Showing 72001 words to 75000 words out of 94923 words

Chapter 25 - WA ZAI FURTA complete

04 Sep 2026

27

kada ki cika mun yaji irin wancen kinji ko?

Naji sai me?

Yayi murmushi sai kiyi kwalliya sosai k

isa gyale Banda wannan Dan iskan zanzo don bama zai San fita ta ba.

Ta ce hmmm.

Ya naji kin yi la'asar ko an Fara fargaba ne?

Ta galla ma wayar harara fargabar meye?

Ya Kara dariya ya ce wallahi basan an mako mun harara.

Tayi murmushi hmm Kai dai ka s

ani.... Kema kin sani kilibabba Anwar na kalbinki amma kina wani sharewa irin ba sosai din nan ba..... Ta kyalkyace da dariya kaiii Anwar Allah ya shirya ka... Hubby zaki ce bagidajiya. Ke wallahi kina Abu kamar wata Yar kauyen kumus.... Tayi murmushi kawa

i.

Yayi kasa da murya kidan canza mun suna Mana sweetheart....... Kai wallahi Zan ajiye wayar Nan ...ya Kara kyalkyacewa da dariya yace ya hakuri nayi shiru.

Ta zumbure baki.

Yaushe Zamu fita yawo cikin gari?

Ana wannan Corona virus din zaka fita yawo

?

Ke ban son unnecessary excuse.... Cutar ce unnecessary???

Ya ja guntun tsoki.... Ko *Amigo* muje please...... Anwar kana so asanya ni a labarai ko?

Yayi murmushi to muje ShopRite nasan kinfi son can.

Ki bari anjima Zan baki labarin abinda ya faru

ranar da na ganki a ShopRite din na buya.... Ta zaro ido ka ganni?

Yayi dariya eh,

Fada mun Yanzu,

Ki Bari sai nazo,

Yanzu nake so .

Yayi murmushi. Kin tuna ranar da Kika tarar da securities a bakin kofa kikayi ta fada a Baki wuri??

Ta zaro ido ba

munyi waya lokacin ba, Ina kallon ki ai nine a wurin..... Innalillahi.

Ranar ne na biyoki har gida naga address dinki.... Na shiga uku.

Kin fita uku....ya fada Yana dariya.

Yau Zan baki labarai kala kala idan nazo kinji ko?

Tohm, ta fada a hankali.

Sai nazo ko?

Okay.

Ta latse.....

Daddy bai Sami damar shiga gida ba sai biyar saura.

Suna falon sama ita da mommy ya shigo... Ta Mike daddy oyoyo... Bilkisu meye kike dahuwa Kuma naji gidan duk ya hargitse da kamshi?

Mommy tayi karaf tana dariya..

.. Aikin Anwar ne.

Yayi murmushi da alama kin gaji uwaki wurin kula da miji ....... Maganar ta makale. Yayi saurin canza Babi da kallon mommy muje na ganki ya juya zuwa daki.

Suna shiga ta kalleshi har an daura?

Eh, Amma fa sun kawo shawara..

T

a me fa?

Ya zauna Baki gado, sun ce a sanar da Bilkisun Kuma I reason with them, kin ga yarinya ce karama kada ta je tana janyo ma kanta bala'i ba tare da tasan akwai sharadin Aure a kanta ba Kinga mu Allah zai Kama da laifin rashin sanar da ita tunda B

ata sani ba..... Zata firgice gara ayi shiru.

Ba wani firgici kar ki nuna kin sani Ni Zan Mata magana da kaina.... Me zai hana ka mayar da ita nan gwagwalada ta karasa ..... Biyota zaiyi, wallahi Anwar bazai yarda ba.

Shikenan, Yanzu goben zamu tafi sok

oton?

Eh, ke zakiyi gaba Zan biyoki bayan kwana biyu tare da Bilkisun.

Shikenan Allah ya tabbatar Mana da alkhairi......ammeeenn.

Bisa bike yazo yau, karar yasa ta fito da sauri ta leka ta taga daidai Yana cire helmet.

