Showing 21001 words to 24000 words out of 42684 words

Chapter 8 - YAR FILLO COMPLETE

29 Aug 2026

58

kifara daga farko ko kuwa bakyaso abari?

Khadija data kankame waya tana faman farin ciki tahau naxari anya kuwa zatayi karatu kuwa?taji fa ana cewa akwai wahala

Tanadason taga yau itanma t

anajin turanci saidai tasan zatasha wahala sosai kafin ta iya wasu abubuwan takalli wayar hannunta tasan ita kadai darasine akan rashin ilimi domin inbakada ilimi ma hatta waya gagararka take ka iyata koda calculata ce

Tanaso kuma ace itama tazama wayay

yiya kodan yan iskan mata yan rainin hankali irinsu Zannura

Dady ne yakatseta da cewa "khadija inkinga bakya ra,ayin karatu bazan takura mk kiyi adoleba dama ra,ayinki nake sonji tunda kokin aminta sai in mijinki ya amince sannan zansa ya nema miki.

Dije ta dago kanta asukawane takalli Abdallah dayake ta danne danne awayarsa kamar bayajin abinda dadyn ke cewa ma

Takalli dady tace masa "na amince dady inaso

Dady ya gyada kansa yace "yayi kyau to Kai Abdallah kaji khadija nason karatu ta amince i

nnema mata kaima ka aminta?

Kansa akasa yana amfani da waya yace da dady "wannan ba matsala bane na amince tayi karatunta.

Dady yace "to ai shikenan saika nema mata akusa da gidanka kuma mekyau nakeso ta fara daga primary yakamata tafara

Abdall

ah yakarkace kai yakalli dije yace "yanzu dady wannan gododen ce zatayi primary ackn yara ? Lallai amma zata zama maman yara kenan

Momy ta tareshi da fadin "to inbanda abinka Abdallah nawa khadijan take da baxata shiga ckn yara ba itada natabbatar ko s

ha bakwai batayiba sannan kuma ai tanada fuskar yara girman jikin me kawai kaidai kawai kayi mata fatan Alherin.

Dady yace "koma dai meye banaso asami matsala nabar maka komai ahannunka indai private ce zasu karbeta ko aji nawa ne tunda kudi za.a kashe

don haka banaso asami matsala katabbatar kuma kai zaka ringa kaita makaranta kanaji

Ran Abdallah abace ya amsa da to kawai badan yasoba

Abu dayane yafaranta masa rai dayaji har zuwa wani lokaci iyayan nasa basui masa magana akan ko dijen takawo karar

sa ba sai hankalinsa ya dan kwanta don ya zaci ko yanda tace masa zata fada din ko ta fada.

Duk yanda ta wakana afalo akan zancen saka dije makaranta Abdulhakim yaji tas dayazo saukowa amatatttakalar benen ransa bai masa dadi ba sbd bayaso ace khadija t

ana futa kullum sbd yasan inhar akace yau khadija ta waye ta bude idonta to za.a sami matsala yatabbatar baxata zauna da dan,uwan saba.

Daki yakoma yazauna akan gado yadafe kai yahau tunanin mafita

Abdalla yashigo dakin nasu yana fadin " dan,uwa wai

dama kana cikin gidan Amma banji motsinka ba?

Abdulhakim yadago kansa yakalli Abdallah yakakaro murmushi yace dashi "ina cikin gidan banfita ba banajin ddi ne.

Abdallah yabashi hannu suka gaisa yace masa "sannu friend ko akwai damuwa ne?

"Babu wa

ta damuwa kawai dai baccine da bai ishe niba jiya nakai dare sosai ina ciccike files dinnan da za.a fita dasu gobe

Abdallah yace masa " Ayya sannu dan,uwa Allah yasauwake.

Amin

Harya juya zai futa Abdulhakim yakirashi yawaigo yace "akwai wani a

bunne?

Abdulhakim yace "kwarai xoka zauna muyi magana me muhimmanci ma kuwa.

Yaxauna kusadashi

Abdulhakim yagyara zama yace dashi "uhhmm akan maganar Khadija ne dama.

