
Kugin mashin taji a bayanta tayi saurin Ka
ra matsawa gefen titi, gabanta suka tsaya, ya sauko sanye da kananan Kaya kamar kullum ya rufe ido da facing cap... Ajiye ni a nan.
Ta dago ido da saurin Jin maganar sa. Shida sadeeq ne bisa sabon mashin fari duk leda jikinsa.
Sadeeq Ina wuni ta fada tan
a murmushi.
Lafiya Lau Bilkisu.
Ta Dan kalli gefen sa Ina wuni.
Yayi kamar baiji ba, ta ce ai kaji tsiyar Shi dizgi wurinsa bai daukeshi bakin komai ba.
Ka kawo man upstairs Yanzu please ya fada Yana kallon sa ya juya da mashin din Shi Kuma ya jera d
a ita suka ci gaba da tafiya bai ce komai ba,
Ina gaishe ka amma kayi shiru.
Ya dago ido cikin facing cap kince sadeeq Ina wuni Ni Kuma kin wani ce Ina wuni sunan nawa Yana Miki wahalar fada ne?
Murmushi tayi kaii ikon Allah Wai haushi kaji?
Anwar Ina
wuni?
Sunana Hamza.... A'a Nan Kuma daya fa. Sunan da kowa ke kiranka Zan ambata sai dai idan kana neman magana ne sai inji.
Shiru kawai yayi Mata.
Tayi Yar dariya yau gadara ake ji, ta fada cikin zuci tana satar kallon sa Yana ta faman Shan kamshi
Yana Bata rai.
Maganar meye zamuyi kace mu hadu yau?
Kina sauri ne?
Tayi dariya ohh ni Bilkisu halan bani da ikon tambaya.
Murmushi kawai yayi ta gefen kunci.
Suka shiga class din ba kowa sai mutum daya shima da alama chargy yakeyi, kasancewa fa
rkon semester ne.
Ta toge bakin sit....ya kalleta wuce ciki ko ni Zaki saka cikin kujera?
Ka zauna ni Bari....... Ya ingizata da karfi tayi ciki ya bita dole ta matsa da sauri kada ya Kara kamata...... Kina da gardama, na fada Miki idan Baki son Ina kam
aki ko taba ki kada kiyi mun gardama amma da alama kina da kunnen Kashi...... Ya karasa maganar Yana Zama kujerar kusa da ita.
Da sai ka bada tazarar kujera daya tunda magana ce zamuyi ba karatu ba...... Bazanyi hakan ba.
Tayi shiru tare da sunkuyar da K
ai tana wasa da yatsun hannunta.
Yasu daddy?
Lafiya lau, dazun munyi waya yace mun zasu tafi Paris da mommy.
Haba?
Allah.
Yayi murmushi *Yan gayu*.
Ta Dan harareshi.
Dafatan baki sanar da kawayenki abinda ya faru jiya ba, kin San bana son yawan s
urutu ne yasa bana nuna ni din wanine.....
Aisha ce Kuma ta rigani sani... Tasan meye?
Kuna da kudi?
Kice wallahi.... Tayi murmushi Allah kuwa, ta bashi labarin yanda sukayi.
Ya danyi tsoki, kawai don Ina sa Kaya masu kyau Shi zai nuna muna da kudi? S
he's not well.
Eh din. An dai gano ka.
Ya danyi dariya kawai.
Wace magana zamuyi kace nazo?
Ba gashi munayi ba?
Ko wata ta daban kike so muyi?...... Tsayuwar mashin din sadeeq yasa maganar da zatayi ta koma.
Ya dora Kai bisa table ta bi bayanshi
da kallo.
Ko baka lafiya ne yau? Naga duk kayi sukuku Anwar..... Sadeeq ya shigo ya ajiye ledoji bisa table din gashi nan Zan je na karbo sako isah kaita idan ka gama ka kirani.
Bai dago Kai ba Yana duke ya rufe ido kawai.
Tayi shiruuuuu tana kallonsa
...
Anwar..... Ta kirashi a hankali.
