Showing 57001 words to 60000 words out of 94923 words
are my personal person am sure you'll do it.... Bazan yi ba.
Naji bazakiyi ba shikenan Amma gobe zanci indomie ko?
Eh, amma daga ita karka Kuma cewa don bazaka samu ba....
Yayi murmushi is alright!
Zan koma ciki, na gaj
i da tsayuwa....... To muje ga bench a can mu zauna akwai sakon da Zan fada Miki...... Tana son mishi gardama tana tsoron ya Kara damkar ta, ta yi Dan jimmm ya tsareta da ido...... Muje ta fada a hankali.
Kaiiii, amma fa kin bani mamaki na ji dadi sosai
ko kefa? Ai gardama bata da amfani..... Suna tafiya Yana surutai kamar ta shako wuyansa takeji.
Suna niyyar Zama wayarsa tayi Kara.
Ya dauka hello.....
Ya zauna tare da Mata nuni da hannu alamar ita ta zauna. Ta Dan raba can karshe a dosane.
Ina jinka
ya fada Kai tsaye.
Ta Dan saci kallon sa sai taga hankalin sa na ga babbar wayar sa Yana latsawa lokacin ne ta lura da iPhone 11x+ yake rikewa ta Dan zaro ido tana satar kallonsa.
Wai ita yau wannan tsadadden yaron ke bi.... Ikon Allah, Ina ma zai *FUR
TA* Yana sonta? Wallahi zata bashi amsa da gaggawa.... Har Yanzu tana wasi wasi shin da gaske friends din ya tsaya ko kuwa ita ya mayar friends???
Ko in jaraba cewa Ina sonsa?...... Tabb idan Kuma yace baya Sona hakan ya kawo karshen friendship din mu?
K
o Yanzu a tafi a Haka nasan wasu zasuyi ta misunderstanding irin su useless mufeeda.... Ko banza dai a FUDMA nabar record............ Ke kici kanki tubbb ya tofa Mata miyau... Tayi firgigi innalillahi...ta sa hijab tana gogewa... Wannan wane danyen wulakan
ci ne haka zaka tofan yawu?.... An tofa sai tsareni da ido kina kallo?
Ya harareta..... Bata San lokacin da tayi dariya ba, lallai wanzami baya son jarfa, Kai duk kallon da kakeyi mun nace me?
Eh, aini bana munafurci nake ba ke kuwa sai kin lura bana kal
lonki sai kina dan sacewa kina..... Mtseww ta doka tsoki.
Ya kyalkyace da dariya.
Ke bakya gajiya da hijab kamar matar liman?
Kai Kuma baka iya gani ka kyale???
Ya langabar da Kai don Allah gobe kisa gyale ki fito idan na zo cin indomie....... Bani da
gyale.
Anan ko?
Abuja kina sa.... Maganar ta makale ta bishi da kallo.
Abuja ma bana sawa ni hijab nake sakawa ko gida..... Dan Allah Bilkisu... Ta kalleshi Kai bana sa gyale fa.
Saboda me?
Saboda Ina kishin mijina!!!
Waye mijinki???
Mai rabo.... Ta
fada tare da Dan kallon sa....
Yayi murmushi, lallai ya more ko wanene.
Ta ce hmmmm.
Amma fa mijinki zai Sha rigima.
Ko? Ta ce tana murmushi.
Eh, Mana.
Hmmm.
Kaima matarka zata rigima..... Ni Ina da rigima???
Kwarai kuwa.
Wace iri?
Na ci, magiy
a, damuwa....Kai komai ma.
Amma Kuma I'm sweet ko?
Ta harareshi a'a chewing gum.... Ya kyalkyace da dariya.....
Tashi muje ki shiga gida idan Kika biye mun zan iya kwana haka dake ban gaji ba..... Tayi zumbur kamar tana jira.
Ya Mata kallon kasa kasa h
ar taji Yar kunya.... Ta Dan juya tana murmushi.
Kin gaji dani already ko?
Um um.
Eh Mana .
Hmmm. Tace.
Zan tura miki assignment din nan ta WhatsApp kinji ko?
Har kayi?
Yayi murmushi kawai.
Har bakin kofa ya raka ta sannan yace okay have a pleasant
sleep....
Same. Ta fada tare da shigewa......
