Showing 135001 words to 138000 words out of 172372 words
/>
"Ok" ya amsa yana kallonta
Sauka tayi daga motar tanufi hanyar shiga gi
dan yabita da kallo harta shiga. Ajiyar zuciya yayi yakoma ya jingina da kujerar motar yana jiranta.
Tadan jima da shiga cen saigata tasake fitowa wannan karon sanyeda maroon abaya tayafa madaidaicin gyalenta.
Iskeshi tayi kamar yadda tabarshi don ki
kashe motar beyiba.
Babu yadda ta iya haka ta shiga motar tanajin dama tun farko bata tattagi fitarba, ita a tunaninta ma idan takoma ta gayawa mamy yadda sukayi dashi zata hana fitar saitaga akasin haka don addu'ar allah ya kiyaye kawai tamata.
Mai
da kofar tayi tarufe tana gyara zamanta, saida yayi making sure tashirya sannan yaja motar sukabar kofar gidan.
Tafe suke babu maicewa kowa uffan, saudart dama tunda tashigo tajuya kanta tana kallon waje ta window kamar yadda tasaba while shi hankalin
shi rabi na kan tuqi rabi akanta.
Jinshi yake so happy having her next to him. Dama yana gidansu sadeeq saqonta yashigo wayarshi.
Da farko kasa believing idanunshi yayi dayaga message from *other half* saida ya murza idanunshi yaqara kallo yaga dagas
ke ita dince.
Cikeda zumudi ya bude saqon ya karanta.
It's just three words amma yajisu har cikin ranshi most especially na qarshen nan wato *permitted?*
Yaji dadin ganin tana neman izininshi ne, hakan yasashi jin kamar ta nuna yanada matsayi awa
jenta.
Babu shiri ya miqe yadauki car keys dinshi ya nufi kofa.
Yanajin sadeeq nata tambayarshi ina zaya yai banza dashi yafice, this is a chance of being with her nawani lokaci and he dont want to lose it.
Saida yakoma gida yayi wanka ya dauki wa
nka sannan yanufo gidan nasu don kaita dakanshi.
Jin motar tadauki shiru sosai yasashi miqa hannunshi nadama ya kunna disc din motar yasa waqar *sorry* na justin biebier
Ahankali waqar tafara tashi acikin motar in a very emotional mode.
Cigaba
yayi da tuqin yanabin waqar acikin zuciyarshi yanajin waqar tayi daidai da yanayin dayake ciki kuma yanajin kamar waqar na isar da saqonshine gareta.
Itama a 6angarenta tunda waqar tafara ta nutsu tana sauraronta, tarasa dalili amma saijitayi waqar n
a tasiri a zuciyarta, tanasa jin wani sense of emotion a tattare daita.
Haka duk sukayi shiru suna sauraron waqar kowa da abinda yake saqawa azuciyarshi harsuka qaraso saloon din...
✍
Ummin fasihu
🧚🏻
♀
️
🤵🏻👰🏻
AUREN KWANGILA
🤵🏻👰🏻
(Contract mar
riage)
Story written by Ashaanty love
💖
(Ummin fasihu)
086
Tsayuwar mota yasata sanin sun qaraso saloon din.
Bin harabar tayi da kallo tacikin motar tana wondering inane nan ya kawota.
Jin an bude murfin 6angarenta yasata dagowa
suka hada idanu dashi tsaye riqeda murfin motar daya bude mata.
Sauke idanunta tayi sannan ta ziro kafarta ahankali ta sauko tana qara qarewa harabar kallo.
Dukda duhun magrib yakawo kai hakan be hanata ganin qawatuwar wajen ba.
Idanunta ne suka
sauka akan logo din wajen wanda ke walainiya cikin kaloli daban daban ansa *EXCLUSIVE BEAUTY SALOON*
Dan wara idanunta tayi ganin inda yakawota don wajen bana qananun mutane bane don tasan dakyar kudin hannunta su isheta ko sun isheta bazata rage ko si
si ba na shopping datayi niyyar yi.
Ganin yayi gaba zai shiga yasata saurin tsaidashi da
"Ehmm.. ba..ba anan nake saloon dina ba" tafada tana janye idanunta ganin ya juya ya zubamata ido.
"Ina kikeyi?" Ya tambayeta yana saka hannayenshi a aljihu
"Mhiz zee saloon" ta amsa ataqaice
"Nan ma sunayin mai kyau, nan baby keyi ma" yafada idanunshi kyar kanta.
