Showing 66001 words to 69000 words out of 172372 words

Chapter 23 - AUREN KWANGILA BOOK1 COMPLETE

suna bin falon da kallo suna murmushi.

Maida kofar tayi ta rufe sannan ta qaraso ciki tana musu tayin zama cik

in fara'a

Babu musu duk suka zauna

"Bari nakawo muku ruwa" tafada cikin turanci

Dakatar daita daya tayi dacewa

"A'a yar uwa, murda ga gidanmu nan kusada ku, bawani tafiya mai tsawo mukayi ba kuma ma sanyi ake ba'a cika shan ruwa ba"

Murmushi

saudart tayi sannan ta koma ta zauna tana cewa

"Kenan Ku maqobtanmu ne?"

"Eh mana, fa gidanmu nan No 35 Itakuma wannan No 37" inji Wanda tayi magana dazu

"Wow, nice to meet you" tafada cikin Sakin fuska.

"Thank you, sunana Loveth wannan kuma Rey

na" inji mai maganar

"Wow nice name, ni sunana saudart" tafada tana murmushi

"Wow nice name too, amma Ku baqi ne ko?" Inji Wanda aka kira da Reyna

"Eh kwananmu biyu yau" saudart tabasu amsa

"Ayyah ai naganku jiya dazaku fita, banma San akwai mu

tane saida naganku jiya" inji Loveth

"Ai saboda bamu Dade bane shiyasa" saudart ta amsa

"Ok, dama zuwa mukayi muji zaki samu zuwa wajen hada kayan Good Friday?"

"Good Friday?* inji saudart cikin Rashin fahimta

"Eh, good Friday wani taro ne haka

mukeyi duk ranar Friday, duka yan yankinan zasu hadu don zumunci, anan muke sanin baqin dasuka shigo kuma mu qulla zumunci" inji Loveth

Reyna ta Dora dacewa

"Akwai wata mata a block 39, doctor ce kuma duk ta fimu shekaru, a gidan ta duk muke taruwa mu

hada kayan da za'a dan ta6a a gathering din, muna zuwane da marece mukama aikin ayi agama da wuri, idan zaki samu damar zuwa saiki leqo ayi dake"

"Wow yayi kyau sosai, insha Allah zan leqo idan nasamu dama" inji saudart tana murmushi

"To Allah yasa"

suka fada suna tashi zasu tafi.

Har waje ta rakasu suka nuna mata gidan doctor din daga nesa sannan sukayi sallama suka tafi.

*5:00pm*

Fitowa tayi cikin shigarta ta doguwar rigar atamfa mai A shape ta Dora Jan rigar sanyi mai hula akai kasanc

ewar cikin atamfar akwai kalar ka, wannan karon ta Dora hular rigar sanyin.

Hannunta daya riqeda wayarta dayan kuma riqeda makullan gidan.

Direct gidan dasuka gwadamata ta nufa tana tafe tana qarewa surrounding din dayayi tsit kallo.

Tun kafin t

a isa gidan tafara jin hayaniya da shewa shewa na fitowa daga gidan ga qamshin girki daya fara ziyartar hancinta.

Ida Qarasowa tayi tana kallon kofar gidan da akasa *39* agaban gidan

Ahankali tafara bugawa amma kasancewar cikin akwai hayaniya sosai b

abu Wanda yajita.

Ganin haka yasata fara bubbugawa da qarfi.

Ta dan Dade tana bubbugawa sannan tajiyo taku alamun ana tahowa hakan yasata gyara tsayuwarta tana kallon kofar.

Ana budewa tayi ido hudu da Reyna dake sanye da apron.

"Yeah! Gatanan

tazo" tafada tana leqa bayanta da alamu da mutanen ciki take

Kan kace me? Sai gasu sunata leqowa don ganinta

Murmushi tayi cikin jin kunyar yadda suka zubamata idanu

"Hyy" tafada tana dagamadu hannu

"Hello... Hyy...hey" duk suka amsa gabadaya

suna mata murmushi

Loveth ce ta leqo sanye da apron hannunta duk fulawa da alamun kwabi take.

"Welcome saudart, Ku matsa tashigo mana, kunwani tare hanya" tafada tana kama hannun saudart suna shiga ciki, taja hannunta har kitchen din gidan Wanda

duk tsarin gidan irin nasu saudart ne kawai banbancin kayan ciki ne

Wata mata Wanda aqalla zatakai shekaru 40 suka gani da wasu yanmata suna aiki suna fira.

