Showing 81001 words to 84000 words out of 172372 words
your life, babu Wanda zaiyi qu
estioning dinki amma mamy fa? Me zaki cemata idan kin koma gida bayan watanni uku a matsayin bazawara?"
Sosai maganar ta daki saudart har saida hakan yanuna a yanayinta.
Ganin hakan yasashi dorawa da
"Yes in so samune murabu din kowa ya kama gaban
shi kowama yahuta, amma me zaki gayama mamy? Don't forget batasan komaiba gameda wannan auren ba, ya zataji idan labari ya risketa na kinfito bayan watanni uku da auren ki? Wane dalili zaki fadamata ya rabamu?" Yafada yana kallon yadda yanayinta ke qara ch
anza wa.
"D..don't worry, nasan me zan gayamata, wannan ba damuwarka bace" tafada trying to be firm
"Me zaki fadamata? Cewa dama auren contract ne auren mu?"
"Wannan be shafeka ba, uwatace ba takaba, babu abinda yashafeka"
"Nikau ya shafa miss,
mezan fadawa Ummy idan muka rabu? Mezance shine silar rabuwarmu?" Yafada trying to convince her
"Look mubar wannan maganar, contract ne ya hadamu, kuma shi zai rabamu, babu ruwan wani da abinda zai fada don gamsar da mahaifiyarshi, besides aure nawa ak
ayi? Normal aure, amma basuyi three months dinba auren ya rabu? Mutuwar auren mu a yanzu ba wani Abu bane it's normal, kana iya gayamata duk abinda kaga dama, I don't care" tafada firmly
Sa halshe yayi ya kashi qasan le66enshi ya tsaya yana kallonta gan
in tarkonshi besamu danuwa ba
"Amma kinsan mutuwar aure saida dalili? Wani dalili zan bayar na rabuwa dake?"
"Dalili? Dama saida wani dalilin, atunanina kafi kowa sanin dalilin haduwarmu shi zai zama silar rabamu"
"Amma wannan ba hujja bace dazamu
rabuba haka kawai, dole sai an samu kwakwarar dalili"
Tsayawa tayi sororo tana kallonshi
"What are you driving at wai?" Ta tambaya tana kallonshi unbelieving
Jan kujerar shi yayi dabaya sannan yamiqe tsaye ya nufi window din office din da labulen
ke bude ya tsaya yana kallon waje hannunshi a aljihu itakau sai binshi da idanu take
"Dukda auren mu ba normal aure bane, auren yarjejeniya ne, hakan be hana asashi a jerin aure saboda shima shafamashi fatiha akayi kuma igiyoyin nan uku akwai su tsaka
nin mu, dan haka shima aurene kuma yana cikin auren da Allah yafada cikin *suratul thalaq*
Inda Allah (swt) yayi hani da saki batareda da qwaqwaran hujjaba, bayyananniya.
Saki yana daya daga cikin abinda Allah beso, Wanda awata ruwayarma cewa ake ida
n aure yarabu, al'arshi girgiza take saboda girman abun koda kuwa akwai kwakwaran dalili bare wannan Wanda bekai hujjar dazamu fake daita ba mu sa6ama mahallicinmu, idan mukayi hakan me zamu cewa mahallicinmu? Dame zamu kare kanmu?"
Saudart datayi mut
uwar zaune tunda yafara magana kasa cewa komai tayi.
Wai meke shirin faruwa ne? Meya kawo wannan maganar kuma? A tunaninta izuwa yanzu sunmance da sun wuce wurin amma sai bullowa yake da abubuwa daban daban
"Look A.A ko mema kake? Meya kawo duk wanna
n wa'azin? Ohh dama duk kasan da wannan ka fara qirqiro maganar auren tun farko? Inajin kai ka faro komai ba wanibs, ina ilimin, ina sanin a lokacin? Koko sai daga baya duk kasan wadannan?
You force me into this marriage kuma yanzu kafara gayamin story
? No way! Bazan ta6a zama dakaiba a matsayin miji, are you not ashamed? Just listen to yourself, bazai ta6a yiwuwa ba kanaji? I can't even stand you, bana jure zama na tsayin lokaci wuri daya dakai, shine kakemin maganar zaman aure, are you kidding me? Loo
k Gwara kabar wannan kwalo kwalon naka and face the reality, this is just business and zai qarene a business! So wa'azinka bazai qareni da komaiba, ka Adana abinka zaifi yimaka amfani mallam" tafada cikin huci
Juyowa yayi yana kallonta tunda tafara har
takai aya,
Takowa yayi cikin takunshi harya iso gabanta inda take zaune yana kallonta
"And who told you nima sonike na cigaba da zama dake din, I have no option ne, abinda nasani shine bazan qara tafka sa6oba kamar yadda nayi a bayaba, bazan sakeki
batareda wata qwaqwarar hujjaba, final!"
