Showing 24001 words to 27000 words out of 94923 words

Chapter 9 - WA ZAI FURTA complete

04 Sep 2026

9

Dan tab

e baki , a'a barci nakeji da wuri sai ko zuwa gobe haka.

Har kofa ta taraka, kafin taja kofar.

......... Gaskiya abinda kakeyi ko kayi Abban Ahmad wallahi baka kyauta ba, Shi ido ba mudu ba yasan kima.

Ka rikeni gaban Ummi ai wannan cin fuska ne.

Ya ka

lleta sosai.......makaho idan Yana Kashi in har ba'a zungureshi ba to bazai gane ana kallonsa ba.

Yarinyar can abinda take nuna mun tun kafin in aureta dole in bita in Mata yanda takeso ita bazata bi ra'ayi na ba.

To Ni da ita wake auren wani?......duk d

a haka Yanzu kaga.....kiranta mukayi?.

Inba kilibibi da tsugudidi ba me ya kawota Yanzu?

Ba a haka......ke naji.

Tayi murmushi.... Ita Amarya ai Bata laifi.

To wannan dai tanayi.

Naji dadin zuwan ta yau din wata kilan ta Dan Sami darasin kula da miji

idan ita din Mai hankali ce.

Ya Mike idan kin Gama sallamar Yara Ina jiranki.

*Ummi* taci kuka kamar ranta zai fita, tabbas ya kamata tayiwa kanta karatun ta natsu. Ashe ita sunan tana Aure Amma har Yanzu Bata San meye Jin dadin Aure ba, ta goge hawaye

n da ke shatatowa, dole in kwantar da kaina inci arziki in barshi inda yake saboda tabbas idan naki abinda yake so nice Masha wuya.............

******************

*Federal University dutsinma*

Shigowar su Aisha ya bata damar neman mafita.

Ita

kanta ma tana son ya zo su gaisa amma bazata iya kiransa ba.

Text ta tura mishi.

_Kaxo ku gaisa da su daddy yanzu_.

Wayar na hannun sa Yana kallon film.

Zaune ya tashi zumbur.

Sadeeq ya kalleshi lafiya?

Ya jefa mishi wayar.

Anzo wurin Dan ubanka sa

i kaje ka gabatar da kanka.

Munafukan banza Kun tsaya sai ba juna wahala kukeyi.....mtsew malam ban wayata.

Ya jefa mishi.

Wani text din ya Kara shigowa ... _zasu tafi in d next 30 minutes so hurry up and come_

Kara jefa ma sadeeq wayar yayi.

Kai seri

ously fa ...ya fada Yana zaro ido.

Ya tuntsire da dariya sai ka tashi ka tafi.

Ku dai tashi mu tafi wallahi bazanje Ni kadai ba. Kasan dai rashin zuwan Nan kuma wani problem din ne.

Anas ya Mike zumbur Tabb ku tashi mu tafi rigima dame ta cimma kurege.

........ Ya kallesu sai faman canza Kaya sukeyi, yayi murmushi wallahi Yan iska ne ku.

Kaman zakuje biki?

Sadeeq ya jefo mishi wani farin boyal malam saka mu tafi...

Ya Mike idan Kun Gama mu je banson shirme.

Duk sukayo mishi chaaaaaa wallahi sai ka c

anza Kaya Dan ubanka da wannan hug din zaka je?

To meye aciki?

Kana hauka ne?

Ku daine mahaukata, Kun zauna Kuna ta faman wata kwalliya kamar zakuje daurin Aure.

Yayi hanyar waje.

Anas ya finciko Shi, kasa manyan kayan nan kada muci ubanka.....kici ki

ci suka Fara kokawar cire mishi riga. Ba arziki ya cire su.

Sukayi juyin duniya yasa hula kube yakiya dole suka hakura sai dariya yakeyi masu duk sun Sha huluna.

Daddy ya Fara mikewa Zan jiraku waje ku karasa kada muyi dare....... Tuni su Aisha sun rufo

mishi baya don barin Bilkisu ta gana da mommy.

Mashin din muhseen roba roba suka amso.

Sadeeq ne driver, Anas tsakiya Anwar karshe.

Suna shawo kwana sadeeq ya kurma zagi ashar, wancen muguwar motar fa?

Dai dai su daddy na kunno Kai sai dai ji suka

yi Anwar ya dire da yake ba gudu sukeyi ba.

