Showing 6001 words to 9000 words out of 42684 words

Chapter 3 - YAR FILLO COMPLETE

29 Aug 2026

55

yahau girgixa kansa yana fadin "ko kusa ko alama babu kaunace ta tsakani da Allah da haduwar jini kawai. Yabaiwa kansa amsa

Abangaren dady kuwa dayajewa da momy wannan

labari ba karamin dadin hakan tajiba itanma domin tanada labarin dijen kauye tun tuni tunda Abdallah naxuwar mata da furarta da nonon

Saigashi xata xama surukarta koda yake dama ita momy ba sawa ba cirewa indai akan dadyne tana son duk abinda zai nun

a yanaso baitaba nuna baki yace farine shi tace masa a.a ba fari bane ina aikomi yace e, hakane shine amsarta

Baikarajin dadi ba sai Aunty maryam tazo taji itanma ta amince da hakan domin taji ance ankai kudin komi kuma baxa.a fasa na Ni,imaba itanma

tanason abinda duk iyayanta keso to balle yarinyar da suke yabo kuma aikin gama yagama tunda antsaida ranar aure ai dole itanma taso ko taki ko taso

Dady ya aika wakilansa suka kai kudin aure gidansu Ni,ima baban Safna mijin Aunty maryam ne yakarbi kudi

n shine waliyyinta amatsayinsa na babban yayanta

Nan ma dai antsaida magana akan cewa nan da sati biyu daurin Aure dai dai dana dijen kauye rana daya za.a daura knn 15/4/2019

Nan ma dadyn yacake makudan kudade

Gida gari guda yasaiwa ango wanda

ke unguwar ladanai babban gidane flat house me part 2

Ango dan gata knn wasuma itasa suke nema basu samuba

😅

Babu wanda yagaya masa koda ta wayane ammafa jikinsa nabashi akwai abinda ke shirin faruwa dashi yakikkira Abdulhakim yafi biyar aranar a

mma bai daga kiran saba kuma bai biyoba to ko daganan yasan ba qalau ba gashi aranar Uncle din nasa yake sanarsa cewa yashirya agobe zasuje kano gidansu Zasuyi muhimmin wani abu.

Nanma yasha jinin jikinsa saiyashiga tunanika barkatai damuwarsa ma rashin

daga wayarsa da Abdul yayi

Yarasa waxai kira yaji news gashi sunbabe da Aunty maryam yai mata laifi ga ta gidansa Zannura tayi fushi dashi duk dayasan shi yayi mata laifi ya disgata gaban kanwarta

To amma dai ahakan yakirata awaya kuma akai sa.a t

adaga masa kamar ma wani abun bai faru tsakaninsuba

Duk yadda yaso yaji ko akwai wani abu dake faruwa agidan bata yarda tasanar ms ba domin ankwabesu sosai itada Mubina sbd ansan zasu iya kiransa su tsurkunta ms duk da Zannun ce auke very close

Abu d

aya tagaya masa cewa "Eh to nikam bansan ko meke tafiya ba nidai naji anata zancen za.aje biki kauyen Rogo amma iya maxane zasuje.

Yatambayeta "bikin waye hakan? Ta tabe baki tace masa "oho walh ban saniba may be ckn familyn dadyne na can zasu Aurar da

"ya"yansu

Yace "anya kuwa? Ai familyn dady a rogo duk sun kare damafa kakannine acan kuma babusu wataqila dai ko ackn abokansane zasuyi wata hidimar kinsanshi da kara shine harda yin gayyarsa shima.

Ta daga kafada tana murmushi tace "inajin dai hakan

ne ma amma yaya yakamata kadawo aje dakai kaima tunda aiduk xumuncine.

Yace "Eh zanzo nima aje dani tunda uncle yamatsa wai dole tare dashi zamuje.

Nan sukai sallama tana ms dariyar mugunta tabbas banda tana qule dashi na abinda yai mata da babu a

binda zaisa taki gaya masa yanda suke ai babu batun ta iya boye masa wani abun balle damuwarsa tatace to amma yajawa kansa

*****A can bangaren Amarya dijen kauye kuwa batasan wainar da ake toyawaba har ana gobe daurin Aure itadai taga iyayanta maxa

sai shige da fice suke ackn gidan sunayin kus kus da Addaji.

