Showing 12001 words to 15000 words out of 70108 words

Chapter 5 - IZZAR SARUTA COMPLATE

mai lallai ita ma sai ta gane kuranta.

Ita ma gimbiya Mabaruka bin bayan shi tayi cike da tashin hankali dan bata tab'a ganin b'acin rai ha

ka ba agun d'an nata, gimbiya Haleematun-Sa'adiya ma haka fada ta nufa jakadiya na mara mata baya.

D'akin ya zama daga gimbiya khaujut sai yarima Aliyu da yake kwance cikin bakin ciki, shi a gurin shi ma gwara mutuwar shi da wannan ranar wai ace yay

an shi na zargin shi da neman matar shi wani irin kuka ne yazo Mai mai karfi wanda besan ya sake shi ba.

Waziri na isa fada ya zauna a gurin zaman shi yana kai gaisuwa ga sarki, haka ma malamin fada ya shigo shima ya kai gaisuwa sannan duk suka nuts

u suna jiran abun da sarki zai ce dan fuskar tashi ta yau ta basu tsoro.

Magana ya fara cikin IZZA aje a dauko mai yarima Aliyu sannan a kira gimbiya khaujut, jikin waziri na rawa ya fara gayawa fadawa sakon sarki.

Ido kawai gimbiya Mabaruka ta z

uba ta kasa cewa hmm balle hummm gimbiya Haleematun-Sa'adiya kuwa murna fal ranta ji take kaman ta zuba ruwa a k'asa tasha.

Duk wani babba na cikin masarautar mure sai da mai-martaba sarki Fahad Abdullah yasa a tara, haka gimbiya khaujut tana zaune

guri daya a fadan, ta rasa ma ya zata yi ji take daman Allah ya dau ranta ta huta ko kuka ta kasa.

Kallon kowa na fadan sarki Fahad Abdullah yayi sannan yayi gyaran murya ya fara magana kaman haka,

"Malam ina so ka gaya mun huguncin wa'inda

suka aikata zina".

Malam isa muhmud yace, "to hukuncin wa'inda suka aikata zina shine, in namiji ne wanda beyi aure ba za'a mai bulala dari, sannan mace mai aure za'a jefe ta".

Shuru mai-martaba yayi sannan ya kalle gimbiya Haleematun-Sa'adiya y

ace, "a wani irin Yana yi kika tsince su?".

Gaban gimbiya Haleematun-Sa'adiya ne yayi wani irin fadu wa dum dum dum jikin ta ya fara rawa sannan tace, "ummmmm hummm mmmmm wanka naga sun fito".

Kallon ta yarima Aliyu yayi sannan ya fashe da kuka y

ace, "insha Allah in Allah ya yarda baza ki gama da duniya lafiya ba wannan sharrin da kikai mana bazai..." Tsawa mai-martaba ya daga mai sannan yace,

"Aliyu a matsayin ka na kanina wanda muka fito ciki daya bazan iya ganin ka shiga wani hali ba amm

a zabi daya zan baka shine daga yanzu d'in nan da nake ma magana ka tattara duk wani abu naka ka bar masarautar nan daga yau ba kai babu wani a ahalin na masarautar nan".

"Innalillahi wa'inan ilaihir rajiun" shine kawai abunda mutana fadan suke fad'a

dan hukuncin yayi tsauri da yawa amma ya zasu tunda mai-martaba ne ya yanke.

Gimbiya Mabaruka tace, "ya kamata kayi binkice ba ka yanke hukunci haka nan ba ko annabi ya hane mu da yanke hukunci cikin fushi".

Girgiza kai yayi be daiyi magana ba

sannan ya cigaba da cewa, "ka tashi kafin in sa a fitar da kai".

Kuka yarima Aliyu ya k'ara fashewa da shi sannan ya tashi jiki a sanyaye ya nufi gurin mai-martaba durkusawa yayi a gaban shi sannan ya rik'e k'afar shi yace,

"Ba wai zan fad'a

wannan maganar bane Dan kar in fita daga masarautar nan A'a dan in kare mutuncin matar yayana ne gimbiya khaujut, Wallahi Wallahi na rantse da Allah bamu aikata abunda ake zirgin mu ba insha Allah in dai na taba aikata zina ya Allah yasa kar in k'ara numfa

shi a yanzu nan".

