Showing 45001 words to 48000 words out of 94923 words
/>
Ya dago Kai, kirjinta ya buga duk ya wani gigice yayi kicin
kicin da rai, ya sunan Wanda Zaki aura?
Ta kalleshi........ Wai shine abinda ya sanyaka damuwa......
Ya Mata wani kallo dole ta kawar da Kai saboda ta tsani kallon banza da rainin wayau.......
Akan meye zai dameni?
Tayi murmushi to naga ka chanza lokac
i guda.......
Kaina ne yake mun ciwo.
Ga tsarabar.....ta Mika mishi ledar.
Ya juya ajiye wurin ki Zan karba......
Wallahi bai yiwuwa. Ina ce shine dalilin biyo ni.
Ya kalleta nace ki ajiye Kuma bana bukata.......
Ta tari gaban sa da sauri Wai me ya
faru?
Bani wuri in wuce please.
Wallahi baka tafiya sai ka fada mun me ya Bata maka Rai....... ( Cikin zuciya kuwa sai dadi takeji watau Anwar ita yake so yake ta gewaye gewaye. )
Ya kalleta sai ya koma jikin bango ya harde hannuwa ya sokar da Kai .
Kai nake sauraro ta rike kugu.....ya yi shiru.
Ta Fara magana cikin fada fada.
Kace in nemo maka matar Aure na zabar maka ni Kuma bani da ikon da Zan ce Ina da Wanda nake so......... Ke ! Ya daka Mata tsawa.... Na ce kada kiso wani?
Tayi baya da sauri,
cikin razana. Ya matso kusa da ita, da kiso wani da ki tsaya haka bai Dame ni ba, I have nothing to do with that, and it doesn't make any difference to me....... ikon Allah ta fada.
Kamar Yana jiranta?
Cikin bacin Rai ta kalleshi, Ni ya dameni ne? Ko mu
feeda Shi yasa da ta tare ni tamun rashin wayau na Bari sai a gabanka na Mata warning... saboda bana tsoron ka baka gaba na..... Damko kafadunta yayi da hannu biyu ya buga bayanta da bango....... Wallahi tallahi idan Kika Kara........kwallah suka zubo Mat
a sharrrr ta fashe ta runtse ido.
Allah yaso duk ba a dawo sosai ba, kofar gidan ba kowa.
Ya runtse ido da karfi ya saketa a hankali......
Ta yunkura zata ruga gida ya tare ta da hannu idan Baki so in Kara taba ki kada ki motsa...... Ta fashe da kuka...
. Hankalin sa yayi kololuwar tashi...... Bai San ya Fadi *Na shiga uku ba*
Bilkisu...... Tasa hannu ta toshe kunnuwanta....
Kiyi hakuri Dan Allah na gwadaki ne kawai.
Ganin yadan matsa baya ta yunkura zata Kara guduwa ya kuwa kamota da karfi ......
. Yaya Zan ta Miki magana Baki ganewa? Nace idan Baki so na Kara taba ki kada kice Zaki gudu ko daman kina son hakan ne?
Ya fada cikin tsawa.
Ta Kara rushewa da karfi....na tsane ka wallahi bana son ganin ka , ka kyaleni.
Har cikin kasan zuciya yaji mag
anar. Ya daure yace ....naji kin tsaneni, kiyi hakuri nayi kuskure bazan Kara ba.....wasa nakeyi.
Nima ai da wasa nakeyi ka Fara .......wasa kikeyi ba a Miki miji ba?
Ta mishi banza...... Saura kadan ya Kara kamota don ya rungume ya saki wani murmushi: n
asan wasa kikeyi Nima. Kawai Ina son ganin fushin ki ne don Shi kadai nayi missing cikin hutu.......kiyi hakuri I'm sorry ya rike kunnuwa.
Kinji?
Dan Allah kiyi hakuri wallahi bazan Kara ba....
Ta goge hawayen da kasan hijab dinta. Kawai tayi shiru kant
a a kasa.
Baki da wahalar yin kuka meye na kuka anan Bilkisu....kina da shagwaba ko?.
Um? Baki magana?
Yau ni Kuma tawa ta sameni an Kara yin fushi Dani...... Dan Allah kiyi hakuri kinji.