Gaban Abdallah saida yafadi domin yasha ko zancen dasukai na shan giyar da

yai ne da ita ko dama Abdul din tagayawa aiko yana shakkar Abdulhakim yaji sbd baya masa ta dadi zai iya juya masa baya su bata

Abdulhakim yace "wato naji maganganunku dasu dady daxu akan batun saka khadija makaranta da za.ayi nikam banso hakan ba ban

so kuma naji ka aminta ba sbd khadija bata san kowa ba akano saimu inajiye maka halin matan birni da maxuga kaga lafiyar Allah take kada tazo ta shiga sch tahadu da muggan kawaye su canxa mata ra.ayi akanka taxo tafi karfinka dan haka ina me kiranka da bab

bar murya akan kadakatar tun wuri sbd....

Abdallah yadaga masa hannu "dakata Abdulhakim wato inna fahimta so kake kace min nan gaba zata iya fin karfina kenan?

Gyada kai kawai Abdulhakim yayi

'"Ta dade batafi karfi naba walh ni da hakan zata kasan

ce zanfi kowa son hakan sbd kai shaidane natsani yarinyar bana sonta adole nake zaune da ita to meye nawa dan tashiga sch aini fatanama Allah yakawo ranar rabuwa ckn sauki ko Allah yasa nasamu na Auri burin raina lowerst

Wani mugun tsaki Abdulhakim yaj

a masa yace "akullum kana bani mamaki domin kana kawo abinda bazai taba yiyuwa bane kuma baxaka gane anmaka gataba sai nan gaba.

"Aini walh ba gata akaiminba dan ancuceni antauyeni kuma nasan dasa hannunka tunda da ace kahana dady da hakan batayiwu ba s

bd yanajin maganarka yana kuma bin abinda ka kawo to amma dayake kashuka min mugunta aikaima boyemin kayi inba hakaba tunda anjona min Ni,ima tokai meya hana ka karbi yar kauyen? Kawai dai bansan nufinka nayin hakanba sbd dakai ta dace kuma kagujeta nikuma

baxata taba samun farin ciki aguna ba sai bakin ciki.

Abdulhakim yace "nikuma inhar ina raye baxan taba barin khadija ta kasance a ckn bakin cikiba... "to ko insaketa ka Aureta danta samu farin cikin? Yatambayeshi ahasale.

Abdulhakim yace "wannan

kai ta shafa gaka ga khadija ga dady nan kakuma san irin hukuncin daya yanke maka nasakin daya daga cikinsu dan haka _is not my concern_

Abdallah yabuga masa tsaki yafuce

Koda yasauka kasa falon bai tadda kowa ba su dady sun tashi haka suma su mubi

na da dije sunkule adakin mubinar

Kai tsaye gidan abokinsa Anwar yawuce domin kwakwalwarsa tadau caji dayawa ruwa yawatsa sannan yazo falo yabaje adoguwar kujera yanashan sigari hankali kwance yana waya da babynsa lowerst

Sai faman zuba masa shagwa

ba takeyi harda kukanta wai itakam _she miss him over_ gaskiya zata diro nigeria akarshen wata koya shiryi tararta bai shiryi xuwantaba dole zatazo dai

Babu yanda zaiyi da ita adole ya amsa mata badan yasoba

**********

Sukuwa su Zannura da Ni,ima

can wani kauye suka je me suna kaburma dake yankin dawanau kwatance sukabi suka kai kansu

Sunsha wahala kafin sugano gidan malamin me suna mallam matawalle wanda ake masa layi sai mutum yayi kusan awa guda kafin aganshi dan cikowar dake gun

Suny

i budu budu dasu nakurar jar kasa wanda danma a achaba suka karaso gidan

Suma layin suka hau don mutane sunkai 20

😱

suka tarar

Dakyar dai da hakuri da juriya suka samu suka shiga dakin da mallam yake

Mallam matawalle yaji bayanin da Ni,ima

takoro na yanda take zaune da mijinta amma baya sonta

Mallam yace "me kk so ayi masa?

"So nake mallam asaka masa azababben sona a zcyrsa wanda zaizamo ma duk abinda nace shi zaibi kuma inaso yarabu da kowacce mace yatsaya akaina kawai

Yahau gyad

a kai sannan yayi rubutu ajikin kasa yabukaci jin sunanta dana mijinta fada masa

Yayi surkullensa yagama sannan yahada mata magunguna nawanka dazatayi da kuma na turarawa da wani rubutu da zata ringa yayyafa masa afilon dayake kwantar da kansa akai inxa

iyi bacci sau uku

Dubu 20 tabashi tana godiya suka tafi ckn farin ciki

Koda suka fito dg kauyen saida suka siyi ruwa suka wanke kafafunsu dankar aganosu agida

*****

"Yanzu matar yaya dan Allah harkin gaji daga dan wannan aikin da kikayi

.?