Ga Anwar nan kuwa inji Aisha.

Murmushi daddy yayi, nesa kadan sukayi parking.

Tare suka jero su uku.

Wata irin faduwar gaba yakeji wacce bai taba Jin irinta ba, duk suna durkushe lokacin da suka karaso.....B

arka da rana.

Idanu su Aisha suka bude duk girman Kan su?

Ya fadada fara'ar sa ya Mika musu hannu, Assalamu alaikum duk Wanda suka gaisa sai ya dago hannun alamar ya Mike tsaye har yakai ga Anwar,

Wani shocking yaji duk illahirin jikinsa ya dauka dai da

i lokacin ne Kuma Bilkisu da mommy suka fito.

Ta danyi dariya to mommy ga Anwar can .

Da sauri ta Fara waige waige Yana Ina?

Gashi can daddy ya rike hannun sa.

Tunda ya dago daddy bai saki hannun sa ba, ya rikeshi gamm suna Yar tafiya hakan yasan su sa

deeq da Aisha stepping back kadan suna bin bayan su.

Sai murmushi yakeyi Yana sunsunne Kai.

Daddy ya kula dashi tsaf!, ( Abinda bai sani ba yasa an kishi bincike kaf akansa tun lokacin da Bilkisu tace wurin Shi take daukar karatu ).

Ya karatu?

Alhamdul

illah! Ya fada,

Kana fama da rigimar Bilkisu ko?

Yar dariya kawai yayi, har lokacin yaki yarda su hada ido dashi.

Ai kullum labarinta Anwar, ko an Kara wani fadan ne?

A'a ya fada Yana murmushi.

Ta ce Kai Dan Kano ne ko?

Eh, ya ce har lokacin fuskarsa

ta kasa daina murmushi.

Me yasa baka jituwa da malamai?

Lokacin ne ya Dan saci kallon daddyn ta gefen fuska....

Ya kasa amsa tambayar.

Ganin haka yasa yaci gaba da cewa, mutunta malamai akeyi ana gaishesu, wasu akasin hakan duk kokarin ka sai sunyi ma

ka mugunta.

Haka ne!, Anwar din ya fada a hankali.

Sai a kiyaye kaji ko?

In shaa Allah. Yace.

A bakin mota suka tsaya.

..........ga Anwar ga Anwar , tun daga nesa mommy ke fada tana dariya.

( Na shiga uku ni Hamza ). Ya fada cikin zuciya.

Duk su sad

eeq suka gaisheta Bilkisu na gabatar dasu.

Ya yunkura zai zukunna don gaisheta daddy ya rikeshi, ku gaisa a tsaye kamar yanda sunna ta koyar.

......ya akayi Kika gane shine Anwar? Daddy ya tambayeta Yana murmushi.

Balky ta nuno min Shi lokacin da mun fi

tto.

Idanun ta na kansa Shima Yana son kallonta Amma ya kasa.

Su Aisha sukayi bankwana suka juya, Shima ya saci kallon su Anas alamarr su ware lokacin dasu daddyn kema su Aishar bankwana da nasiha.

Sai dariya sukeyi mishi daga nesa. Daman tun da suka t

aho da daddy din suke mishi dariya ganin duk yanda ya dabarbarce.

Anas yace munafuki kaga duk rashin kunyarsa yaki sakewa Kuma don sun dauki mutane Yan iska Basu so a gane suna son juna.

Anas ne ya matso ya Dan rusuna zamu koma hostel Allah ya tsare ha

nya...... Amin Amin ya zaro envelope ya Mika musu. Har lokacin hannun daddy na cikin na Anwar.

Ya kalli Anwar tafiyar ku daban ko?

Ya Dan sunkuyar da Kai tare muka zo.

Ohhh, to su tafi sai mu ajiyeka...... Ba Anwar din ba ita kanta Bilkisu tayi mamaki

n hakan.

Ya kalli Bilkisu ba abinda kike bukata Kuma?

Tace eh. Okay muje kada dare yayi suka bude mota.

Lokacin ne ya Sami hada ido da ita.

Ya sakar mata murmushi sai kawai ta harareshi ta juya.

Gaba ya shiga Yana nuna hanya.

Allah dai ya baku sa

'ar karatu ya kareku daga dukkan sharri.

Yace Amin

Dan Allah kusa tsoron Allah ga dukkan al'amuran ku Anwar kada kuci amanar iyayenku, kaji ko ?