Gaba daya fadan ya ba koya tausayi gimbiya Mabaruka tashi tayi ta rungume shi tana kuka amma shi kon mai-martaba sarki Fahad Abdullah ko a jikin shi.

Zamai jikin shi yayi a jikin gimbiya Mabaruka sannan yace, "dan Allah ki yaf

e min in na miki laifi dan nasa ni da in k'ara tako masarautar nan har abada" be jira amsar ta ba kawai ya juya ya fita a fadan.

Fada tayi tsit ana jiran hukuncin da za'a yanke ma gimbiya khaujut kuma wacce gaba daya kaman ma batq san mai ake yi ba

bata cikin haiyacin ta.

Ko kallon gimbiya khaujut baya son yi shiyasa yace kawai ta tashi ta shirya yau zata koma k'asar ta sannan kuma a bisa alfarmar da yayi mata shine ya sake ta be dai fad'a ko sake nawa bane sannan awa daya ya bata ta gama shir

ya komai nata.

Kukan da take ta fata yazo shine sai yanzu ya zo ta fashe da kuka mai cin rai sannan ta tashi ta fita a fadan, Nan yace, kowa zai iya tafiya.

Tana shiga bedroom d'in ta kuka ta kara fashewa da shi tana data sanin auran shi har ta

rabu da iyayan ta akan shi sannan ya riga da ya gama da rayuwar ta tun tana shekara sha-bakwai.

"Innalillahi wa'inan ilaihir rajiun yanzu ma zata je ta gayawa Iyayan ta zasu barta a gidan su ko zasu kore ta" wannan abu shi yafi tsaya mata a rai ba

wani kaya ta d'iba ba kawai ta saka abaya da ta fito.

Part d'in gimbiya Mabaruka kawai ta shiga ta mata sallama kuka sosai gimbiya Mabaruka take yi tana k'ara bata hakuri, haka nan sukai ta kuka sannan gimbiya khaujut ta mata sallama sannan ta fito.

Kilisar mai-martaba ta huce akwai taci sa'a yana nan hawayen da suke zuban mata ta share sannan tace, "Wallahi bazan tab'a yafe ma ba a duniya tun da ka shigo rayuwata ka ruguza min farin ciki na sannan yanzu ka sake ni akan abun da banji ba ban gani

ba insha Allah sai Allah ya min sa kaiya" sannan tayi hanyar fita har ta kai kofa ta jiyo muryan shi yana cewa,

"Ki shirya min d'ana Ina nan zuwa amsar shi" ko sauraran shi batai ba ta fita, waziri ya kira sannan yace, fadawa su kaita har airport sai

sunga jirgin su ya tashi sannan su dawo yanda yace, kuwa haka akai waziri da kanshi ya kaita airport dan ba k'aramin tausayin ta yake ji ba.

Taci sa'a kuwa ba'a dade ba jirgin su ya tashi, tun da ta shiga jirgin kuka take har dai Allah ya kai su lafi

ya direct gidan su ta wace lokacin wajan karfe biyu na dare.

Tana isa tayi noking aka bud'e mata sannan ta shiga lokacin Iyayan nata na parlour duk, ganin ta kawai sukai kaman daga sama abun ya Basu mamaki ba waya ba komai.

Yanda suka gan ta

ne abun ya basu tsoro idon ta gaba daya yayi ja kuma har lokacin kuka take, da sauri maman ta ta tashi ta rungume ta tana Shafa kanta, kukan ta kara fashewa dashi tana cewa su yafe Mata.

Baban yace, wani irin yafiya kuma ko wani abun ne ya samu miji

n nata, shuru tayi kawai tana kara shartar hawaye.

