Showing 93001 words to 96000 words out of 172372 words

Chapter 32 - AUREN KWANGILA BOOK1 COMPLETE

wanda zai zargi komai, suka yanke

wannan shawarar akan babu abinda zai shiga tsakaninsu har su rabu wanda lokacinda zasu rabu kuma zaiyi daidai da nagama karatu sai muyi aurenmu'"

Shiru baby tayi tana sheshekan kukan da tundazu tafarashi, shikau ashraf kamar statue yakoma sai binta da

kallo yake babu ko kyaftawa.

"Yaya wlh bakaji yadda najiba alokacin, zuciyata kamar ta tarwatse, nasan karya take yaya, sharri take qulamaku kaida anty hakan yasa natashi nasake nufarta ina bugunta ina kuka ina cewa karya take wlh sharri take muku.

Ita

dai ummy batace konaiba, she's shocked to death don tama kasa motsawa.

Dakyar suzy ta kwaci kanta ta tureni nafadi sannan ta watsamana wasu takardu tana magana cikin qaraji wai muduba idan qarya take don harda shaidu gasunan.

Duqawa ummy tayi ta tatt

ara takardun tana dubawa nan mukaga takardar comtract ne na auren kamar yadda tafada ga sa hannunka 6aro 6aro gana aunty ga kuma na sadeeq na hudun kuma tace natane.

Mun shiga rudani sosai don sosai hankalinmu yatashi.

Dayar takardar kuma na gwajin j

una biyu ne nata na wata biyu sai hotuna dakuke tare.

Ahankali ummy ta dago ta kalleta sannan ta sake kallon hotunan taga eh ita dince tareda kai.

'Juna biyu gareki?' Ummy ta tambaya

'Eh ummy kuma nashine wlh' ta amsa tana matsar hawaye

'To mey

asa kika tonaku bayan ba haka kukayi dashi ba?' Ummy tasake tambaya

'Saboda yanason tilastamin zubarwa ne kuma ni ina tsoron aikata kisan kai, dana gayamashi yace to ku in zubar ko intafi can nida cikin kar in alaqantashi dashi don ba shirya zubewar mut

uncinshi ba, nikuma naji haushi nafara masifar be isaba don tun farko shiya lallatani ba wani ba, shine yayiman mugun bugu yakuma ce yafasa auren kuma karna sake nanuna nasanshi.

Ganin ban iya facing din family dina da wannan abin kunyar yasani tahowa n

an don a warware komai asamamin mafita'

Tashi nasakeyi ina qaryata cikin kuka

'Ummy qarya take wlh, son yaya take da aure shikuma yaqi saurarenta shine tabiyo ta wannan hanyar tayaya za'ace anty saudart karuwa ce? Tayaya yaya zaiyi zina? Wannan sherrin

editing ne'

Dagaman hannu ummy tayi sannan tace ma suzy ta tafi zata nemeta saita tashi ta tafi.

Zuwa nayi kusada ummy nayita mata rantse rantse cewa qaryane, sharri ne

Batace mani komai ba sai shirun datayi na wani lokaci sannan ta umarceni na k

ira aunty saudart.

Kira biyar nayimata lafiyayye amma bata dagaba hakan yasa ta kiraka tace kuzo.

Saigashi kuna zuwa kuka gasgata abin"

Ta qarashe tana kifa kanta a dining table din.

Tsitt wurin ya dauka bakajin komai sai kadawar a.c dake wajen

Idanunshi sun kada sosai kamar gauta yayinda numfashinshi ke fita da nauyi har kana iya hango yadda qirjinshi ke sama da qasa.

Motsin dataji yasata dagowa daga kifa kan datayi taga shine ya miqe.

Sosai yanayinshi ya tsoratata hakan yaqara bugun

zuciyarta.

Juyawa yayi batareda yace komaiba ya fice daga dining din dama falon gabadaya yanufi parking space cikin wani irin taku nashi wanda ban ta6a ganiba saiyau.