In shaa Allah mommy. Ya fada.

Yayi matukar godiya lokacin da suka ajiye Shi daddy ya umurci driver ya sauke

mishi sauran kayan dake boot , sannan ya Mika mishi envelope Mai kauri.

Yayi godiya sosai. Aka Fara sauke Kaya, cartons din lemuka , ruwan roba, carton din indomie, oat,Madara family size 3, corn flakes, biscuits kala kala,Dan kalin turawa cikin buhu, pl

aintain, kwai Crete hudu,fresh milki, gasassun kaji, kilishi, soyayyar miyar naman rago, dambun Daman kaji, fanka Mai chargy ( Daman Yana da ita ), sabon carpet kato Mai laushi da turaruka.

Cikin kwalaye aka jero kayan.

Yabi kayan da kallo kafin ya Ka

ra komawa bakin tagar motar yadan rusuna, Angode Allah ya Kara arziki Mai albarka ya bada lafiya da tsawancin kwana. Duk suka amsa Amin Amin.

Ya daga musu hannu Allah ya kiyaye lokacin da driver yaja mota, gaban hostel din cike da mutane Shi kawai ake kal

lo saboda motar da ta janyo hankalin kowa.

Da gudu su sadeeq suka karaso.

Ya kallesu ku shiga da kayan Nan zanje in ga Bilkisu......kawai ya tsaida mashin ya koma..............Tana ta faman shirya kayan Jennifer ta shigo, Bilkisu Anwar want you......ta k

alleta da sauri Anwar?

Yah, he's out side...... Tana fadar haka ta fice abinta.

Ikon Allah, lallai ni ta bance , duk FUDMA kuwa akwai macen dake juya Anwar kamar Ni?.

Wallahi Bata taba tunanin zaizo ba lokacin da tayi mishi text despite fushi da rashin

daukar wayarsa, Wai me yasa Baya mata fushi da gadara da Kuma wulakanci kamar yanda ya Raina kowa?.

Hijabi ta saka ta janyo dakin.

Yana tsaye ya harde hannu duka biyu a kirji.

Manyan Kaya na mishi kyau matuka, ya Kura Mata ido kamar zai cinyeta.

Ta kar

aso kanta kasa, Ina wuni.....ban amsawa.

Wai Bilkisu me kike nufi ne?

Me Kika fadawa su daddy akaina?

Ta dago Kai me fa, wani abu ya faru?

Komai ma ya faru gashi kince dole nazo mu gaisa ya Mika Mata kudi Kinga bayan Wanda aka ba su sadeeq ga nawa Kaya

Kuma nacan an ajiye mun kamar.....to meye ne ba kyauta bace?

Ya kalleta, Kuma only me?

Ta daure fuska Ni ban gane abinda kake nufi ba...... Meye Kika fada ma iyayenki a kaina? Simple question.

Ta gyara tsayuwa, sun San cewa Kaine kake koya mun karatu K

uma Koda yaushe Ina Basu labarin karatun da mukayi.....ya akayi daddy yasan bana shiri da malamai?

Ta zaro ido wallahi bamuyi wannan maganar ba.

Kin tabbatar?

Ta balla mishi harara na maka ta kudin ka.

Ya kyalkyace da dariya, to ai abun ne ya bani tsor

o,

Mtsew ....tayi tsoki.

Mun shirya ko? Tunda na amsa Kira na Kuma bada hakuri Nima ayi hakuri na gaji da fadan Nan wallahi.

Mun shirya ko? Ya Kara maimaitawa Yana murmushi,

Ta yi Yar dariya eh,

Good, Dan Allah kiyi mun godiya sosai na gode.

Ba komai

. Sai gobe.

Korata kikeyi?

A'a bana son dai a Kira magriba kana Nan ko?

Hmmm, kawai kin koreni sai anjima ya Dan juya kamar yayi fushi.

Allah ya baka hakuri ka dawo ban koreka ba.....ya juyo Yana murmushi tunda kin bada hakuri kin tsira.

Zan kiraki pl

ease.

Ta juya.

Kinji?

Na ce toh.

Tuni magana ta Game ko'ina akan zuwan iyayen Bilkisu Kuma anga Anwar a wurin.

Hankalin mufeeda yayi mugun tashi ta dunga bala'i a daki. Tare da Shan alwashin dole ta gyarawa Bilkisu Zama ta Kuma ja mata kunne akan Anwa

r.