"No nafi son can" tayi saurin fada don she's not ready to embarass herself
"Why?" Ya tambaya.
Haushi yacikata, wai ina ruwanshi daita ne
? Meye ruwanshi da inda zatayi?
"Just" ta amsa ataqaice tana tamke fuska
"Then let's go, i bet you'll like it here too" yana fadin haka yajuya yanufi cikin wurin cikin tafiyarshi ta qasaita data riga tabimashi jiki.
Binshi tayi da kallon taqaici r
anta na mugun 6aci, wai wacce qaddara ma tasata tarkar fitar tun farko? Yazo ya kawota saloon din masu kudi cemashi akayi nan takeyi? Koko wani kilbibi ne wannan?
Jin kamar ba'a biyoshi ba yasashi juyowa yana kallonta.
Sake hade rai tayi sannan tafar
a takowa wajenshi tanajin kamar tayi bindiga.
Binta yake da kallo harta qaraso wajenshi ta giftashi tawuce batareda ta kalleshi ba.
Dan murmushi yasaki sannan yabi bayanta shima yashiga.
Saloon din ya amsa sunanshi na manyan mutane don kallo daya
zakamashi kasan bana irin namu na yaku bayi bane.
Koina naciki is glass, gawani sanyin A.C dake chakude da qamshin freshener dake iya samutun ya 6ingire da gyangyadi batareda yayi aune ba.
Gaba yayi tana binshi har suka wajen wata waiter.
Itadai t
ana daga baya bataji abinda suke cewa ba saigani tayi waitress din tamiqa mashi dan kati ya amsa sannan yajuyo yayimata alama da tabiyoshi.
Babu yadda ta iya haka tabishi suka haye sama tana kallon yadda aka qawata wajen kamar ba saloon ba.
Kofofi ta
gani asaman jere duk anyi numbering dinsu, haka sukaita tafiya har suka isa wata kofa mai number 22.
Murda handle din kofar yayi ya bude yakoma gefe yana kallonta alamun tashiga.
Babu musu tazo tashige tanajin kamar taita ihu, ta tabbata yanzu magrub
tayi don anan ciki ba ganewaba ake kasancewar koina tarr yake da haske.
Ahankali ta tako ta qaraso ciki tana kallon yadda aka qawata dakin, ga mayyukan mai kala kala kan wani mirror mai qatoton madubi, ga naurorin wankin kai kala kala, su dangin wigs,
weavon babu wanda babu ga kalandodi na hair styles da henna manne a bangayen dakin bayaga magazines dinsu dake ajiye akan kowanne stool dake gefen kujera.
Qarasawa tayi ga wata kujerar ta zauna tanajin kamar tayi kuka, ita datasan haka abun zai zama d
a ta wanke kanta dakanta cikin kwanciyan hankali, yanzu yaushe akafara wankin kan bare ayi maganar tafiya gida? Ga shopping din da takeson tayi, that's idan kudin hannunta sun rage.
Tsaki tayi cikin zuciyarta tanajin mugun haushi.
Bude kofar da aka
yi yasata dagowa, wata budurwa ce tashigo sanye da irin uniform din jikin waitress din qasa.
Cikin fara'a duk ta gaidasu tana masu maraba dazuwa exclusive saloon.
Saudart kadai ta amsa while ashraf kanshi kawai ya dagamata.
Kallon tsadadden wristw
atch din hannunshi yayi sannan ya kalli budurwar yace
"Zan shiga sallah, idan kun gama let me know"
"Yes sir" ta amsa a girmame.
Juyowa yayi ya kalleta tayi saurin kauda kai tana hade gira, murmushin gefen baki yayi sannan yafita.
"Ok ma'am pleas
e have your seat" inji yarinyar tana murmushi.
"Zanyi sallah nima, ina zanyi ablution?"
Leading dinta tayi inda akeyi ta dauro alwallar sannan tadawo dakin taga har an shimfida mata sallaya.
Hawa tayi ta kabbarta sallarta tafarayi.
Saida tagama
tashafa addu'a sannan tadago tana kallon yarinyar wanda da alama christian ce don ga yanayinta ma zaka gane.
"Kin gama ma'am?" Ta tambayeta cikin murmushi
Gyada mata kai tayi tana miqewa tsaye tana linke sallayar.
Amsa yarinyar tayi taje ta adana
sannan tadawo ta nunamata wata turning chair tana cewa
"Please have your seat ma'am"
Ba musu tazo ta zauna, hankalinta duk yakoma gida ta qagara agama sutafi.