Ya dago Kai ya akayi?
Baka lafiya ne?
Ya yamutsa fuska yunwa nake ji ..... To ba gashi nan sadeeq ya kawo maka ba Kuma kana Jin sa Anwar kamar karamin yaro kayi shiru.
Fiddo ki ban ya fada tare da kokawa ya kife...
.. Bata San lokacin da tayi dariya ba ta Mike tare da saka hannu ta janyo ledar sai gogar jikinsa takeyi yaki Kuma gyarawa.
Ta fiddo hollandia biyu milk and strawberry, tashi gashi ta fada tare da fiddo wata leda, katuwar gasassar kaza ce taji cabbage d
a kayan miya nade a foil paper.
Ta bude ikon Allah dadi za'aci Alhaji Anwar..... Ya dago Yana Yar dariya keni wallahi tuwo nake son ci miyar kuka..... Ta kalleshi ka iya tukawa ko?.
Yayi murmushi Allah da gaske nake Ina son cin tuwo Bilkisu ya langabe
Kai.
To ka je ka siyo Mana.
Ke zakiyi mun. Zan siyo semo kiyi mun anjima...... Kam wallahi kada kasa ma ranka abinda bazaka samu ba. Zan samu yau sai naci tuwo Kuma ke zakiyi mun.
Ya bude kazar ya cire wurin cinya ya Fara ci.
Tayi shiru kawai.
Wa
ne kike so milk din ko strawberry?
Kai wane zaka sha?
Bani da choice as long as nidai cikina zai cika..... Ta yi dariya kawai ta dauko milk din ta Fara Sha a hankali.
Zakici kazar ko kunya kike ji?
Ta Kara Yar dariya, na ci abinci na koshi.
Me Kika ci
?
Taliya muka dafa.
Zaki mun tuwon?
Zan maka Amma ka Bari sai gobe yau dai marece yayi sosai.
In siyo semo din?
Ina dashi Kar ka damu.
Good.
Ba za kici ba da gaske?
Allah na koshi....... Zan baking baki matukar Baki sa hannu kinci ba..... Rage mu
n idan naje daki zanci da dare.
Mtsew, Allah ya raba ki da gardama.
Yaci gaba da cin abinsa.
Mamaki kawai takeyi Wai me yasa maza Basu da kunya ?
Kamar ya karanci zuciyar ta ya kalleta...... Ni banjin kunyar ki.
Ta danyi dariya ....yabi kuncinta da
kallo....
Kin San cewa kina da kyau kuwa?....... Ta kalleshi da kyau me kace?
Yayi murmushi kina son in maimaita abinda Kika Riga kinji?
Hmm, tace.
Samarin ki nawa?
Zaka Fara ko?
Ana zaman lafiya ka Fara tamabayoyi marassa amfani kuma azo ayi f
ada ko?
Ba Kya so na sani ne?
Ina ruwanka da samari na an fada maka irin ka ce da kowace jik and jak ...... Ya sa hannu ya buge Mata Baki...... Kai Kai Kai ta rike Baki.... Sai tayi kwal kwal zatayi kuka.
Ya harareta wallahi yau kikayi mun kuka Zan ba
ki mamaki ke baki da aiki sai shagwaba.?
Gaskiya bana son abinda kakeyi mun Anwar..... Gaskiya bana son abinda kake yi mun Anwar ya maimaita Yana kwaikwayonta.
Karfe nawa Zan zo na karbi tuwo gobe.... Zan Aiko maka Dan Allah ba sai kazo ba ko ka turo
sadeeq ya karba.... Wani kallo ya jefe ta dashi kafin yace *why are you pushing me away?*
Ba haka bane...... Haka ne.
Bazan zo ba, ki Aiko mun ya Miki ko?
Tayi murmushi eh,
Duk ya kware tsokokin kazar ya tura Mata kasusuwa ga naki..... Ta danyi dar
iya wallahi kana da ci Anwar...... Ya yunkura zai Kara buge bakin ta tayi baya tana dariya.
Tashi muje kada six tayi na gaji tunda ka gama.