Wayarshi yaciro yana dailing din number yana bude motar.

Ba'a dagaba harta tsin

ke hakan yasa yasake bugawa lokacin harya shiga motar ya tadata.

Sai a kira na uku aka daga, lokacin harya fara reverse

"Fuck you! Ina kake!" Yafada cikin wani irin murya

Bansan kome aka fadamashi ba saiya sake cewa

"Damn you! Nace where the hell

are you before I straggled you to death!" Yafada tsakankanin haqora, qirjinshi sai sama da qasa yake alamun zuciya

Bansan kome akace ba sai gani nayi yayi tilli da wayar seat din baya sannan ya bama motar wuta yafice daga gidan kamar zai tashi sama...

✍

️

Ummin fasihu ce

🧚🏻

‍♀

️

👰🏻🤵🏻

AUREN KWANGILA

🤵🏻👰🏻

(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)

🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu

🤲

Story written by Ashaanty love

💖

(Ummin fasihu)

064

Tsit dakin yayi bakajin komai sai qarar a.c dake aiki.

"Kutt... amma anyi tsinnaniyar yarinya, ciki? How and when?" Inji sadeeq cikin tsananin 6acin rai

Cize le6enshi na qasa Ashraf yayi yana kalkada kafa daga inda yake zaune, shik

adai yasan abinda yakeji acikin zuciyarshi.

"Lallai dolene akoyama yarinyarnan lesson, ni wlh nama manta da ita ashe tananan tana bibbiyarku, abu mafi daure kai anan shine ina tasan cewa auren contract kukayi? There is something fishy here" yafada yan

a zagaye dakin

"I can't believe ummy kallon mazinaci takemin a jiyan nan, kallon me lallata yanmata, ni... ni Ashraf" yafada cikin wani yanayi

"Dolene mu nunamata kuskurenta Ashraf wanda nan gaba ko wuqa akasamata a maqoshi bazata qara gigin yima wa

ni qaxafi ba, qazafin zina ba qaramin abu bane musanmman ma akan Saudart kamilar mace... baiwar Allah, allah kadai yasan yadda zataji idan labarin nan ya risketa"

Shiru dakin yasake dauka kowa da kalar tunanin dayake.

Ringing din wayar sadeeq ne ta

katse musu tunaninsu.

Zaro wayar yayi ya duba sannan ya dago ta kalli Ashraf daya lumshe idanunshi.

"Ashraf.. ummy ce" yafada yana maida kallon ga wayar kuma

Bude idanunshi yayi yazuba mashi kawai batareda yace komaiba.

Ganin kiran zai tsinke

yasashi saurin dagawa yakara a kunne.

Sallama yafara yimata sannan ya gaisheta a ladabce.

Bansan kome tacemishi ba saiya dago ya kalli Ashraf da shima kallonshi yake yace

"Eh gashinan ummy"

Magana aka sakeyi tacan 6angaren sannan yace

"Insha

allah ummy"

Katse wayar yayi ya maido kallonshi ga ashraf dake kallonshi haryanzu.

"Ka tashi mutafi"

"Ina?" Ya tambayeshi ahankali

"Ummy ke nemanmu tace takira wayarka ba'a dagawa" inji sadeeq yana nufan closet dinshi don zaro rigar dazai daura

bisa singlet din jikinshi.

"Ban iyawa, bazan iya fuskantar ummy ba ahalin yanzu" yafada yana dafe kan dake saramashi

"Meyasa? Yanzu ne the right time dazamu fahimtar da ita komai tun kafin abu ya girmama, yau zatasan komai so stand up dalla" inji sa

deeq yana dora shirt saman singlet din.

"Allah kadai yasan kallon datakemin yanzu, i swear sai suzy tayi nadamar zuwanta duniya" yaqarashe yana huci

"Ai fadi ma 6ata baki, she really need to learn the lesson of her life, tashi mutafi"

Jiki asanyay

e ashraf yatashi, besan yadda zekuma qara facing din ummy bayan yagama sanin kallon datake mashi.