Miqewa tsaye saudart tayi ba shiri
"What!" Tafada tana zare tabarau dinta, jikinta har rawa rawa yake saboda tashin hankali
"Look are you ok? What did you mean by bazaka sakeni ba? Me kake nufi? Na zauna da
Wanda duk duniya babu Wanda natsana kamarshi? No way!" Tafada cikin qaraji, tashin hankali qarara a fuskar
Kalmar tsanar data ambata ba qaramin dukanshi tayi ba hakan yasa ya dago idanunshi dasuka fara chanza launi shima ya zubamata
"Nikuma bazan
sakekiba! No way!" Yafada cikin 6acin rai
Kallo tabishi dashi na yan daqiqu sannan tasaki wata bushashiyar dariya Wanda daga ji iyakarta fatar bakin
"Wlh kayi kadan Ashraf, baka isaba, dolene ka sakeni! Saika sakeni wlh!"
"Nikuma bazan sakekiba!
Aure yanzu aka farashi, sai kisani sakinki din!" Shima yafada a tsawace
"I hate you! You brat! I hate you!!" Tafada cikin qaraji hawaye na 6alle mata.
sai kuma tafara daukar files files din table din tana jifanshi dasu kamar sabuwar kamu tana nannat
a I hate you din cikin kuka sosai.
Be kare kanshi ba haka yatsaya yana kallonta zuciyarshi na bleeding, duk Kalmar ta daya na I hate you jinshi yake kamar sukar wuqa a zuciyarshi.
Saida tagama watsar da kayan table din sannan tadawo kanshi tana dukan
shi da hannu tana kuka sosai sai nannata Kalmar ta tsaneshi take.
Sakin Jikinshi yayi tana dukanshi yana kallonta Yanajin kamar zuciyarshi zata tarwatse.
Jiyake inama zai iya yin kuka da yayi yarage rada din dayake ji a zuciya
Ganin abin nata bana
qarewa bane yasashi Kamo kanta, yayi locking din la66ensu waje daya yashiga bata the hottest kiss ever...
✍
️
Ummin fasihu ce
🧚
♀
🤵🏻👰🏻
AUREN KWANGILA
👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)
🤲
Allah ka ji6an
ci lamuranmu, karka barmu da kanmu
🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
058
Waro dukkan idanunta tayi kamar zasu fado daga socket dinsu tana kar6ar the shock of her life.
Jikinta ya mutu nan take kamar Wanda aka zarewa l
akka, tayi baya baya zata fadi ya sa hannu daya ya tarbota ta qugu yasake mannata da Jikinshi yana kissing dinta kamar kura tasamu nama Jikinshi har rawa rawa yake.
Sun kai minti daya ahakan, saudart kam bata iya misalta yanayin datake ciki don batama c
ikin hayyacinta.
Ashraf kam wani irin yanayi ya tsinci kanshi, having the extra soft lips of the love of his life in his mouth is undescribable.
Kissing dinta yake yana licking kamar yasamu tomtom shi kanshi yafara fita ahayyacinshi
Ahankali ya
fara cire bakinshi daga nata yana kallon fuskarta daya koma jaa kamar tomato.
Kallon juna suke suna sauke numfashi ahankali tare kamar wadanda sukayi wasan tsere.
Dukansu sun kasa yarda da abinda yafaru yanzu.
Kallon juna suka cigaba dayi kowa na
qoqarin daidaita numfashin shi.
Saudart takasa yarda da abinda yafaru yanzu, she can't believe yau tasamu first kiss dinta, kuma da Wanda duk duniya babu Wanda ta tsana kamarshi.
Wani ihu tafasa mai mugun qara Wanda saida Ashraf yasaketa babu shiri.
Jada baya tayi ta mannu da bango tana qara fasa wani Qarar Wanda yafi na farko, jikinta sai 6ari yake.
Nufota Ashraf yayi da niyyar yimata magana amma ganin ya tunkarota yasata taqarqarewa ta fasa wata Qarar Wanda saida ya toshe kunnuwanshi.