Zubewa kasa tayi sannan tace, "abun da kuke ta nuna min kenan lokacin ban gane ba daman yan Nigeria basu da rokon Amana wai yanzu Abban Dameer ya sake ni" sai ta kara fashewa da kuka.

"Innalilla

hi wa'inan ilaihir rajiun" shine kawai abunda babanta yace zufa ne ya fara zubo mai lallai yaron nan ya cika maci Amana yanzu duk irin sharudan da suka kafa mai sai da ya musu wannan abun.

Rungume ta maman ta tayi tana kara lallashin ta akan haka

Allah yaso basu da yarda zasu yi kuma insha Allah sai Allah ya saka mata.

Washe gari.

Ko da Dameer ya tashi ya ganta yayi murna sosai sai tambayar Ina Abban shi yake kawai yake yi, sai tace Mai zai zo ya gan shi har yaron ya manta da abun.

Hak

a ta saka kanta a damuwa Bata cin abinci bata wal-walan ko yan uwan ta sun zo bata sakin jiki da su kullum cikin kuka take, gashi yanzu wani irin so take Mai da shi yake wahalar da ita.

Maman ta da baban ta burin su ta manta da komai ta barshi ta rain

i yaron ta Amma Ina abun yaci tura, har Al'mustapha ya dawo ganin gida ko da yaji abunda ya faru cewa yayi bazai yarda ba sai ya dau Mata fansa tunda shi ba Dan halak bane tunda har yayi wa khaujut wannan rashin mutuncin.

Iyayan su ne sukai ta bashi

hakuri akan ai aikin gama ya gama ya barshi kawai zai girbi abunda ya shuka, hakan nan yayi hakuri ba dan son ranshi ba.

Ita kuma khaujut yace ta shirya su tafi Dubai d'in tare ko acen ta cire damuwar da ta daura wa ranta da da farko cewa tayi baza t

a ba Dan bata son tayi nisa da yaron ta Amma daga baya da aka Mata mgn sai tace to.

Haka nan suka shirya suka tafi aka bar Dameer a hannun iyayan ta yaci gaba da zuwa makarantar shi, Daman ba wani Sabawa yayi da ita ba shiyasa be damu ba.

Yar

ima Aliyu kon ko da ya fita daga masarautar be San in da zashi ba tafiya kawai yake har Allah ya Kai shi wata kasuwa, nan ne da yaga mutane ya zauna a wata yar runfa mutane sai kallon shi suke tunda sanye yake da kayan sarauta.

Da yaga kallon yayi y

awa sai ya shiga wani shago a kasuwar ya siyo wasu k'ananan kaya da yan kudin da ya fito da shi a jikin shi sannan ya cire wannan kayan sarauta da ke jikin shi ya sanya wannan wanda ya siya, ragowar kudin kuma ya siya abinci.

Haka ya koma rufar nan

ya zauna har dare kowa ya ta tashi a kasuwar sabida dare yayi ya tafi gida shi kon bashi da in da zashi sai kawai ya jera kwali a runfar yayi kwanciyar shi.

Haka ya kwana a nan sai da asuba ya tashi ya alwala yayi Sallah sannan ya k'ara zaunawa a cik

in runfar, haka har mutane suka fara zuwa kasuwar kowa na siyar da abunda yake siyar wa har dai yamma ta k'ara yi.

Ga wata irin yunwa da yake ji bashi da ko sisi haka ya kwanta yana tuna irin rayuwa da yake da, a kwai wani mutumi da tun jiya yake lura

da shi ya kasa dauke ido a kanshi gani tunda ya shigo kasuwa yana zaune a runfa kuma shi ba wani abu yake siyarwa ba.

Kau da idon shi yayi a kan shi yaci gaba da kasuwanci shi har dare yayi zai tafi gida, runfar ya k'ara lekawa har lokacin Yana kwanc

e sai yaji bazai iya tafiya ba tare da ya tambaye shi menene yasa yake zaune tun jiya a runfar ba.

Sallama yayi mai yarima Aliyu da ke kwance yaji ana mai sallama sai ya tashi zaune yana kallon wqnnan bawan Allah, hannu ya Mika mai suka gaisa sannan

mutumin yace,

"Dan samari lafiya kuwa kike zaune anan tun jiya ko bata kayi ne? ".

