Showing 66001 words to 69000 words out of 70108 words
nonon yake ba fa kuma gashi yawan ci a gida take barin shi tunda tana zuwa makaranta" "to shikenan amma gaskiya yayi k'ank'a
nta da yawa ni da zaka bari ko wata biyar ya kara Amma yanzu fa ya shiga shekara daya dan dai ku y'ay'an zamani kun cika fitana ne amma ai Abdul be isa yaye ba komai shan nonon da bayayi".
Shuru yayi dai yana jin Ammi dan bata san matsalan da yake c
iki bane tashi yayi sannan yace, "Ammi ni na tafi sai gobe kuma" "to Allah ya bamu alkhairi" Ammi ta fad'a tana gyara ma Abdul riga.
Yana fita gidan su ya koma har lokacin bata bude kofan fa zaunawa yayi a Parlour yana tunanin abunda ya faru d'azu, h
ar dare yana zaune a Parlour ko abinci ya kasa ci sai kai kawo yake kuma ya buga kofar har ya gaji tki budewa.
Misalin karfe sha-biyu na dare ya gaji ya tashi ya tafi part d'in shi nan ma ya kasa baccin alwala yayi yazo yayi ta sallah yana rokan All
ah ya dai-dai ta shi da matar shi farin ciki shi, ita kam Deeyana tana can tana aikin kuka da k'yar ta tashi tayi wanka tayi sallah ta dauke Qur'ani ta fara karantawa.
Nan taji zuciyar ta tayi mugun sanyi duk abunda ya faru d'azu yayi ta dawo mata d
afe kanta tayi yanzu duk wannan rashin mutunci tayi ma mijin ta innalillahi mai ya rufe mata ido haka tayi ta mai wannan rashin kunyar, fashewa tayi da kuka tana rokan Allah ya yafe mata tashi tayi a hankali ta bude kofa ta duba baya parlour.
Tasan
yana part d'in shi nan ta huce part d'in nashi a hankali ta fara kwankwasa kofa, yana zaune kan sallaya yaji kaman ana k'wank'wasa mai kofa tashi yayi ya isa gun kafar ya bude idon shi na kan kofar Deeyana ya gani kan ta a kasa tsaye yayi yana kallon ta da
raunannin idanun shi.
Da gudu taje ta rungume shi tana kuka mai ban tausayi shima rungume ta yayi yana goge kwalla da ta cika mai ido, sun kusa minti biyar a haka can dai ta sake shi ta saka gwaiwar ta a kasa ta fara mai magana.
"Hayatee dan
Allah dan girman Allah kayi hakuri wallahi lokacin idona ya rufe ban san nayi ma wannan abun ba dan Allah ka yafe min wallahi fushin ka kaman wuta ce a zuciyata" saurin mikar da ita yayi sannan ya rungume ta ya sanya ta cikin kirjin shi yana cewa,
"Har abada na yafe miki ke ma ki yafe min Marin da na Miki kiyi hakuri" girgiza Kai Deeyana tayi da sauri sannan tace, "Wallahi baka da laifi ko daya insha Allah kuma zan raina cikin nan kaman yanda na Raina na Abdul" .
Shafa kanta yayi sannan yace,
"yawa Allah ya miki albarka" "ameen" Deeyana tace tana mai murmushi, daukan ta yayi cak ya kaita bedroom d'in shi ya daura ta saman bed nan da nan bacci ya dauke su.
Haka Deeyana ta cigaba da rainan cikin ta cikin kwanciyar hankali Dameer na ta
ya ta sabida kuyangu da da yace baya so yanzu duk ya dibo su, ko makaranta ma Deeyana ta daina zuwa Dameer yace ta dunga zuwa tunda dai cikin bamai laulayin bane tace, "Aa in ta haihu ta dunga zuwa" .
Abdul sai wayyon shi yake kara yi yana samun kul
awa sosai gun Ammi dan yanzu kowa yasan Deeyana nada ciki sai fatan Allah ya sauke ta lafiya kuma.