Sha daya da kwata na dare ya kirata. Labarin kayan da aka kawo mishi da makudan kudin da aka bashi yake lissafa Mata sanannan yadanyi Mata bayanin course din da zasuyi gobe.

Sha biyu ta wuce suka ajiye.

Su sadeeq sunyi sunyi yayi confessing akan

Bilkisu Amma amsar kamar kullum itace, *baku da hankali*

Kowa yayi mamakin ganin su rumi rumi.

Sai karfe hudu suka gama lecture.

Duk ta gaji tana tafiya da kyar kawai taji anfinciko hijabin ta.......jira karamar Yar iska.

Kafin ta Ankara sun Mata zob

e.

Ta kallesu daya bayan daya tace *Anzo wurin* cikin zuciya.

Lafiya?

Ta bukata tana musu kallon up and down.

Ko zamuji na jaki ne tukun?

Ko Kuma Ni ko?

Wallahi tallahi duk Yar iskar da ta Kara ja mun jiba sai naci kutumar........ke banza...mufeed

a ta katseta.

Wani kallo ta wurga Mata nice banza?

Eh kece banza ko Zaki Rama ne?

Akan meye Zaki kirani banza?

Saboda Anwar..!

Wallahi idan Baki fita harkar sa ba Zaki......Zaki fiddani karatu FUDMA?

Ta bukata.

Amma ke a matan ma rakiya kikayo, ai m

ace idan ta cika mace namiji binta yakeyi ba itace ke bin sa ba. Kije ki tambaya Dani da Anwar waye ke bin wani?

Ko an fada Miki dashi da Babu suna da banbanci a wurina?

Karatu ma da mukeyi Shi ke rokona da inzo ba Ni ce ke makalewa ba. Ta fiddo waya ta

latso missed calls.....ta nuna Mata fuskar wayar kalla ki gani.....don haka wallahi tallahi sai kinyi Dana sanin kirana banza......ta ingijeta ta wuce , gigin yasa jamcy ta Kai hannu zata rikota ji kake faaass.... Ta wanka Mata Mari , Marin da ya janyo duk

illahirin masu wucewa da wadanda ke zaune sannan ta daga murya....duk wacce Kuma take ganin ita Yar Tasha ce tazo ta yi gigin kwatanta abinda tayi ko a nemi wata ta Rama Mata...... Bilkisu lafiya meke faruwa?

Suleiman ta gani.

Tayi murmushi cike da taka

ici duka na suka zo yi saboda inji tsoro in daina karatu da kula Anwar .

Duka?

To bisimillah kuzo ku dake ta wallahi summa tallahi da na karya hannun yarinya ko waye ubanta....duk suka juya suna gunguni, yace:, Yan iskan karya.

Muje kyalesu. Suka jera..

...

Haushi ya kamata lokacin da ya Kira taki daukar wayar.

Tasan akan maganar test din *GST* ne. Yasan cewa ta tsani CBT,

Ya buga tsoki, duk duniya Babu Mai Sanya mishi ciwon Kai irin Bilkisu.

Bakin Auditorium din cike da dalibai abinka ga general

course. Tana can gefe ta makure sai faman karatun past question takeyi, Shi kuwa sai wurge wurgen ido yake ta inda zai hangota,

Mufeeda na can jikin bedi sun Kura mishi ido.

.......Wai Daman kina Nan? Yanzu naga Anwar Yana nemanki nace bamu hadu ba,

Aisha ce ta karaso rike da past Q din itama.

Yana Ina?

Gashi can....

Ta Mike , okay jirani Ina zuwa.

Yana hangota ya nufo ta.

Tayi kamar Bata ganshi ba ta nufi inda su mufeeda.

Ya biyota.......ke nake nema fa tun dazun kin Kuma hangoni kina neman s

harewa........ Da karfi ta finciko mufeeda tare da bankada ta kusa dashi har yayi saurin ja da baya ganin zata fado jikinsa.

Ya zaro ido.....ita Kuma ta juyo a hasale ta Kara maida keyar ta tare da nuna ta da yatsa.......Ni agabansa Zan Miki *warning*



Ko a Yanzu wakika ga yabi wani cikin mu?

Tuni an musu zobe ana kallon ikon Allah,

Ta daka Mata tsawa nace ubanwa Kika ga yabi wani cikin mu?

