Showing 69001 words to 70108 words out of 70108 words
kuma zata ga babban kyautar da zai mata.
Nan suka had'a kayan jenior gaba daya rabar jumm'a suka shirya suka kai shi gun Amma ita ma fad'a ta fara musu sai daga baya ta fahince kaman ciki Deeyana take
dashi sai tayi shuru kuma, Ammi kam tun da taga sun kawo jenior tace, "Allah ya sauke ki lafiya dan tasan ciki ne".
Haka kam Deeyana tayi ta rainon cikin ta har Allah ya sauke ta lafiya ta k'ara samun danta namiji wanda aka saka mai sunan mai-martab
a tsohun sarki Fahad wayyo shima anyi shagali har ake ce mata uwar maza su uku duk maza Abdul jenior sai kuma Fahad shi Ba'a boye sunan shi ba.
Shekaran shi daya da wata uku ta samu wani cikin wannan karon ko hmmmm bata ce ba a zuciyar ta tace ba wa
nda zata kaima yaye ai sai a gaji da ita ma ko Dameer ta kasa gayawa tana da ciki dai rainon abinta take kuma tana ba Fahad nono har ya kai wata biyar lokacin Dameer ma ya riga ya sani.
Ayusha ta haihu xasu tafi suna anan ne Ammi ta san Deeyana nada
ciki fasa zuwa sunan tayi ta amsa Fahad d'in tace, "a yaye shi haka tunda yanxu shekaran shi daya da wata bakwai ai ya isa yaye kar shan cikin da yake kuma ya saka mai wani cutar".
Nan Dameer da Deeyana suka tafi Saudi Arabia satin su biyu suka daw
o Nigeria, Dameer ba k'aramin kulawa yake da Deeyana ba dan gani yake kaman rabin ran shi ce duk ranar da aka ce ba Deeyana to yana ji bazai tab'a kara numfashi a duniya ba ita ma haka ko tafiya Dameer yayi bata iya bacci shiyasa yanxu baya tafiya ta kwana
ko da kuwa kasashan waje ne.
Cikin ta har ya shiga wata goma shuru kullum cikin addu'a ake Allah ya sauke ta lafiya in ta zauna tayi shuru tace, "to ko dai mutuwa zatayi" haka dai har wata ranar talata Allah ya sauke ta lafiya ta samu yaran ta tw
in's duka mata masu kama da juna gashi komai na Deeyana suka yo.
Fadan irin farin ciki da masarautar mure ta shiga baya musaltuwa tun da ta haihu kullum sai an yanka ragona da shanu har ranar suna ranar irin kyautar da mai-martaba tsohun sarki da
sabon sarki sukai baya faduwa, haka uban gaiyar ma yarima Dameer.
Haka dai akai suna lafiya aka tashi lafiya yara sunci sunan Ammi da Amma wanda za'a dunga ce musu Nihal da Nayal, Abdul da Fahad suna gun Ammi jenior kuma na gun Amma.
Dameer a
je komai nashi yayi ya dawo gida gaba daya yana kula da habibaty shi da yan twins d'in shi wanda suke ta girma abin su, yayi yayi ma Deeyana ta koma makaranta taki sabida tace, bata ga amfanin karatun ta ba tunda ko ta fara ciki zai tsayar da ita, murmushi
Dameer yayi sannan yace, "hakan nan zaki daure ki cigaba da zuwa bana so kiyi ta wasting time d'in nan a banza".
"Hmmmmm hayatee kenan to ya zanyi tunda haka Allah ya tsara min ciki da goyo sai dai fatan Allah ya shirya mana su cikin tafarkin islam
a" Deeyana tayi maganar muryan ta a raunane.
Rungume ta yayi sannan yace, "Allah ya miki albarka Deeyana ina son ki ina sonki Deeyana Allah ya barmu tare har a aljanna" ita ma Deeyana rungume shi tayi tana sakan mai zafafan kiss shima ya fara mayar
mata daga nan suka cilla wata duniyar.
๐๐ฟ
โโ
Bayan shekara biyar.
Zaune na hango sarauniya Deeyana a tafkeken parlour ya tsaru iya tsaruwa yara ne wanda baza su wuce shekaru biyar ba su biyu duk mata daga gane dai twins ne Nihal da Nayal sa
nyi cikin uniform din makaranta sun dawo da gudu suka rungume "Deeyana suna cewa Momy Momy mun dawo".
Ita ma rungume su tayi tana murmushi sannan tace "wow twins d'in Momy sannun ku da dawowa ya school d'in anyi karatu da kyau dai ko?".
Daga
kai sukai sannan suka fara cire duguwar rigar tasu kuyangu ne suka shigo da sauri suka gaishe da Deeyana sannan suka kama hannun yaran suka tafi dasu dan su shirya su su baau abinci, Abdul jenior Fahad duk suna gurin su Ammi, tun daga kan twins Deeyana bat
a Kara haihuwa ba ta cigaba da karantun ta har yanxu ta kammala.
Amma Dameer ya hana ta zuwa aiki wai aikin jarida bai dace da ita ba dan ta matsa ne ma yasa ya barta ta karanta miss communication d'in.
Da daddare misalin takwas Dameer ya daw
o cike da daukin ganin tauraruwar shi ai kam ta tare shi da murnar ta ita ma tayi mai shiri sosai ga abinci da ta had'a mai kala-kala wanka ma ita tayi mai bayan sun fito ta shirya shi kaya ta fito mai dashi mara su nauyi wanda baza su takura mai ba sannan
ta riko hannun shi sukai wajan dining table.
Sai da yaci ya koshi sannan su twins suka zo wajan shi nan suka fara wasa yana ta biye musu sai gurin goma na dare sannan yaran suka tashi suka ce "Momy Daddy bye good night".
Hannu Dameer ya d'aga
musu sannan yace, bye twins d'in Momy ayi addu'a in za'a kwanta" suka ce to sannan suka tafi tashi Deeyana tayi ta bisu sai da taga ko wacce fa hau Bed d'in ta sannan ta musu addu'a duk ta shafa kan su sannan ta fito daga dak'in nasu ta dawo gurin oga Dame
er.
๐คญ
Tun kafin ta karaso ya taso ya sure ta sai Bedroom d'in shi yace, "yau sai sun saman ma twins k'ani ko kanwa".
To ni kam aunty baby nace a buga kwallo da kyau har aci sa'a ta fad'a raga
๐คฉ
.
*TO ALHAMDULILLAH A NAN NA KAWO KARSHEN
WANNAN LITTAFI NAWA KUSKURAN DA NAYI A CIKI YA ALLAH KA YAFE MIN ALLAH YASA SAKON DA NAKE SON ISARWA YA ISA KAMAN YANDA NAKE SA RAI*
~Godiya ta musanman gare ku masoyana Allah ya bar kauna nagode sosai da irin kulawar da kuke bani Allah ya bani i
kon fadakar da ku dai-dai, sai kun sake jina a sabon littafai na kamar haka *MIJIN FATIMA* and *NAHEEDARH* ku dai kuci gaba da kasancewa tare dani *NAHEEDARH* labari ne mai ban tausayi soyayya da kuma nishadi insha Allah first January zan fara suburbudo mu
ku Allah dai ya k'ara min lafiya~
*Naheedarh*
*MIJIN FATIMA*
*Coming soon*
๐
*Aunty baby ce*
โ