Showing 105001 words to 108000 words out of 172372 words
hakan yasa hankalinshi qara tashi.
Hannu na rawa ya danna last floor elevator din yabude yafada ciki yana addu'ar allah ya tsare ashraf don beta6a jinshi cikin irin wannan yanayin ba.
"And nagayamashi zan raka
shi amma yaqiya, ai ga irintanan" yafada restlessly yana dan zagaye zagaye a elevator din yanajin kamar va tafiya yakeba.
Elevatorn ba tsayawa yayi saurin fitowa yayi parking space dagudu ya bude motarshi yashiga ya kunnata yayi reverse.
Saida ta
ci kukanta ta qoshi sannan ta dago ahankali ta kalli mirror din jikin sink din tana kallon yadda fuskarta tayi jaa ta kumbura.
Kunna fanfon tayi ta tara hannunta ta debi ruwa ta wanke fuskarta sannan tajawo hand towel dake rataye awajen ta tsane fuskart
a sannan tafito tana dan layi saboda yadda kuka yayi exhausting din qarfinta.
Jakkarta kawai tabude ta watsa wayoyinta aciki sannan ta zage ta ratayeta tasaka sunglass dinta wanda yarufe asirin kumburan da idanunta sukayi tafito don batajin zata iya qar
a koda minti dayane a bakery din.
Haduwa sukayi da maryam data fito daga wani office
"Ma'am fita zakiyi?" Injita tana kallonta.
Kanta kawai ta iya kadamata ta fice da sauri itama ta bude motarta tashiga ta kunna itama tafice daga bakery din...
✍
Manage please
👏
Ummin fasihu ce
🧚🏻
♀
️
👰🏻🤵🏻
AUREN KWANGILA
🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Happy edl-mubaraq fans
🧚🏻
♀
️
Fatan anyi sallah lfy, fatan kuma ba'ayiwa nama cin rashin mutunci ba
😏
Kodayake ai ko kunyima zai rama ne
😆
Am back again, masu cigiyata ngd, masu kira kudos
🤙🏻
Ashaanty loves you
😍
070
Tuqi yake amma yarasa inda zai nufa, besan inda zai fara nemanshi ba.
Fatanshi daya shine Allah yasa kar yace zaiyi driving acikin wannan halin.
*sauda
rt ce sadeeq, I love her... she hate me... zuciyata zafi*
Maganar Ashraf tadawo mishi.
Kenan sun hadu? Definately sun hadu, yabama kanshi tabbaci.
Karya motarshi yayi yakama hanyar gidansu saudart.
*wannan hannayen.... bazasu iya rubutamaki
abinda kikeso ba*
*yatsuna bazasu iya riqe pen ba dasunam datse abinda yayi bonding dinmu ba*
Cize le6enta naqasa dasukayi jaa saboda kuka tayi tana lumshe idanu don ba hawayen dasuka qara forming a idanunta damar gangarowa.
Zafi takeji a zuciyar
ta marar misaltuwa, she can't believe yau itace abin wasa, abin toying.
Ita zai nunama isa da iko? Dama yace zai nunamata koshi wanene, dama abinda yake shiryawa kenan?
Dama burinshi ya daqilemata duk wani farinciki nata?
Burinshi ya ganta cikin
dawwamammen qunci?
Bayan hannu tasa ta sharce hawayen fuskarta ta cigaba da tuqin wanda allah allah take ta isa gida don tuqin ma yafara gagararta.
Jin motsin mutum na kusanto gate din yasashi tsagaitawa da knocking din yana kallon ruffafen gat
e din.
Qaramar kofar gate din aka bude fuskar maigadin ya bayyana.
Ganin sadeeq yasashi washe baki don be manceshi ba kuma ranan dazai tafi saida yaimashi alhairi.
"A'a? Kaine?"
Shima sadeeq cikin fara'a yace "nine wlh, barka da warhaka"
"Ba
rkanka dai, ya aiki?"
"Alhamdulillah" yafada yana gyara tsayuwarshi
"Erm... tananan?" Ya tambaya
"Wlh kau yau kayi rashin sa'a, yau tunda safe hajiya tafita, dazunma wani yazo nemanta saidai tafiya yayi"
Dan daga gira sadeeq yayi
'Wani? Cou
ld that be Ashraf?'
Uban horn din da aka danna ta bayanshi ya katse mashi guntun tunaninshi.
Tare suka waiga shi da maigadin don ganin wanene ke shirin dodemasu kunnuwa.
"Yar halaq gatanan" inji maigadin yana komawa ciki da sauri don budemata babb
an kofar gate din.
Bin motar sadeeq yatsaya yi da kallo na yan daqiqu sannan yatako a nitse ya nufo motar.
Gab da zai karaso ta sake tada motar ta figeta tashige cikin gidan kasancewar har anbude gate din tana badeshi da kura.
Bin motar yayi d
a kallo yadan girgiza kai sannan shima ya maramata baya.
Sadda yashigo harta fito daga motar.