A kwana a tashi ba wuya yanzu cikin Deeyana ya shiga wata tara kullum sa ran haihuwa suke komai sun tana ja na haihuwa, tafiya ta kama Dameer zuwa Sa
udi Arabia jaddah bata da lafiya dole sai yaje sabida yaga jikin ta.
Dole sai manyan kuyangu aka dauka suna kula da Deeyana sabida kar haihuwa ta kamata ba wani babban a gidan, kwana uku kawai zaiyi a can ranar da zai tafi Deeyana tasha kuka wai sai
dai ya tafi da ita da k'yar dai ta barshi ya tafi.
*Kuyi hakuri da wannan*
๐
*Aunty Baby ce*
โ
๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ
๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ
๐ฆ๐ฆ๐ฆ
๐ฆ๐ฆ
๐ฆ
๐คด๐ป
*IZZAR SARAUTA*
๐คด
๐
*_ALHERI WRITER'S* *ASSOCIATION_*
โ
*~[ Al
heri danko ne, duk inda kayi shi zai dawo gare ka, burin mu mu ribantu da alherin da ke cikin wannan harka]~*
*ALHERI SAI DAN AlHERI*
๐
*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby*
โ
*DEDICATED TO..*
*
MY MUNAT*
*EESHAA*
*MAMUU*
*MINAT SS*
*AUNTY SARAH*
*Sadaukarwa ga UMAIMA ALIYU*
```My fan's ku taya ni murna da godiya gurin my khausar ta sadaukar da littafin ta gare ni, ya Allah ka sakawa wannan baiwar taka da alkhairi a gaskiya
naji dadi Wanda bazai tab'a musaltuwa ba ace littafin ta na farko ta sadaukar gare Ni ai ban san ma irin godiyar da zan mata ba naji dadi sosai Allah ya bar zumunci Allah ya daukaka wannan littafi nake ya kuma baki ikon isar da sakon da kike son isarwa amm
a naji dadi sosai nagode kuma kin nuna min kin san mutunci wasu ko hmmmm ba'a magana ai.```
*Wannan littafin nawa gaba dayan shi tukuici ne ga neat lady da miss Xerks Allah ya bar kauna da zamunci nagode sosai da irin gudunmawar da kuka bani a
rayuwata gaba daya ku ne sanadiyar fitowa ta social media bazan tab'a mantawa da ku ba Allah ya bar kauna har abada muna tare ya Allah ya bamu miji na gari dukan mu, d'an halak baya manta alkhairi komai k'ank'antar shi kuwa*
๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*
๐
*Page* 6
โฃ
9
โฃ
โฉ
7
โฃ
0
โฃ
________
๐
tun ranar da ya tafi take dan jin yanayin ta ya canja kullum da ciwan mara take kwana haka dai take daurewa sai ranar da ya cika kwana biyu da tafiya ranar bata iy
a bacci ba nan ta tashi tayi ta zagaye dak'in har dai kusan asuba sannan ta fito parlour.
Daya daga cikin kuyangu ta farka fitsari ta ganta sai zagaye dak'in take matsowa tayi ta fara tambayar ta ko lafiya cike da dauriya ta fara magana "je ki kira
min driver kice ya fito da mota zai kani hospital".
Da sauri ta tafi ta taso driver ya fito da mota nan ta sanya hijab ta fito ta shiga motan ita ma kuyangan ta shiga suka tafi hospital d'in, tun a hanya ta fara zubar da farin ruwa suna isa hospital
d'in kuyangan ta fita da sauri ta kira nurses.
Suka tawo da sauri suka dauke ta sai cikin labour room ko minti goma batai da shiga ba Allah ya sauke ta lafiya, ta samu dan ta namiji nurses d'in suka gyara ta da baby boy d'in ta sannan suka kaita da
k'in hutu lokacin har an idar da sallah asuba.
