Showing 63001 words to 66000 words out of 94923 words
taba hutawa ba saboda kina matukar kaunarsa.... Bilkisu nasanki nasan wacece ke, gwargwado nasan waye Anwar shima wallahi tallahi matukar baku fito Kun fadawa junanku surrin da ke zukatanku ba tabbas zaku kashe kank
u a banza...... Ni na taba ganin jarababbiyar soyayya irin taku?
Ko wane idan kishin Dan uwansa ya motsa sai ya Kare kansa?...... Ta kife Kai a filo ...ta Kara sakin kuka a hankali.......
Idan kin gama ki tashi kiyi parking, ga maganin nan na dauki kwaki
goma .... Ta fice jikinta duk ya mutu tana mamakin irin wannan soyayya wacce ko a littafi Bata taba karanta irin ta ba.
Gaban sadeeq ya Fadi....... Anwar lafiya na ganka a firgice haka ko jikin....... Tashi ka shirya mu tafi Kano.
What?
Ya mishi w
ani kallo gaban Sadeeq ya Fadi ya tsorata Anwar lafiya?
Zaka je ko na tafi?
Ya kamo Shi ......ya fizge sadeeq Dan Allah ka kyaleni *I hate this world*........ Ya ci gaba da harhada Kaya...... Dole sadeeq ya Mike shima ya Fara hada jaka..... Amma wallahi
bazaka tuka mu cikin wannan mood din ba ... Bai rufe Baki ba ya wurga mishi keys din a kirji ya figi jakar sa yayi waje..... sadeeq ya bishi da gudu tare da rufe dakin....Sha biyu da Rabi na dare suka bar dutsinma yana kwance a sit ya Dora kafa daya a dash
board ya kwantar da sit yayi filo da hannayen sa idanun sa rufe..... Kadan kadan sadeeq na lura dashi sai faman tsoki yakeyi.
Batayi tunanin abin zai dameta ba sai da ta koma gida, kwana daya , biyu...sati. Anwar bai nemeta ba.
Suleiman kuwa yayi Kir
an duniya ta kasa dauka kamar tana son Jin haushin sa ganin shine jigon wannan fitina.
Gaba daya gidan an ga canjinta, bata walwala, kullum tana daki kwance.
Ranar da tayi sati biyu da dawowa mommy ta sameta daki, ta zauna bakin gado, Bilkisu mi ke d
amunki? Na lura tunda Kika dawo Baki da walwala, meke damunki? Saboda har dadyn ki ya Kai ga yin magana...... Ko maganin da Kika ce Anwar ya siya Miki ne kike ganin yayi yawa?....sai kawai taga kwallah na zubo Mata.... Hankalin momy ya tashi ko dai daukar
magana Yar tata taje......subhanallah. tayi saurin kawar da tunanin. Ta janyota fada mun menene?
Ta goge hawayen mommy bana Jin dadin abinda Anwar keyi mun...... Ta Bata labarin duk abinda ya faru..... Sai kawai taga mommy na dariya.
To Bilkisu Anwar a
i kishi ne ke damunsa tunda baya son ki kula Suleiman din sai ki kyaleshi....
Ina wayar ki?
Ta Mika Mata kawai..... A'a Anwar din Zaki Kira kice yayi hakuri tunda ke kin damu bai Kira ba..... Tabbb wallahi bazan kirashi ba mommy..... To ya Zama dole ki f
itar dashi a Ranki domin Shi da alama ya manta da ke kamar yanda Kika mishi gargadi...... Kirjinta ya buga da karfi kwallah suka Kara cika idonta ...mommy ta mike wannan shine sai ki zabi daya cikin biyu, Amma bazan dauki wannan dararewar ba da kikeyi ciki
n gidan Nan... Tana Gama fada ta fice tare da Jan kofa gammmm.
Tayi zugummm, dabara ta fado Mata kawai Bari ta Kira Sadeeq......
Anwar kuwa yafi Bilkisu shiga tashin hankali, ya koma kurman karfi da yaji, hankalin Hajiya yayi mummunan tashi t
ana zargin ASIRI ne ke son kamashi.