*************************************

Zaune suke gabanta qasan rug kamar dai jiya kowanne kanshi sunkuye.

"Ina kiranka baka dagaba" inji um

my tana kallon Ashraf daya kasa hada idanu da ita

"Am..sorry, na..barota a mota ne" yafada kanshi still a qasa

"Wacece wannan?" Tafada tana turomashi wani pics gabanshi.

Dagowa yadanyi yana kallon pics din.

Hotonshi ne da suzy tadan shige mashi

ajiki tana dariya shikuma yadanyi murmushi

Bazai manta ranar dasukayi hoton ba, ranar suna school ba'a dade da gama sheqa ruwan sama ba, garin yayi shar mutane sun fito waje sai daukar pics suke.

Saukowa shima yayi hannunshi riqeda wani qaton littaf

i shima yatsaya yana kallon students din

"My.." yaji an kwala mashi kira abaya.

ko be juyoba yasan itace

Qarasowa tayi gabanshi tana haki, binta yayi da kallo yadda kayan jikinta suka dan jiqe gashi tawani tsuqe cikin jumpsuit (biri da wando) babu

ko mayafi sai yar hular datasa akai.

"Please muma muyi hoton..please" tafada zata riqe hannunshi.

Dan zamewa yayi yana harararta

"Look at you, wai bakijin sanyi ne kam?" Ya tambaya yana binta da kallo cikin kishi

Itama kallon kanta tayi sannan

ta kwa6e fuska

"Am sorry zan chanza yanzu, please mu dauka ko dayane"

"No" yafada firmly yana juyawa zai tafi.

Bunshi tayi tafara mishi magiyar ya bari ko dayane suyi, ganin bazata barshiba yasashi hqr ta tsaya ta fiddo wayarta ta matso jikinshi

kadan, bece mata komaiba don aqagare yake tayi din yatafi.

"Please kayi murmushi mana wannan hade ran dukna menene?" Tafada a shagwa6e

Tsaki yaja sannan yadanyi yaqe ta daukesu sannan yadan tureta daga jikinshi yana cewa

"Ai shikenan ko? Am going t

o the library, see yah" yajuya yatafi.

"Nace wacece wannan?" Muryar ummy tasake maidoshi daga duniyar tunanin daya lula.

Ajiyar zuciya yasaki sannan ya bude bakinshi dakyar

"Tsohuwar budurwa ta ce"

Shiru dakin ya sake dauka.

Rintse idan

unshi yayi snnan yacigaba dacewa

"A school muka hadu kuma muka fara soyyaya... saidai tafiyarmu batayi wani nisaba muka rabu don kwata kwata batada kamun kai, ga shigar datakeyi anyhow dukda ina nuna mata rashin dacewar haka amma bata dauka..."

Shiru

yasakeyi idanunshi still rintse yana sauraron bugun zuciyarshi.

"Mun..mun rabune ranar dana..."

Shiru yasakeyi hoton yadda ya taddata suna musayar hot kiss dawani qaton arne a wani class na dawomashi a qwanya.

"Sadda na.. naganta dawani suna.." s

ai yayi shiru yakasa idawa.

Ummy kallonshi take tunda yafara magana kuma haryanzu bata daina kallonshi ba

"Ummy na rantse ban ta6a zina ba, ko zanyi bazanyi da qazamiyar yarinyarnan ba, bansaniba.. bansan abinda aka fadamaki kenan ba, yes aurenmu da

Saudart AUREN KWANGILA ne amma babu wata yarjejeniya makamanciyar wadda ta fadamaki a tsakaninmu da saudart, she's innocent.. hasalima..bada son ranta akayi auren ba, believe me ummy.. kinfi kowa sanin halin danki..."

Ya qarashe maganar muryarshi nadan r

awa rawa.