Bani tsarabar ya Mika hannu........ Ta maida duka hannuwanta
baya ta boye ledar har lokacin Bata dago Kai ba .
Ba zaki bayar ba?, Zan Kara taba ki wallahi don Zan karba da karfi kibani da arziki kawai....
Zan ajiye sai lokacin da ka nema....
Yanzu na nema saboda haka bani....ya Kara Mika Mata hannu.
Yasa hannu zai janyo hannayenta tayi saurin fiddowa ta Mika mishi. Ta kalleshi Rai bace idan ka Kara gigin taba ni wallahi zakayi Dana sani....... Ya karba Yana murmushi naji bazan Kara ba.
Mun shirya ko?
Ya fada Yana kallonta.
Kinji?
Mun shirya?
Ba z
akiyi magana ba?I prefer kiyi mun masifa da wannan shirun fa.
Bani da wannan lokacin......
Me yasa kike da wuyar lallashi haka?
Kai Kuma ka fiye naci ko?
Ya yi Yar dariya. Wallahi naci gareni tabbas ko zamu kwana anan sai kince mun shirya sannan kinyi
dariya.
Matukar babu wadannan wallahi kinji na rantse a nan zamu kwana.
Idan Kuma kikayi kokarin guduwa Zan rikeki a hannu na bazan sakeki ba har sai na tashi tafiya, idan Kuma kika Sami damar shiga gida da gudun nan naki binki zanyi har ciki in kamo ki.
....... Na shiga uku ni Bilkisu akan meye Wai wannan dokokin????
Ya Kara Yar dariya, akan Ina so mu shirya kada mu Bata.... Na ce mun Bata ne? Ko kaji nace nayi fushi?
Au haba? Wai babu ko daya ciki?.... Ta harareshi kawai.
Ya Kara Yar dariya, shikenan.
Maganar lecture, wannan semester din idan na saki na ganki da Suleiman na rantse da Allah zan dauki mataki akansa........ A wane dalili?
Very good question ya gyara tsayuwa....
Na farko ni nake koya Miki karuwa ba Shi ba, na biyu ko Kun zauna a jar
abawa ke kike bashi amsa bashi ne ke Baki ba, na uku.....idan ba zaman class din ba ka taba zuwa ka ganshi anan?
Ta rike kugu akan wane dalili zaka Sanya mishi doka akaina?
Na taba hanaka tsayuwa ko magana da ajabon Yan matanka?.
Ya kyalkyace da dariya
Yan matan nawa ne ajebo?
Tayi shiru,
To ki ci gaba da kulashi kiga idan bai bace ba bat!
Ta danyi dariya ........ Ya kura Mata ido, lallai mun shirya. Ya daga hannu sama Alhamdulillah!........ Wayarsa ta yi Kara akayi ta Kira yaki dauka....
Kina ganin
wasa ko?
Allah sanyawa zanyi ayi kuku dashi....... Matsayinka naa???
Ta tsareshi da ido, matsayin abokin Bilkisu Wanda bai son kowa ya rabe ta....... Maganar ta makale da alama ya kusa yin *subul da baka*.
Shima abokina nane kamar ka nafi sakewa dashi f
iye dakai saboda bashi da fada ko kadan ni Kuma na tsani fada rayuwata wannan abotar da kyar zatayi lasting.....
Ya zaro ido da gaske kikeyi ko wasa?
Tayi shiru tana murmushi,
Ke!, Dago Kai ki kalleni ki Kuma maimaita abinda Kika ce Ni da Suleiman duk
matsayin mu daya?.......
Ta Dora hannu bisa Kai *wallahi idan akwai abinda ya fi shiga uku a yau to cikin sa nake*.... Dan Allah Anwar kabar ni haka nan na gaji yunwa nakeji har an kusa Kiran sallah.......
Zan dawo anjima.....
Basai ka dawo ba zamuyi ma
gana ko ta waya ne....... Zan dawo da karfe 8 idan Baki fito ba Zan shiga har ciki in fiddo ki.....
Ta bude Baki, sannan ta tsuke fuska, nifa bana fitowa da dare na Kuma fada maka tun last semester.
