Showing 18001 words to 21000 words out of 94923 words

Chapter 7 - WA ZAI FURTA complete

04 Sep 2026

6

mutane magana, na biyu, ka ringa yarda ana hada ido da Kai sai kayi Dan murmushi.......wata muguwar dariya ya saki har Yana buga kafa kasa.

Yarinyar nan wallahi kin rainani da yawa. Watan kaman wani karamin yaro ko?

Suka ci gaba da tafiya.

Nid

ai na fada maka.

To naji, sai Kuma me?

............. Shegen gora, wallahi daman sai da Anas yace tare da Bilkisu kake wannan ihun.

Dukkan su suka juya, sadeeq ne da Anas.

Yawwa sadeeq Allah ya kawoka zo ka taya ni yi mishi fada.......duk suka zaro ido

fada Kuma? Ai wannan mugun dan daba ne wallahi yafi karfin mu.

Au baku fada mishi gaskiya kenan?

Kedai jaraba....suka ce tare da wucewa suna Yar dariya.

Shi kuwa sai hararar su yakeyi.

Ta rike baki....ohh, watan Kai kowa tsoron ka yakeyi......Banda ke,

Hmmm,ai wallahi koni ma ta Kara sauri sai anjima kaga tafiyata.

Shima ya Kara sauri Ina zakije Ina Jin yunwa muje ki siya mun abinci tunda kin Fara dandana mun.....eh lallai yi kokari ka cinye Yan pocket money din ta fada tana hararar sa.

Ba Shi kenan

ba mun koma 1/1 kenan..... Amma muje Zan jira ki dafo mun indomie....ta zaro ido, Kai rufan asiri koma kada ma ka janyo mun surutai ace .......kin Fara yawo da Dan iska?

Ko kin Fara zuwa da Dan iska kofar gida......na tuba, ba haka nake nufi ba, inba haka

kike nufi ba sai ki zabi daya, ko ki dafon indomie ko muje ki siya mun suya ko kaza ko chips......ta kyalkyace da dariya watan sai ma ka zaba,

Ka jira anan naje na fito da kudin nan Babu a jaka, muje na ranta miki gobe ki fito mun da kudi.

Ikon Allah k

amar cin rabo?

Eh, ai nasan karamin aikin ki ne idan kin shiga inji shiru kinki fitowa.

Mtseww......au abinda kasa ma ranka kenan.....ke mufa juya wallahi bazaki shiga gida ba.

Haka ta juya badon ranta yaso ba suka je shagon Alhaji Hari, ta kalleshi zab

i abinda kakeso toh.

Ya koma gefe zabo mun dai ni wace gareni tunda kawoni akayi?

Kamar ta nutse kasa don kunya shagon cike mutane an musu ratai da ido. Kowa yasan Anwar Kuma Mai shagon yasan wanene Shi mamaki kawai yakeyi yau shine tare da mace?

Ta Sha

mur Alhaji bani meat pie hudu, Pepsi biyu, shortbread biscuit din can manya biyu.....gaban Anwar ya Fadi Jin kayan tsadar da take lafto mishi Amma da ya tuna Shi zai biya kudin sai ya kyaleta.

Leda bammm aka cika. Ya mata totalling dubu hudu da dari shid

da....... Ta bude jaka ta fiddo ATM Daman Yana da *POS* tace fidda kudin pls.

Ba karamin faduwa gaban Anwar yayi ba.

Ya rasa yanda zaiyi duk yaji wani iri.

Ta fito niki niki da leda oya muje ta fada tana hararar sa.

Ya sunne Yana Yar dariya.

Dan mas

hin ta tsaida mishi sannan ta kalleshi Yanzu ka shafan lafiya ka tafi ko?

Ya kyalkyace da dariya korata kikeyi?

Eh, ka isheni...go!

Wannan karon dariya sosai yayi, shikenan ba damuwa.

Zaki Kuma nemane ai.

Ta Mika mishi ledar bayan ya zauna kaci yau ka

ci gobe acici.

Wannan lokacin tare sukayi dariya.

Ta wuce tabarsu anan.

Tana niyyar tsallakawa titi ne suka suka zo zasu wuce yace: *A ringa duba titi*

Ta mishi murmushi kawai tare da daga hannu.