Ta biya dakin su Aisha ta dauki key ta wuce.
Kagare take taga turarukan da yace.
Ai kuwa ta gansu don tsadaddu ne designers Kai Anwar babba ne ta fada tana juya daya Wanda yafi daukar hankalinta.
Mash
in ya hau bai Kira sadeeq ba.
Kai Yanzu ka gane firar dare ko?
Kai Kuma ka gane sa ido nonsense ya Kai mishi duka.
Allah Anwar Kai munafuki ne....... Ya kyalkyace da dariya Kai Allah ne ya fiddani da wuri ina zuwa na tarar da mufeeda ta janyo gardawa
zasu daki Bilkisu..... Ya dauki waya ya Fara nemanta.
Da gaske??? Sadeeq ya fada Yana mamaki.
Wallahi, yarinyar Bata da tarbiyya....kaga Ina Kira taki dauka gobe Zan buge Mata warning na karshe idan Kuma bata ji ba nasa a koreta ko waye ubanta.....
Anwar kabi sannu, fitina kwance take....
Sannan yarinyar nan kada ka takura Mata fa.
Naji. Ya fada Yana kokarin tube Kaya.
Washe gari ta tashi da wani ciwon ciki Mai tsanani ta kasa zuwa class.
Suleiman na ganin an Gama lecture ya kirata saboda yas
an ta dawo.... Anwar na bayansa Koda yaga yasa waya a kunne sai ya kura mishi ido yasan tabbas Bilkisu yake nema.
Hello....
Lafiya dai ko? Naji muryar kamar Mai bacci kamar Kuma wacce bata lafiya....
Ciki?, Subhanallahi..... Anwar najin haka yayi zumbur
ya mike ya ce zo muje sadeeq... Sauri yakeyi sosai, sadeeq ya fito da gudu, Ina zamu je?
Bilkisu ce Bata lafiya.... Me ya sameta?
Kamar naji Yana ambaton ciki it might be ciwon ciki... Suna zuwa bakin titi yace tare Mai napep ka taho dashi.... Ya ts
allaka da sauri.
Allah ya rufa Mata asiri akwai doguwar Riga a jikinta , Aisha na ta faman dama Mata oat ya shigo dakin..... Kanta ba kallabi gashi ya bazo a gadon bayanta ta kifa Kai a filo tana ta murkususu Aisha kuwa daga ita sai shimi.... Ya fado da
kin.... Duk suka firgita.
Aisha tayi saurin janyo bargo .
Ko kallonta baiyi ba ya zauna bakin katifar.... Ciwon ciki ke damunki? Ya fada Yana kallon Bilkisu cikin damuwa....
Firgigi ta dago tare da janyo towel dake kusa da filon ta rufe kanta.... Anwar
meye haka? Ta fada da kyar .
Ya doka tsoki. Tashi muje hospital.
Ba sai naje ba na Sha magani..... Tashi muje hospital ya fada cikin daga murya..... Ta kalli Aisha ita Daman su kawai take kallo.
Cikin ya Kara katsawa ta runtse ido tare da dukewa.... Ya
dagota da karfi ya kalli Aisha Ina hijab dinta?????.... Wayarsa tayi Kara... Ya dauka sadeeq ya?
Kana inane? Gani a bakin gidan ban ganka ba.... Okay Ina zuwa...ya kashe.
Tana son magana amma ta kasa saboda murdawar da cikin keyi ... Ya taimaka ma Aisha
suka saka Mata hijab kawai sai ya sungumeta.......
Yi sauri ki fito...ya fada Yana kokarin fita da ita.
Sadeeq ya zaro ido Wai ciki ka shiga???? Seriously tayi penting ne????
Aisha ta fito da gudu rike da kofin oat.
Sadeeq ka same mu Sima hospital ya f
ada, ya kalli Mai napep muje sima.
Suna Zama ta janye jikinta daga nashi ta dora kanta bisa kafadar Aisha.
Bai bi ta kanta ba yace Aisha meye taci ne?
Bata ci komai ba Daman haka take fama dashi..... Ciwon cikin?
Eh, tana da wani magani da take Sha ne
?
Eh, Amma dai baya lafawa da wuri.
Wane irin ciwon ciki ne Haka?
Tayi shiru kawai.
Kinji?
