Showing 147001 words to 150000 words out of 172372 words
tun jiya kafin yaje daukota.
Sakarmata cool smile dinshi yayi yace
"How are you?"
Batareda ta kalleshi ba tace
"Alhamd
ulillah" a takaice.
"Baby serve your brother" inji ummy dahar yanzu taki dagowa daga abincinta.
Tashi baby tayi ta zari plate tashiga zubama ashraf abincin tana satan kallon yadda yake kallon saudart ta qasan ido.
Sosai tayimashi kyau cikin doguwa
r rigar atamfa mai manyan flawowi yellow and dark green dake jikinta dinkin pieces taji stone works agaba, ta kamata cif cif kamar ajikinta aka dinka sai dankwalin data daura zahra buhari style, fuskarta has usual dauke da simple makeup don yau ko kwalli b
atasa a idanu ba sai lining din datayiwa saman idanun mai kyau.
Beta6a ganinta acikin shigar atamfa ba sai yau, yafi ganinta cikin arabian gowns ko shadda hakan yasa yaga ta chanzamashi sosai kamar ba itaba.
Dan ture plate din gabanta tayi ba don ta
koshi ba sai don takasa kai komai abakinta saboda yadda takejin piercing eyes dinshi akanta ta zari tissue tana dan goge baki.
Dagowa ummy tayi tana kallonta ciki kulawa tace
"Ya dai?"
Murmushi tasakar mata tadan yamutse fuska tace
"Am full ummy"
Wani irin binta yayi da kallo ganin yadda ta shagwa6e fuska kamar wata baby doll yanajin kamar ya cinyeta don so.
"Hmm keda baby bansan gwani ba wurin rashin cin abinci, ku kuka sani ai" tafada tana sipping din ruwa.
Murmushi kawai tayi sannan tad
anja kujerarta baya ta tashi tana cewa
"Ina zuwa"
Ta juya batareda jiran amsar kowaba tashiga takawa cikin takunta mai cikeda da nutsuwa tabar wajen.
Binta yayi da kallo qasa qasa yanajin badadi don beso ta tashi ba, begaji da kallonta ba da shaqar
qamshinta.
Maida hankalinshi yayi kan abincin yanaci yana tunanin ta ina zai 6illowa ummy ta taimaka tabashi matarshi.
Ba'a jimaba baby ma ta ture plate dinta tana goge bakinta da tissue itama tayimusu sallama tabar dining din.
Shiru wurin ya dauk
a sai qarar cokala dazakaji suna haduwa da plate.
Shidai ashraf tsakurar abincin kawai yake, soyake ya dauko maganan amma yarasa ta inda zai fara.
Can dai ya nisa ya dago ya kalli ummy da kanta ke bisa abincinta tanaci fuska daure.
Ajiye spoon din
shi yayi sannan yayi interlocking din yatsun hannayenshi ya dora kan table yana kallonta.
"Ummy.." yafada ahankali yana zubamata hazal eyes dinshi daya gado wajenta.
Dagowa tayi itama ta zubamashi nata batareda tace mashi komaiba.
Ajiyar zuciya ya
sauke sannan yaqara yin qasa da murya yace
"Ummy don Allah laifin me nayimiki ne kiketa fushi dani? Dan allah kiyi haquri ki gayamin ummy, wlh bansan me nayiba" yafada yana langwa6a kai kamar wani maraya.
Dauke kai tayi daga kanshi ta maida a abincint
a tana cewa
"Cema nayi kayimin wani abu?"
"Ko bakice ba ummy ai fuskarki ta nuna, don allah ki taimaka ki gayamin ummyna" yafada cikin sigar rarrashi.
Ta6e baki tayi tace
"To ni bakamin komaiba, idan ma kayimin kasan ba tsoronka ba nake dazan tsaya
6oye 6oye, fitowa zanyi infadama inkuma dauki matakin daya dace akai, so stop bothering me" tafada tana kai abincin data debo abaki.
Shiru yayi yana kallonta nawani lokaci sannan ya sauke ajiyar zuciya ahankali
"To amma ummy meyasa kika hanani tafiya
da saudart jiya?" Ya tambaya ahankali
"Saboda na isa daku duka, daga kai har saudart din, idan kuma nunamin zakayi ban isa dinba to" tafada tana binshi da harara.
Shiru yayi yana kallonta zuciyarshi namai zafi.
Wai meyasa ummy kemashi haka? Meyayi m
ata take son ganinshi cikin 6acin rai da kunci.