Ita kadai ke shiga dakin sa sai kuwa sadeeq, kullum sai ta lallasheshi yake cin abinci....
Abun har ya Fara affecting kasuwar sa, kowa shakkar kiransa yakeyi a waya saboda masifa da bala'i.
Tana zaune ta tsar
eshi ya shanye tea din ta Sha mur alamar ba wasa kamar kullum, ya Sha mur, ya tsuke fuska rabonsa da dariya tun ranar da ya rabu da Bilkisu Yana cusa kwai a Baki jinsa yakeyi kamar madaci.
....... Sadeeq ne ya turo kofa Assalamu alaikum.
Hajiya yau ki
na ciki?
Eh sadeeq maraba, Wa'alaikumus Salam.
Kamar zatayi kuka ta kalli sadeeq na rasa ainahin meke damun Anwar, shin ko ta sanar dakai ......ya wurga mishi harara Yana horonsa da ido kamar kullum akan kada yace wani Abu...... Hajiya ina ga malaria
ce, kin San fa dutsinma akwai sauro sosai Daman ya Saba duk hutu sai ya kwanta ..... Ba irin wannan kwanciyar ba. Yaro ya takure ya makure sammm Anwar ko murmushi ya daina yi...... Zai dawo normal hajia aci gaba da addu'a.
Ta Mike , kaima ai bakin ku
daya, ko ma menene bazan yarda da wasa da abinci ba... Ta fita.
Ya kalleshi ...ya kamata ko don tsohuwar nan ka daina wannan abun, nasan wallahi duk wannan damuwar Bilkisu ce... Ta kirani dazun ta fada mun duk abinda ya faru hada kukanta, ta ce wallah
i Babu abinda ke tsakanin ta da Suleiman, Anwar hakuri akeyi..... Please sadeeq ka kyaleni..... Bazan kyaleka ba tunda kaima baka kyale kanka ba .
Ta ce na baka hakuri....bazanyi ba tace na Kyaleta hakurin me zata bani?..... Har wannan maganar ta fada m
un ta ce kuskure ne bacin Rai yasa ta Fadi hakan..... Karya takeyi. Tana son bani haushi ne don na Mari Suleiman...... Wannan zafin kishin naka bazai taba sany.... Kishin ubanwa zanyi? Ya Mike ....ya kamoshi da karfi ya mayar.... Dan Allah kayi hakuri Anwa
r tunda wallahi Koda mukayi ways kuka takeyi..... Kaine zata Kira taba hakuri ba ni ba? Tunda Kaine tayi wa laifi ko?
Ikon Allah.... Tana tsoron kada ku Kara wani fadan ko kaki dauka ....... Ni zaka zo ka tsara sadeeq???
Tsari??? Wallahi da gaske nake
ita ce ta kirani....ya fiddo waya aljihu...duba ka gani ni na Kira ko ita? Minti nawa ka gani?
Sai kawai yayi murmushi ko kadan bai San yayi ba.....ya zaro ido are you smiling?????
Ya Kai mishi duka ya goce..... Munafuki ni na dade da sanin wannan cut
ar taka Bilkisu ce.... Dan Allah fada mun tayi maganar cikin damuwa?
Wallahi kuka takeyi lokacin da muna maganar alamar abun ya dameta...... Mtseww ita ce ke Sanya mu damuwa ai..... Iye? Sadeeq ya fada , ya banka mishi harara Yanzu dai kirata kace ta
kirani da kanta ta bani hakuri..... Message ya shiga wayar Anwar din karammm..... Ya dauko da sauri jin alamar shigowar message din ta ne,
```I'm sorry very sorry please and I don't mean to hurt you```..... Sai kawai ya washe fuska.... Sadeeq Bilkisu ce.
...
Dan Allah Kira mun ita.... Suna Kira wayar a kashe. Abu kamar wasa kusan kwana uku duk lokacin da aka Kira a kashe..... Shi kansa ya nema Amma bai Samu ba.... Hajiya dai taga Anwar lokaci guda an warware har Yana fita tawon *Bike* da suke zuwa da m
arece Shi da yaran governor.