Girgiza Kai yarima Aliyu yayi sannan yace, "ba Bata nayi ba kawai Ina zaune ne kafin na samu warin zama".

Kallon shi mutumin yayi sannan yace, "wurin zama

kuma Dan samari Kai bako ne kenan? ".

Kai ya d'aga Mai alamar eh, mutumin yace, "in ba damuwa ka taso in Kai ka gida na wala Allah ko gobe sai ka tafi Amma kwana a kasuwa ai hadari ne".

Girgiza Kai yarima Aliyu yayi sannan yace, "ai bansan yaush

e zan samu gidan ba na gode kawai baba sannan ya juya ya kwanta".

Tsayawa mutumin yayi tsaf yana kallon shi kaman yana cikin damuwa Amma zai taimaka mai tunda duk Wanda ya taimake wani Allah zai taimake shi, sannan yace, "dan samari akwai wani Abu d

a yake damun ka ka fada min insha Allah Zan taimake ka".

Hakan nan yarima Aliyu yaji mutumin ya kwanta Mai kawai sai ya tashi zaune wasu zafafan hawaye suka wanke mai fuska sannan ya fara ba mutumin labari Wanda ya boye Mai abu daya cewa shi d'in Da

n gidan sarauta ne cewa yayi kawai matar yayan shi ta mai Sharri shida amaryar matar yayan nashi.

Mutumin ya tausaya mai sosai sannan yace insha Allah zai taimake shi ya dauke shi kamar uba shi kuma zai dauke shi d'a yana da Mata daya da yara biyu duk

a Mata in zai Iya zama da su to bashi da matsala kuma yasan matar shi ma haka.

Daga Mai Kai kawai Aliyu yayi sannan mutumin ya rik'e Mai hannu suka fita a runfar mashin din mutumin suka hau daga Nan suka wace gidan shi.

Ko da suka je gidan mutu

min ya shedawa matar shi halin da yaga yaron ita ma ta tausaya mai sosai sannan tace, "insha Allah zasu rike shi hannu bibiyu shima ya dauke su iyayan shi ya zama Yaya kuma a gurin 'ya'ya su" yace, "insha Allah" sannan aka Kai shi daki aka bashi abinci.

Washe gari haka aka kawo Mai abin Kare sannan yaran Mata suka shigo suka gaishe shi baban yace, ga yayan su nan su shima aka nuna Mai su akan ce ga kannin shi nan.

Tun daga lokacin ya saki jikin shi dasu Mariya wacce suke ce ma mama tana bashi ku

lawa sosai da sosai haka shima yana ba Yan yaran kulawa da babban mai suna fateema sai k'aramar mai suna Faiza.

Fateema shekaran ta sha-bakwai sai k'aramar Faiza shekaran ta sha-hudu, Nan da nan suka saba sosai da sosai.

Ya fara bin baban kasu

wa, a hankali ya fara koya mai kasuwanci har ya saba, suna dawowa daga kasuwa zasu zube parlour suyi ta hira wani zubin hiran duk fad'a ne shida fateema mama tayi ta musu dariya.

Haka Yarima Aliyu yake ta rayuwa a gidan be tab'a nuna musu daga in da

ya fito ba, shakuwa na Kara shiga tsakin su da fateema, wanda daga gani kasan soyayya ce.

Tunda mama ta fahince da kwai soyayya a tsakanin su sai ta sanar da baba yayi farin ciki sosai da jin haka dan D'an zaman da yayi da Aliyu ya karanci halayan sh

i mutun ne Mai son ibada sannan kuma ga amfani dashi.

Haka ya tara Aliyu da fateema ya tambaye su ko suna son junan su k'asa Aliyu yayi da Kai Dan har cikin zuciya shi yake son fateema nan baba ya fahinci shi kunya yake ji itama fateema haka ne tana

masifar son Aliyu shiyasa ita ma ta k'asa da Kai harda boye fuska a hijabi.