Kuyangan ce ta shigo dak'in ta tatda ta zaune saman bed ta dafe cikin ta da yake murda mata kad'an-kadan, cikin ladabi tace, "barka da sauka lafiya uwar dakina" murmushi Deeyana tayi mata dan bata jin z
ata iya magana, can dai kusan minti goma ta samu ta Mik'a mata wayan ta tace, "ta kira Ammi da Amma ta gaya musu" .
Wayan ta amsa sannan ta fara kiran Amma ta gaya mata cewa suna hospital sarauniya Deeyana ta sauka lafiya nan Amma tayi murna sosai,
nan sukai sallama ta kira Ammi ai ko aje wayan basu ba Ammi ta fara shirin tawo wa hospital d'in, kafin kace mai har zancen haihuwar yq badai masarautar mure.
Ammi ce ta fara zuwa hospital d'in lokacin Deeyana ta samu bacci, bed d'in da jaririn yake
taje daukan shi tayi da addu'a a bakin ta "masha Allah" tace, ganin irin Kyau jaririn shima dai kaman su daya da Dameer dan kaman yayi kaki ya zubar ko kad'an baya kama da Dameer murmushi ta dunga yi sannan ta dauke waya ta fara mai pic ko hmmmm bata ce m
a Dameer ba ta fara tura mai ta WhatsApp.
Wajan karfe takwas sai gasu gimbiya Aisha da marwa, sunyo breakfast har lokacin Deeyana bacci take sai jariri da ke ta wutsi-wutsin din shi, gimbiya Aisha da ta dauka yaron sai ta fara mai tsiya wai Abdul ya
fishi kyau ita kuma gimbiya marwa tace, shine mijin nata yafi Abdul kyau haka dai sukai ta musu Ammi na musu dariya dan tace, ita ta yarta take.
Jikin jaddah yayi sauki sosai shirin dawowa ma Dameer yake dan ya gama komai karfe sha-biyu jirgin su z
ai tashi zuwa Nigeria, wayan shi ya dauka ya fara kiran Deeyana dan yau basu waya ba amma a kashe yaji wayan sai kawai ya fara kiran Ammi, Ammi da ke zaune bakin Bed d'in da Deeyana take taji wayan ta na ringing dauka tayi tana murmushi dan tasan Dameer ne
.
Gaishe ta ya fara yi sannan ta tambaye shi jikin jaddah yace, alhamdllh taji sauki har dai suka gama wayan Ammi bata ji yayi maganar haihuwar Deeyana ba sai tace, "hala dai baka duba WhatsApp d'in ka bane?" murmushi yayi sannan yace, Ammi yau tun
safe ban duba wayana ba ma sbd tafiyan nan gashi jaddah ta matsa sai munji siyan wasu kayan baby's shiyasa".
"Ohh to ka duba zaka ga sakon da na turo ma" to kawai Dameer yace, sannan sukai sallama, WhatsApp d'in ya shiga nan ya fara cin karo da dun
bin mutane suna turo mai pic d'in baby boy ana mai barka duk be duba ba dai na Ammi da ya shiga nan ya fara ganin pic din baby boy kallon pic d'in yake cike da murna Deeyana ta haihu kenan allahu akbar nan yayi sunjada yana nuna godiyar shi ga Allah da ya
bashi komai na rayuwa yanzu yaran shi biyu kenan Allah kenan.
Da sauri ya fito daga dak'in ya isa su jaddah da ke parlour ya fara nuna musu pic din yaron nan murna ya barge ai ji yayi kaman ya jawo sha-biyu sabida kosawa da yayi yaje yaga Deeyana na
r shi da kuma sabon babyn da tayi mai.
Sosai mutane suka cika a hospital d'in kowa na murnan sabon baby da suka samu nan kuma Deeyana ta farka kowa na mata sannu da ya jiki aka kira nurse ta kara duba ta sannan ta mata wasu alluran, had'a mata tea
gimbiya Aisha tayi sannan ta zuba mata farfesun kayan cikin da aka yo mata, ta dan ci ba laifi sannan aka mika mata jaririn da sai yanzu ma ta dauke shi.