Kananan Kaya ne jikin sa, ya a

jiye helmet din ya saka facing cap.... Mommy zo kiga Anwar yau a bike yazo.... Ta yi murmushi, daga race ya wuto nan din ko?

Race Kuma?

Eh, kin manta da marece idan mun fita muna haduwa dasu da yawa yaran ministers, president da su Anwar din?

Wai sune

?, Hada Shi kenan?.... Gashi Kinga alama.!.

Zata Kara magana ta ce kije tun kafin ya nemeki ta Haye sama abinta.

Yana tsaye bakin kofar ta karaso, bazaka shigo daga ciki ba kayi tsaye?

Ta juya ciki ya biyo bayanta kin yi wa mommy magana Zan dauk

eki muje yawo?

Ta mishi banza har suka zauna bisa dining.

Kinji?

Ta ce a'a bazamu fita mu biyu ba..... Saboda kada na gudu dake?

Ta Dan kalleshi, Yanzu fa wannan maganar na iya haddasa matsala...kinji?

Kaci abincin Mana..... Ya janyo plate gabansa

zanci amma kibani amsa.

Tayi shiru,

Ko na tamabayeta da kaina?

Ta kalleshi da sauri, yayi murmushi Allah kuwa.... Ya kamata kana da kawaici fa.... Akanki fa bani da Shi gara ma ki sani....

Zamu je?

Kaiii Wai Kai me yasa ka fiye naci?

Saboda n

a turo da maganar neman auren ki.

Ka bari sai Nan gaba....

Family na sunji dadin zuwa gidan nan fa, suna ta mun addu'a da murnar na dace da Mata in shaa Allah....

Ta ce hmm.

Yayi dariya Allah kuwa, an karamta su mood din su ya kasa boye hakan Amma su

n dawo da wasu Kaya da goro Wai namu ne Haka akeyi?

Kai ni ban sani ba...... Ya kyalkyace da dariya ke wannan kunyar fa dole ki ajiye ta gefe kinji.... Ta galla mishi harara. Ya Kara yin dariya.....wannan hararar bansan lokacin da za a daina ta ba ko kuwa

salon kallon love din naki ne Haka...... Sai kawai tayi murmushi tare da doka guntun tsoki....Kai dai ka sani....kema kin sani. Duk sukayi dariya.

Hajiya na son ganinki duk ta rikice na aika Mata da hotunan ki Wai Bata yarda ba zakuyi video call.....

Ina ka Sami hotuna na?

A wayar ki na dauka lokacin Dana tafi da ita kin tuna????

Ta galla mishi harara tun lokacin abinda ke ranka kenan???

Ya kyalkyace da dariya meye ke Raina?

Tayi mishi banza.

Ya Dan gyara Zama ya lunkuma yamball baki kin San fa

tun ranar da Kika raba kudin da hahilin nan ya baki class zuciyata ta bani na Sami matar Aure....ta Kara galla mishi harara.

Ya yi murmushi me yasa Wai ranar bakiyi gardama ba Kika bani kudin?

Ta ce hmm.

Anya ba tun tsiwar farko kin kamu da so na .....t

a dauki robar ruwa ta Mike kawai ya taso bowl din yamball din a hannu da sauri Yana dariya zo ki daukon meat pie din idan kin gaji da table din..... Nima fa nafi son Zama kasa..... Ya zauna bisa carpet ya Mike kafa.

Ta dauko ita ma ta zauna dan nesa das

hi kadan suna kallon juna.... Ya kalleta yace kamar irin Amarya da angon Nan ko?

Ta galla mishi harara. Yayi murmushi, Dan matso Nan kin mun nisa gaskiya... Ta Dan matsa kadan kada taja kuma ya kamota.

Ina son wannan rigar ina Kika siye ta?

Mommy ta siy

o mun Dubai...okkay.

Me yasa bazakiyi mun kwalliya da wadanda na kawo Miki ba ko kina Jin kunya?

Tayi murmushi kawai.

Dan Allah ki saka,

Waye telan ki?

Mace ce,can cikin Area 8 ne shagon yake.

Ki debo kayan da Zaki Kai dinki gobe idan mun fita mu biy

a kinji ko?.....

Nifa bazan bika ba..