Na fi kowa sanin haka sai nidin Anwar ne dole ki fito
saboda....... Maganar ta makale. Ita Kuma ta tattara hankalinta kaf akansa......
Yayi murmushi, kije ciki sai na dawo anjima.......
***************
*KADUNA RIGASA*
Tayi turus, duk sukayi tsuru tsuru ba kamar Shi guiltiness ya kamashi........
Ta kakaro murmushi Wanda yafi kuka ciwo kafin tace .... Ohhh sorry ta juya yayi Kiran duniya amma Bata dawo ba,
Ya saki Amira da sauri yabi bayanta Nan da Nan kishi ya turnuke ta itama.....hawaye suka shatato Mata sharrrr.β¦...
β
πΌ
β
πΌπ
*Zainab Dahiru wowo
* ce
π
Ayi hakuri da kadan
π€
*WA ZAI FURTA?*
π€
1
β£
5
β£
*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*
*****************
*Federal University dutsinma*
Anwar din nan ya mayar dani sakarai. Shi girman Kai ya hana ya fito yace Yana Sona shine yake ta gewaye gewaye, bai San h
alina ba, a dole yanda banzayen Yan matansa ke zubda class suna crushing din sa nima haka yakeso nayi..... Ba dai Bilkisu ba, ko Zan mutu bazan ce Ina son sa ba.
Zan daure na cije na nuna mishi ban San inda ya dosa ba inaga idan yaji uwar Bari *Zai furta*
.
Ya fada bisa gado...... Ya kalli sama .
Sadeeq ya kalleshi an dawo fa!
Baka ga missed calls Dina ba?
Ina so ince ka amso Mana abinci *M&M*...... Abdul din fa ya daina dafa indomie ne?
Kai ubanka da indomie din Nan, Wai me yasa kake son gana M
ana azaba?......
Ya kyalkyace da dariya azabace cin indomie?
Nifa bazanje wani *M&M* ba kawai muyi normal life na student kada mu banbanta...... Ubanwa yace to baka sai Mana gida ba ka kawo mu hostel?
Ya Kara murmushi....ba za ka gane ba..
Ban ganewa
wallahi....
Ranar da aka ganoka tabbas ka shiga uku.....in shaa Allah har na gama babu wanda zai sani,
Ya bude ledar da Bilkisu ta bashi kamshi ya doki hancin sa, rantsattsen agogo ne Mai tsada cikin cover....... Kai ya tashi zaune.
Menene?
Bilkisu ta
siya mun agogo wallahi.
Ya fada Yana daga Shi sama.......
Hmmm, wannan babbar kyauta ce, ka daina cinyewa Yar mutane kudi fa.
Yayi murmushi ya cire na hannunsa ya mayar da nata.......
Anwar a fidda maganar wasa ka dubi girman Allah ka sai Mana gid
a ko ka Kama Mana haya mubar wannan kwamachalar......
So kakeyi nayi ma wata ciki..... Ya zaro ido.
Yes! Bari na fito maka a mutum sak!
Dan ubanka yanda Yan matan nan ke kawo man hari kana tunanin idan na ware baxasu bini daki ba? Ko ni katako ne da Za
n ga mace daga ni sai ita na....... Shikenan, ai shikenan next year by now mun Fara bankwana ma.
Wayarsa tayi Kara ya dauka....... Ya Dan kalli sadeeq buga mun sixteen million times 42 please..........
Bayan ya ajiye sadeeq ya hado musu oat suka Sha s
annan suka tafi masallaci.
Akan hanyar su ta dawowa yace sadeeq Ina son ka Sami Suleiman kace kada na Kara ganin sa da Bilkisu....... Dalili?
Ya katseshi.
Haka Nan.....
Zancen banza kenan, haka kawai sai ka raba su babu dalili?
Yaron banza ne bana
son sa.....kada ka tsani Dan mutane. Kowa yasan Shi mutumen arziki ne idan kana da wata hujja ka fiddo kafin ka yanke zumunci.
Kana ganin wasa nake ko?
Wallahi semester din nan takunkumi Zan sakawa Bilkisu akan Shi saboda Shi kadai take kulawa yaron Y
ana da mugun shisshigi.