Ki shanye tukun.
Tabbb bazan ya ba.
Shi yasa ba Kya kiba.
Hmm, kawai tace.
Wayarsa tayi Kara Yana dubawa ya
Mike please Ina zuwa...... Ta mishi wani kallo ya nuna Mata fuskar wayar Alhaji Abbas ne kin gani?... Ya fice Yana dariya kunya ta Dan Kama ta ganin zai fassara ta.
Ya Dan dade kafin ya dawo tana ta latsa waya taji yayi fit da ita.......
Bani naga
suwaye samarinki.......Aka Kara kiransa a waya.
Ya kalla sai kawai yayi tsoki, sai ka bar nan ka kirata ne?...... Sai bani kawai yayi picking yasa handsfree.....
Ya akayi?
Haka ma zaka ce?
Baki bani amsa ba nace ya akayi ne?
Jiya an Kai maka abinci
ka dawo dashi, tun jiyan nake kiranka kaki dauka Wai me yasa..... Nace kiyi mun abinci?
Sai kace sannan zaka ci?
Ke idan Baki da abin fada Ina da abinyi ya kashe wayar.
Ya kalleta kin yarda Yanzu ita ce ke damuna bani nake binta ba?.
Kai ji Ni me nace
toh?
Sai kince? Rigimar ki ai nasan ta.
Wannan semester din na ganki da wani Kato wallahi sai naci ...... Maganar ta makale ta zaro ido ya Mike da sauri tashi muje na rakaki.
Ka karasa abinda kake son fada?
Yayi murmushi kawai,
Ya daure fuska ta mik
e ka Isa ka hanani gaisawa da mutanen arziki na?
A matsayin a na wa to da zaka Sanya mun irin wannan dokar?
Ke ya Isa tunda nayi shiru kuma Dan Allah ki kyaleni.
Suka jera suna tafiya.
Suna karyo wata kwana su mufeeda na tahowa ta tsaya gaban sa kut
umar uba Wai kana cikin school din Nan............???????
✍
🏼
*Zainab wowo*
💖💖
Zan kawo muku wani true life story anjima Dan Allah Ina bukatar comments din ku please. Na gode masoyana Ina kaunarku.
💖
🤐
*WA ZAI FURTA?*
🤐
1
⃣
7
⃣
*T
ukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
***************
*KADUNA RIGASA*
Duk ina son ganin ku falona da karfe takwas...
Ya tura ma kowace sako.
Duk sun you zugum suna mamakin wannan Kira , abinda bai taba ba.
Ya rage karar TV.
Agurguje ba lokaci maganar zata dauka ba, da fark
o Ina godiya da Jin dadin yanda ko wace ke kokarin faranta mun da Kuma dagewa wurin kyautatawa, hakika naga canji a gidan Nan. Allah ya saka ma ko wace da mafificin alkhairi.
Magana ta karshe doka ce Zan saka na neman shawara ko neman izini ba.
Daga yau
na Hana ko wace ziyarar dakina matukar ba ita ce da girki ba. Sannan daga yau kada wacce ta Kara bina ko ta shiga sashen dayar ku matukar Ina ciki.
Wannan shine.
Ummi kina iya tashi ki tafi sai da safe...... Ya Mike yayi ciki.
***************
*Federal University dutsinma*
Gaban Bilkisu ya fadi ita Kam ta tsani fitina a rayuwar ta, tayi kasa da Kai tare da wucewa a hankali..... Ya chafko hannunta ya rike gammm, ba Bilkisu da mufeedar ba duk wadanda ke wurin sai da suka fiddo idanu waje.
Yas
ha mur ya Kara janyo facing cap dinsa ya rufe idanun sa Yana kallon kowa kasa kasa sannan ya maida kallon sa ga Bilkisu Yana janyota baya a hankali Yana fadin ```yaya Zaki tafi ki barni bayan kin San...``` Amma Anwar ka maida mayar dani Yar iska. Au daman
saboda wannan sillan Karan kake Mana yawo da hankali....tabbas yau na gane ma ido na.....