"Ummy suzy shaidaniyace, sharri ta qullamasu saboda daga baya tadawoma ashraf yaqi sauraronta shiyasa ta buyomashi ta wannan hanyar, ummy ni aminin ashraf ne tare muke akoda yaushe, ko alokacin dasuke soyyayar ban ta6a ganin ya riqe koda dan q

aramin yatsanta ba, hasalima bawani sonta yakeba duk ita taita cusa kanta gareshi" inji sadeeq

"Hakane ummy, nima nasan suzy farin sani, qawayenta kawai zaki kalla kisan ko ita wacece, tasha cusa kanta gareni don tasamu shiga awajen yaya akaro na biyu,

tasha tazo taita rarrashina akan nabata number yaya amma naqiya, ga sa bikin su yayama saida suka fito qarara suka nuna baqincikinsu, magangannu kala2 babu wanda basu fadaba, ummy ko rantsuwa nayi bazanyi kaffaraba suzy qarya tashiryama yaya do n tasamu a

liqamashi ita" inji baby itama fuskarta bayyane da 6acin rai.

Shiru dakin yasake dauka, kan ashraf haryanzu aqasa zuciyarshi na bugawa yanason jin wane hukunci ummy zata yanke.

Ajiyar zuciya ummy tasauke mai sauti sannan tace

"Kalleni Ashraf"

Shiru yayi yakasa dagowa, bejin zai iya dagowa su hada ido daita, wani irin nauyinta yakeji

"Nace ka kalleni"

Ahankali yadago ya kalleta saikuma yayi saurin kauda kai ganin ta kafeshi da ido.

"Nasani, nasan qarya take kuma sharri takemuku tun a

lokacin datake maganar, nasan cikinku babu wanda zai iya aikata abinda tace kun aikata, nidama ban zargeka ba ban kuma zargi daughter ba cos I trust you both"

Ajiyar zuciya ashraf yasauke mai sauti yanajin kamar ana lifting din wani qaton dutse a qirji

nshi.

"Wacece saudart? Meya hadaku? Meye silar wannan auren naku na contract?"

Tambayar ummy tasauka a dodon kunnensu.

Kowannensu shiru yayi zuciyarsu na bugawa.

"Magana nike" tafada tana binsu da kallo.

"Ummy.."

"Shhhh.. barshi yayi ma

gana, dashi nake ba kai ba, ka gayamin komai ashraf karka saki ka 6oyemin komai" tafada tana kallonshi.

Shiru falon yasake dauka, sai motsi yake da baki amma yakasa magana, yarasa ta inama zai fara.

"Saudart diyace ga SHAMSU KANKIYA...Tsohon aminin A

bbu" yafada yana lumshe idanu.

Ware idanu Ummy tayi tana kallon Ashraf unbelievably

Bakinta na rawa tace "Shamsu qolo?"

Kada kai yayi zuciyarshi na suya.

"Nafara ganin appointment letter dinshi ne wattanin baya dasuka wuce, akan yanason ra

nce don farfado da company dinshi dake neman collapsing... ina ganin sunan naga tabbas kamar nasanshi wani wuri, hakan yasa babi diddigin qundinshi ta internet anan naga shidinne bawani ba... nan take tsohon raunin dayaimana a zuciya ya motsa naji na tsane

shi fiyeda yadda na tsaneshi da, dafarko sai naso qin taimaka mashi amma sai wata idea ta fadomin, mezai hana inyi ramuwar gayya nima in dandana mashi abunda ya dandana mana?

Saina amsa buqatarshi nabashi ranar dazamu hadu sannan nakoma naita bin diddig

inshi daga kan iyalanshi zuwa abokan aikinshi dakuma abinda ya tara da abinda ake binshi bashi.

Saura kwana daya mu hadu na gayawa sadeeq plan dina, dafarko yaso hanani yacemin inbarshi da allah kawai mai yiwuwa sakkayar allah ce yake gani tun yanzu amm

a sainaqi saurararshi don alokacin *WUTAR FANSA

🔥

*(littafina ba gaba insha allah) ke ruruwa azuciyata, na nunamashi bansan zancenba acewata don indauki fansa yasa allah yaturoshi wajena..dakyar nayi convincing din sadeeq ya amince min shima.