Ta ce hmmm, Daman duk wata sai tayi?
Bai gane ba ya kalleta duk wata Kuma?
Eh.
Mtseww...... Ya kalli Bilkisu kin taba zuwa asibiti an Miki test?
Tayi shi
ru kawai tana murkususu.
Ya Kara doka tsoki.
Ya dauki waya....hello yah good morning doctor please I have emergency patient are you.... Good. On my way...
Ya ajiye.
Ya kalleta sorry.
Aisha dai tayi zugum.
Bakin gate suka tarar da kijerar daukar marar
lafiya.
Aisha ta Fara sumke dariya.
Suna saukowa yace hau Bilkisu...... Tayi karfin halin maka mishi harara sannan ta dafa Aisha suka wuce..... Ya biyota Baki lafiya amma Baki daina gardama ba ko?
Dashi aka shiga wurin doctor.
Ka ce ya fita , ta f
ada tana kallon doctor din cikin fushi..,.. yadanyi dariya to kaji yallabai an koreka.
Wallahi ba inda zanje ka Mata test kayi scanning..... Ya Fara Mata tambayoyi.
Ta yi shiru.. akayi Justin duniya tayi magana taki.
Dole Anwar ya fita. Yana fita sadeeq
na isowa....Aisha na zaune tayi zugummm tana kallon ikon Allah.
Doctor menstrual pain ke damuna Amma bana son ya sani. Ina Shan wannan maganin amma baya mun idan akwai Wanda ya fishi pls help me...... Ya danyi murmushi I expect it.
Ya karbi maganin ta
runtse ido tare da dafe cikin lokacin da ya katsa.....
Sorry ya fada tare da mikewa..... Ya dauko wata allura yace Amma fa zata Sanya ki barci sosai, sannan ya rubuta wani magani ya ce gaskiya babu Shi anan sai Kano ko katsina Yana da tsada kwarai.... Ba
komai rubuta... Burummm ya banko kofa daidai ya Gama allurar tana murzawa. Ta dalla mishi harara.....
Doctor meye tace Yana damunta?
Yayi dariya it's normal an Mata allura ga magani nan na rubuta Yana da tsada da kudi sosai....... Ya karbe takardar Yana
karanta sunan maganin.
Ya fiddo waya..... Hello musbah ga magani Nan Zan turo maka asiyo mun carton dinsa a Aiko Yanzu Yanzu ko ka tado wani ya kawo sannan kace a fada maka maganin menene da Kuma yanda ake shansa.
Kaje wurin nagari pharmacy kace ni na A
iko kaga hamisu a wurin.......
Ya Mika mishi hannu thank you doctor.
Tashi muje.... Idan kin hada Baki da doctor wannan maganin zaisa na San komai.
Idanunta suka Fara nauyi alamar allurar ya Fara aiki.
Allaurar zata sanyata barci sosai fa.....okay.
Ya
ce Yana Shirin Kai hannu ya taba ta, ta mike da sauri tare da maka mishi harara...... Yayi dariya Kai yau Ina Shan harara ni Hamza.
Ta fito ya biyota ga oat din ki zauna Kisha Aisha Bata... Ka barshi Zan Sha a daki.. muje please.
Ya kalli Aisha allura a
kayi Mata Mai Sanya barci shine ke dibarta ga idanunta nan sun Fara canzawa da kunje kada ki yarda ta kwanta bata ci komai ba...... Ko na ajiyeta.... Ya banka mishi wani kallo. Wancen Mai napep din da na tsayar Kuma fa?
Ta kalleshi ka bi sadeeq ku taf
i mu sai muje a napep din na gode.
Kamar zaiyi gardama yayi shiru....sai Kuma ya kada Kai okay.
Idan kin tashi barcin ki mun flashing please.
Ta ce toh.
Ya zaro dubu biyu ya Mika ma driver yace mayar dasu inda ka dauko mu.
Ya Dan leka Allah ya bada la
fiya Zan kawo Miki maganin kinji ko?
Ta ce toh, tana ta faman lumshe ido..... Jinsa take har cikin ranta. Bata so ya tafi.....ashe shima hakan yakeji.......Sadeeq ya kalleshi abokin Bilkisu..... Ya Kai mishi duka. Shi Kuma ya tuntsure da dariya.....