Taga kuma yan garinsu Addaji da wasu yan uwan sunxoxxo gidan wai biki sukaxo har ana ce mata amarya! Nan tahau tuhumar kanta wacece amaryar?! To bikin wa akeyi haka da batada masaniya abu har

ckin gidansu akeyi?

Da dare ta tisa Addaji a daki ita kadai ta sata agaba da tambaya

"Addaji wai bikin wa akeyi ackn gidan nan dahar ban saniba? Waye adangi ake bikinsa kuma ackn gidanmu?

Addaji takalleta da tausayi tace "Dije Aurenki ne mana kina

nufin baki ganeba? Ko bake kk kawo mijin ba??

Da sauri dije ta ja baya tarea dafe kirji idanu awaje ckn rawar jiki tahau fadin "Aurena kuma Addaji!? Dawa za.ai min Aure ban saniba?? Yaushe nakawo mijin walh bansan wani mijiba nikam bansan zancenba da

n Allah kiyi min bayanin daxan fahimta.

Nan Addaji ta warware mata magana tace mata Alh mustafha me gidan gonane yaxo dakansa gidan yanemi Aurenta ga dansa kuma iyayanta suka amince kuma ance kina son yaron Ko Abdul sunansa ko miye ma na manta.

Dije

ta tsaya cak tunaninta yadawo tahau tunanin wani abu tayi shiru domin tunaninta bata yayi wato dady yaxo yanemawa Abdulhakim Auranta knn har An bashi amma bata saniba to meyasa Abdul yai mata hakan meyaa baizo yasanarta ba har suka tafin. Ita ai dama shi

takeso wannan ai abin farin cikin tane.

Ta mike asanyaye tafuta taje dakinta takwanta tana tunanin Abdul

MurmuShi tahau zabgawa tana farin cikin wannan lamari

Wai gobe iwar haka taxama mata agun Abdulhakim tabbas dole tayi godiya ga Allah daya cik

a mata burinta yabata Abdul A salin Alin batareda tasha wahala wajen bayyana tana sonsa ba.

Kwana tayi tana farin ciki tayi baccin dadi sosai harda makara wajen yin sallah

Allah Allah taringayi axo adaura tayita kasa kunne son taji ana daurin aur

e amma har hantsi bataji anxo daurin Aurenba tace Allah yasadai bafasawa sukaiba

To acan birni kuwa saida "yan daurin Aure suka fara zuwa Aka dauro Auren Ni,ima sannan Aka rankayo kauyen rogo domin Daura aure na biyu

Ango dai yadawo gidansu Amma bais

ami zuwa kowanne daurin Aurenba domin rashin lfyr karya yakwanta dasukazo da uncle wai duk don dadynsa yatausaya masa kada yai masa fadan barin gidan dayai hhhmmm shiko dady kallonsa kawai yai ba magana me tsayi sai Allah ya sawwaqe

;

Abdallah yabi aya

ri zuwa kauyen rogo daurin Aure



Sai shabiyu daidai suka isa

Ba b'ata lokaci aka daura Aure aka kawo musu fura taji nono da sukari suka hau sha suna yin santi harda masu qulla zasuyi guxuri da ita

Kafin sukoma Abdulhakim yasamu kebewa da Amarya

asoro

Taxo tasha kwalliya kanta lullube ruf da mayafi kowa yai xaton shine angon ackn gidan domin yasha babbar riga yai kyau ainun

Yarasa da wane lafazi zaiyi mata bayanin komi

Saida tadago idanunta takalleshi da wani kayataccen murmushinta take

yaji wani yarrr!

Abinda bai tabaji atattare da itaba sai yau

Tagaidashi tace "Ango na ina wuni.