Anwar! Anwar!! ..... Idan son yarinyar nan kakeyi........ Wai Kai me yasa baka ganewa? Dole sai Ina son ta Zan Sanya doka akanta????
Ni Sona takeyi da take Sanya mun doka inabi?
Ko kasan yarinyar nan juyani takeyi kamar waina?(
Masa ).
Kuna dai juya juna.
Kuma duk laifinka ne, ka zauna wurin kallon ruwa kwado yayi ma.....
Sadeeq Banda wani personal business da yarinyar nan da ya wuce friend, kawai bana son tana kula Suleiman period.
Mtseew to ka jaraba ai Bilkisun ba bakuwar
ka bace na tabbatar akan Suleiman tana iya kyaleka kwata kwata...... Da gaske? Ya zaro ido.
Lallai dole naci uban yaron nan.
Sadeeq ya tuntsure da dariya, Allah gamu fareka.... Sai ka maida hankali toh.
Kai da Bilkisun duk munafukai ne kowa Yana fama
da ciwo ya gwammace ya mutu da ya fitar da cutar......
Kamar ya?
Kai ba bahaushe bane?
Ya doka tsoki....... inyamiri ne ni.
Yaushe Anas yace zai dawo?
Sunday.
Ai Kaine ka kwaso mu badon na shirya ba wlhi.
To ya zanyi?
Ya kalleshi ya zakayi? W
ani ya tilasta maka?
Ya kada kafada tare da watsa hannu yace ko daya.
Zaku kaisu idan Kaya ne.
Ina tausaya maka ranar da wani zai maka shigar kutse......
Ku bakwa ganewa, yarinyar nan tana Sona fiye da duk wata yarinya da ke hauka a school din nan,
na rasa girman Kan da ya ke hanata *FURTAWA*....... Kai ba sai ka *FURTA* ba?
Mtsew....your are not well.
Ya kwanta bisa gado, ka dafa Mana shinkafa muci da miyar can Mana.yayi murmushi ka canza maganar Kuma? Toh
Yanzu kuwa ya Fara Shirin aiki.
Ya janyo waya ya Kira Bilkisu,
Tana kokarin fere doya Aisha na warming Miya daga gefe Kiran ya shigo,
Ta ce hmm sannan ta daga .....
Hello, Ina wuni......
Ya lumshe ido Yana son gaisuwar ta yarinyar nan nada da'a sosai.
Lafiya, ya kike?
Qalau.
Ke
da waye nake Jin motsi?
Aisha,
Kuna meye?
Girki.
Me ye ne ?
Kai ai da gangan akai tamabayo......
Doya da Miya.
Zanci.....
Aikuwa baka cinsa sarkin roko....... Ya tuntsure da dariya har Yana sarkewa da miyau.... Aisha ta kura Mata ido tana kallonta.
Keda waye?
Ta bude Baki ta Mata alamar Anwar ne ba tare da sautin ya fito ba.
Rowa Zaki mun?
An maka........
Shikenan. Ki shirya anjima zamu je na siya Miki wani Abu cikin kudin Dana tara ko kuwa?
Ka dai ka siyo ka kawon ba sai munje tare ba.
Saboda
me?
Haka Nan.
Karya kikeyi ba Kya son samarinki su ganki Dani........ Sadeeq ya kalleshi Kai da wa??????
Harar sa kawai yayi.
Kinji?
Ni nakeyin karya?
Eh, ko gaskiya Kika fada?
Kai Ni ban iya abinda ka iya ba..... Meye na iya Wanda Baki iya ba?
Ne
man magana...... Ina mamakin yanda ake cewa baka magana kana da jiji da Kai amma Ni wallahi nace surutu gareka ga roko....... Ya Kara yin dariya.... Ke Kuma rowa gareki ko?
Rowar me?
Meye ka ce na baka na Hana?
Abinci.
Mtsew...tayi murmushi badai zance
kazo kaci ba .
Muma ga sadeeq na dafa Mana shinkafa Mai dadi Ni na kawo Miki?..... Na koshi aci lafiya.
Allah kuwa..... Bana ci na gode malam .
Kai lazy baka dahuwa sai an dafa an baka ko?
Inji waye? Nafi sadeeq iya girki ko kina musu?
Eh.
In dafo
in kawo Miki Zaki ci?