Miqomata magazine tayi tana cewa
"Pick your choice ma'am"
"Look kawai retouching zaki
yimin shikenan" tafada batareda ta amshi magazine dinba.
"Hennah fa? Ko manicure da pedicure? Munayin foot bath ma"
Rolling din idanunta saudart tayi cikin qosawa tace
"Yes duk nasan kunayi, retouching kawai nike so"
"Ok ma'am"
Nan da nan aka
fara wankin kan.
Itadai saudart tana zaune tana kallonsu ta mirrorn gabanta, ta matsa wannan ta shafa wannan ta diga wannan kamar baza'ayi wankin kanba.
Saida tagama hade hadenta sannan ta kwantar mata kan tabaya inda za'a tara a wanke tafara wankema
ta gently da ruwan dumi tana dan cuccuda mata gashin ahankali.
Sosai saudart kejin dadin wankin kan don jitake kamar ana messaging din kan, har wani gyangyadi gyangadi ke son dauketa.
Ba'a dadeba aka gama aka nade kan da qaramin towel yarinyar tafi
ta don discharging din ruwan wankin.
Ba dadewa tadawo tafara tsane mata kan ahankali da towel din sannan ta warwareshi ta kauda, ta dauko hair dryer tafara busarmata dakan.
Cikin dan qanqanin lokacin tagama sannan ta dauko maya mayai na kai masu qam
shin gaske tafara mulkemata gashin dasu, nan take gashin yadauki extra sheqi da qamshi saida tagama sannan ta dauko hair straighter tafara straighting din gashin dashi.
Sai gashin duk wanda tariqe da straighter din taja sai su zubo luff harkan kafadarta
suna daukan ido.
Haka tayita straighting din gashin harta gama sannan tayimata bonding dinshi a tsakiyar kai in a stylish way ta saki jelar data fado mata har qarshen wuya.
Bayan haka tabi da hair perfume ta feffesa mata akan.
Juyo daita tayi tan
a fuskantar madubi tana cewa "how was that?"
Shiru saudart tayi tana kallon kanta a mirror, tunda take ba'a ta6a mata irin wannan gyaran gashin ba, it look soo muah!
Murmushi tasaki tana sake kallon kanta a mirrorn tace "great! Yayi kyau sosai"
Wa
she baki yarinyar tayi cikin jindadin an yabi aikinta tace
"Awnn thanks ma'am, ayimiki hennan? Please just yatsu kawai" tafada cikin marairaicewa
"No gaskiya, yanzu dai nawa ne wankin kan?" Tafada tana addu'ar allah yasa karsu zuqamata kudin da batada
su yanzu ga ATM dinta ta baroshi gida.
"Bari dai agama ma'am, bari kiga you'll like it"
Kafin tasamu zarafin amsawa harta dauko abubuwan qunshin.
Amsar hannunta tayi ta zauna kusada ita tana cewa "wlh harna hango wanda zaiyi fitting din hannunki,
bari kiga"
Itadai saudart shiru tayi tana kallonta.
Wanke mata akaifu tafarayi tayi filling sannan ta dauko jan lalle nacikin kwarkwaro takama hannun tafara zanamata simple but breathtaking style a yatsu.
Tsayawa saudart tayi tana kallon yadda tak
e henna din cikin qwarewa, ita kanta henna ba qaramin birgeta ba yayi dukda bada son rantaba akeyi.
Cikin qanqanin lokaci tagama mata, haka ta zauna tanata kallon qunshin harya bushe sannan ta tashi da jagorancin yarinyar taje ta wanke ta dauro alwalla
daga nan don har isha'i tayi.
Saida tagama sallar sannan yarinyar tazo tana duba qunshin datayi mata din tana washe baki don tasan baqaramin kyau yayiba, hotuna taita daukar qunshin don sawa ajerin hotunan dasuke talla dasu.
Saida tagama sannan sauda
rt ta sauke ajiyar zuciya ta dau purse dinta tace
"Yanzu nawane bill din?"
Dan bude idanu yarinyar tayi tace "bill? Your husband has settled it ai"
*Husband* ta nanata a zuciyarta jin sunan wani banbarakwai.
"Ok thanks" tafada cikin basarwa ta gy
ara yafin gyallenta.
"Thanks ma'am, do come back another time" tafada cikin fara'a
"Insha allah" tafada itama tana murmushi.
Tare suka fita daga dakin suka sauka qasa.
Har harabar wajen ta rakota sannan tajuya.