Kallo daya zaka mata kasan ba lafiya ba.
Zuwa tayi zata giftashi ta wuce batareda tanuna tasan an dasashi awajenba
"Miss saudart.." yafada ganin zata
wuce
Ko iskan daya kwasoshi bata kallaba tacigaba da tafiyarta.
Binta yayi yana cewa
"Good day miss saudart.. please listen to m..."
Kasa qarasawa yayi ganin ta tsaya cak daga tafiyar datake kamar wanda aka tsaida da remote.
A nitse ta juy
o ta kalleshi ta cikin sunglass din idanunta sannan ta kalli saitin gate ta kwalawa maigadi kira cikin muryar da bata ta6a yimashi amfani dashi ba.
Da sauri maigadin ya iso wajensu yana dan russunawa cikin girmamawa.
"Wayace ka dinga shigo da kowacce
shara agidan nan?" Ta jefa mashi tambayar cikin tsuke fuska.
Dan dagowa maigadin yayi ya kalleta a mammakince don wulaqanci ba halin saudart bane shi shaidane.
"Ayi haquri.. gani nayi.."
Katseshi tayi ta hanyar daga mashi hannu.
Sannan ta nuna
shi da car key din hannunta.
"Kasake barin irin wadanan gabbages din shigowa gidannan... believe me abincinka yaqare a gidannan, now ka gwadamashi hanyar fita"
"To..to hajiya insha allah" inji maigadin a sanyaye.
Juyawa tayi zata wuce saikuma ta
tsaya daga takunta tana dan cije le6en qasa.
Juyowa tayi a nitse ta kalli sadeeq dashima ita yake kallo expressionless.
Cikin sanyin murya mai shige da rada tace
"Zan gwadamashi... zan gwadamashi mata ma suna suka tara, zan gwadamashi ba kowa zaka
iya takawaba kuma ya taku... he's playing with fire and he'll get burns. I'll made life a living hell to him.... *mark it*"
Tana kaiwa nan tajuya tawuce.
Binta da kallo sadeeq yayi harta shige sannan ya dauke kai daga barin kallonta yana sauke ajiy
ar zuciya.
Maigadi dake tsaye haryanzu yace
"Kayi hqr amma wannan ba halin hajiya bane, qila 6atamata rai akayi waje"
Kallon maigadin sadeeq yayi sannan yadan saki murmushi
"Ba damuwa ai" yafada yana saka hannu cikin aljihu ya fiddo kudi yaba ma
igadin.
Qin amsa maigadin yayi dafarko saida sadeeq ya 6atarai sannan ya amsa yana kwarara mashi godiya sannan yarakashi haryaga tashin motarshi sannan ya maida gate din yarufe.
Ahankali take taka stairs din kanta qasa harta kai qarshe sannan ta is
a bakin kofarta tasa hannu cikin sanyi ta murda yabude tashiga.
Maida kofar tayi ta rufe sannan ta jingina da kofar tana sakin jakkar hannunta a wajen tareda lumshe idanunta dasuke mata yaji yaji tsabar zubda hawaye.
Wannan wacce iriyar qaddarace? As
hraf qaddarartace tasani, tun shigowarshi arayuwarta tarasa walwalarta da farinciki.
Tasan qar6ar kowacce iriyar qaddara yana cikin cikon imani amma bata tunanin zata iya qar6ar wannan qaddarar.
Bazata iya zama cikin qunci ba tsawon rayuwarta ba, baz
ata iya zama da wanda ita kanta batasan iya tsanar datake mishiba.
Wannan be dauki dan adam a bakin komaiba, wanda besan darajar iyaye ba.
Zata iya rungumar kowacce qaddara amma banda wannan, banda wannan baqar qaddarar.
💖💖💖💖💖💖💖💖💖
Tuqi yake amma kallo daya zaka mashi kaga damuwa qarara a fuskarshi.
Wannan wacce iriyar qaddarace? Tausayi suke bashi dukkansu, yasan they are having tough time dukkansu.
Kofar gate din gidan yatsaya akayi scanning dinshi sannan ya shiga.
A mammakince yake kallon motar dake tsaye a passage wanda ko arxiqin a qarasa da ita parking space bata samuba.
Saurin tsaida motarshi yayi yafito yanufi motar.
Kasancewar tinted ne glasses din motar be hangen naciki hakan yasashi bubbuga glass d
in 6angaren driver ahankali.
Shiru... hakan yasashi qara bubbugawa nan na tsit.
Duqowa yayi yana leqe ta baqin glass din kozai iya hango mutum ciki.
Hangowa yayi dishi dishi kamar mutum hakan yasashi sake bubbuga glass din.
Zaune yake cikin
motar kanshi kife da sterring din motar.
Dakyar yasamu yakawo kanshi gida inda ko qarasawa parking space yakasa ya tsaya anan.
Duk bubbugar glass din da'ake yanaji amma beda kuzarin motsawa, he's so weak har cikin zuciya, jinshi yake kamar marar lak
ka.