Ta
kalli Aisha kinji yayi waya maganin da aka rubuta a kawo carton dinsa daga Kano.....ta zaro ido carton?
Wallahi....
Bilkisu Anwar ya Fara bani tsoro...Nima Aisha. Anwar Yana bani tsoro. Da na motsa sai yace mun friend.... Ke ya mayar friend wannan abun
nasa ya Fara wuce shari'a...Ni saboda ma duk na rikice can daki na bar wayar.
Aisha tayi dariya nima. Wai Kinga yanda ya wani fado kamar an jefo Shi????
Tayi tagumi tawa ta sameni Aisha......
Ta kyalkyace da dariya ai sai ma ya *FURTA* saboda tabbas An
war gabbb yake da furta Miki Yana sonki alamomi dai sun gama bayyana..... Gabanta ya Fadi ta dafe kirji..... Na shiga uku.....ta galla Mata harara *Baki sonsa?*..........
β
πΌ
*Zainab wowo*
π
ππΌπ
mowa
ππΌπ
Unex
ππΌπ‘
Alaweez
π€
*WA ZAI FURTA?*
π€
1
β£
9
β£
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo mi
ji na gari I pray*
ππΌπππ
*RUKAYYA DAN BATTA I love you so much, remember this always*
π₯°
ππ
.
***************
*Federal University dutsinma*
........ Bani da wani feelings akan Anwar he always telling me we are just friends....just
friends, so Ina tunanin all this is because he likes me as that shine kawai....... Kada ki yaudari zuciyar ki wallahi....... Kada ki rantse Anwar bashi da alkibla.
Idan Yana Sona let him say it idan Kuma bai *FURTA* ba I cannot waste my time and wait fo
r unknown..... Anwar din ne unknown...yes to me he is.
Abinda na tabbatar wa kaina shine ko naji Ina sonsa bazan taba yarda ya gane ba bare har nace Zan fada mishi..nooo! Bana iya hakan.
Dai dai sunzo kofar gida, suka sauka Aisha ta biyota da sauri gani
n ta yi saurin shigewa....... Amma saboda Allah bakya jin kin Fara son sa?
Tayi murmushi.
Um?
Aisha forget about this.... Dan Allah ki amsa ni. Ko kadan bakya jin kina sonsa?...
So!, So!.... Ta maimaita.
Suka bude daki ta fada bisa katifa..... To
Wai ya zanji idan na Fara sonsa?
Yawan tunanin sa, son ganinsa ko Jin muryar sa, komeye zai yi zakiga baya Baki haushi.... Koda kin fusata zakiji azuciya Baki Jin haushinsa, kishin sa...... Tayi Yar dariya.... Please Aisha fita Kija mun daki barcin nan
ya dameni.
Anya Bilkisu????
Anya meye?
To nidai Kisha oat din kada ki haddasa mun fitina anjima don Anwar sai ke wallahi.... Abeg go.!!
Zan fita but please Kisha.... Zan Sha Yanzu.
..........ya dafa kafadar sadeeq, kaji menstrual pain ke damun B
ilkisu.... Ka dubi girman Allah kada ka nuna Mata kasan haka zaka Bata kunya Anwar.
Ya tuntsure da dariya, to me yasa Bata boyewa Dr ba sai .....
Sai ubanwa? Shi ba Dr bane? Idan bata fada mishi rashin lafiyar ta ba zai San wane magani zai bata ne?..
.. Ikon Allah, sadeeq akan Bilkisu wata Rana kilan ka dakan ko?
Tabbas, saboda ka takura Mata da yawa fa...... Meye abin takura anan.
Na dai fada ma, wallahi kada ka nuna kasan me ke damunta zata ji babu dadi... Kai nafi so ta Saba da Hali na tun Yanz...
. Maganar ta makale da alama yayi *Subul da baka*.
Hahahahahahahaha, finally..... Ya galla mishi harara finally what?
Nothing forget...ya fada Yana dariya.
*Sixtus* ya shigo kunji anyi closing school till further notice?????
Sadeeq ya kalleshi saboda m
e?
Corona virus...... Anwar yace hazbunallah are you serious?
Of course. Ya fada.
Anwar yayi saurin daukar waya ya Kira academic secretary.... Ya tabbatar mishi....
Ya kalleshi sadeeq is true.