Ranar farko

n dayazo...."

Nan yashiga bata labarin zuwan Alhaji shamsu nafarko company dinshi da yadda suka kaya sai kuma zuwanshi da biyu da yadda ya gabatarmashi da sharaddinshi dakuma amsar daya bayar na zaije ya shawarta.

Yakuma gayamata zuwan da saudart tay

i da abinda yafaru tsakaninsu wanda hakan yaqara 6atamashi rai dakuma qara jin lallai saiya aureta donya koyamusu hankali gabadaya.

Yabata labarin yadda alhaji yaita fadi tashi har yasamu saudart ta yarda dakuma yadda aurensu yakasance har izuwa zaman a

urensu ya gangaro zuwa fara aikinta a companynshi da abubuwan dayaita mata na muzgunawa ya gangaro zuwa tafiyarsu spain da zamansu acan dakuma yadda ta taimaka mashi wajen kama mayaudaran mutanen dasukaso karyashi har zuwa lokacin dasuka dawomashi da kudi

nshi da niyyar kawo qarshen contract din da abinda yafaru aranar dukda ya 6oyemata kissing dinta dayayi sannan ya gangaro har zuwan da sadeeq yace yayi gidansu jiya da barazanar makashi kotu datayi.

Shiru yayi yana sauke numfashi ahankali saboda dogu

war maganar dayayi.

Dakin yayi tsit babu mai ko motsi yadda kasan babu kowa ciki.

"Na aureta ne badon komaiba saidon in rama abinda yayimana ko fiyeda hakan, nabashi rancen ne bisa tsarin zanyi shige da fice yadda komai nashi zai lallace yakasance ba

bu uwar kudi ba riba ga kuma uban bashi.

Nikuma lokacin sai in nuna bansan zancenba saiya biyani inhar yanason diyarshi, sonake ya talauce shima yakoma bayada komai shima ya dandana abinda ya dandana inyaso shima zuciyarshi ta buga ya fadi mattac..."

Tasss! Sautin dayaji a qunnenshi ya hanashi qarasawa.

Kafin ya tantance meyake faruwa tasake daukeshi dawani zazzafan marin a dayan kumatun

Dafe duka kumatun yayi ta dogo da sauri yana kallon ummy daka tsaye sai huci take idanunta sun chanza launi

.

Toshe baki baby tayi da hannu biyu tana ware idanu, tashin hankali qarara a fuskarta.

"Da hankalinka?" Ummy ta fada tana nunashi da yatsa manuniya.

"Nace da hankalinka da iliminka ka aikata wannan abin da ko jahili bazai aikataba?"

Kasa ko

da motsi yayi daga tsugunnen dayake hannayenshi dafe da kunci yana kallonta

Yakasa yara yau ummy ta dora hannu akanshi da sunan duka abinda bazai iya tuna when last tayimashi va tsawon rayuwarshi

"Fansa haukane?! Aure? Aure ka maida abin wasa? Abun d

aukar fansa? Ka rusa rayuwar yarinya da future dinta duk akan fansa?" Ta tambaya cikin zaremashi idanu.

"Ummy don alla.." katseshi tayi ta hanyar qamtsamashi nashi qason marin

"Yimin shiru! Harda kai? Atunanina kafishi hankali ashe taron zamuce ta t

adda muje?!"

Dafe kuncinshi shima yayi yana sadda kai qasa

"Kaiga sarkin zuciya? Mai zuciyar qarfe dabakasan kabar mutum da allah ba? Akan banzar daukar fansarka ka janyo wanda bata jiba bata ganiba kana neman lallatamata rayuwa?! Kana..."

Kasa i

dawa tayi ta juya kawai ta dafe kanta kasancewar ta mai zuciya idan ranta yayi mugun 6aci maganama gagararta yake.