Ya kalleta dalili??

Tayi shiru.

Kina Jin nauyin tambayar mommy ko?

Tayi shiru.

Shikenan, Yanzu Zaki iya magana da Hajiya?

Ta danyi kasa da Kai tana murmushi nidai ka jira ba yau ba...

Ya kura Mata ido Anya ba s

auri zanyi a daura Mana Aure ba?

Ta dago da karfi... Ya maida bayansa jikin kujera ya Dan kwanta.... Yes, saboda kunyarki tayi yawa gaskiya gara kawai na kawar da ita da wuri don Zaki ringa takurani.

Yar tsiwar ma an daina mun sai uwar harara .......Kai

zaka karasa mun karatun?

Waya fada miki Aure na Hana karatu?

Ta harareshi Yanzu ma kana neman kisan Kai Ina ga da Aure Kuma???

Yayi murmushi ko Yanzu ma nikaf Zan siya Miki masu yawa ba shegen da zai Kuma ganin wannan beauty face din ba.... Ta zaro i

do nikaf?????

Kwarai kuwa.

Ta zumburo Baki...

Ya danyi dariya ya tashi zaune ko kin fi son kullum ana tashin hankali????

Tayi shiru yaga kamar ranta ya baci.

Ya Kira sunanta a hankali..... Kinji haushi ko?

Ai wannan tsananin ke bana so, kana abu

kamar Wanda bai yarda Dani ba kullum...

Yayi murmushi, wallahi na yarda dake.... To me yasa kake da takura?

Saboda *Ina son ki*

Ta kalleshi da sauri.. watau duk lokacin da yake cewa saboda ..yayi shiru abinda baya son fada kenan?

Kin gane ai Yanzu ko

?

Ta Dan harareshi kawai. Ya kyalkyace da dariya yace *Bilkisu H. Bushara*........ Ta Kara galla mishi harara.

Sai goma da Rabi yabar gidan.

Tana shiga ta tarar da daddy falon Yana kallon News.

Ta wuce sum, sum, sum..... Zo nan Bilkisu.

Cikin

Jin kunya ta karaso ta zauna kasa kusa da kafafun sa.

Anwar din ya tafi?

Eh,

Da alama zaiyi kula sosai ko?

Tayi shiru tana sunne Kai.

Sai dai Shi din ya fiye damuwa ko?

Ta Kara yin shiru tana murmushi.

Ya Aiko da iyayensa kamar yanda na umurta hak

an ya nuna tabbas sonki yakeyi da gaskiya.

Amma kina ganin zaman ku makaranta Yanzu a Haka bazai takura ki ba yayi affecting karatun ki ba Bilkisu?

Nima Ina tunanin haka daddy, saboda Yana da rigima sosai..... Na sani.

Ko muyi wata shawara nida ke ba

zaki fadawa mommy ba?

Eh, daddy. Ta fada da sauri.

Kinga tashin hankalin baya shakkar kowa kada yaje wata Rana ba fata akeyi ba yayi aika aika.....ko ?

Ta daga Kai.

Ko in sa iyayensa su dawo na daura Miki Aure dashi cikin sirri ba tare da ya sani ba?

Ta zaro ido cikin firgici zatayi magana yace jira kiji dabarata.......

Bazamu yarda ya sani ba, dalili kuwa shine irin damukar da yake Miki tabbas Yanzu zai Kara sake salo Kinga hakan akwai haramci Amma idan akwai Aure ko hannun ki ya taba ga Allah babu

laifi iyaka kici gaba da nuna mishi Baki so har a Samu ku Gama... Kin gane ai ko?

Ta daga Kai.

Koda wasa kada ki fadawa kowa kinji ko?

Ta ce toh, Yanzu mubi wannan shawarar tayi ko?

Ta daga Kai yawwa,to ungo ya Mika Mata kudi...sadakin ki ne dazun ka

fin su tafi an riga an daura Miki...... Kudin suka Fadi sai kyarma kyaf,kyaf,kyaf..... Ya Bata labarin duk yanda akayi sannan yaci gaba da lallashinta har ta daina zubda hawaye.