"Ummy kin isa damu mana amma gani nayi wannan..."
Dakatar dashi tayi ta hanyar dagamashi hannu.
Shiru yayi yana kallonta da idanunshi dasuka fara kadawa, yanajin zafi sosai azuciyarshi
"Idan magan
ar dazaka cigaba dayimin kenan kindly leave, kokuma ni inbarma wurin":tafada tana kallonshi strictly.
Sadda kanshi kawai yayi bece komaiba zuciyarshi na suya sosai, jiyake kamar yaita kuka ko zaiji sassauci.
Ko gefenshi bata qara kallo ba harta gama
cin abincinta ta tashi takoma falo tabarshi awajen.
Haka ya zauna shiru a dining din, shikadai yasan yadda yakeji azuciyarshi, jiyake kamar yaita watsa kayan kan dining table din ko zaiji sauqi.
Jin ana kiraye kirayen sallar asr yasashi tattaro kingi
n kuzarinshi yatashi yana qoqarin wajen ganin yayi controlling din kanshi.
Falon shima yadawo inda ya tadda ummy zaune remote a hannunta.
Zama yayi kan wata kujera dan nesa da ita batareda ya dagoba yace
"Ummy zan tafi masjid"
Itama batareda ta k
alleshi ba tace
"To allah ya tsare"
Tashi yayi yana cewa amin sannan ya nufi kofar fita yana ayyana shida gidan nan kuma sai baba tagani tunda babu mai sonshi agidan.
Direct motarshi yanufa yashige ya tada yabar gidan.
Tanajin fitar motar ta ta6e
baki tana cewa
"Kafi ruwa gudu" itama ta tashi ta haura sama don haramar sallah.
Masjid yafara biyawa yayi sallah sannan yawuce gida.
Ranar dai haka yawuni rai adagule gashi fushi yake da sadeeq bare yakirashi yadanji sanyi, kodayake yanama iya
kiranshi yafara 6a66akamashi wannan dariyar tashi ta mahaukata gwara ya rarrashi kanshi da kanshi amma yadauki alwashin bazai qara zuwa gidanba da sunan abashi saudart, yabarmasu su cinyeta.
Washegari ma haka ya tashi rai adagule, sadeeq tunjiya yake ki
ranshi amma yaqi dagawa don haryanzu fushi yake dashi, ummy kau saidai yakirata suka gaisa kawai don yariga ya qudura aranshi yayima gidan yaji bazasu qara ganinshiba saisun nemeshi dakansu.
Ranarma haka yawuni cikin kunci, ganin abin yayimashi yawa yas
ashi fita bayan asr yaita zagaye gari bashi yadawo ba sai wajajen 9 din dare.
Ranar ma kamar kingin ranakun haka ya kwana cikin kewar abar kaunar tashi.
Washegari monday tunda wuri ya tashi yafara shirin fita company don jiyayi duk zaman gidan ya fic
e mashi akai, gwara yafita aikin ko ya deba mashi kewa.
Wajajen 8:30am sadeeq ya iso company din.
Sosai mammaki ya cikashi dayaga wani staff yafito daga office din ashraf don beyi tunanin zaizo ba.
Gaidashi staff din yayi a girmame, amsawa yayi
cikin fara'a yana tambayarshi ya iyali.
Fasa shiga office din nashi yayi yanufi na ashraf din ya kwankwasa ya murda handle din yashiga da sallama.
Ko dago kai daga typing din dayake beyiba bare yasaka ran zai amsa mashi sallamar, be damu da hakan ba
saima qarasowa dayayi cikin office din yaja kujera ya zauna yana kallon yadda yawani hade rai yana sarrafa system din gabanshi.
Ganin beda niyyar kulashi yasashi jan tsaki yace
"Kaifa dan air ne, ji yadda kawani yi banza dani kamar ba wajenkaba nazo"
Dago kai ashraf yayi ya yimashi kallon up & down sannan ya maida kanshi kan abinda yake.
Ta6e baki sadeeq yayi yace
"Shine naketa kiranka kaqi picking ko?"
Shima ta6e bakin yayi batareda ya tankashi ba.
"Allah dai ya yayemaka wannan baqar zuci
yar taka kona huta wlh, kaikam matarka tabani... wai yama naganka a office yau, kaida yakamata ace kanacan kuna honeymoon da sweetien taka?"
Wani mugun kallon yadago ya watsa mashi sannan ya kauda kai
Dariya sadeeq yafashe dashi yana cewa
"Au na man
ta ashe an kwace matar, hhhhh wannan shi ake kira ga qoshi ga kwanan yunwa, wai ya kuka qare da ummyn? Kashawo kanta din?"