Banko
kofar office din akayi, Alhaji yafado ciki kamar an jefoshi sadeeq biye dashi dukansu a giggice da alamun ihunta sukaji suka shigo.
Ganin saudart sukayi manne da bango tanata ihu shikuma Ashraf na daga can gefe hannayenshi Dade da kunnuwa.
Da sauri
Alhaji ya nufi saudart ya riqota
Jin an riqota yasata fasa wata Qarar tana qanqame jikinta cikin fitan hayyaci.
"Shalele! Shalele!! Nine... Meya faru? Open your eyes and look at me.. Daddy ne..open your eyes!" Inji Alhaji yana riqeta gagaam ganin yad
da take kiciniyar qwacewa.
"Shalele listen to me, daddy ne..daddy, please look at me" yafada yana rungumeta
Jin kamar muryar daddy yasata dagowa ta dubeshi ganin shine din yasata qara qanqame shi tana kuka kamar zata shige cikinshi
"Take me out
dad! Ka fiddani daga nan" tafada cikin gunjin kuka.
"Shalele..."
"Please dad! Take me out" tafada tana qara qanqame shi
"Ok..ok" inji daddy da duk ya rikice suka nufi kofar still tana maqale dashi sannan ya bude suka fita.
Binsu da kallo su
kayi har suka fita sannan ahankali sadeeq yajuyo yana kallon Ashraf, kallon tuhuma.
Shikau Ashraf cizon le6enshi na qasa yayi yana runtse idanunshi da qarfi zuciyarshi na mashi wani irin zafi.
"Me kayi mata?" Inji sadeeq yana cigaba da jifanshi d
a kallon tuhuma.
Bude idanunshi dasuka rine yayi yana sauke numfashi mai nauyi har kana iya ganin yadda qirjinshi ke sama da kasa tacikin rigar shi.
Jiyake inama zai iya kuka kamar yadda yaga saudart nayi yasan ko babu komai zaiji dan sauqi sauqi a z
uciyarshi.
Yasan yanzu beda wani chance kuma, maimakon ya gyara abubuwa gashi ya ida lalatasu.
"Nace what did you do to her?" Inji sadeeq yana matsowa gabanshi.
Juyamashi baya Ashraf yayi tareda dafa desk dinshi da hannu biyu Yanajin kamar ya da
uke sadeeq da mari don da yasan yadda yakeji da bazaima fara tanka mashi ba.
Abin ne yaba sadeeq haushi ganin magana yake mashi amma yawani juyamashi baya, hakan yasashi juyoshi da qarfi yana cewa
"Am talking you junk!"
Be qarasa maganar ba yaji an
shaqeshi, kafin yasan meke faruwa harya mannashi da bango still shaqe da wuyanshi sai huci yake.
Waro idanu sadeeq yayi yana kallonshi not believing what is happening sai qoqarin kwatar kanshi yake amma yakasa.
Haryanzu qirjinshi sama da qasa yake sa
i motsa bakinshi yake amma wani Abu daya toshe mashi maqoshi yaqi barin maganar tafito.
"She is.. My.. Wife" yafada da daddaya kamar mai cutar asthma
Kusantoshi yayi har yana kusan hade fuskarsu
"So... Fuck off" yafada yana sakinshi sannan yaja d
abaya yana dafe gefen qirjinshi daya dayake ji kamar ana hura mashi wuta awajen sannan yajuya yafita cikin sassarfa.
Sulalewa sadeeq yayi yana zama qasa yana murza wuyanshi don ba qarya ya shaqu, sai jujjuya wuyanshi yake don jinshi yake kamar ba na
shi ba.
************************************************
Kasa gane kan saudart daddy yayi don tunda suka fito take kuka kamar ranta zai fita duk inda suka gitta sai an bisu da kallo.
Dakyar yasamu suka isa motarsu yabude bangaren mai zaman ban
za ya turata ta zauna sannan yarufe shima cikin sauri ya zagayo yashiga mazaunin driver ya rufo ya tada motar yayi reverse suka fita daga company din gabadaya.
Akan hanyar ma bata bar kukanba muryarta harya fara shaqewa, baqincikin da take ciki bazai
ta6a misaltuwa ba, bakinta sai zugi yake don ba qarya yasha tsotsa, duk zugi daya dazaiyi saiya tunamata da abinda yafaru, saiya tunamata she just kissed her worst enemy hakan ba qaramin tsimata yakeba hakan yasa takasa tsaida kukanta duk rarrashi da magiy
ar da daddy ke mata.