Haka kawai ta tsinci kanta cikin wani irin matsanan cin

farin ciki,

Shi kuwa Anwar gaba daya ya kasa fassara yanayin da yake ciki haka kawai fuskar sa ta kasa daina guntuwar dariyar da yakeyi lokacin da suka daga ma juna hannu.

Anas ya rabka salati......Wai da gaske Bilkisu ta maka shopping yau ma?

Murmus

hi kawai yayi,

Sadeeq ya Kai mishi duka, munafuki kwa gama sumke sunken ku bayyana kanku, Daman na lura ka Fara tsanar Suleiman simply don Yana tare da ita, Kiri kiri dazun ka hanashi amsa wallahi baka kyauta ba Anwar........suka dunga mishi surutai ya mu

su banza miskilin bai dai ce kunyi gaskiya ba bai Kuma karyata su ba.

Duk abinda Bilkisu Bata so Yanzu kafa biyu Anwar gudun sa yakeyi.

Ba Wai ajin nasu kadai ba har takai aji daya ma nemansa sukeyi don ya koya musu.

Maimakon hakan yayi wa Bilkis

un dadi sai ya kasance kullum cikin fada da rigima sukeyi musamman idan ta ganshi tsundum cikin mata sun saka Shi tsakiya kamar tayi hauka sai su kwana biyu uku Bata mishi magana ba Shi Kuma ya rasa dalili.

Idan kuwa ya kuskure ya dauki hoto da wasu to

sai sun kusa sati bai sanyata ido ba, ko lecture sai dai tasa a mata attendance.

Ya rasa inda zai saka kansa.

Taki yarda suyi magana daya nemeta sai ta zille,

Yan mata sunyo mishi chaaaaaa har Yan wasu department ashe daman ko wace ta ciki na ciki ras

hin bada fuska ne.

Hakan ya Kara harzuka Bilkisu Jin kowa Anwar .... Anwar.

Gashi ta riga ta Saba da bayanin sa, duk Wanda zai mata sai dai ya Gama babatunsa Amma Sam Bata fahimta.

Shi kansa yana bala'in son koya mata.

Ranar Alhamis ana fitowa lecture

tana kokarin fita ya tare kofa ya maida ya kulle.......gaba daya ajin akayo masu chaaaaaa da ido.

Kamar ta bude kasa ta shige don kunya.....ke me na Miki kike fushi Dani?, Na gaji da fadan hakanan wallahi mu shirya.......Dan Allah bani wuri in wuce ji yan

da kasa ake kallona.

Duk wannan mazuran naki yau bazasuyi tasiri ba sai kin fada mun Yanzu Kuma laifin me nayi naga abun naki Dada hauhawa yakeyi.

Ta kalleshi sama da kasa , sai naji zafin makara tukun ta ja kofar da karfi ta fice ya bita a fusace saboda

yaji haushin abinda tayi...

Wai Bilkisu me na Miki haka? Ko kin gaji dani ne kina son in Baki wuri in kyaleki?

Yau kusan kwana uku Ina kokarin kizo muyi karatu kina zillewa.......ta dallo mishi manyan idanun ta, yaushe kake da wannan lokacin?

Ai Yanzu

mutane sun Fara maka yawa batani kake ba......Nan da Nan ya sauko zuciyarsa tayi sanyi kalau sauran kadan dariya ma ta kubce mishi Wai yarinyar nan badai kishi ke damunta ba?

Ya tari gabanta.....jira muyi magana daina tafiya.

Wallahi tallahi Ina da loka

cin ki, basune suke zuwa na koya musu ba?

Ke kuwa nemanki nakeyi ko ranar Monday nace ki jira Ina son ganin ki kawai Kika gudu Kuma kece kemun fadan Ina sharesu da farko Yanzu kulawar ce zata haddasa Mana matsala?

Gabanta ya Fadi kada fa ya mata fassara.

Ta Fara in..in..in.

Bude Baki kiyi magana. Idan har Baki son in koya ma kowa wallahi daga yau na daina.

Ni Yanzu Kika ce Babu ruwan ki Dani Bilkisu ai na shiga uku waye zai ringa siya mun kayan dadi?

Bata San lokacin da ta yi dariya ba.

Shima dariyar

yayi...kiyi hakuri na tuba bazan Kara ba. Daga Yanzu matukar kina son time dina ko wane lokaci ne Zan baki Ina ce Daman shine damuwar ko?

Ta Dan zumburo Baki eh.