Tundaga nesa ta hangoshi zaun
e cikin motar kasancewar harabar pauu yake da gaske gashi kuma glass din motar duk a qasa suke, sauke kanta tayi aqasa ta nufi motar kamar mai tausayin taka qasa.
Tunda ta taho yake kallonta babu ko kyaftawa, yarasa dalilin dayasa duk sadda ya kalleta
saiyaga kamar anchanzata, yarasa abinda yasa yakejin nishadi azuciyarshi idan yana kallonta.
Jin qarar bude kofar yasashi blinking din idanunshi wanda beyiba tunda yafara kallonta.
Shigowa tayi motar da bismillah kasa kasa sannan tajawo murfin mota
r tarufe.
Sauke kanta tayi qasa tana wasa da yatsunta jin idanunshi akanta, ita ta tsani kallon nan wlh, bata sonshi kwata kwata.
Ahankali yamaida kallonshi kan yatsun datake wasa dashi ya kafesu da idanu suma don sun mugun tafiya dashi.
Jin shiru
n yayi yawa yasata dan dagowa ta kalleshi.
Ganin yatsunta yake kallo yasata saurin maidasu cikin gyalenta tana tamke fuska.
Kallonta yayi yadanyi murmushi sannan ya kunna motar yaja suka fice daga wajen.
Tafe suke in silent don wannan karon be k
unna komaiba.
Satan kallonta yayi yakuma maida kanshi ga tuqi.
"It's soo cute" taji yafada cikin cool voice
Juyowa tadanyi ta kalleshi shima daidai yajuyo ya kalleta.
Kashemata ido daya yayi yana murmushi yace "qunshin"
Janye idanunta tayi t
a kauda kai.
"Please mugani" yafada yana shan wani round about.
Juyowa tayi tasake kallonshi.
Marairaice fuska yayi dayayi mugun yimashi kyau yace "please?"
Saurin dauke kai tasakeyi tana qara qudundune hannun cikin gyalenta.
Murmushi yayi
yace "shikenan, zan rama nima, zanyi new low cut bazan bari ki ganiba" yafada kamar dan yaro
Itadai bata juyoba saima qara kallon waje datayi yayinda zuciyarta ke chanxa beat.
Agaban wani qaton supermarket taga yayi parker.
Dan waro idanu tayi d
on ita duk atunaninta gida sukayi batama lurada sun dauke hanyar gida ba.
Saurin juyowa tayi ganin yana neman sauka.
"I... i thought gida zamu" tafada tana kallonshi.
"No, zan danyi shopping ne" yafada yana fasa fitan
"No please ka maidani gid
a this is almost 9" tafada tana dan ware manyan idanunta.
"Bazamu dadeb.."
"No nidai mutafi please, mamy tafara kirana, it's late" tafada tanajin kamar tafasa ihu.
"Ok let's do this, mushiga muyi shopping cikin 5mins mu fito bazamuyi taking time b
a" yafada persaudingly, shi wannan ma maganar dasuke dadinta yakeji har beson maganar ta yanke
"No ni i dont need anything, idan kuma kai kana buqata kindly take me home idan kakaini kadawo or better still in hau adaidaita" tafada cikin son danne 6acin
ranta.
Ganin kamar ranta ya 6aci yasashi sauke ajiyar zuciya yace "Alright then" ya maido kaffafunshi ciki ya maido murfin kofar ya rufe.
Furzar da iska tayi ahankali tana komawa ta jungina da kujerar motar.
Babu yadda ya iya haka ta tada motar su
ka bar harabar wajen.
Shi da so samune da ba yanzu zasu koma ba, bayan shopping dinnan ma har restaurant yaso suje suyi having dinner tare, jiyake beson abinda zaisa surabu daidaida second daya, soyake su dawwama ahaka har abada.
Jin motar ta dauki s
hiru yasashi kunna disc din motar, wani cool love music mai antaya mutum cikin shauqi yafara tashi ahankali amotar.
Wani uban zagaye yayi dasu da gangan don kwata kwata beson su isa gidan dawuri, saigashi tafiyar dabata wuce ta minti 15 ba ta daukesu 40
mins.
Wani ajiyar zuciya saudart ta sauke ganin sun shigo layinsu atlast don harta fara tantamar anya yasan inda zaikaisu kuwa.
A bakin gate din gidan yatsaya yana sauke ajiyar zuciya.
Dan jimm tayi kamar bazata motsaba saikuma ta sa hannu zata
bude murfin kofar tajita gamm.