Amatsayin sa na uba na gari ya fada Mata sharuddan Aure don ta kiyaye......

...

Tana shiga daki ta fada Kan gado ta rushe da wani irin Kuka Mai tsima Rai.

Anwar kuwa na shawo kwana ya haska sadeeq can nesa bisa wani dakali da alama waya ce yakeyi.

Ko gida bai shiga ba masu gadi suka bude gate da sauri securities suka fito

....

Ya sauka yace su shiga dashi ciki ya koma Yana sando a hankali ya nufi gurin da ya hasko sadeeq....

Zaune yake ya bada baya Yana waya.

Ya daga hannu zai bashi tsoro sai kawai yaji Yana cewa...... Wallahi tallahi baba an daura mishi Aure yau.. y

a koma ya tsaya tare da rungume hannu.

.... Hajiya ke fada mun Amma basa son Anwar din ya sani..... Gabansa ya bada dammmmm....

Yaci gaba da cewa, wallahi kudin neman aure suka Kai shine mahaifin yarinyar kawai yace sun Isa shaida Aure aka daura... Walla

hi kuwa.

Amin amin...

Eh, bana tunanin yarinyar ta sani gaskiya.

A yanda aka ce mahaifin yarinyar ne yace lallai sai an daura auren saboda rawar Kan Anwar yayi yawa..... Eh sai dai mun dawo din. Amma Dan Allah baba kada ka fada ma kowa babu Wanda yasan

hakan.

Amin ya Rabbi.

Ya Mike ....juyowar da zaiyi suka hada ido da Anwar din cikin want irin yanayi ya razana ya firgita yayi baya da sauri ..........

πŸ˜„

✍

🏼

*MAMAN ABDALLAH*

πŸ’–πŸ’–πŸ’–

Assalamu alaikum. Ina Kara godiya ga masoya, Kuma Ina Kara bada

hakuri Dan Allah masu kirana a waya a ringa mun chat saboda Kiran Yana hanani typing da wasu ayyuka. Duk wacce ta Aiko da sako Zan gani Zan kuma bada amsa ko amun voice idan bayanin nada tsawo Zan tura Mata hotunan magungunan da bayanan su.

Na gode Ina ma

ku fatan alkhairi.

πŸ‘πŸΌ

Alawiyya

πŸ—£πŸ—£πŸ—£

Aiko da 24 yau an Sami daya as usual

πŸ˜„πŸ˜„πŸƒπŸ»

‍♀

πŸƒπŸ»

‍♀ *Uwa Mai bada mama, I love you Mom ( Maryam adamu tikau maman amannas)*

🀐

*WA ZAI FURTA?*

🀐

2

⃣

4

⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi bada

wi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

πŸ‘‰πŸΌπŸ’žπŸ’•πŸ’•

*RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love y

ou so much, remember this always*

πŸ₯°

😍😘

.

****************

*KADUNA RIGASA*

Wannan doka da tsari ya Kara taimaka wa zaman su sosai da sosai, gidan ya zauna qalau ba sauran tashin hankali idan Yana gari ko wace zata kama tsaginta har ya gama kwa

nakin sa ya koma sannan zasu ci gaba da ziyarar juna, Koda yaushe Ummi na sashen Amira musamman da ta Fara laulayi...........

***************

*ABUJA NIGERIA*

...... Juyowar da zaiyi suka hada ido da Anwar din cikin wani irin yanayi.....ya raz

ana ya firgita, sannan yayi baya da sauri tare da fadin *You scared me*...... Meye naji kana fada?....idanun sa sun kada sunyi jawur kamar garwashin wuta..... Ya daka mishi tsawa nace meye naji kana fada??????

Look please understand...... Ya shako wuyan

rigarsa Kai munafuki na ne ba Amini ba sadeeq?????