Banza yayi dashi don koyace yayi magana yasan bamai dadi zaiyi ba.
"Kaji? Dakaifa nake"
Nan ma ko kallonshi beyiba bare ya
tanka
"Karfa ace kayi surrender ne, lallai ma, to wlh ka zauna kaga zama na rantse, ni i thought ma tun ranar zaka dawo da matarka, ca6! Wlh idan nine idan na yarda intafi tsaye, matar tawa wanda dakyar nasamu bata kufcemin ba azo kuma sake nisantamu sa
lon komai yaqara dagulewa? Ta6!"
Kallonshi ashraf dahar mood dinshi ya chanza yayi yanajin zafin abun aranshi sosai yace
"Na barmata ita, i've promised bazan qara samunta akan wannan case dinba, nabarmata tayi yadda taga dama daita nikam na haqura"
Wani kallon uku saura kwabo sadeeq ke binshi dashi haryakai aya sannan yaja wani dogon tsaki yace
"Ban ta6a sanin rashin hankalin naka yakai hakaba sai yau, sannu zuciyatu, ai gwara kayi zuciyar kabarmata din, tunda gaka sarkin masu zuciya, to wlh kayi zu
ciyar angayama tanada asara ne, kai an da asara, abanza ciwon zuciya zai kamaka, kuma wlh babu ruwana bazanyi jinyar kowaba.
Lallai ma, wai na barmata to kabarmata din, abanza ciwo zai kamaka bamuda asara, dama gashi cikin kwanaki biyu harka fara qarmashe
wa, lokacin da kake ikirarin ummy zata baka ita dakanta kakoma 1, dama yaya lafiyar giwa? Kadawo anbaka itan amma tsoronka take kakoma kifin gpanla, mtcheew so annoying" yafada yana girgiza kai cikeda takaici
"To ya kakeson inyi da rayuwata uhm? I begge
d and begged and begged taqi ta saurareni, ya zanyi?" Ya qarashe zancen kamar zaiyi kuka
"Kuma shine akace don you begged and begged and begged taqi sauraronka saikayi giving up? Dama yaya lafiyar giwa? Allah ne kawai ya dubeka yaji qanka badon halinka
ba yabaka ita akaro na biyu, maimakon kayi grabbing din opportunity dinka ka gyara kuskurenka kajawota jiki ka dasa sonka azuciyarta ta hanyar wanzar da shakuwa atsakaninku shine zakayi nisa da ita har kana ikirarin ka haqura? Mtcheew amma a gaisheka" yafa
da yana girgixa kai.
Shiru ashraf yayi yana auna magangganun sadeeq don bakomai aciki sai gaskiya.
Yasan halin ummy idan ta nace kan abu dakyar take chanza ra'ayi gashi dukda yayi zuciyan abun na maqale aranshi don sosai abin ke damunshi kuma yasan b
a qaramin aikin ummy bane tashareshi tayi kamar batasan yana yiba harsai ya jigata sosai
"To yanzu meye mafita?" Yafada yana kallon sadeeq.
Harara sadeeq ya watsa mashi sannan yaja tsaki yana cewa
"Kayan takaici kawai"
Shidai bece komaiba don yas
an shike nema don haka dole yayi haquri
"Ni nazaci wlh tun ranar zaka magance abin amma dayake kai solo6iyo ne kodayake harda wauta irinta yan fari..."
"Look yafa isheka, wai yaya don zaka bani shawara zaka tisani gaba kanata debemin albarka tundazu,
wlh kashiga hankalinka ina ganin girmanka" inji ashraf yana makamashi mugun kallo.
"Au dama yaushe kafara ganin girman nawa? Da kana ganin girman nawa da duk rashin m din dakake shufkamin bazakamin ba"
"Naji please let's talk like two matured people
, please let's be serious" yafada cikin dan kwantar dakai
Tsaki sadeeq yaja yana yamutse fuska irin ana nema wurinshi dinnan sannan agadarance yace
"Yanzu abinda zakayi shine ka tattara yanaka yanaka kabi matarka wlh, idan ka zauna zakaga zama ne na ra
ntse, follow her there and pretend ku kadaine agidan, ka nuna bakasan da zaman kowaba gidan, abin nufi duk kulawa da tarairayar dazakayimata kuna ku biyu kayimata acan ba ruwanka dasu, ka cire kunya ka nunawa matarka love agaban koma wanene, am telling you
su zasu koma sunajin kunya idan kuma abin ya ishesu bashiri zasu hadoka da matarka su watsoku waje, koya kace?" Ya qarashe zancen yana dagamashi gira daya
"Kenan in koma gidan?,but how sure are you ba zata bani ita din?"