Juyowa tayi ta kalleshi taga shima ita yake kallo.
Murmushinshi ya sakarmata mai kyau yana dagamata gira daya.
Daure fuska tayi tareda kauda kai gefe wanda hakan yasashi sakin wani murmushin.
"Ka budemin kofar" ta
fada batareda tajuyoba
"A nawa?" Yafada yana kallon qeyar data juyamashi
Shiru tayi batace komaiba kuma bata juyoba.
Shima shirun yayi yana aikin kallonta.
Ganin batada niyyar juyowa ko tasake magana yasashi sakin murmushi mai sauti yace
"Alri
ght sorry angry bird, i don't mean to annoy you, just want to say... being with you is the sweetest thing ever, thank you for today" yaqarasa ahankali kamar mai rada
Shiru tayi tana sauraronshi still bata juyoba
"Idan zaki sake fita, alert me, zanzo
if kuma am busy zan aiko driver, kinji?" Yafada cikin murya mai kamada ta rarrashi.
Kada mashi kai tayi ahankali batareda ta dagoba.
Shiru motar taqara dauka sai cool music din dake tashi qasa qasa a motar.
Qara kai hannun tayi a handle din motar
ta murda dukda tasan be budeba.
Ahankali shima yakai hannu anashi gefen idanunshi akanta yayi unlocking din kofar.
Ganin haka yasata bude motar tazira kafarta daya zata sauka.
Cak ta tsaya jin an riqomata hannu.
Tsayawa tayi daga yunkurin sauka
r baterada ta juyoba gabanta na faduwa.
"I'll miss you" yafada ahankali
Shiru tayi kuma bata juyoba.
"Please find a place in your heart and squeeze me in, i'll be grateful no matter how tiny the space it... don't let me keep wandering about helple
ssly in your love" yafada emotionally.
Shiru tayi bugun zuciyarta na qaruwa sosai, she's feeling somehow, tanajin wani iri sosai.
"Please give me another chance.... the chance to show you how i really feel about you" yasake fada still riqeda soft han
nunta.
"I... i want to go, dare... yayi" tafada muryarta nadan cracking
Shiru yayi yana kallonta na wasu mintuna sannan ahankali taji yana dago hannunta dake cikin nashi.
Saurin runtse idanu tayi don tasan abinda zai biyo baya.
"Muah!" Yaba ha
nnun light kiss wanda saida tajishi har cikin ranta.
"I love you" yafada ahankali sannan ya saki hannun.
Kamar jira take yasaki sai tayi saurin sauka daga motar tayi gaba batareda ta juyoba don ko rufe murfin kofar batayi ba.
Binta yayi da kallo c
ikin wani yanayi harta shige sannan ya sauke ajiyar xuciya ahankali.
Yadan dade anan sannan yafito ya zagayo yarufe kofar sannan yakoma mazauninshi ya rufo kofar ya tada motar yabar kofar gidan feeling so empty again...
✍
Ummin fasihu
🧚🏻
♀
️
🤵🏻👰
🏻
AUREN KWANGILA
🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Story written by Ashaanty love
💖
(Ummin fasihu)
087
Itakau dakyar tasamu tashige gidan tana tafiya tanajin kafaffuwanta na dan harhardewa.
Wani irin abu takeji wanda batasan taqamaimen mene
ne ba, sosai magangganun ashraf suka shigeta ga dumin da hannunta keyi haryanzu kamar yana cikin nashi.
Tsayawa tayi bakin kofar falo tana qoqarin daidaita nutsuwanta, danna power botton din wayarta tayi takawo haske.
Wara manyan idanunta tayi ganin
har 9:27 yayi.
Yanxu me zata cema mamy ya tsaidata har wannan lokacin?
Ganin qara 6ata lokaci take yasa tayi taking din deep breath sannan ta danna doorbell ahankali.
Ba'a wani dau lokaci ba aka bude kofar
Ido hudun dasukayi da mamy yasa qirjin
ta bugawa tayi saurin sunkuyar dakai cikin diriricewa.
Wucewa ciki mamy tayi batareda ta kulata ba hakan yasa itama tabiyota ciki kamar kazar da kwai yafashemawa aciki
Saida ta ida qarasowa ciki taga ashe harda Abba a falon.
Gabadaya taji ta dabur
ce don tafiyarma saida ta nemi gagararta.
Abdul ne yarugo dagudu ya rungumeta yana tsalle yana mata oyoyo.
Saurin riqeshi tayi itama ganin