Kallon shi tayi kaman shi daya da Dameer shima murmushi tayi sannan ta fara bashi nono nan kuw
a ya cafke kaman jira yake ya fara sha sosai, murmushi gimbiya Aisha tayi sannan tace, "wai acici kenan wannan ai yafi kowa ci cibi daga bashi nono ya cafke kaman jira yake?".
Ita ma gimbiya marwa murmushi tayi sannan tace, "ba komai dai ai wayewar
kenan" haka dai sukai ta caftar su suna dariya ita dai Deeyana murmushi kawai take musu.
Sha-biyu dai-dai Dameer ya Isa airport Dan ya kosa yaga Deeyanar shi da kuma baby boy d'in shi nan da nan jirgin su ya tashi sai Nigeria, Deeyana Kam tana zau
ne sai tunanin Dameer d'in ta take ko ya sani oho Bata sani ba ita da badan su gimbiya Marwa ba tambayar Ammi zata Yi.
Dr ya shigo ya k'ara duba su lafiyan su lau ita da jaririn ta sannan yace nan da two hours zasu iya tafiya, k'arfe hudu dai-dai
jirgin su Dameer ya sauka Daman fadawa suna airport d'in suna jiran shi direct hospital d'in yace a huce da shi sabida hankalin shi gaba daya na kan Deeyana nan shi.
Lokacin su Deeyana kuma sun gama had'a komai zasu tafi gida har ma sun fito daga ho
spital d'in zasu shiga mota shi kuma Dameer d'in ya fito, da sauri ya k'ara su gurin su da murmushi a fuskar shi, k'amshin turaren shi kawai Deeyana taji tasan shine da saurin ta ta juya bayan ta.
Nan sukai ido hudu sakan mata wani shu'umin murmushi
yayi ita ma murmushi tayi, Ammi tace, "Aa Dameer Ashe kun sauka" "eh Ammi tafiya gida zakuyi haka? " yayi maganar yana kallon Deeyana.
Gimbiya Marwa tace, "eh tafiya zamuyi an duba su Alhmdllh basu da matsalan komai" jinjina kai yayi Ammi ta kama
hannun Deeyana suka shiga mota gimbiya Aisha da babyn yake hannun ta ta shiga dayan motar gimbiya Marwa kuma motar da su Ammi suke ta shiga shi kuma Dameer ya shiga motar da aka kawo shi suka tafi.
A hanya gimbiya Marwa take tambayar Ammi Ina za'a
huce da Deeyana Ammi tace, gidan ta sai a Kai mata ko wanda zata dunga mata wanka ne, gimbiya Marwa tace, "Aa gwara a kaita masarauta sabida gida daga ita sai shi akwai matsala".
Ammi tayi murmushi dan tasan halin y'a'yan nata sai tace, "ai Deeyana
yanzu ba yariya bace tasan yanda zatayi ta kula da kanta" to gimbiya Marwa tace, kawai nan aka drive ya huce dasu gidan su Deeyana, tana jin su addu'a take Kar Allah yasa Ammi tace, za'a kaita masarauta sabida tasan halin mijin ta gwara in a gidan su ne ta
san yanda zata tafiyar da kayan ta.
Suna isa gida duk suka fito a motar suka shiga cikin gidan bedroom d'in Deeyana suka huce tana shiga kwanciya tayi sabida cikin ta da ke matsa mata nan kuyangu suka fara daura abinci gimbiya Marwa kuma ta shiga to
ilet ta had'a ma Deeyana ruwan wanka sannan tace ta tashi tayi mata ko jinin ya sauka na in yaji ruwan zafi tunda shi yake sata ciwan cikin.
Dameer kam ko da suka iso yaga motocin su Ammi ba k'aramin dadi yaji ba sabida bai tab'a zaton Ammi zata b
ari a kawo Deeyana gidan su ba ai kon part din Deeyana ya shiga lokacin har an ma jararin wanka an shirya shi cikin kayan shi masu Kyau da tsari, da murnan shi ya dauka yaron.