Sake mun hannu Bilkisu ta fada tana doka mishi harara, yayi kamar baiji ta ba.
Ya kalli mufeeda kin gama mu tafi?...... Na gama ai daman ban tsayar da Kai ba ko?
Ta fada tana huci.... Ya ja hannun Bilkisu suka wuce..... Kwallah suka zubo Mata sharrrrrr ta fizge hannun ta da karfi yayi saurin kallonta cikin hula Yana Mai daga kansa sama..... Kuka again?
Ya fada Yana kallonta.
Ni zaka zubda wa mutunci a gaban baina
r jama'a? Ana ganina da kima da mutunci.....ke! Wai me nayi?
Hannu na da ka rike ni muharramarka ce? Ta zaro mishi ido. Yayi murmushi Bilkisu rigima, na lura duk duniya ba abinda Kika fi so da kauna irin na taba ki saboda na fada Miki cewar matukar Ina ta
re dake ban sallameki ba Kika nemi Bari na ki tafi wallahi ko a gaban waye Zan Kama ki, me yasa ke baki ganewa kiyi mun biyayya?......
Bazanyi biyayyar ba, na ce bazanyi biyayyar ba.... Ta nuna Shi da yatsa jira kaji Anwar na lura da take taken ka kana so
n mayar dani irin su mufeeda da ke binka suna maka biyayya kana musu yanda kaga dama ko?
Saurara da kyau, bana tsoron ka , bana shakkar ka na gaji da wannan dokokina naka marassa Kan gado.
Ka tafi kaje mufeeda is ready for that not me.....ta hada hannuwa
alamar tana rokonsa abeg leave me alone.... Ya rungume hannuwa duka a kirji ya tsareta da ido kawai Yana kallo.
Ta mishi kallon up and down ta wuce tabarshi a tsaye.
Yabita da ido har ya daina ganinta...
Yayi shiruuu, me yasa bazan kyale yarinyar ca
n ba?
Anya Bilkisu ta damu dani kamar yanda nake jinta azuciya?
Me yasa ta fita daban cikin matan jami'ar nan take bani wahala ta kasa gane irin qimar da nake da ita.?
Wai ko wannan haukan da Yan Mata keyi a kaina me yasa ita bazata ringa mun yanda nake
so ba don su fahimci tafisu?
Mtsewww yaja dogon tsoki, sannan ya fiddo waya ya kira sadeeq, *zo ka daukeni*
Yanayin muryar sa kawai yaji yasan an Kara kwafsawa .
Kicin kicin ya iskeshi bakin gate ya hau mashin din kawai suka tafi.
Yana zuwa daki ya
fada bisa gado yayi ruf da ciki....
A bakin kofa ta hadu da Aisha ta bita da kallo kafin ta rufa Mata baya suka nufi dakin Aishar........ Yau ma kuka?
Kuka Zaki ringa mishi lallai kina da aiki...... Aisha bana son abinda Anwar kemun kawai a gaban su m
ufeeda ya rikon hannu Kuma ya rikeni yaki saki saboda Allah me zasu daukeni?
Ke yau ai na shiga uku Kinga kallon da kawayenta ke mun da ita kanta....... Ai dole. Kut! Wallahi dole su kalleki, Al'amarin Anwar ya Fara ta'azzara gaskiya Kuma Shi yaki fitowa
ya Fadi ainahin abinda ke ransa ...... Yana jiran ni na bishi irin su mufeeda haka na lura amma wallahi ki barshi idan yasan wata bai San wata ba.
Ta wuce dakin ta don ta gabatar da alwalar magriba.
Ta kashe wayarta kada ma ya kirata,
Washe gar
i tara suke da lecture, akayi sa'a malamin ya zo. Ya bayar da first assignment cikin part of outline din da zasuyi semester din, Anwar na baya can karshe idanun sa na Kan Bilkisu dake tsakiya ita da su Joseph, lokacin da ya fita ne ta karbi littafin Joseph
din tana rubuta inda aka wuce ta. Tana gamawa ta mike Anwar ya