Mubina ta tambayi dije tana me jan babbar silbar fulawar da suka buga gabanta

Dije tahau dariya tana fadin "ke walh bakida tausayi mubina yanzu duk irin wannan Dukan da naiwa fulawar baisa kinyabamin ba saima mita xakiyimin Allah zangudu gun

momy

Dije takarasa fada tana dariya

Mubina tace "haba matar yaya ke yanzu saiki tafi kibarni da uban aikin nan me yawa kinga fa ko cincin din bamu fara ba cake kawai mukaifa bamuyi su samosa ba balle azo kan meet pie

"Kai yau naga ta kaina

dai danazo taya aiki gashi za.a wahalar dani akan za.a burge sirika

Mubina tahau dry tace "to amma dai naga kema zaki amfana tunda ko banza zaki gwanance awannan bangaren ko.?

"Eh kumafa hakane. Dije tafada. Tana janyo silbar gabanta kinga bani wan

nan aikin kama wani kawai.

Haka sukaita hira har suka gama abubuwan da suka tsara zasuyiwa saurayin mubina faisal wanda zaitafarwa mamansa shi dayake tana son mubina tana mata aike sosai shiyasa itama yau zata burge

Koda Su Ni,ima suka dawo basub

i takan su Dijeba sai suka qule suma adaki suna qullequllensu

Cikin ledar take Away taf mubina tabaiwa dije snaks din ta tafi dashi don magriba nayi Abdallah yaxo Daukarsu don komawa gida

Abdallah Sbd Ya qular da dije sai yace da Ni,ima "ke shi

ga gaba dan kinfi kalar gaban mota

Aiko ta shige tana wani yauki da yatsina Wai nan annuna mata so

Allah Sarki dije ko ajikinta don hankalinta kwance tashiga baya ko afuska bata nuna jin haushin hakanba …………

_muje zuwa_

πŸ„

*YAR FILLO*

πŸ„

_D

ijen Kauye_

πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•



πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•



πŸ•πŸ•πŸ•



πŸ•πŸ•



πŸ•

*True life Story*

*Nabilancy Luv*

πŸ’˜

(Auntyn S&S)

*SADAUKARWA GAREKU*

*Takwarorina abin Alfaha

rina ina yinku!ina sonku!!inaji daku manyan mata!!* Luv you all....

*Nabila maman khalil*

*Nabila Rabiu zango*

*Nabila Dikko*

πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ˜˜πŸ˜˜

_Kaga hazik'an marubuta kaga jaruman marubuta kaga Nagartattun marubuta anbuga anbarku kun iya kun huta

Nabil..-Bil..'s_

πŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘ŒπŸΌπŸ‘ŒπŸΌπŸ˜‚πŸ˜…

PG 75-80

Abdallah yashiga tambayar kansa "shin wai son yarinyar nan nake yi kome? Wai yaushe ma zan daina mata kallon mata tane? Yar kauyen har yau zanji kishinta wacce natsana.yarinyar da ba wayyiyaba

.,mittsss!! Yaja tsaki tareda tashi yafuto daga dakin yai zaton zai tadda Abdallah don yabagarar sugaisa sai yaga ashe yatafi ma.

Tana zaune akan 3 siter tanata buga game abinta ko daga kai takalleshi batayiba duk da taji motsinsa

Shima kallo daya

yai mata yafice ransa nai masa quna

Baisan daliliba ganin yarinyar natada masa wani abu arai bayama inyaganta ayanayi irin nayau.

Ranar Asabar yana kwance akan doguwar kujerar dake falon da lowerst takama a hotel din da remote a hannunsa yana c

kn chanza tasha babyn nasa ta fito daga toilet da tawul ajikinta iya guiwa tazo ta dane cinyarsa tana fadin "ohh!my real gaskiya yau saika kaini yawo na zaga gari inba hakaba baxaka je koina ba kuma sainaje na nemi gidan dady ayau.

Da sauri yazabura y

azauna daidai yana fadin "zan kaiki babyna shirya shirya maza inkaiki kada ki ballomin ruwa.