Noooo, ta fada da sauri. Yayi murmushi yarinyar da kinji akul.
Ta ce hmm.
Zan zo anjima kinji ko?
Okay.
Ki gaishe mun da Aishar Bari na dauki wata waya...... Ya katse Kiran.
Ta kalli Aisha Anwar case ne.
......... Gaskiya ai Ya
na bala'in yinki. Anwar Dan gadara Shi yake Kiran mace kinji yanda ake surutun miskilancin sa kuwa?
Inaji amma nake ga kamar hada Sheri..... Wallahi da gaske ne.
Yan matan ne basu da zuciya. Kinga wulakancin da ya ringa yi ma khausar har kuka take mishi
.... Jakka kuwa ki Sami fareeda yarinyar nan Bata da zuciya wallahi..... Ke Aisha namiji munafuki ne kedai baki sani ba ko Yana gewaye wa.
Last semester gab da za ayi hutu da yazo cewa yayi zance ya fito ya biyo wurina Kuma kema kinsan kilan bai wuce mufe
eda ko wannan dayar banzar Yar aji hudu.
Hmmm, kawai Aisha tace.
Salim bai dawo ba Ina Zan Sami aron mashin?
Sadeeq ya Fara maka mishi uwar harara ai taurin Kai da wulakanci ya Hana ka siya Mana sai kaje ka hau kabu kabu......... Wohohoho..... Wai
nawa mashin din yake in siya a huta?
150-200k wannan range din.
Mtsew...... Ka shirya gobe ka shiga katsina ka siyo Mana...... Ya buga ihu.
Ya shako wuyansa..... Koda wasa ka nuna inada alaka da hakan ubanka zanci..... Bazan fada ba cika ni mugu......
Ya wuce har ya Kai bakin kofa ya waigo wane police station ne DPO ke Zama a garin Nan??....... Ya zaro ido DPO? Lafiya meye zakayo wurin DPO?
Zan sa ya ma Dr Dan Musa warning da Suleiman akan Bilkisu.......... Wata muguwar dariya ya saki munafuki karsh
en tuka tika tik... Yanzu ka *FURTA* mun abinda nake son...... Dawowa yayi zai Kara shako Shi yayi bisa gado.... Allah ya baka hakuri.
Amma Ina baka shawara zaka tona asirinka a banza saboda zasu so sanin wanene....inji waye?
Ba zai fada ba. *This is le
gal warning* ...... Ya fice da sauri Yana duba agogo.
Ya daga murya inzo in raka ka??....... Da ga can waje yajiyo Yana surfa mishi zagi.
Yana sauka achaba Aisha na zuwa zata tsallaka titi..... Aisha. Ya Kira sunan ta.
Laaa Anwar Barka da dare an da
wo lafiya?
Qalau, je Kira mun Bilkisu..... Tayi jimmm sannan ta ce toh ta juya Shi Kuma yayi tsaye maimakon yabi bayanta.
Tana tafe tana masifa, je Kira mun Bilkisu kamar wata barar sa..mtsew. Haushi na da Shi Sam bai da manner of speaking Yana magana a
gadarance da Isa na tsani wannan wulakancin wallahi.
Tana wankin toilet ta shigo.... Kizo inji Anwar.
Ta dafe kirji...kin ban tsoro wallahi.
Ta harareta kawai zata juya..... Aisha Wai ya akayi?
....... Pad Zan jarbo Ina sauri ya ganni kawai ba wata
magana Wai *je Kiran Bilkisu* irin yarinyar nan wacce ya ajiye....
Kiyi hakuri kin dai San Hali...... Eh amma ki ringa kwatanta mishi wata rana Zan yankwana Shi..... Kiyi hakuri dai, jira mu fita tare Dan Allah. Idan mun Gama Zan rakaki..... Wai injira ki
wurin sa?
Baki da hankali wallahi idan yamun wani dizgin inyi Yaya dashi?,
Bazaiyi ba, idan ya ganmu tare bazai...... Wallahi bazan je ba. Kina tare da Anwar seems like you don't know him ko? Mtsew taja guntun tsoki ta fice abinta.
Ikon Allah. Kai An
war nikam tawa ta sameni........ A yanda yayi rantsuwa