Jin hakan yasa yadaure yafara mata bayani " khadija ina me bakin cikin sanar miki cewa ba dani aka daura mk Aure ba nasan zakiyi tunanin ko nine mijin n

aki to bani bane dan,uwana ne Dady shi yayi sha,awar yahada auranki da jininsa sbd kyan halinki da yayi dan haka kiyi hkr kiyi hkr khadija Abdalla ne mijinki baniba ……

Xumbur ta mike tsaye ta yaye gyalen ta jingina da bango jin zata fadi ta nunashi da y

atsa tana kuka takasa ma maganar donta makale amakoshinta

Tuno fuskar Abdallah datayi yasa taji wani jiri tareda ganin wani duhu aitake taxube agun

Suma tayi na awa biyu anata shafa mata ruwa don matane suka fito suka dauketa aka kaita dakin Addaji

Shiko duk yarike yashiga damuwa sai alokacin yahau nadamar abinda yayi

Wayyo khadija kada ki mutu baki yafenba.nayi nadamar wannan hadin domin ji yayi xcyrs na mata wani mugun tausayi fiye da yanda xai tausayawa kansa.

Yan taron daurin aure basusan

komi daya faru da amaryaba suka hau shirin komawa

Abd dady yace sai sati yazagayo za.a dawo daukar amarya kafin nan aun gama bikin al,adunsu suma na kauye

Jikin Abdulhakim Asanyaye yabisu suka koma birni ransa ba dadi.

Dije tafarka taganta ajiki

n Addaji jikinta sharkaf da ruwa da alamar shafa mata akai tayi don tafarfado

Subiyune adakin u u

Tana farkawa tahau kuka ckn harshen fillaci tahau fadin " *Wallahi mi yid'a mo Addaji mi wanyi ma lara yeso mako* (walh banasonshi Addaji,natsaneshi b

ana qaunar inbude ido inganshi)

Addaji tahau bugun bayanta ahankali " *wadu munyal dije, Allah su'bine ko lati khairu* (kiyi hakuri dije kada kibujire Allah yasa hakkane mafi Alkairinki)

Dije tahau kuka tana share kwalla

Addaji tace "kada kinuna

wa jama.a cewar bamu isa dakeba tunda kuma anriga andaura hkr xakiyi kixama me biyayya don kiga dakyau arayuwa kiyi shiru kinji dijena kixama me bin iyaye da miji.

Maganganun addaji sunshigeta nan tayi lakwas ajikinta tana faman matse kwalla tana fidda

numfarfashi

Addaji taci gaba da bata baki cikin fillanci " *jedu accu vojji, d'o on jarabu ma ambo* (kiyi shiru kidaina kuka jarabawarki kenan)

dije ckn sanyin murya tace " to *Addaji wannam do'a, Allah wadu hanjum on khairu me* (addaji kiyimin Addu

,a Allah yasa hakan yaxamar min Alkairi Arayuwata)

"Allah yasa dijena.Allah hokkumo sa.a.

Itakanta Addaji saida tayi mata kuka abayan idonta don ta bata tausayi data nuna hkr lokaci guda

Tunani yaiwa dije yawa yaya zatayi da son da takewa Abdulh

akim knn?bazata iya cireshi arai ba

Ta wani bangaren kuma ai burinta yacika naxuwa birni

To amma wane irin rayuwa zatayi a birni da wanda bataso baya sonta ????? ………

_muje zuwa_[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:

🙆🏼

🐄

*"YAR FILLO…*

🐄



🏕

🏕🏕🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕



🏕🏕



🏕

*True life story*

*Nabilancy Luv*

💘

(Auntyn S&S)

PG 20-25

Cikin kwana guda da yin daurin Aure Dije ta rame ta f

uta hayyacinta danma tanada garin jiki dama batayo jikin siraran fulanin rugaba

Addaji taringa matsa mata akan saitaci abinci dole ga "yan taron biki basu watseba domin sai anyi sati ana biki ana shad'i dayin bikin mard'on na fulanin kauye wanda "yam

mata ke hadawa a dandali da daddare

Bikin mard'on bikine nashan damammen gero dafaffe yasha nono da sugari

Kwarya kwarya ake hadoshi daga gidan amare akawo "yammata susha suda samarinsu ana hira ana nishadi me kida nayin kidansa afili wasu na liki

To ita dije dama bawani kawaye take dasu wararruba

Kawayen kara dai sunzo mata "yan unguwa da sa,o,inta "yan uwa ancika anyi bidi,a ta al,ada

Ba laifi ta saki jikinta ackn yan biki wanda ba kowanema yafuskanci tanada damuwa ba

Akwai "yar gidan

kawunta sa,ar tace wato indo itace ma tasan abinda ke wakana atare da ita insun kebe takan tausheta da bata baki harda ce mata "aike ki godewa Allah ma da zakiyi rayuwar Aure a birni don wasu hakan suke nema ma kuma mijinki dan gayu ga kudi dan Allah kicir

e damuwa aranki kiyita Addu,a Allah yasaka mk sonshi kawai.