"Mtcheew kai hamago ne wlh,
kai ai zakasa tabaka din kotaqi ko taso, cire kunya zakayi kana abubuwan da dole zasuji kunya da gangan, pretend ku kadai ne agidan, afterall matarkace ai, kazama bita zaizai, duk inda take ka bita, kaita maqalemata kana baje kolin love dinka babu abinda
yashamaka kai, idan taga rashin kunyar tayi yawa da kanta zata baka matarka.
Ca6 ai anbar sanya yanzu, ni har umma zata riqemin mata tayi kwana uku wajenta? Lallai na rantse idanba aranar idan naga damar kasancewa da matata saina kasance daitaba intafi
tsaye, ko dakinta ta 6oyeta saina lalla6a nabita wlh.
Ka duba kaga fa, yau 5months kenan da aurenku amma babu abinda kuka tsinana, sai yanzu komai ya warware shine kuma za'a tsiro wani sabon case? Ca6!
Kodayake harda laifin ka ai, Allah ma yaqara, tu
n farko kaine ummul'abaisan faruwar komai, shegen girman kanka yajamaka tun farko kaqi bada kai bori yahau shiyasa ai aketa garaka takoina, dama ai ance idan bakayi sharar massalaci ba zakayi na kasuwa, da..."
"Yanxu dai ya isheka, nagode da shawararka,
zan duba ingani don haka atashi abarmin office hakanan, thanks for the concern" yafada yana 6allamashi harara.
Sakin baki sadeeq yayi yana kallonshi a mammakince sannan yace
"Kutt.. hakama zakace bayan kasamu na nemomaka mafita?"
Yatsine fuska ashr
af yayi yace
"Kuma cema akayi amfani da crooked shawarar taka zanyi? Idanma kaga nayi amfani daita to dama can nayi niyyar yin haka tunkafin kafada don haka atashi abarmin office nace, gauro kawai" yafada cikin son qular dashi
"Kutt.. amma kau wlh kayi
da dan halaq, zaka gane bakada wayau wlh" yafada yana miqewa cikin fushi
"Eh, agayas, gauro kawai" yafada yana qyalqyalewa da dariya ganin yadda ya kunnu
"Gakanan jibgegen gauro, ai gwara ni dakai wlh tunda ni banida matar ne amma kai gashi kanada
matar amma baka tashi a layin gaurayen ba kuma insha allahu ummy bazata baka matarkaba sainan da shekara daya, insha allahu saina rigaka angwancewa" yafada cikin kumfar baki
Qara kecewa da dariya ashraf yayi yace
"Oho dai, a duk lalacewar goma tafi bi
yar albarka kuma dai dolene ko a suna ne akirani da mai iyali don wlh nafi qarfin akirani da gauro kuma ko shekaru nawa ummy zata dauka kafin tabani ita bazai ta6a chanza batun narigaka aure ba bare insha allah saina rigaka angwancewa, kai in taqaicemaka d
a d'ana zamuje daurin aurenka insha allahu, so jeka rungumi transformer" yafada yana dariya sosai kamar ba A.A dinnan ba mai saurin hayaqa.
"Allah ya kiyaye wlh, bakinka ya sari danyen kashi, wazai zauna harku gama wannan shirmen naku har kusamu d'a bey
i aure ba? Bakada hankali kuma wlh munanan dakai zaka sake zuwamin da matsalarka, zakaga yadda ake ainihin rashin mutunci" yana kaiwa nan yabude kofa yafita ya maidota da qarfi.
Dariya ashraf yasake fashewa dashi yana komawa kan kujera yana jujjuyawa, s
adeeq is just the best, sadeeq ba qaramin kyauta bane da allah yabashi, bazai iya misalta yadda rayuwa zata kaya batareda shiba, gashi cikin dan qanqanin lokaci yakawomashi mafita yakuma sauya mashi mood daga baqinciki zuwa farinciki.
Jujjuyawa yacigaba
dayi kan kujerar yana qara tunanin magangganun sadeeq yana ayyana yadda zai gudanar dasu a zahirance...