"Dr zahra, ga baquwar nan tazo"

Nan duk suka dago suna kallonta

"Wow she's so cute, w

elcome baquwar mu" tafada tana Qarasowa wajen ta tana murmushi

Itama murmushin ta maidamata tana gaidata sannan suka gaisa da duk yanmatan gidan sannan aka koma bakin aiki.

"Amma daga Africa kike ko?" Inji Dr zahra

"Eh daga Nigeria"

"Wow, ni

daga Pakistan nake amma na ta6a zuwa Nigeria, a wane state kike?"

"A kano state" inji saudart tana amsar wuqar dake hannun Dr din da cabbage datake yankawa.

"Ohh nikuma Abuja naje, ai Nigeria is a lovely country, har yanzu nakasa mantawa daita" inji

Dr zahra din

Haka sukaita fira a tsakaninsu, dayake saudart batada baqunta nan da nan ta ware duma fira kamar sun Dade da sanin juna sai tsokanar juna suke.

Babu abinda ke tashi a gidan sai hayaniya da darairaku.

Sosai saudart taji dadin zuwa gida

n don tasamu nishadi sosai, da yanzu tana can qunqume cikin gida babu abokin fira.

Abinka da aikin yawa nan da nan suka kammala komai.

Tare dasu Loveth suka fito daga gidan suka Kamo hanyar gida suna tafe suna fira har suka iso gidansu saudart.

Lo

kacin har anfara kiraye kirayen magrib. Sallama sukayi da juna akan saisun hadu anjima.

*************************************

Tsaye take gaban gadonta sai kallon kayyayakin data baza kan gado take tarasa Wanda zata za6a don ruwan ido.

Can

dai ta dauki wata dark purple din Arabian gown din roba mai dogon hannu tareda farar jacket marar hannu mai gashi ajiki Wanda takawo har gwiwa sannan ta yane kanta da farin gyale.

Kamar kullum yauma simple makeup tayi, sai kuma purple janbakin datasa ab

aki ta feshe jikinta da turare mai sanyin qamshi sannan ta dauki wayarta ta fito.

Direct gidan Dr zahra tanufa.

Nan ta tarda su Loveth da sauransu ansha gayu sai hada hadan fita da abinci suke.

Suna ganinta suka ja suka tsaya baki bude suna kall

onta.

Qarasawa tayi tana rufemasu baki tana cewa

"Kurufe kar quda yashiga" tafada tana hararsu

Sai a sannan sukadan sun bude baki

"Wow saudart, you look soo takeaway!" Inji Reyna

"Ni banma ganetaba dafarko na rantse" inji Loveth

Wata yar

Korea mai suna chuchu tace

"Anya are you sure you're a Nigerian? Ni idan aka fadi Nigeria the first thing dake zuwa min arai shine baqaqe, munana, gajeru..." Hararar da saudart ke antayamata ya hanata qarasawa tafara dariya

"Nikuma idan akace Kore

a Abu na farko dake zuwa min arai shine mitsi mitsin idanu, qurmemen goshi, tsawo kamar pole sai nannanan hanci" saudart itama ta rama.

Nan duk aka kwashe da dariya, nan fa aka Dora kan inda aka tsaya dazu, suna kai abinci suna cafta har suka gama, nan

suka fito suka zauna.

Wajen filine kamar filin kwallo qasan shimfide da Grass carpet, koina fayau kamar ba dareba.

Mata na daga bangaren haggu sun hada group dinsu hakama maza a bangaren dama sai cafta suke Wanda be wuce ta kwallo ko wrestling.

Sai gashi estate din dake tsit kodayaushe yau tacika da hayaniya yadda kukasan sallah ake ko wani gaggarumin Abu.

Saudart na can tsakiyar yanmatan tana maida yadda akayi, yadda kukasan ta Dade da saninsu, kusan itace centre of concentration don duk Wand

a yabude baki saudart yake kira.

Cafta suke kan qasashe kowa na kare nashi yana kushwle na dan uwanshi, kusan duk tararmata sukayi don duk tafisu baki kuma tasan amsarda zataba mutum daidai da maganar shi kuma da wuya ta bada amsa bata Baku dariya ba, h

akan yasa duk suka tararmata suna sukan Nigeria Itakuma tana karemu.

Acan bangaren maza kau zaune suke kashi kashi, wasu na games irinsu ludo ko whot wasu na caftar kwallo ko wrestling.

Ashraf na cikin masu buga whot, game suke mai zafi Wanda ko daga

kai beson yi.