Ya zaro ido Nawaoooo..... ya zanyi da yarinyar nan sadeeq?
?
Kamar ya?
Sai yayi shiru..... Ya kura mishi ido huh?
Mtsew ya buga tsoki ya fita waje.... Ya bishi da ido Yana murmushi, saboda ya gano inda zancen sa ya dosa.
Abinda ya tayar mishi da hankali ganin student nata parking ana buga ma wadanda Basu da
wo ba akan su yi zamansu.....
Ya Kira number Bilkisu gashi tana ringing Amma Bata dauka ba, saboda barci ta sanyata silent mode da alama ta sami yin barci.
Aisha ta Kyaleta har kusan karfe shidda ta wuni zungur tana barci... Ko da ta tashi wata azabab
biyar yunwa ce ta tashe ta, ga mamakin ta taga Yar cooler kusa da katifar, tana budawa taga kuskus da miyar Dankalin turawa, tayi murmushi Allah sarki Aisha.
Sai da taci nayi nat! Sannan ta shiga wanka ..... Tana cikin saka riga Aisha ta shigo, kin tashi?
Ta fada tana murmushi, ta mayar mata da murmushin ta nuna Mata cooler da Baki tace Kinga alama can..... Sai duk sukayi dariya.
Yunwa ta tasheni, wallahi kin taimaka..... Ai kin shaa barci, Ni kuwa nasan haka na farka naga 23 missed calls..... Tabbb.
Ki
n kirasu ko?
Mommy kadai na Kira sauran sa nemeni idan ya damesuuu......wayar ta Fara kugi duk suka kalli juna.
Ta nufi wayar, ta Dan kalli Aisha *Anwar* ne.... Tayi Yar dariya Ina zuwa , ta juya tabar dakin....
Assalamu alaikum,
Kin tashi kenann....
Amsa sallama wajibi ne malam..... Wa'alaiki assalam. Sai me Kuma? Tayi Yar dariya, Ina wuni?
Ya kike ya jiki?
Alhamdulillah.
Cikin ya daina ciwo ko kina ji har Yanzu?
Bana ji da sauki sosai.
Zan kawo Miki maganin anjima kinji ko?
Ka bada akawo mun Ma
na ..... Saboda bakya son ganina?
Ba haka bane.
Haka ne Mana . Ba maganin kadai Zan kawo ba ai Ina son duba jikin ki ne...
Shikenan sai kazo.
Zaki iya dafan indomie din????
Innalillahi kaii Anwar fitina ne wallahi.... Nine fitina Bilkisu.????
Ta zar
o ido kayi hakuri wallahi maganar zuci ce ta fito....... Da kyau Ashe a fili kike nunan ba wani abu kina can kina zagina cikin Rai ko?
A'a wallahi....eh Mana. Gashi kin kirani da fitina....Dan Allah kayi hakuri.
Bazanyi ba.... Ya Fara fada kamar da gask
e Yana son yaga how much she care about him ... Kina da fuska biyu kenan Bilkisu? Watau a fuska kike nuna mun .....Anwar kayi hakuri.... Bazanyi ba nace.
Ba zakayi hakurin ba?
Gabansa ya Fadi ya tuna fadan su na baya..... Yayi saurin cewa zanyi amma ba Y
anzu ba .
Sai yaushe?
Sai nazo anjima kin kalleni kin bani hakurin da gaske..... Tayi Yar dariya wannan na karya ne?
Da alama. Ya fada.
Shikenan sai kazo. Ya kake son indomie din?
Ki barshi kawai bana ci.
Dan Allah kayi hakuri..... Na ce ban hakura b
a?
To ka fada mun yanda kake son indomie din kasan kowa da yanda yake son dahuwar indomie.....kiyi mun yarda ki ke dafawa idan zakici... Karfe nawa zaka zo?
Eight, ya fada Yana Yar dariya ko nayi latti?
Ta Dan harari wayar kamar Yana kallonta kawai tayi
shiru..
Kinyi shiru kina ta Duran zagi a zuciya ko?..... Kaiii Anwar.
Eh Mana.
A'a wallahi.
To fadan da kikayi shiru me zuciyarki ta saka Miki?
Ta kyalkyace da dariya kaiii nikam na bani ..... Yayi murmushi.
Ke