✍
Ummin fasihu
🧚🏻
♀
️
🤵🏻👰🏻
AUREN KWANGILA
👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Story written by Ashaanty love
💖
(ummin fasihu)
kumun hkuri naji
na kwan biyu da bakuba zashinan hadda bashi nabiya
🤧
093& 94& 95
A.A dogon nunfashi ya sauki tare da kallan hannunta da ke kan bakinsa san nan ya kalli fuskar ta kafin yay niyar maga yaga ta kara hade jikinta da nasa dasana diyar tafiyar ummma data
ji tana yowa wanja mutuwar tsayee yayayi da kar yake iya jan yo nunfashin sa dake bara zanar daukewakdnmkllnbbbbnkkkkjjnjjikkkmjvhllllllbfjkllll
Bayan yagama komai nashi yayi shirin kwanciya yahau shirya kayanshi cikin wata qatuwar trolley, kaya sosai y
a loda don ya quduri aniyar duk rintsi bazai dawo hannu biyu ba, duk dadewar dazaiyi ya shirya idanma takama ayi zaman auren can sai ayi ai ba akansu aka fara ba.
Ataqaice dai shine har wajajen 12 yana shirin kaya, dakyar yasamu yagama ya lalla6a ya kwa
nta cikeda zumudin gobe, jiyake kamar yajawo daren gari ya waye hakanan.
***
Washegari as usual qarfe 9 saura ya isa company, kamar yawuce office dinshi saikuma yajuya yanufi office dinshi.
Murda handle din yayi yajishi gaam alamun babu kowa cik
i.
Wani malalacin murmushi yasaki yana wurwura keys dinshi yanufi office dinshi.
Saida yayi settling sannan ya zaro phone dinshi ya danna mashi kira ya kara a kunne yawani murtuke kamar yana gabanshi.
Ringing taitayi harta katse ba'a dagaba hakan
yasashi sakin tsaki yasake danna mashi wani kiran yana ta6e baki wondering ko ina yashiga?
Saida kiran yakusan tsinkewa sannan aka daga.
"Heelloo?.." yaji anfada cikin muryar barci
Dan waro idanu sadeeq yayi sannan ya kalli agogon bango yaga 9 sau
ra minti 2 hakan yasashi cewa
"Inyee? Wato barcima kake haryanzu, don ubanka qarfe nawa?"
Cikin muryar barcin yasake cewa
"Yes... am...coming"
"Coming din gidanku? Mtcheew wlh danazo naga baka zoba i thought ka dauki shawarata ce yanzu haka kana gi
dan ummy, amma kai kasani ai, scallywag kawai" ya katse wayar yanajan tsaki.
Wani mugun tumble ashraf yayi daga kan gado sai jinshi yayi qasa kasancewar dama baki bakin gadon yake.
Wawware idanu yashigayi don shapp ya mance dawanu zuwa gidan ummy, wa
i tayama wani barcin ya daukeshi, abu na qarshe dazai iya tunawa shine ya zauna gefen gado ya dan kishingida da kan gado yana lazimi yana jiran garin yadanyi haske yatashi yafara shiri. Kai amma a gaisheshi.
Saurin miqewa yayi tsaye yana cire brown jall
abiyar jikinshi.
Agaggauce ya tu6e ya rage saura boxer kawai ajikinshi ya rataya towel a wuya yashige bathroom.
Saida yakusan awa daya sannan yafito don yau wanka na musanmman ne
😉
ba irin na kullum bane.
Koda yafito direct yawuce gaban mirror din
shi yaja kujera ya zauna kamar irin mace ta zauna zatayi kwalliya.
Sosai ya 6ata lokaci wajen shafe shafenshi don yau komai saida aka qara akan nada, sumar kanshi banda kyalli babu abinda take, dan siririn sajenshi sun kwanta luff sai shining suke, roll
on ma saida ya murza kala uku duk masu shegen sanyin dadi.
Saida yagama kwalailaitar sannan yawuce gaban closet dinshi yabude yaciro kayan da dama tun jiya aka riga aka waresu akan su za'asa yau.
Cikin dan qanqanin lokaci ya gama shirin.
Wow! As-
in WOW! duk inda haduwa takai to ya kureta, sosai ya hade cikin qannanun kaya wando fari mai layi biyu a gefe gefe kalar royal blue, rigar kuma kalar royal blue mai hula daya saketa abaya, a bayan rigar akwai logo da akayi printing kalar fari mai taken *MO
NARCH*
kaffafuwanshi sanye da fararen shoes hannunshi na dama daureda agogon kirar Apple fari sai wani qwamemmen shade daya qwamama fuska shima fari amma glass din baqine wulik don bakama hango kwayar idanunshi.