A cikin mazan akwai wani dan Spain dake zaune can gefe tundazu ya zubama bangaren mata idanu kuma ba kowa yake kallo ba sai wata cute, unique babe dabe ta6a ganin mai tafiya da zuciya farat dayaba irinta.

Tunda ya qyalla idanu akanta

yakasa dauke ido akanta.

Maganarta, murmushinta, harararta duk sun tafi da imaninshi

Yana lura da yadda idan suka hada idanu take saurin kauda Kai cikin basarwa tana cigaba da surutunta.

Hannu bibbiyu yasa yabuga tagumi yana kallonta babu ko kyaf

tawa.

Jitayi an ta6oshi hakan yasashi dagowa ya kalli mutumin

"Yadai amir? Bakayin komai, kawani dawo nan ka buga tagumi, lfy?"

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yasake kallon saitinta kafin yace

"Ta tafi dani" yafada cikin shauqi

"Wa?" Inji mut

umin

"Cutie... Na fada soyyayar cutie" yafada yana lumshe idanu

"Wacece cutie" inji mutumin

"Kalli can, duba dakyau, wacece kamar zahra acikin taurari? Haskenta na dabanne, kyawunta na dabanne, murmushinta? Wayyo! Idan tayi murmushi jiyake kamarvz

an narke, ji idanun, soo perfect! Ya rabb kabani ita badon halina ba" yafada yana qara kallonta

"Wai wancan mai purple and white din?" Inji mutumin

"Hell yes! Itace, mii ruhi" yafada yana dafa saitin zuciyarshi

"Sistern wannan baqonne, I asked h

im yace tareda qanwarshi yake, qanwarshi ce"

Waro idanu amir yayi

"Dagaske? Ina yake?"

Nuna mashi Ashraf yayi dake buga whot dinshi hankali kwance.

Zumbur amir ya miqe yanufi wajensu ya zauna kusada Ashraf.

"Aslm alaika" yafada yana miqa mashi

hannu

"Wslm" Ashraf ya amsa yana shaking dinshi

"Kaine baqonmu ko?" Inji amir yana murmushi

"Eh nine" inji shi yana murmushi

"Wow, nice to meet you, ni sunana Amir Khalid, iyayena mutanen morroco ne, amma anan suke zaune, nan suka haifeni, n

an nayi karatuna har zuwa matakin PhD, yanzu ni constructional engineer ne ina aiki a company AL-DABB COMPANY LTD.."

nan yaita rattafo tarihinshi, Shidai Ashraf sauraron shi yake yana tunanin shi wannan kanshi daya kuwa? Daga ganin mutum saika bugs da b

ashi tarihinka?

Be qaseshi ba har saida yagama yadora da

"Tun ina qarami nake son Africans, kuma ina mararin hada alaqa dasu.. ERM..naga qanwarka...tunda nake ban ta6ajin abinda nakeji gameda itaba..please.. Please ka bani dama in tunkareta...ina...

Sonta" ya qarashe maganar cikin dar dar don ganin yadda harya daga kati zai buga amma kalamanshi sunsa hannun maqalewa a iska.

Shima shiru yayi yana kallonshi a daddarce don ganin abinda zai biyo baya.

Sai gani yayi ya kara waya a kunnenshi yana ams

a waya ya tashi ya matsa can gefe yana cigaba da amsar kiran.

Ajiyar zuciya amir ya sauke ganin Ashe waya zaiyi don shi a tunaninshi shi yasashi wannan qamewar.

Saitin matan yasake kallo yaganta tsaye itada wata zasu tafi hakan yasashi saurin miqewa

yabi bayan su

Suna cikin tafiya da Reyna zasu qaro juice sukaji anaqwalamasu kira daga bayansu

Juyawa sukai, gabanta ne yafadi ganin wannan mayen mutumin ne daya addabeta da kallo.

Saurin Kamo hannun Reyna tayi don su tafi don ita tsoron shi ma ta

ke amma sai Reyna ta cije.

Dagudu ya qaraso wajensu yana shesheka duqewa.

"Kai matan nan saurin tsiya gareku" yafada yana shesheka

"Wai ma, muda muke tfy ahankali" inji Reyna tana bin saudart datayi gaba

Shima saurin bindu yayi yana cewa

"E

h mana, ba kamar wannan ba qauyar" yafada cikin tsokana

Harara saudart ta gallamashi Wanda saida zuciyarshi takusan barin aiki

"Wacece baqauyar?" Inji Reyna tana dry

Dakyar ya lalubo muryarshi yace " wannan mana, halan kurma ce?"