Yayi murmushi, Zan kiyaye. Yanzu Ina zakije?

Daki.

Karatun fa?

Tayi shiru,

Kinji?

Ko h

ar Yanzu Baki huce ba?.....

Kai Dan Allah. Ta fada tana Yar dariya.

To muje muyi ko sai anjima?

Eh,

Da karfe nawa?

Hudu.

Yanzu meye zakiyi idan kinje dakin?

Girki.

To zanci. Kizo mun dashi 4 din.

Okay.

In rakaki ko in kyaleki?

Kyaleni kada ka ja

nyo mun duka gun Yan......maganar ta makale.

Ya zaro ido gun wa? Karasa Mana.

Tayi Yar dariya kawai, ya kuwa bita da kallo har tayi nisa........ Kyaleta hakanan tunda tayi nisa maye. Sadeeq ya gani gabansa.

Ya dunkule hannu zai Kai mishi duka ya goje.

Zanci ubanka ne, na gaji da wannan sa idon naka Kuma da alama kaman Bilkisu kawai kake man wannan shisshigin.

Kai mugu ai na lura kwana biyu baka da sukuni saboda ta Fara daina kulaka.

Mtsew you are not well, ya fada tare da barinshi wurin tsaye .



**************

*KADUNA RIGASA*

Ya Fara dukan kofar kamar mahaukaci, Amira Ni Zaki rufewa kofa?

Naje na rufe, Daman baka shirya ma irin wannan ranar ba da mace zata hanaka barci ka karo auren?

Idan laifi kayi mata sai ka koma ka Bata hakuri ku s

asanta da matar ka...idan kuma ita ce ke da laifi sai ka koyi yanda ake hukunta mace dai dai laifinta ba ka kaurace mata ba.

Kaine ka kawo dokar Banda raba kwana Koda za'ayi soke soken wuka...au fadan na maganganu ka kasa dauka har Kaine yau zaka karya d

okar ka da kanka?.......Amira ki dubi girman Allah ki buden kofa zuciyata na iya bugawa......

Wallahi bazan bude ba saboda hakan haramun ne a wurin ka dani.

Ka koma can dakin matar ka.....watan idan ana dadi zanji shiru sai ta baci .......kada kishi ya j

anyo kiyi mun butulci.

Butulci ai Kai ne kayi mun tunda har ka iya hango wata bayan ni.......kasa daurewa yayi yabar gidan a fusace.........Ya duba agogo karfe Sha daya saura, ya kuwa Danna Kira......

Bugu biyu ya dauka.

Hello Abokina ya?

Kazo gidana

Yanzu Ina nemanka, Ummi na bani matsala mukhtar.

Gabansa ya Fadi yasan a rina, ko a gida Ummi bata da kunya ta Raina kowa.

Cikin mintuna Sha shidda ya karaso.

A waje ya tareshi saboda tun fitar sa zuwa gidan Amira itama ta garkame side din nasa.

Tare d

a mukhtar din sukayi ta dukan kofa Amma taking budewa su duka suka hasala.

Cikin fushi ya kalleshi Abokina gobe kawai ka maido Yar iska gida idan ta dandana zaman gidan a matsayin zawarci ......bani sakinta wallahi. Ya katseshi.

To ka mayar da ita duk da

haka ka Bata hutu kamar na wata guda taji taji. Kuma kada kaje ka Bari Ni Zan ma su hajiya bayani babu ruwanka.

Yayi shiruuuuuuuuu......ya ka sa magana Yana dai nazari.

Ayi ta hakuri kaman yarda na ce Ina da hidindimu Shi yasa

*Zainab wowo ce*...

✍

πŸΌπŸ’–

🀐

*WA ZAI FURTA?*

🀐

0

⃣

7

⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*

*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki...... beloved si

ster Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

*Ina alfahari daku kawayen yarinta:*

*Rakiya Amadu m/bread da badiyya Amadu m/bread*

***************

*Federal University dutsinma*

Aisha, sumayya da khausar sune kawayen Bilkisu na kut da ku

t!, Tare suka zo makarantar secondary school daya sukayi watan federal Bakori dake shiyyar funtua ta jihar katsina.

Aisha da sumayya political science sukeyi, khausar na micro biology sai ita Bilkisu dake Economics.

Su ukun dakin su daya, Bilkisu kadai k

e nata dakin.

