Showing 42001 words to 42684 words out of 42684 words
kawai tabishi dashi batada bakin magana tunda sambatu yakeyi
Yama mance ba itace zata
bashi namijinba Allah ne
Da taga da gaske yk ne sai tace dashi "Yayan love kayi addu.a Kawai.
Yace "yakamata kiyi scaining ko ?
Ta girgiza kanta "basai nayiba yaya mubarwa Allah lamarin kada muyi masa shishshigi.
Ya gyada kai kawai.
******
Wata hudu da haihuwar mubina knn Abulkairi yayi wayo alokacin Dije ta haihu Allah cikin ikonsa ta haifo tagwaye duka maxa kuma batasha wani wahala ba wajen labour ckn mintina twins suka zo duniya
Yara gwanin sha.awa kowa sonsu yaringayi tun daga asibiti
n farin jininsu ya watsu farare tas kamar "yayan larabawa sunyi kama da babansu shikansa Abdallah saida yaringajin wani annashuwa aransa yaita godiya ga Allah aransa da bayyane
Aranar suna kuwa canza musu suna yayi yasakawa hassan suna Abdulhakim li
ttle hussain kuma jiniour Abdallah
Haka yaran suka taso da farin jini sosai Ni,ima ma tana nuna musu kauna me aikinta ke daukosu takawo matasu kokuma dijen takai matasu har part dinta su
Wuni tare
Alokacin kuwa da suka isa yaye momy ce ta karbesu
ta yaye su agidanta
Dije hankali yakwanta mijinta na nuna mata soyayya gashi inda yakara burgeta yakara saka sonsa aranta Abdallah mutum ne domin yaje can kauyensu yahada matasan garin da basuda aikinyi yabasu aiki a gidan gonar dady da aka yanki gefe
yayi floti biyu aka bude kamfanin shinkafa gashi yaja wuta garin yayiyyi rigiyoyin burtsatsai da fanfuna ko ina kayi saidai kaji ana shi masa Albarka tabbas kayen marina suna alfahari da Auren dije da Abdallah
Don Yamayar da kauyensu
Birni ya haskak
a musu karkara koina fitilune ahanyoyin da ake shirin futar musu da tituna
Su littel da junior sunada shekara uku daidai dije ta haifi "ya mace wanda ita kuma kama tayi da ita futuk daka ganta kaga "yar fillo zam.
Abdallah yaso yasaka wa diyar ta
shi Sunan margayya Zannura to sai Dije tace itakam magaji da rai zatayi Ni,ima take so asakawa Babyn
Baiki tatan ba tunda Abin alherine hakan Ba.a boye mataba kumma Ni,imatullah akece mata
Ni,ima naji da takwara sosai agunta take wuni wani sa,ilin
ma intaji shiru kafin akawota da kanta take dingisawa taje ta gano takwara
Bayan shekara biyu Dije manyan mata ana zaune ana koyawa Ni,ima baby fullanci Abdallah yashigo da twins sukayo kanta suka daneta "momy oyoyo mundawo sannu da gida.
Ta hade rai
tana turarsu "kada ku ballani mana meye hakan.
Littel Yahade rai yace "gaskiya momy muma kiringa koya mana fulatancin nan kullum saidai muji kina yiwa baby bandamu.
Abdallah yakaraso ciki yana musu dariya dijen ma dariyar takeyiwa littel ganin yana
nuna kishinsa karara akan Baby Ni,imar wacce bakinta ma baibude sosaiba
Abdallah ya daga mata gira "kibashi amsa mana kinyi shiru nima ina kishi da hakan fadane banyiba yarigani ne kawai.
Tayi dariya tace "to ya kuke so inyi daku nagadai kaima gaba
kake sasu kana koya musu turanci ko gayyata ta bakwayi toni meye aibuna da abin kishi dan na koyawa diyata fulfulde.
Abdallah yace "mudai munji munki wayon dole muma ahada damu akoya mana ko mu rigime tunda ai babyn ba yarenta bane yaren mamantane.
Dije tayi dariya tace "Amma dai kasan itace asalin *"YAR FILLON* KO? KAMMANNI sunnuna komai nata na Dijen kauyene.... yatoshe mata baki "kul! Dijen Abdallah kike ba dijen kauyeba plz mubar maganar nan ma mudawo ta batun abinda nake muradi agunki yaushe za
nbaki ajiyatane?
tayi kamar bata fahimtaba tace "meke nan?
Yashafa cikinta "Inaso ahaifarmin Zannura ne
ta kanne ido daya tace masa"kasha kuruminka takusa zuwa ma.
cikin murna yace "da gaske?dama nabayarma ashe ba.a gayan ba. Yakai mata sumbata
agoshi
ta nuna masa yaran dake gefe suna sabgarsu tace "Dadyn love yara fa ka ankare plz.
ya fakaici idon yaran ya sunkuceta yayi bedroom dinsa da ita ……………
🖐🏻👏🏻😃
asha love lfy masoya Allah yabar so da kauna Dije da Abdallah.
*
Auntyn Sayyada da Shahida ce*
👌🏼