Dariya sosai

Reyna tayi tace "A'a ba kurma bace amma baqauya ce, qauyen Nigeria" tafada tana dariya ganin yadda saudart ke hararta

"Nigeria Nigeria? Inanema Nigeria? Sai sunan yayi min shige da sunan zoo" inji amir cikin tsokana

Harara saudart ta gallamashi for

the first time tace

"A'a cave ne ba zoo ba"

Dariya sukayi gabadaya

Amir yace

"Allah na ta6a zuwa Nigeria sau daya cikin wani watan Ramadan, munje wani project, the country is damn hot, kamar da oven akayi gidajen, ataqaice muna tsakiyar yin projec

t din nafara ganin wani hazo hazo, inajin dum dum cikin kaina kamar ana daka, ataqaice saidai farkwa nayi naganni hospital, anamin qarin ruwa" dariya su saudart suke tunda yafara lbrin don yadda yake lbrin sai kayi dry

Cikin jin dadin sasu dry dayayi

ya cigaba dacewa

"Ataqaice ranar aka samamin visar dawowa, azumi na kau tuni yazama sheqaqqe"

Nanma dariya suka fashe dashi amir na tayasu, basu ankaraba sukaga ansha Gabansu Wanda hakan yasa su saurin dagowa.

Ware idanu saudart tayi cikin matsana

ncin faduwar gaba ganin Wanda yasha Gabansu, fuskarnan tashi babu rahma...

✍

Ummin fasihu ce

🧚

‍♀

🤵🏻👰🏻

AUREN KWANGILA

👰🏻🤵🏻

(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)

🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da

kanmu

🤲

Story written by Ashaanty love

(Ummin fasihu)

050

Kallonta yake da rinnanun idanunshi dasuka chanza kala bako kyaftawa, hakan yasata jin cikinta na Neman juyewa don bata ta6a ganinshi a irin wannan yanayin ba.

Bata ankara

ba taji ya chafko hannunta yafara janta.

Amir da Reyna dasukayi mutuwar tsaye tundazu sukayi saurin binsu

"Bro please don't hurt her, wlh I mean no harm, don Allah kayi hqr" inji amir dake binshi da sauri don shi duk a tunaninshi hukuntata zaiyi a ma

tsayinshi na yayanta sbd ya ganta tsaye da wani.

"Please bro listen to me" yafada Yanajin kamar ya kwaceta da qarfi don be qaunar abinda zai ta6a lu'u lu'u dinshi

Ko kallon gefenshi Ashraf beyi sai Jan saudart dayake da sauri yanufi gida itakau sauda

rt kasa magantuwa tayi sai binshi take kamar raqumi da akala

Saurin shan Gabansu amir din yayi yana cewa

"Please bro listen to me"

"Get lost you fool!" Inji Ashraf cikin qaraji

"Please kayi hqr, ni nazo na sameta, please don't hurt her" yafa

da pleadingly

"Bazaka kauceba?!" Inji Ashraf dakeson controlling din kanshi don jiyake kamar ya shimfidar dashi yaita naushinshi a fuska

"Please.."

Wani wawan bangaza Ashraf yayi mashi Wanda har saida yakai qasa sannan yasake damkar hannun saudar

t, fuuu sai hanyar gidansu.

Halbi daya yayi ma kofar ta bude yashiga yana tura saudart ciki Wanda batayi masauki a koina ba sai kan kujera.

Dagowa tayi tana kallonshi da idanunta dasuka fara chanza kala taga shima kallonta yake da rinnannun idanu

nshi.

"Waye shi?" Ya tambaya yana huci

Bata amsaba kuma bata bar kallonshi ba.

"Nace who the hell is he?!" Yafada cikin qaraji har jijjiyoyin wuyanshi na bayyana.

Gyara zamanta tayi batareda tace komai ba zuciyarta na suya, tashi tayi tana gyar

a squeezing din rigarta sannan tanufi hanyar dakinta

Shan gabanta yayi cikin quluwa

"Magana nake maki!" Ya daka mata tsawa

Watsamashi jajjayen idanunta tayi Wanda ke qoqarin Tara ruwa tace

"Give way"

"nace meye hadinki dashi?! Eh! Kin wani

taho kina yaqe mashi baki kan hanya, abinda yakawoki nan kenan? No modesty no class, yazo yana maki magana..boom sai washe baki, wayasan what will come next? Are you that desperate?" Yafada cikin hayyayakowa

"And don't forget it's me! My life! Ina ruwan

ka! The last time I checked babu wata alaqa a tsakaninmu, I owe you no explanation, it's none of your damn business ko me kaga munayi! Ko hugging dinshi kaga nayi banga abinda yashafeka ba" tafada cikin tsawa itama

Damkar hannunta yasakeyi da qarfi don

jitayi kamar zai qille dan hannun.