Ta warware amma duk ta Dan rame kadan..... Kullum tunanin Anwar.
Ta kasa bude wayar ta saboda tana Jin kunyar idan ya Kira me zata fada mishi bayan ita ce ta bayar da hakuri?
Ta Kama lahadi suna gida duka har daddy,
tana sanye da Riga da skirt na atamfa super Holland Mai flower yellow dinkin ya bi jikinta, dogon hannu ne na *net* yellow duk atamfar yayyabe flowers din suke da stones masu sheki kamar diamond.
Kanta ba kallabi ta maida gashinta baya ta kulle jelar k
wance bisa bayanta..... Motsin get suka jiyo. Daddy ya Mike da sauri ya daga labule....jibga jibgan motoci ne bakake suke shigowa.... Ya ce innalillahi.. waye zai bamu surprise visit Haka?.. aka Fara fitowa yaga securities ko wane da abin magana a kunnensa
ya saki labule da sauri, ya kallesu inajin foreign affairs minister ne ..... Yayi ciki da sauri..
Suka tashi duk suka fada daki. Bilkisu ma ta shige nata.
Ya fito Yana gyara hula, falon kamshi kawai ke tashi na freshner ta ko Ina .... Ga A.C ta gauray
e ko'ina.... Ring bell ya Fara kadawa a hankali... Da daddy da kansa ya bude..... Ya bude ido sosai cike da mamaki compound din gidan makil da securities suna tsaye ya Sha fararr gizna dinkin falmara ce yasha aiki kansa cikin kube murjin kanawa...... *Waye
in ba Anwar ba*....... Anwar??? Daddy ya fada ....sukayi saurin zubewa shida Sadeeq daddy Barka da yammaci...... Ku tashi .... ku tashi.... Ya kamo Anwar.... Ya riko hannun sa suka shigo ya kwadawa mommy Kira ta fito da sauri.... Tayi turus ganin Anwar ta
re da washe Baki *Anwar a gidan mu*?
Sai sumke Kai yakeyi.... Daddy ya zauna suka gaisa sosai ya kasa hada ido dashi sai sadeeq ne ke faman amsawa .
Tuni mommy tayi ciki tasa Rahina Mai aiki ta fara kawo musu abin Sha....
Daddy ya Mike ya haye sama.
Mommy ta shigo suka Kara gaisawa ta koma ciki.... ya kalli sadeeq Dan ubanka ka tamabaya kace Ina Bilkisu?????...... Ya zaro ido ya Kai mishi duka......
Tana kwance ta kunna t.v din ta tana kallon wani Korea series *Innocent man*
Mommy ta shigo, ke
kullum idan anyi Baki sai ance kizo ki gaishesu??? Tayi zumbur Ina da niyya mommy ayi hakuri..... Ta galla Mata harara.... Tabbas kowa yasan surprise visit ya Bata don me zata fada Mata.... Gara ta fita idanunta su gane Mata.
Ta dauki dan mitsilin gya
le ta Yana a fuska bai ko rufe rufe rabin gashinta dake kwance a baya ba..... Ta raba momyn ta wuce ..
Assalamu alai........ Ya dago da sauri sukayi tozali.... Sai kawai ta dafe kirji tayi baya da sauri kamar wacce taji tsoro , mommy na tsaye bakin kof
ar dakinta Bata fita ba.... Ta ruga ta makalkaleta..... Mommy da gaske Anwar ne?.........
β
πΌ
*Zainab wowo*
π
π€
*WA ZAI FURTA?*
π€
2
β£
1
β£
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shi
rya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
ππΌπππ
*RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*
π₯°
ππ
.
**************
*ABUJA NIGERIA*
Ya kyalkyace da dariya, ya kalli sadeeq she was shocked..... Ai dole ta razana wannan babban surprise ne. Ya Kara dariya.
Yeah I like surprise
...... Da gaske Anwar ne mommy????
Tayi Yar dariya shina halan bai
hwada Miki zai zo ba?