Daddy kau abin ba qaramin kulle mashi kai yayi ba, me Ashraf ya fadawa shalele daya rikitata har haka?
Shidai normal ya taddasu bare yayi zargin wani abun.
Kukanta ba qaramin rikitashi yakeba hakan yasashi qara speed ya nufi
gidan shi direct.
Hannu dafe da qirji yafito yana tsoma qafarshi duk inda yaga dama harya samu yafito.
Motarshi ta nufa direct ya bude ya fada ciki ya rufo da qarfi ya maida kanshi kan seat din yana numfashi ahankali still hannunshi dafe da gefen
zuciya.
Ya Dade ahakan, saida yafara jin sauqin abinda yakeji sannan ya miqe zaune ya kunna motar shima yabata wuta ya fice daga company din cikin wani mugun speed Wanda saida duk aka bishi da kallo.
Tuqi kawai yake amma badan kariyar Allah ba da
komai na iya faruwa don tuqin ganganci yake sosai, zagi kau yashashi wajen mutane amma a banza don besan suna yiba.
Ahakan ya qarasa gida yayi wani irin parking a tsakar hanya ya sauko ya nufi cikin gidan yana hada hanya.
A falo ya zube qasa yana wan
i irin haki kamar zai mutu, hannunshi dafe da zuciya sai ambaton sunan Allah yake ko zaiji sauqin abinda ke damunshi
Abu daya yasani, son saudart jarabta ce daga Allah kuma wataqila cutar Sonta zaiyi ajalinshi don dukda halin dayake ciki, soyyayarta qar
a farashi take a zuciyarshi, wutar soyyayarta qara ruruwa take a zuciyarshi.
A bangaren saudart kau suna yin parking a parking space din gidan ta 6alle murfin motar tafito tayi cikin gidan dagudu.
Saurin kashe motar Alhaji shamsu yayi shima y
afito ya maramata baya yana qwalamata kira.
Ina? Ko sauraronshi batayi ba ta haye sama ta bude dakinta tashige sannan ta maido kofar ta rufe harda saka sakata sannan ta sulale wajen ta cusa kanta tsakankanin cinyoyinta tana cigaba da kukanta cikin shaqa
qqiyar muryarta.
Duk bugun kofa da magiyar da daddy yake mata akan ya bude besata ta motsa daga inda take ba, kukanta kawai take yayinda kanta ke saramata kamar zai rabe gida biyu.
Dakyar ya iya tashi daga inda ya jibge tundazu, hannunshi still
a wuyanshi yana murzawa.
Tunda yake be ta6a ganin Ashraf acikin irin wannan yanayin ba, duk karfinshi kasa qwatar kanshi yayi Wanda yasan da zai kara minti daya be sakeshi ba da tuni ya margaya.
Nufar qofa yayi ahankali still yana jujjuya wuyanshi d
ayake jin dole yaje ganin mai gyara don Yanajin akwai qashin daya goce
😆
Fita yayi shima yanufi motarshi dafeda wuya sannan yashiga ya tada motar yanufi gidan Ashraf don yasan yadda yafita cikin wannan yanayin dole asamu matsala.
Direct gidan yanuf
a, tun a yanayin parking din Ashraf yasashi tabbatar da hasashenshi.
Saurin kashe motar yayi ya sauko sannan yanufi ciki dagudu.
Afalo ya taddashi zube bisa rug din tsakiyar falon.
Dasauri ya nufeshi tareda dagoshi.
"Ya sallam" yafada jin jik
in Ashraf rau kamar garwashi.
Ahankali ya taimaka mashi ya kwantar dashi akan three seater din falon sannan ya tsuggunna gabanshi
"Ashraf? Ashraf are you ok?" Yafada cikin tsananin damuwa
Dakyar Ashraf ya bude idanunshi wadanda sukayi nauyi ya kal
leshi.
"Sorry ok? Zan kira doctor yanzu ok?" Yafada yana murza hannunshi daya
Ahankali Ashraf ya motsa bakinshi alamun zaiyi magana, hakan yasa sadeeq saurin matsowa saitin bakinshi
"She.. Hates me" yafada cikin wata iriyar murya
Wani mugun t
ausayinshi sadeeq yaji ya lullubeshi
"Shhhh it ok, bata tsanekaba kaji?" Yafada cikin sigar lallashi
"She do... Ta tsaneni" yafada yana lumshe idanu
"Shhh it ok, karka sake magana ok? Bari nakira Dr"
Nan yafiddo wayarshi yakira doctor din.