Ganin hakan yasashi saurin rarrafowa yana riqemata qafa.

"Ummy am sorry, am soo sorry"

Fizge kafarta tayi da karfi taja baya.

"

You're not but you will be, kutashi kufita! Kutashi nace!!"

Tafada tsakankanin abinda ya toshemata maqoshi.

Saurin tashi sadeeq yayi amma ashraf ko gezau

"Kutafi nace kuma kai.."

Ta nuna ashraf

"Gobe kamar yanzu inason ganinka anan gidan da ta

kardar saudart, banaso ko igiya daya ta rage atsakaninku"

Agigice ya dago yana kallonta yayinda zuciyarshi tayi wani mugun bugawa.

"Kaji nagayamaka! Ke tashi kitafi dakinki!"

Ta dakama baby tsawa.

Dagudu ta tashi tayi sama aguje.

Itama bin b

ayanta tayi tahaye sama batareda tasake kallonsu ba.

Dafe kanshi ashraf yayi cikin tashin hankali wanda tunda yake beta6a shigaba yayinda zuciyarshi ke bada wani hucin zafi kamar a oven....

✍

️

*WAYE ASHRAF?*

Ummin fasihu ce

🧚🏻

‍♀

️

👰🏻🤵🏻

AURE

N KWANGILA

🤵🏻👰🏻

(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)

🤲

Allah ka ji6anci lamurranmu, karka barmu da kanmu

🤲

Story written by Ashaanty love

💖

(Ummin fasihu)

065

*WANENE ASHRAF?*

*AUWAL MUHAMMAD* Haifaffen garin wudil ne dake jahar kano.

Su shidda ne awajen iyayensu *MUHAMMAD JARIRI* wanda akafi sani da *MAMMAN* da matarshi *AMEENATU*

Yayansu shidda, maza hudu mata biyu.

Auwal shine d'a nafarko, sai ibrahim dake bimishi sa

i Nuradeen, sai Jamila, sai Zaharadini sai auta Halimatu wanda watanta uku a duniya ta rasu.

*MALLAM MAMMAN* manomine wanda ya riqe noma amatsayin sana'arshi, yanada rufin asiri daidai gwargwado don cikin noman yake samun abinci dazasuci harkuma su sa

yar.

Duk cikin yaranshi babu wanda yayi boko don lokacin ba'a wani bama karatun boko muhinmmanci ba.

Iyakarsu makarantar allo sai suwuce gona idan sun tashi don taimakawa babansu.

Jamila nada shekaru sha shidda akayimata aure dawani d'an abokin

Mallam Mamman dake qauyen kakumi.

Auwal tun tasowarshi yakasance yaro mai hazaqa da zuciyar nema, duk yafi sauran yan uwanshi kazar kazar da qoqarin aiki.

Shiyasa sukafi shaquwa da Mallam Mamman don sosai yake taimakamashi a gona.

Auwal da kingi

n yan uwanshi sunada hadin kai ga girmama na gaba dasu suk qarantar taxarar dake tsakaninsu kau, hakan yasa zaman lfy, girmama juna da hadin kai ya wanzu a ahalin.

Koda sukadan qara tasawa sai suka amshi ragamar nomar yakasance mallam mamman ya sakarm

usu komai yakoma yana hutawa.

Haka rayuwa tacigaba da kasancewa a wannan ahalin har watarana wani abokin mallam mamman dake zaune cikin garin kano yakawo mashi ziyara.

Anan su Auwal suka taddasu lokacin sun dawo daga gona, saida suka gaishesu sanna

n suka shiga cikin gidan.

Bayan sun shige ne abokin mallam mamman wato *MALLAM SANI* yayima mallam mamman tayin mezai hana yabashi daya daga cikin yaran yabishi kano ya hadashi da d'anshi sudinga aikin tuqin dayake.

Dafarko mallam be yarda ba, dakyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login