Bai hwada min ba mommy muje ki raka Ni..... Walla Baki da hankali ni Zan kaiki inda Anwar?
Ta Fara dire diren shagwaba.
Walla bani rakaki keji min ja'ira..... Ki kaisu can Fallon daddyn ki na baki zasu fi sakewa naga Anwar duk y
a takura.... Mommy Dan Allah muje ki raka Ni.....
Ta kyalkyace da dariya yau naga ikon Allah....
To Wai ya ankayi yasan gidan mu?
Idan kinje Kya tambayeshi.
Ta tura ta waje daya ta fito da sauri..... Ta biyota da gudu mommy jirani....
Ta boye bayan t
a, Koda yaga mommy ce ta fito yayi saurin yin kasa da Kai.... ta wuce abinta tana dariya.
Tayi tsaye tana Yar kyarma tana murmushi kanta kasa.
Sadeeq ya tsura Mata ido kinyi tsaye ki karaso Mana Bilkisu.
Tayi Yar dariya sannun ku da zuwa ya hanya....
.
Sadeeq ya ce qalau.
Ta bi bayan kujeru kuzo muje tayi gaba kadan duk suka Mike..... Tana zuwa saitin kujerar sa ya yi charaf da hannun ta ya kalli sadeeq Dan ubanka shiga gaba.... Ya tuntsure da dariya, idan na shiga gaba in kaimu Ina?
Kwatanta mishi
Bilkisu...... ta fizge hannun ta lokacin ne ta Sami damar kallonsa don ta bashi harara.....kyaleshi sadeeq muje..... Ya dawo da ita da sauri jeki sanyo hijab...... Ta kalleshi zaka Fara ko? Gidan namu ban tsira ba? Yasha mur jeki sanyo hijab wallahi kada m
u sayar da Hali anan...... Dole ta juya tayi daki ya bita da kallo har ta shige ya hadiye wani tsinkakken miyau ya dawo Kan sadeeq ya Kai mishi uban duka Allah ya Isa Dan ubanka ka ga harammmm.....
Wata muguwar dariya sadeeq din ya saki .... Kayi a hank
ali fa...
Ashe duk dramar nan mommy na kitchen na hangen su..... Ta Kama dariya ita kadai....lallai Bilkisu tana da aiki.
Ta fito da doguwar hijab har kasa ta banka mishi harara muje..... Suka bi bayanta..
Ba sadeeq ba, Anwar kansa falon ya tafi
da imanin sa, ya zauna bisa two sitter sadeeq Kuma ya zauna kujerar dake can karshe Shi kadai ya ma t.v kuriiiii ganin ana best film dinsa *mortal combat*
Ta zauna bisa three sitter tana facing sadeeq ta Kara gaishesu
Sadeeq ya kalleta Yana dariya sa
i Kika ganmu ko?
Tayi murmushi hmm,
Hakuri muka zo badawa..... Ke ki dawo Nan kin mun nisa... Ya fada Yana kallonta.
Tayi kamar Bata ji ba, sai kawai taga ya Mike tayi saurin kallonsa... Yana tasowa ya figo hannun ta Yana fadin ke wallahi wata bagi
dajiya kike wancen Dan iskan ba dashi zakiyi fira ba ni ne bakon...... Ta fizge hannunta... Akwai CCTV ta nuna mishi da hannu.... And then?
Ta zaro ido.... Kai Wai baka da tsoro?
Mtsew yaja guntun tsoki tare da figarta da karfi ya zaunar da ita kusa da
shi, just sit down here.
Kaii Allah ya raba ka da rigima..... Allah ya rabaki da gardama kema.
Rahina ta shigo da tray cike da kayan marmari da lemuka masu sanyi ta Fara jerawa a dining table sannan ta fita tana kawo kuloli kala kala.....
Baza mu
ci abinci ba fa saboda bamu sanar ba kada a takura ayi Mana.
Har an gama ai, idan baku ci ba mommy zataji babu dadi?
Me yasa Kika kashe wayar ki?
Tayi shiru tana murmushi.
Kinji?
Duk kin rame kinyi rashin lafiya ne?
Um, ta ce.