Dije bata ce mata komi saidai tace mata "hhhhmmmm

Ita kadai tasan me takeji aranta mekuma take hange agaba don ko tayi addu.a Allah yasa mata sonshi aranta to shikumafa yazatayi da tsa

nar dayai mata, itakam har Abada zuciyarta Abdulhakim take kauna kuma baxata dainaba abinda ma yasa taji hankalinta yadan kwanta tuno kalaman Abdul din datayi nayanda ya bata hkr da kuma nuna mata cewar akullum acan zai kasance tare da ita xaikuma taimaka

mata baxai bari Abdallah yacuce taba.

To wadannan kalami inta tuno takanji sanyi aranta.

**** *****

Daga can bangaren ango Abdallah kuwa baitashi saniba sai dare yaji Abokansa ta koina suna masa waya ana masa Allah yasanya Alkairi wasuma harda n

una fushinsu akan bai gaya musu ba

Mamaki yamamaye shi farko yaringa musu dry don yazaci ko zolayace to inbanda tsokanarsa suka shiryi yi yama xa.ai ace yai aure arana guda ya auri mata har biyu kuma daya a kauye daya abirni duk shi kadai

Bai gaska

tasu ba saida Uncle dinsa yatashi tfy yakirashi daki agaban mahaifinsa ya shiryasu yai masa fadan gudu yabar gidan dayayi yakumace masa shima yatabbatar yabar maganar Lowerst domin ayanzu shi din me Aure ne akansa Aure ma harna mata biyu.

Ya zabura yari

kice yace da uncle "Aure kuma uncle? Ni?!! A,a badai niba walh bansan maganar ba

Uncle din yace dashi "Abdallah kanutsu kazauna inyi maka bayanin yanda akai aka daura maka Aure da "Yammata biyu ayau.

Wato Abdallah kai me hankaline amma kanaso kaz

ama wawa manufa ka girma amma gakanan ne kamar yaro sbd wauta iyayanka na duniya amma kana neman kabata dasu baka son kaxama meyi musu biyayya yanzu abinda kayi na nuna fushi ga mahaifinka daidai ne? Daga gaya maka gaskiya akan yarinya saika gujeshi wannan

abu yakona masa rai da baka nuna kabi maganarsa ba kuma yayarka takawo maka magana kasa kafa ka shurs sannan ance akwai yarinyar da a can kauyen rogo kake wulakantawa akan tana nuna maka SO to sune dadynka yadaura maka Aure dasu ita waccen khadija da kanw

ar mijin maryam ni,imah dan haka inaso kazama jarumi kaxama me hkr da bin iyayae kada kanuna jin haushi ko fushinka kada kace zaka bujire ka kunyatasu tunda anriga andaura maka Aurs dasu.

Wasu zafafan hawaye yaji sun sauko masa akunci dama ashe haka a

ka shiryi yi masa lallai yau annuna masa rashin kauna kuma saiya nuna shi Abdallah ne

Yakalli mahaifinsa yana kuka kamar wani yaro karami yace "dady Amma wannan matakin da hukuncin naka sunyimin tsauri dayawa walh duka yaran bana sonsu araina kuma baxan

iya zama dasu amatsyin matanaba kayiwa Allah dady kasa inwarware wannan Auren Akan nasu walh indai akan yarinyar can dana kawo maka zancen tane to na hkr kabani kowacce ackn "yan uwa amma banda wadancan

Dady yahade rai tamkar bai tab'ayin murmushi k

o dariya ba yace da Abdallah

"Kuma ni dasu nake son kazauna kakuma basu babban matsayi ackn gidanka inkuma kanuna min ban isa ba insallama ka

Dan haka kaxaba koni ko ra,ayinka.