"Ni kike fadawa haka?"

Kiciniyar kwace hannunta take hawayen datake qoqarin 6oyewa na gangarowa

"Ka cikani you dirty pig!" Tafada cikin cracked voice

"Nace ni kike cewa you can hug him!" Yafada still damke da

hannunshi, shi kanshi yasan what he's doing was wrong, amma yarasa dalilin dayasa yakasa controlling din kanshi, wani Abu mai zafi ke tasomashi daga qasan zuciya har zuwa maqoshi.

"Leave me alone!" Tafada tana daga dayan free hannun da niyyar marinshi a

mma ya damqeshi shima ya hada ta wancan ya riqe.

Fashewa tayi da kuka tana kiciniyar kwacewa don jitake kamar qarwashin wuta ke riqe hannun.

Jingina ta da bango yayi still riqeda hannayenta da hannunshi guda dayan kuma ya dago fuskarta data jiqe shar

kaf da hawaye yace

"Don't.. Ever..let me see.. You with that.. Guy..again" yafada yana nishi sama sama kaman Wanda yayi wasan tsere.

Qalato yawu tayi a bakinta ta tofamashi yayi saurin kauda fuska

"I hate you! Damn you!" Tafada cikin kuka sosai

Tsayawa yayi yana kallon yadda take kukan jikinta har rawa yake in the process.

Sai yanzu yake wondering why yake behaving like this? Meye nashi don yaganta da wani? Ina ruwanshi?

Tsayawa yayi yana kallon yadda hawayen ta ke gangarowa, duk ga gangar

a daya jinshi yake kamar gangarar darma acikin zuciyarshi.

"I..hate..you...with passion" tafada cikin rawar muryar kuka.

Sosai Kalmar ta dakeshi, wannan shine karo na biyu data ta6a furta mashi Kalmar qi. Amma wannan Karon Kalmar tafi dukanshi bisa n

a farko.

Sakin hannayenta yayi yana kallonta.

Sulalewa tayi ta zauna qasa sannan ta cusa kanta tsakiyar kaffafunta tana cigaba da kuka.

Ahankali ya dinga ja baya still idanunshi akanta harya isa bakin kofarshi sannan yajuya ya budeta yashiga yaruf

o.

Jingina yayi da kofar yana sauraron siririyar sautin kukanta.

Hannu yasa cikin gashinshi yana dan harmutsawa, yarasa abinda yazo kanshi, he's too harsh on her, yarasa dalilin daukar zafin dayayi nan take.

Abinda yaguda kenan shiyasa tunda amir

yafara gayamashi yana Sonta dazu yayi saurin bar mashi wajen don jiyayi yana Neman kasa controlling din kanshi.

Amma sai me? Sai ganinta yayi tareda shi suna fira harda dariya, be iya misalta abinda yaji a lokacin don baya misaltuwa, jiyayi kamar yayi d

iving wuqa acikin mutumin.

Shiru yayi yana sauraron sautin kukanta daya fara raguwa Wanda yakejin kamar ana digamashi darma ne a zuciya.

Jin be iya cigaba da sauraronta yasashi shigewa toilet yaje bakin sink ya bude tap din yana dauraye hannunshi

"I hate you!" Maganar ta ta dawo mashi.

Yasani tun ba yau ba cewa ta tsaneshi amma furtawan datayi dakuma yanayin data furta yau yasashi sanin ba qaramin tsana tayimashi ba Wanda kuma hakan ba qaramin karta mashi zuciya yakeba.

"Ya rabb, take control

" yafada yana kallon kanshi ta madubin toilet din.

Itakau saida tasha kukanta ta qoshi sannan ta lalla6a tashige dakinta a daddafe ta kwanta sannan ta Dora daga inda ta tsaya, tunda take bata ta6a tsanar hallita kamar yadda ta tsani A.A ba kuma ba

tajin zata iya tsanar wani kamar yadda ta tsaneshi.

Ataqaice dai dukansu biyun kai harma da amir yadda sukaga rana haka sukaga dare don babu Wanda tunani yabari yayi barci.

Washegari bayan sallar asuba Ashraf nakan hanyar shi ta dawow

a gida yaji ana mashi sallama ta baya.

Ko be juyaba yasan amir ne, da farko kamar yayi banza dashi saikuma ya tsaya ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login