Mafi yawa su ne suka fi zuwa dakinta ko a secondary ana tare Amma ita komai nata daban ne.

Tana yawan yin girki baka raba ta da ko miya ce Shi yasa Mafi yawa sune ke zuwa wurinta neman abincin musamman irin lokacin da semester ta raba tsaki

ya komai yayi zafi.

Khausar na bala'in son Anwar Amma tun lokacin da ya dizga ta daga magana taji ya fita ranta.

Aisha ce ta shigo dakin tana ta kokarin yanka carrot da zata Sanya cikin farar hinkafar Daman tun safe kafin ta fita tayi miyar kifinta.

Ke

yunwa fa nakeji har bana gani.

Tayi murmushi to gashi Bata karasa tsanewa ba ko zakiyi tsame yau ma?

Mtsew tayi guntun tsoki, tare da kwanciya bisa lumtsetsiyar katifarta, wannan uwar shinkafar Kuma fa ko yau kin tabbatar zamu zo kwaraka ne?

Ta dan tabe

baki Anwar ne Mana da rigimar sa nace zanyi girki Wai zaici na tafin mishi dashi class 4 idan zamuyi tutorial.

Hmmm, kawai tace.

Ta Dan waigo Fadi kada ta kasheki.

Ta kyalkyace da dariya keji Kama Kai ai bandai *furta* ba ko?

Murmushi tayi kawai,

Da

ga Nan Bata kara mata magana ba.

Yar madaidaiciyar cooler ta samu ta zuba mishi miyar Kuma tayi amfani da Yar roba Mai marfi.

Saboda kurewar lokaci a daki tayi sallah tun kafin ta sallame yayi mata missed call biyu.

A gurguje ta shirya ta fito.

A

bakin gate ta kirawo shi, bugu daya ya dauka.

Malama kinfa shanyani,

Ya hankuri gani na shigo school kana Ina?

Lecture room 2, ya fada.

Okay I'm coming......ta kashe wayar.

Sanye take da doguwar riga ta lace coffee brown, hijqbinta kalar flowers lace

din maroon.

Tana saka kafa wayar ta na Kara *Daddy ne ke mata video call* ta karasa da sauri tana murmushi.

Ya hangota Amma sai yayi kaman bai ganta ba har ta zauna kusa dashi dai dai kuma lokacin da ta ajiye mishi ledar abincin sannan ta latsa wayar...

..Hello daddy. Ta fada tare da fadada murmushinta zuwa Yar dariya.

Yabi fuskar ta ta da kallo Yana masifar son tayi dariya Shi kadai yake ganin abinda yake gani.

Bilkisu ya kike?

Kina class ne?

Eh daddy kaga nazo karatu ne wurin Anwar ta kanga fuskar w

ayar saitin Anwar din.

Yayi saurin sunkuyar da Kai...... yarinyar nan nada hankali kuwa?

Anwar?.......ya dago ido da sauri....barka da wuni Daddy ya fada da sauri tare da rusunawa Yana Dan murmushi.

Dariya yayi ......Kaine Anwar? Yau ba'ayi fadan ba ken

an?

Ya zaro ido kadan kunya ta baibayeshi yayi saurin kallon Bilkisu atuhumce.

Ta janye wayar.....mun shirya daddy yaban hakuri ta fada tana dariya.

To yayi kyau. Allah ya taimaka a kula dai kada amanta Allah Yana tare da kowa a zahiri ko badini.

Na

sani daddy.

Ta zaro ido Wai daddy kana sokoto ne???

Eh mun zo nida mommy bikin saifullahi ko?

Ta zumburo Baki daddy......ke sai anjima kuyi karatu kada lokaci ya shige......

Daddy zakuzo din ko?

Eh in shaa Allah zamu shigo jibi......yeeeeeee ta fasa

Kara yayi saurin latse wayar Yana dariya.

Ta kalli Anwar su daddy zasu zo jibi......ya dalla mata harara. Ya akayi yasan muna fada?

Ta danyi guntun tsoki.... Ai sun Sanka Ina Basu labarinka sosai.....kina cewa me?

Tayi murmushi.

Kinji?

Hmmm kawai tac

e.

Magana zakiyi meye kike fada ne?

Ka gane sun San wajen ka nake daukar karatu to ya kirane yace yau bamuje karatu ba nace munyi fada dakai shine........yaushe mukayi fada?