Na tabbatar tun dazun ya ganki anan Amma bai nemeki ba saboda haka kece *BANZA* Gashi nan nabar Miki Shi duniy

a da lahira idan kina bukata Ni karatu ya kawoni ba shashanci da bin maza ba don haka idan kina son sanin wacece Bilkisu please try and confront me again wallahi you'll regret it for the rest of your life useless fool.........

Kawai ta bi cikin mutane ta

wuce abinta.

😝

Zainab wowo ce dai

πŸ˜„

✍

πŸΌπŸ’–

🀐

*WA ZAI FURTA?*

🀐

0

⃣

9

⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*

*Wallahi tallahi inaj

in dadin masu kirana da mun text WhatsApp musamman don jinjinawa Aunty Rabi dayi Mata addu'a da masu yiwa mahaifina addu'a na gode Allah yabar kauna my fans my pride ana mugun tare irin sosai dinnan*

πŸ’–πŸ€πŸΌ

.

*Arziki irin na Aunty Rabi kowa ke fata Wanda za

ka ba kowa ba arziki irin nasu o'e ba daga mu sai 'ya'yanmu

πŸ™„

Wanda ya tsargu dashi nake*

πŸ˜πŸ€£πŸ€£πŸ€£πŸƒπŸ»

‍♀

_Wayata na bani matsala wallahi Shi yasa bana update da wuri_

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo mi

ji na gari I pray*

*Ke ta tabance UMMI MAMAN KHAIRAT DA ZARAH, makwabciyar Alawiyya Ina godiya*

πŸ‘‰πŸΌ

*Unex*

πŸ’–

( Babu kamar ki ).

*Alawiyya Ina Kara godiya fa Allah yabar tare Allah yabarki da malam ya tsone idon munafukai*

πŸ˜„

πŸ‘‰πŸΌ

*AUREN FARI FAN

S*

πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•

one love well.

*INA CIGIYAR MZ*

πŸ—£πŸ—£πŸ—£πŸ˜„

***************

*KADUNA RIGASA*

Tabbas Ummi Taji uwar bari,

Ta zabga uban tagumi, competition zanyi da Amira wallahi dole in ajiye wannan jahilcin in kwatar ma kaina yanci. Mutane dake cewa

r duk namijin da yayi sabuwar Amarya uwargida ta Zama banza yau na karyata hakan, naga inda year gida ke fin Amarya daraja da kima.

Tun kafin inzo gidan Nan yakeyi man gargadi akan matarsa, ban Kara tabbatar da hakan ba sai da nazo, Bata laifi, bata gun

durar sa. Ya Zama wajibi Nima nabi hanyar da tabi don mallakarsa.

Ranar ya koma aiki, tunda ya tafi tana bangaren Amira suna fira, abin ya bata mamaki ganin ba wani alamun sauyi daga fuskarta, ta sakar Mata jiki suna ta fira Mai dadi ( ba abinda yafi Zama

lafiya dadi, abinda mutane suka kasa ganewa kenan ).

Ta Dan muskuta Aunty wata alfarma nake nema wurin ki.

Ta kalleta cikin natsuwa sosai kafin tace Ina jinki ummi.

Wallahi Aunty na rasa gane Kan Abban Ahmad ko wane lokaci duk abinda nayi Ni Kam ban

iya ba.

Kinga ko abinci na dafa mishi idan na kawo mafi yawa fushi yakeyi yabarshi a wurin Koda kuwa nayi abinda yake so. Idan Kuma na sameshi daki...........ohhhhh na fahimci zancen ki. Ta katseta tana Yar dariya.

Baya Miki korafin Baki da kula?

Wallah

i yanayi Aunty.

Yawwa, kin gane, Shi mutum ne Mai son kula gaskiya.

Misali: wurin abincin da kike korafi, Shi yafi so idan Kika kawo mishi abinci ko ki zauna kuci tare, ko Kuma ki zauna kusa dashi yanaci Koda kuwa kin koshi, ya tsani ki bashi abinci kiba

r wurin.....ke abinda ma yafi so Bari in fada Miki shine ki na bashi da kansa.

Ya tsani lokacin da yake zaune dake ki maida hankali akan waya ko kallo ko wani abu saboda Shi mutum ne Mai tsananin son kula.

Ko a kwanciya ya tsani mace tayi mishi tabababaa

a Nan da Nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login