Abdallah yayi shiru yana jan ajiyar zuciya ransa na masa quna

Uncl

e yadafa shi yace masa "Abdallah kaxama namiji gwarxo jarumi mana kadauki wannan tamkar kaddararka knn kayi godiya da Allah dataka jarabawar ma taxo cikin sauki tunda kai da kanka zaka iya daidaita lamarinka wajen karbar taka jarabawar ahannunka manufata k

arike matanka batare da nunawa ubangijinka cewar baka son zabinsa ba domin zabin Allah ne su kuma zabin mahaifinka dan hk kada kaki amincewa sbd kada kasami sabani akan wannan kaida mahaifinka kaji,

Cikin sanyin jiki yahau gyada kansa da alamar yadauki

maganarsa

Dady yadubi uncle da zafin rai da daga murya yace "kasan Allah Alh inhar bai bi wannan abinda na shirya masa ba bai karbi zabin danai masa ba to walh yasani bani bashi bakuma "yan,uwana bashi hakama dangin mahaifiyarsa kada yasa ran xuwansa gu

nsu dan zan hana su karbeka kuma tsinuwace zata biyo bayanka

Wani abu ne yatsaye axcyrsa lallai dady yadauka da xafi ba dashi xa.ai hakanba ckn kwantar da murya yace da dady

"Allah yahuci zuciyarsa dady na amince zan zauna dasu amatsayin matana

Uncle yace "to aikaji Alh saikasa masa Albarka tunda ya amince da abinda kayi masa.

Dady yasaki rai yace "to naji Allah yayi mk Albarka tashi kaje.

Yatashi asanyaye yafuta

Kai tsaye dakinsu yanufa yatarar da Abdulhakim yafito daga wanka yax

ira jallabiya

Da bacin rai yatunkareshi yanunashi da hannu "kai tsohon munafuki ashe Aurena kukaje shine baka gaya minba kuke ta boyaemin kaketa kumbiya kumbiya to walh nasan ma akwai hadin bakinka ack

Abdulhakim yace "hhhmmm koma me zakace kace

naji amma kasani cewar kai kaja komi tunda da ace kana daukar shawarata da hakan baxata faru dakai ba

Yanxun da akai hakan wa gari yawaya? Tokasani duk abinda yafaru dakai ka tuhumi kanka

Abdallah yakufula yace "Au haka kace ko?

Abdullha

kim yaxuciyo shima yace "nafada din me zaka iya?

Abdallah ya buga masa tsaki yafuta yana xaginsa

Saida yafuta shikuma yaxauna gefen gado yadafe kansa domin yanajin tausayin abokinsa dan,uwansa sosai bayaso yanuna masa ne

Adaidai lokacin da a

bin duniya yaiwa Abdallah yawane ita kuma Amarya Ni,imah Abin duniya yai mata dadi domin Allah yacika mata burinta yabata wanda ta dade tana kauna

Bata taba zaton wannan rana zatazo mata kwana kusaba lallai angama mata komi da aka jajirce aka ga andaura

mata aure da Abdallah

Abu dayane yatsaye mata arai bawai jin Abdallan baya son taba ko baya dokin Auran a,a jin cewar Tanada kishiya ashe su biyune amaren na Abdallahn.

Tabbas inta tuno kyanta da matsayinta na ita dangin arxikice saitaji bacin r

ai wai ace itace me kishiya "yar kauye

Abinda take yawan tunani shine shin itanma yar kauyen baya son tane? koko ita yakeso ba ita Ni,iman ba …… ????

*Auntyn Sayyada da Shahidah ce*[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:

👌🏼

🐄

*"YAR FILLO*



🐄

_Dijen kauye_



🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕



🏕🏕



🏕

*True life Story*

*Nabilancy Luv*

💘

(Auntyn S &S)

PG 25 - 30

Tamfatsetsen gida Dady yabaiwa Abdallah me part biyu

Sannan kowanne yazuba furnitures masu tsada da kayan kicin ack

Kowanne part yahadu iya haduwa babu banbancin kaya da akayi sai daga gidansu Ni,imane suka karayiwa amaryarsu wasu karin decoration

din suka kuma kara zuba kayan kicin din amaryarsu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login