Mama da baba duk duka sa ta dariya nan baba yace, "ya tsayar da ranar aure wata daya tunda duk gida ne ba sai anyi wani Abu ba".

Farin ciki da Aliyu ya shiga ciki ba'a

magana kuka kawai ya fashe da shi yana k'ara gode ma baba akan dawainiyar da yake da shi.

*************

Masarautar mure kuwa tun daga wannan lokacin mai-martaba sarki Fahad Abdullah ya canja gaba daya, duk wani adalci da yake ya daina duk wata mak

aranta da ya bud'e sai da ya maida ta ta kudi.

Islamiyya da ya bud'e ya maida ta ta kudi asbitocin shi komai dai mulkin shi ya koma IZZAR abu kad'an zakai a yanke ma hukunci.

Gaba daya yanzu garin tsoron shi ake da mulkin shi kuma kwata-kw

ata besan adalici ba IZZAR SARAUTA kawai ya sa a gaba.

Bayan wata daya da yin wannan abun aka daura Mai aure da Mata biyu gimbiya Marwa da gimbiya Aisha, ya mance shafin wata khaujut ko D'an shi ma Sai wata ran ne yake Tina wa yana da d'a Amma kwata-k

wata yaji baya son shi.

Jin tsanar yaron kawai yake shiyasa ya yanke ma Kan shi hukunci ya bar Mata Dan tayi duk yanda take so da shi, gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta zama hamshakiya a masarautar mure sai abunda tace ayi ake yi.

Gimbiya Mabaruka

nata Ido bata cewa hmmm Bata cewa ummmmm sai yanda sukai, gimbiya Marwa ta samu ciki Amma shima be zauna ba ya zube ita kam gimbiya Aisha bata tab'a ko batan wata ba.

******

Shirye-shiryan biki ake fateema da Aliyu Wanda ba wani bidi'a zasu yi ba

walima ce kawai bayan daurin aure, haka kon aka yi an daura aure lafiya an tashi lafiya.

In da akai walima kowa ya tafi cikin farin ciki, wani dan matsakaicin gida baba ya gina musu Wanda ya ba Aliyu halak malak, Aliyu har rasa bakin godiya yake Dan a

bun da baba yake Mai ko mahaifin shi sai haka.

An Kai amarya fateema gidan ta lafiya Wanda aka barta daga ita Sai mijin ta Aliyu, nisiha Aliyu ke Mata sosai Mai ratsa jini da jijiya sannan suka gabatar da Sallah bayan sun idar suka ci kaza daga nan Al

iyu ya mori amarcin shi.

🙈

Alhamdulillah komai Yana tafiyar musu dai-dai Aliyu Yana da Dan rufin asirin shi haka yake taltalin fateeman shi har Allah ya basu rabo, baba da mama sunyi farin ciki sosai da addu'ar Allah ya sauke ta lafiya.

Wata Ta

ra cif Allah ya sauke ta lafiya ta samu yarta mace, wacce aka sa mata sunan mama suna mata lakabi da Deeyana, Aliyu ya dauki san duniya ya daurawa Deeyana .

Deeyana nata girma Masha Allah ga shegen wayyo, har aka yaye ta suna ta rainon yarsu ciki so d

a Kauna har ta kai shekara uku Aliyu ya sanya ta a mkrt yariyar ta taso da wayyo da kok'ari kowa burge shi take.

Deeyana tun tana karama kyakyawa ce sosai fara ce sol ga gashi Dan komai uban ta ta biyo Aliyu..

*****

Dameer yayi girma ya za

ma kyakyawan saurayi jinin larabawa ajin karshe ga kyau ga ilimi lokacin da ya Kai shekara 20 a duniya ya matsa ma kakan nin shi akan sai sun kaishe Nigeria yaga mahaifin shi.

Haka nan khaujut ba yanda ta iya ta shirya suka tawo Nigeria hotel suka far

a sauka sannan washe gari ta Kai shi har kofar Gate d'in masarautar mure, tace, ya shiga ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login