Me yasa zakiyi karya? Sai kice fushi nakeyi dashi ba kice muna fada ba.......na

ji sorry oya muje ta bude littafin.

Ko sai kaci abincin zamuyi?

No, Zan tafi dashi hostel ne.

Okay.

Lafiya lau sukeyi tana ganewa sosai, yana magana tana satar kallonsa idan taga ya maida hankali ga littafin sai ta daddage kuwa ta Kura mishi ido.

Yana

da kyau, natsuwa da Kuma kamala problem dinsa kawai miskilanci.....da yazo zai kalleta sai tayi saurin kawar da ido....haka..haka....sunyi nisa sosai sai taji an kwada mishi Kira ```ANWAR```.....

Dukkansu suka kalli wajen... Mufeeda ce.

Gaban Bilkisu ya

yi mummunan faduwa.

Saboda, mufeeda ana raderadin budurwar Anwar ce physics department take yarinyar ta hadu karshe saboda iya daukar wanka, Bata fi Bilkisu kyau ba Amma saboda iya gayun ta yasa idan tana wajen baza'a taba ganin kyan Bilkisu ba da kullum

cikin hijabi.

Sanye take da wani material dinkin Riga da skirt, tayi kyau matuka fuskarta sanye da kwamemen glass ya mata kyau sosai.

......... Ta tsaya daga jikin taga alamar ganinsa take sonyi.

Kawayen ta Kuma na gefe suna jiranta.

Ya kalli Bilkisu

please Ina zuwa, ya mike.

Wani abu ya taso mata ya tokare a makogoro tunda ta yi kasa da Kai bata dago ba.

Tana ta latsa waya ta ma kasa gane inane take shiga tana fita.

Agogo kawai take dubawa.

Mufeeda nada daukar hankali, kafin kace me.....Anwar ya

fara shafa'a.

Ai nayi tunanin bazaka taso ba tunda ance tsoron ta kake ji.

Yayi murmushi sai kuma na taso Kika gane hakan ba gaskiya bane ko?

Wai meye tsakanin ka da yarinyar can da kullum baka tashi koya mata sai da marece Kuma ku biyu kawai?.

Yanzu d

ai gani. Ya fada Yana murmushi.....

Ta dalla mishi harara minti nawa ta baka ne?

Ni kamar baka cikin natsuwa ma wallahi. Baka daukar waya baka amsa gayyata idan ma an iske ka..... Ikon Allah mufeeda ki Bari zamuyi waya anjima Kinga Babu dadi......babu da

di ka barota kazo wurina?

Bai San lokacin da ya kyalkyace da dariya ba ......dai dai lokacin da Bilkisu ta dago Kai, kutumar bala'i....

Yana mamakin yanda yanmata ke tuhumar Shi akan Bilkisu.

Mikewa tayi ta hada litattafan sannan ta dauki ledar abincin

kawai ta fito......

Ba karamin razana yayi ba don yasan kwanan zancen..... *Bilkisu*.......... *Bilkisu*.... *Bilkisu*!!!....... Amma Ina! Ko waige....

Duka yaushe ya samu suka daidaita, mtseww.

Please zamuyi waya ya fada tare da Dan rugawa *Bilkisu*...

....

Sauri takeyi sosai, ya cimmata da kyar...Dan Allah kiyi hakuri.

KO kallonsa batayi ba.

Wallahi ban manta dake ba Ina cikin kwatanta mata naga kin fito......... Nace ka manta Dani ne? Ko kaji nace nayi fushi ne? Kaje ka gama da ita ni lokacin da

kake free Zan dawo tunda nice nake nema a wurinka......kiyi hakuri Dan Allah.

Ta tsaya cak tare da kallonsa..... Banyi fushi ba, kamar yanda ba haushi naji ba, ai kana da damar ka ko?

Wannan bin da kakeyi mun Shi zai hasalani don haka ka koma ka kyaleni

.......ya daga hannuwa sama, naji Amma kiban abincin Mana......wallahi bazaka ci Shi ba. Ta fada tare da wurga mishi kallon da yafi komai tsana sannan ta tafi tabar Shi tsaye.

Wai me yasa bazai kyale yarinyar nan ba?

Duk Yan mata na shakkar sa me yasa

ita bata tsoron yi mishi gadara?

Ko ya ayyana zaiyi fushi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login