Cikin dan qanqanin lokaci Dr din ya qaraso, nan yashiga duba Ashraf sadeeq na gefenshi yana kallon amininshi cikin tausayawa.
Saida yagama dubashi sannan ya umarci sadeeq yakamashi sukaishi daki.
Haka suka kamashi su biyu suka kaishi daki suka kwanta
r dashi sannan aka daura mashi drip akayi mashi allurar barci sannan Dr ya rubuta ma sadeeq wasu magunguna yabashi akan su za'a bashi idan ya farka.
Kiran messenger sadeeq yayi ya bashi umarnin yasiyo magugunan dazaimashi text yanzu yakawo gidan A.A
Sannan yayi mishi txt din sunayen magungunan yakoma ya zauna gefen Ashraf daketa barci yana sauke numfashi ahankali ya kama hannunshi guda yana murzawa cikin tsananin tausayinshi...
✍
️
Ummin fasihu ce
🧚
♀
🤵🏻👰🏻
AUREN KWANGILA
👰🏻🤵🏻
(Contract ma
rriage)
Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)
🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu
🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
😆😆😆
gaskiya jiya kun bani dariya musanmman yan AUREN KWANGILA NOVEL GROUP.
Team S
.S duk kurin da cika bakin? Yada saurin karaya haka?
Gaskiya bakuyiwa S.S adalci ba da kuke hijira kuna komawa A.A, tace agayamaku tana tsananin fushi daku
😡
kuma zaku gane shayi ruwane biredi soso ne
😠
059
Kiraye kirayen sallar azaha
r yasata dago kanta daga gwiwarta a inda take zaune bakin kofa tunda tashigo.
Ta Dade da barin kukan saidai na zuci datake.
Jiki ba kwari tamiqe tana dafa bango ciwon kanta na tsananta.
Da bin bango ta isa toilet ta daura alwala sannan tafito tana
takowa ahankali.
Shimfida sallayarta tayi ta gabatarda sallar zuhr dinta sannan takoma ta zauna ta jingina da jikin gadon ta tareda lumshe idanu.
Abubuwan dasuka faru yau tun daga zuwansu company har yanzu yashiga dawomata a kwanya.
Wani murmushi
n takaici ya su6uce mata
Lallai saita gwadawa A.A ba kowa ake takawa kuma ya takuba.
Yayi kadan yayi controlling din life dinta, dolene yasake ta koda kuwa sai an hada da shari'a.
Bazata iya da irinshi ba, bazatama iya misalta hakan ba ko da wasa.
Sh
e hate him with passion don haka maganar zaman aure dashi ma bai tasoba kwata kwata.
Bubbugar kofar dataji ya katse mata guntun tunaninta.
Kallon saitin kofar tayi batareda tace komaiba
"Shalele?" Taji muryar daddy a tausashe
"Please open the
door for daddy, ki bude kinji yar leleta?"
Shiru tayi kawai tana kallon kofar tanajin kanta cikin wani yanayi
"Kinga lokacin sallah yayi, please ki bude, ina cikin damuwa sosai, do you want daddy to be sad?" Yafada cikin sigar lallashi.
Girgiza m
ashi kai tayi kamar yana ganinta sannan ta yuqura ta tashi dakyar ta nufo kofar.
Jin motsinta kusada kofar yasashi dakatawa da rarrashi dayake mata yana kallon kofar.
Murda handle din yaji anyi sannan aka bude kofar saudart ta bayyana fuskarnan fayau
.
Saurin shiga yayi yana rungumeta Itakuma kamar abinda take jira kenan saita fashe da kuka dakusashiyar muryarta.
Bubbuga mata baya yafara yi cikin sigar rarrashi yana cewa
"Shhhh ya isa hakanan, please stop crying kar wani ciwon yakamaki" yafada
yana nufar gadonta daita sannan ya zaunar daita ahankali Itakuma ta Dora kanta a kafadarshi tana sauke ajiyar zuciya akai akai
"Am so sorry shalele, duk nine silar komai" yafada asanyaye
Girgiza mashi kai kawai ta iyayi hawaye na gangaro mata.
"K
iyi hqr ki fada min me yayi miki, please" yafada yana shafar kanta
Shiru saudart tayi tana sauke ajiyar zuciya ahankali, tasan ko giyan wake tasha bazata ta6a fadamashi abinda ya faruba.