Ta tashi daga kan cinyar nasa tana dry tashige dakin gadon nata ckn yan mintina ta shiryo ckn riga da wando tafito tana tashin kamshi

Yakalleta ckn mayen

so da sha.awa yace mata " _your dress is fine my baby_

tahau yarfa hannuwa tana murmushi tace "tanks my real.

Yadauki key dinsa akan table yai waje tabishi abaya.

Gidan Anwar yafara kaita sukasha hira suka kuma kora abar

Sun watse acan don

sun tadda wasu makakkun mata gogaggun "yan bariki acan sunata shan shisha

Kafin su tafi matan sukai sabo da lowerst har musanyen lamba sukai "yammatan subiyu musulmaine

Anwar yaita kallon lowesrt kamar maye dan rayawa yai aransa saiya dandaneta shim

a don tayi masa

Duka '"yammatan fa dama nasane amma dan hadama bai hkr ba kai

πŸ˜ͺπŸ™†πŸΌ

A dabarance ya kwafi nambar lowerst dayaji tana baiwa yammatan nasa

Grand Squar yakaita tayo siyayya na kayan kwalan da abubuwan bukatu sannan suka fito

Akan

hanyarsu ta komawa hotel yaji wayarsa na ring

Yana dubawa yaga Dadyne yad'aga da sallama

Aiko amsa masa sallamar baiyiba yabal baleshi da fada "Abdallah bakajin maganar mahaifa kafuta daban ackn yarana,maxa maxa kazo gida yanzun nan yaron banxa y

aron wofi.

Ckn kidima ya amsa da "To dady ganinan zuwa yanzun.

Yana kashe wayar yakalli babynsa dake gefe guda yace mata "Dady ne baby fada yake tamin bansan daliliba yace min maxa yanzun inje yana son ganina.

Tayi fari da ido tace "to muje mana.

Yazaro ido yace "ke!kina haukane ?dawa zanje ke?tabdijan kice akasheni yau knn haba baby keda naketa boyeki sbd tsadar ki to meye amfanin aganka da wacce zaka Aura mukam akwai matsala hakan a addininmu

Ta lumshe idonta tareda budesu tar akansa tace "

to ba matsala ka kaini masaukina saikaje din.

Yai kasa da motarsa daga kan kwalta yarage tafiya yatsaya cak yakalleta yace "ina girmama maganar dady na bana so inga yana min fada sosai kuma tunda kkga hakan akwai matsala dan haka kiyimin afuwa kitari ma

shin dan sahu kije zanzo da dare muyi maganar

"To amma dai inkazo kwana zakayi ko? Tafada da shagawaba

Ya daga kansa yace "kwana biyu ma kuwa.

Yazaro kudi yabata

Takarbesu kuwa tafuce

Yaja motarsa sai gidansu gabansa na dukan uku uku

***

***

Wani bugawa da kirjinsa yayi kamar anbuga durom saida najiyo bugun don fargaba data d'arsar masa naganin falon ack da "yan gidan gefe guda azaune akan kujera dady da momy ne

Sai Aunty maryam acan kan one siter azaune

Mubina na gefe akasa z

aune ta zabga tagumi kanta akasa

Zannura kuwa tana gefe itama sai kuka takeyi kasa kasa tana share hawaye

Abdulhakim na zaune kansa shima akasa yana goge zufa

Jikin Abdallah yagama bashi babu lfy yau agidan

Asanyaye yasamu guri kusada Abdulhaki

m yazauna

Yagaida iyayan Nasa ckn ladabi

Dady yahau harararsa yana fadin "gaka dai kamar na Allah to amma ashe me sabon Allah ne tahanyar dayafi tsana shan giya... "wa,iyazubillah.

Wata zufa ce ta karyo masa agoshi yahau sharcewa

Dijece tafado

masa arai domin ita kadaice sukai zancen yana shan giya yakuma roketa Alfarmar karta fada

Ya manta da Ni,ima taganshi ahalin maye ko don ba.a hayyacinsa taganshiba kuma basuyi maganarba

"Yaushe kafara shan giya bansaniba "?

Dady ya watso masa yam

baya wacce yakasa amsata

Dady yadubi Abdulhakim yace "kai.fadamin yaushe dan,uwanka yafara shaye shaye bansaniba? Nasan lanada masaniya saidai in boyemin zakayi amma kasan komai akan Abdallah.