"Woow Masha Allah" kawai yace sannan ya fara mai addu'a, "wannan ma kama
r mu daya" shine kawai abunda Dameer ya maimaita yana kissing d'in jararin haka Deeyana ta fito daga toilet ta samai shi ya manne shi a k'irjin shi sai murmushi kuma yake.
Zaunawa tayi bak'in Bed tana goge ruwan jikin ta da towel, kuri ya mata da
ido yana jin wani irin sonta na kara shiga ko wani bargo na jikin shi, turo baki tayi sannan tace, "kallon fa? " tasowa yayi daga inda yake ya matso kusa da ita sannan yace, habibaty bani ma da bakin gode miki Wallahi kin bani duk wani farin ciki na duniy
a Allah ya miki albarka ya raya mana yaran mu".
Murmushi Deeyana tayi sannan tace, "Ameen hayatee Ashe kana hanya ya jikin Jadda? " "Hmmmmm ko ban tashi dawowa ba ai dole na dawo kuma daman yau zan dawo nayi ta Kiran wayan ki ashe lokacin ma kina h
ospital" yayi maganar yana gyara ma jararin hular kan shi.
Haka dai sukai ta firan su har aka kawo ma Deeyana abinci dan Ammi ma ta tafi gida sai gimbiya Marwa da gimbiya Aisha kawai aka bari, ai kam tare suka ci abincin suna ta hiran su har aka kir
a maghrib Dameer ya tashi ya tafi dan yayi wanka yayi Sallah.
Bayan kwana shida yau ya kama ana gobe suna sai shirye-shirye ake yan uwa da abokan aziki duk sun zo dan tunda Deeyana ta haihu gimbiya mabaruka ta dawo gidan gaba daya sai kuma kuyangu
manya masu manyan shekaru da aka kara kawowa dan su dunga kula da Deeyana da kuma baby boy d'in ta.
Mai-martaba ya kira Dameer ya tambaye shi sunan da za'a sama jaririn yace, Aliyu shima ba k'aramin murna mai-martaba yayi ba dan yaji dadin yanda Da
meer d'in ke mai kara nan aka sanar a masarautar kowa ya shiga murna sarki Aliyu kuwa ai baki har kunne haka akai ta saka ma jaririn albarka.
Washe gari ya kama suna anyi shagali kala-kala sannan an rada ma yaro sunan shi Aliyu za'a dunga kiran shi da
jenior sosai Deeyana tayi murna da farin ciki dan b'ata kawo sunan Abban ta za'a saka ba haka aka yi taron suna lafiya aka tashi lafiya.
Bayan wata biyar Deeyana da jenior sunyi Kyau abin su har yanzu Abdul na hannun Ammi yana samun kulawa sosai De
eyana har ta cigaba da zuwa makarantar ta dan jenior bashi da rigima a gida take barin shi, shima Dameer kasuwancin shi yaci uban na da dan sosai kudi ke shigo mai sai abun alkhairi da yake ta ma talakawa.
Watan jenior goma sha-daya Deeyana ta daina
ganin period d'in ta tun da taga haka ta san ciki ne kuka kan tasha shi ba adadi har rama tayi sabida damuwa da ta saka ma ranta shi kam Dameer bai sani ba amma shima yaji ta canja mai ta ko ina ma kullum tambayar ta yake tace lafiya.
Akwai wata ra
na da ya kusance ta kwata-kwata manta kan shi yayi sai santi yake zuba mata yana tambayar ta wai menene sirrin ta zama kaman wani zuma baya gajiya da ita sai dai tayi murmushi kawai, haka har jenior ya shiga shekara daya cif lokacin ba in da baya zuwa sann
an tace ma Dameer zata yaye shi.
Da farko kin yarda yayi wai bai isa yaye ba tace, "Abdul ma isa yayan yayi aka yaye shi to shima wannan hakan nan za'a yaye shi" tun da tayi wannan maganar ya gane ashe ciki gare ta yayi murna sosaii dan har mota ya
siyo mata akan tukuici Allah ya sauke ta lafiya