Ya girgiza Shi ya tura baya da karfi... Yayi taga taga zai Fadi.... *What the hell are you doing*..... Shima ya daka mishi tsawa.... Sai kawai ya dafe Kai ya duke wurin Yana fadin *Innalillahi wa'inna il

aihi raji'un*..... Hankalin sadeeq ya tashi ya kamo sa Anwar please.... Ya ingije Shi.. kyaleni sadeeq...kyaleni bana so... Zan maka bayani Anwar please calm down..ya Mike a hargitse ni za'a daura ma Aure ba tare da na sani ba??? Ya nuna kirjinsa Yana zaro

mishi idanu.... Please.... Ya tura Shi baya I don't want to hear it..... Ya yi gida da gudu... Shima ya rufa mishi baya ya biyo shi....tare suka shiga daki Yana kokarin turo kofa ya rufe sadeeq din ya banka da karfi .... *Get out*.... Ya daka mishi tsawa.

.. Ya maida kofar ya rufe , mutanen gida kowa ya fito yayi jugun , jigumm ......

Cikin bacin Rai sadeeq din ya Fara magana; Kana ganin laifi nane??

Ko kana tunanin Ina da laifi ko hannu aciki????....... Ya akayi ka sani ni ban sani ba???

Sadeeq wa

ne laifi nayi da za a dauran Aure ba tare da na sani ba??

Ya bude fridge ya dauko ruwa Mai sanyi ya Mika mishi a cup ungo kasha let's talk peacefully please..... Bana Sha ka fada mun waye ya dauran Aure Kuma meye hujja???

Ita Bilkisun ta sani???? Y

a Kara zaro mishi idanu...

Daddyn Bilkisu ya ce a daura.... Dalili????? Ya Kara tsareshi da ido....

Wallahi itama Bilkisun bata da masaniya, Kai waye ya fada ma???

Ban sani ba ya daka mishi tsawa..... Ya Mike tsaye bari kaji Anwar bana tsoron ka ba

na shakkar ka, ka saurara Zan fada ma abinda na sani akan wannan daurin auren idan kaga dama ka yarda idan Kuma ka ga dama ka Sanya a daureni sannan kaje ka dauki duk matakin da ka dauka...... Ya kura mishi ido, yau sadeeq ke mishi tsawa haka?

Lokacin

da aka Kai kayan daddyn nasu ne yace a daura Aure saboda yanayin rawar kanka musamman yanda kake kakkama mishi 'ya.... Ko kasan cewa ya bada labarin duk bidirin da akeyi school???? Musamman Yana da wadanda suke bin yarsa suna monitoring?? Kasan gidan akwai

CCTV wacce yake ganin duk zancen da kakeyi da Bilkisu???? Kaga laifin sa don ya kubutar daku daga halaka?

Muharramar ka ce da zaka na irin wadannan abubuwan?

To Alhaji Hassan ya sanar dani dalili kuwa saboda sun san nine shakikin ka ni kuma na shaida

wa mahaifina akara samun shedu kasan duk duniya maganar nan bazata taba fita ba daga bakunan mu bacin da ka jiye ma kunnen ka.

...... Ya juya zai bar dakin cikin bacin Rai Anwar din ya riko hannun sa da sauri, sadeeq din yace good cikin zuciya saboda ya

yi hargagin ne don ya nutsar dashi.

Ya dawo dashi a hankali duk jikin sa ya mutu ya ce zo zauna sadeeq.... Bazan zauna ba Ina ce ni munafukin ka ne ba Amini ba ..... Kayi hakuri I regret it.... Kayi hakuri.... Shima sadeeq din duk jikin sa yayi sanyi ya

dawo ya zauna.

Sadeeq meye shawara?

Ya kalleshi kamar zaiyi kuka.... Kayi hakuri Anwar I know how you feel about this...... Forget about my feelings please what shall I do????

Shawara daya ce Anwar pretend as you don't know. Ka nuna Sam baka sani b

a..... Zanyi haka saboda Zan tayar ma Bilkisu da hankali.... Ai anyi shawarar ita a sanar da ita saboda ta kiyaye sharuddan Aure...... Ya dafe Kai tare da runtse ido to ni me yasa basa so na sani?????? ...... Saboda rawar kanka. Sadeeq ya fada Kai tsaye...

.. Zan basu mamaki sadeeq.... Wallahi Zan nuna masu how true I love 'yarsu........ Alhamdulillah sadeeq ya fada tare da janyo Shi ya rungume Shi.....

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login