"Walh bansanshi da dabi.ar shaye shayeba saidai in yanz

u yakeyi bansaniba

Abdul yafada asanyaye

Abdallah dayai tsuru agefe dabara tafado masa ckn ladabi kansa akas yace "Walh dady bana shan komai na buguwa abinda yafaru ranar munje wani partyn abokina nida wasu abokanmu to sai mukai dare kuma sukaimin mu

gunta alemo suka saka min abinda zai bugarni walh anan nasha yabugarni dan Allah dady kayi hkr kayafemin bada sanina nasha ba .

Dady yace "ohhh!nayi zaton koka fara shan giyane da sai ince kasako min yarana don baxan yarda su zauna da dan giyaba tunda

akwai cutuwa don wataran zaka iya dawowa kai mata duka.to amma tunda hakane ya wuce.

Ohhh shet!Abdallah yaji inama yafadi gaskiya dayasan za.ace yasakesu tunda yana a maxaunin mashayi walh inama yafada da tuni yarabu da alakakai.

Dady yanuna z

annura yace "kaga kanwar kanan zannurat tun daxu take mana kuka akan nace mata ta fito da mijin Aure taki domin nan da wata guda zan daura mata aure intaki fidda miji domin mubina da Abdulhakim zanhadasu aure tunda naga tasu tazo daya.

Abdallah yaji d

adin hakan sai yahau yiwa zannura magana ckn sanyi don jininsu yafi haduwa "kiyi shiru sis kifidda mijin kinji

Aunty maryam tace mata "kinga malama kitsahirta mana da kukan ya isa hakan.

Momy tace "kunga kukyaleta tayi mai isarta dole tayi shiru a

i.

Zannura bakin ciki da takaicine yasata wannan kukan son Abdulhakim ne aranta yanzu shikenan kanwar tace zata zama matarsa knn? Ko dai tafada ne kawai ko adawo mata dashi kanta.

Itanma mubina ranta ba dadi take jinsa domin tanada wanda takeso kuma

taga dai yaya Abdul ba sonta yakeba kawai dai Amintace ta yaya da kanwa tsakaninsu tokenan anxaci soyayya sukeyi yanzu yazatayi da nata saurayin dan fillo?

Abdulhakim dinma zufar dayakeyi bata dadi bace domin anmasa shigar sauri tunda a matsayin kanwa

ta ck guda yadauki mubina kuma sam bayajin zai iya son ta. To nawa ma take itada baifi watanni da gama sec.datayi yanzu yaya kenan bakuma zai taba iya bujirewa ba domin dady ubane cikakke yana masa ladabi da biyayya bai isa ayau yai masa musuba

Dady

yai tambayar duniya ga Abdul ko yanada ta cewa akan batul koda wacce ykso amma fafur tai shiru kamar yadda itanma mubina tayi

Ahaka taron yawatse babu mafita rai babu dadi domin Abdallah ne kawai ransa qal yasami mafita shikam yafidda kansa a gun dady

Yana zuwa gida sashin dije yawuce yataddata afalo tana kallo

Kai tsaye yakashe kallon dama yashiryi mata wulaqanci dan yana xaton ita tahadashi da iyayansa yau

Da daga murya tace "mallam meye hakan ?

Yace "na tsofaffine ?ko dasu kkzo? "Yar k

auye kawai

Ta bugi kirji da tsiwwa tace "fadi ka kara bana jin haushi dijen kauye nake kuma badasu nazoba amma kamar mallaki na suke tunda bakai kasakamin adakinba da kunnena naji agidanku ance kaf komai na gidan nan har gidan dadyne yabaka dan haka mey

e naka na gadara mallam.?

Yace

"Ohh!ranar da kikaje gulma da kai karar nasha giya knn? To karyarki muna fuka ke baki isa kihadani da iyayenaba don ayau na wanke kaina fadamusun da kkyi inashan giya baiyi tasiri aransuba kuma giya yanzu nafara sha.

Wannan kai tashafa kaida Allahnka.

"To inkinsan nida Allah nane meyasa baki barni dashiba kika gayawa su dadi kodon kin saba gulma.?

Tace "kai nafada da ban fadaba walh kai baka isa kayimin sharriba aiwalh danasan hakama dana fada din aikin banza

....saukar mari taji akuncinta har sau biyu

Ta dafe gun tana kuka ta zabura tayi kicin tatafi dauko madoki danta rama

Aikafin tadawo yafuce da sauri sashen Ni,ima

Ni,ima yau burinta yacika hakanta yacimma ruwa domin kuwa tatsala kwalliya ta gani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login