Ko dai tunani na
ne?
Ta galla mishi harara , ya kyalkyace da dariya ni ma na rame ko?
Um, ta ce.
To ki tambayeni dalili Mana ...... Ta danyi murmushi kaiiiiiii Anwar.
Me yasa Kika koma da gudu bayan kin ganni?
Tayi Yar dariya....
Murna CE?
Ta Kara galla mishi har
ara.
Bacin wancen Dan iskan da Baki sako hijab din nan ba kayan sun Miki kyau kin San Haka?
Ta ce hmmm, kawai.
Gobe Zan dawo ni kadai kada ki Sanya hijab kinji ko?
Ta harareshi kammmm.
Yayi murmushi Dan Allah kisa irin gyalen dazun.... Bafa Zan sak
a ba dazun ma na manta ne..... Zan cireta idan Kika saka wallahi...... Anwar Nan fa gidan mu ne nidai ka rufa mun asiri. Ni Yanzu ka janyo mun anjima dole in amsa tambayoyi wurin daddy?
Na mene?
Dalilin zuwan ka ko?
Kice fada mukayi gashi kin kashe waya
rki nazo bayar da hakuri...... Nidai Dan Allah da baka zo ba saboda zai...... Ya tsareta da ido. Tayi shiru.
Uhum, Ina jinki saboda zai ce meye?
Nidai shikenan.
Ya kalli sadeeq jeka ci abinci fa, okay ya Mike ya nufi wurin
....ke Kuma kawon nawa ana
n inci.
Saboda me?
Saboda bana son kimun nisa Kuma bazan yarda gani ga ki ga sadeeq a wuri daya ba muna ci...... Wai Kai meke damunka....????
Yayi dariya kawai.
Suleiman ya kiraki?
Gabanta ya Fadi, wace amsa zata bashi kada Kuma ya Kara hasala sa
boda ta lura tabbas baya kaunar Shi.
Bari kawai na fada mishi gaskiya..... Ya yi ta Kira Amma ban dauka ba wallahi...au haba?
Allah kuwa.
Ko shine dalilin da yasa Kika kashe wayarki?
A'a ba Shi bane.
To nine?
Tayi shiru.
Saboda me Kika ki daukar w
ayarsa?
Anwar ka daina kawo maganar Suleiman tunda ita ke kawo Mana sabani..... Dole ki canza layi..... Ta zaro ido dole fa kace .
Yasha mur tabbatas and I mean it.
Ta Mike kawai tana hararar sa, ya Kai hannu zai kamata tayi baya da sauri tana fadin
Zan kawo ma abinci ne.... Sadeeq ya banka mishi harara kaidai wallahi bakayi ba..... Yayi murmushi ka Gama kazo ka bar Falon nan ka isheni haka Nan .... Babu inda zaije. Ta fada tana zuba mishi farfesun Koda da dankalin turawa....
Ki hanashi din ki jany
o ma kanki Yanzu in ci ubansa anan har su daddy suji.... Gabanta ya Fadi tasan karamin aikin sa ne.
Ta kawo Masa ta Dan janyo stool ta ajiye ta koma ta dauko mishi juice exotic Mai sanyi na kwakwa da abarba.
Ke ce kikayi?
Ya kalleta lokacin da yayi
lomar farko...... Mommy ce.
Yayi dadi amma gobe komeye za'ayi kiyi mun kinji ko?
Ta galla mishi harara kawaiyayi murmushi Ina dai Shan harara Ni Anwar.
In tambayeki???
Ya tsareta da ido.
Um,
Tsakanin ki da Allah kinji dadin zuwa na?
Tayi Yar d
ariya kawai..... Kinji?
Wai ya akayi kasan address din nan gidan?
Yayi murmushi sirri ne.
Ta Dan harareshi ka Sanya mun ido da yawa me yasa ka damu dani haka?
Saboda....... Yayi shiru Yana Yar dariya.
Ta tsareshi da ido, saboda me?
Saboda kawata ce
ke my best friend.... Ta buga tsoki.... Ya kyalkyace da dariya. Yana ci gaba