"Ashraf...Ashraf open up" inji sadeeq yana bubbugawa yana leqenshi at the same time.
Shiru ashraf yayi don be iyawa, da yana iyawa da be dauki tsawon lokaciba a zaune haka ba.
Ganin beda niyyar motsawa yasa sadeeq miqewa yanufi cikin gidan
da sauri, shi tsoronshi ma kar ace asume yake.
Dakin ashraf yashiga ya nufi locker dayake aje keys dinshi.
Kwasosu yayi batareda ya tsaya dubawaba yayo waje cikin sassarfa.
Agefen drivern yakoma ya saki keys din qasa yashiga lalluben spare key din
motar.
Dakyar yagano key din sannan ya tashi ya zira a motar yabude.
Gabanshi ne yafadi ganinshi zaune kanshi kife da sterring.
"Subhanallilah! Ashraf?" Inji sadeeq yana dagoshi.
Kamar marar lakka haka ya fadamashi ajiki yana sauke numfashi
mai nauyi.
"Ashraf? Are you ok?" Inji sadeeq yana nishi dakyar a dalilin nauyin da ya sakarmashi.
Shiru kuma be bude lumsassun idonshi ba.
Ganin haka yasashi qoqarin fiddoshi a motar.
Dakyar ya fiddoshi ya ratayo hannunshi a wuyanshi yana qoqar
in gyara tsayuwarshi.
Sake tamke idanunshi ashraf yayi saboda ranar dake hasko saitin fuskarshi wanda hakan ke qaramashi sarar da kanshi kemashi.
Dakyar sadeeq yasamu yakaishi falon ya kwantar dashi kan three seater ya dora kaffafunshi sama tareda
zaremashi takalmin kafarshi sannan yadawo saitin fuskarshi ya zauna ya riqo hannunshi cikin tausayawa, ganin kamar yanajin sanyi yasashi daukar remote ya kashe A.C din dakin yadawo kusadashi yana dan murza hannunshi.
"A.A are you ok?"
Shiru..
"
Bari nakira doctor" yafada yana zaro wayarshi.
Ahankali ashraf yashiga girgiza kai idanunshi still a lumshe, shi kadai yasan abinda yakeji.
"No ashraf kana buqatar doctor" inji sadeeq yana laluban number wayar Dr.
Bece komaiba sai hawayen dasuka s
ulalo ahankali daga rufaffen idanunshi suka gangaro mashi.
Babu abinda ke yawo kuma yake amo a kwanyarshi sai kalmomin saudart na daxu.
Ganin hawayen ashraf yasa hankalin sadeeq ida tashi.
Rungumoshi yayi sosai jikinshi cikin tausayawa
"Ashraf
please take it easy..insha Allah komai zaiyi daidai please" yafada cikin karyayar murya
Shidai ashraf be tankaba yananan yadda yake sai hawayen dake zuba daya bayan daya.
Suna haka Dr yazo.
Da taimakonshi aka kamashi suka kaishi daki, izuwa yanzu
jikinshi yayi rau kamar garwashi.
Kwantar dashi sukayi sannan Dr yashiga dubashi sadeeq na gefe yana kallonsu cikin mutuwar jiki.
Drip ya daura mashi yayimashi allurar barci sannan ya rubuta masu magunguna.
Zaune sadeeq yayi gabanshi yana kallon
cute face dinshi, tunda yake beta6a ganin ashraf cikin makammanciyar damuwa irin wannan ba, jiyake kamar ya daukemashi abinda yakeji ya maidoshi jikinshi.
Qara kiran wayar ummy yayi karo na uku amma ba'a dagaba kamar sauran.
Ajiyar zuciya yayi ya aj
iye wayar ya zabga tagumi yana kallon sleeping ashraf kamar mirror.
A taqaice dai ranar takasance ranar qunci garesu, damuwa qararra ya bayyana a rayuwar wadannan bayin allan,
Dakyar sukaga wayewar garin.
WASHEGARI
Jin bubbugar bata han
kali bane yasata katse lazumin nata tamiqe da sauri ta nufi kofar tabude.
Baby ce ta fadomata ajiki tana kuka sosai.
Saurin dagota ummy tayi tana kallonta
"Meye haka? Lafiyarki kuwa?"
Cikin kuka baby tace
"Ummy... yaya ashraf" saikuma tafashe
da kuka
"Wai menene? Meya sameshi?" Inji ummy hankalinta na dan tashi
"Beda lfy... yanzu haka suna hospital" tafada cikin kuka sosai.
Shiru tayi saidai kallo daya zaka mata kasan hankalinta atashe yake.
"Ummy please muje...karya mutu" tafada
cikin kuka sosai
"Jeki shirya maza" inji ummy tana komawa ciki itama don shiryawa.
Hankalinta yatashi matuqa.
Ita bazata iya tuna rabon ashraf da kwanciya asibiti ba.
He's always healthy and energetic, ba qaramin abu zai kwantar dashi ba.
"Y
a rahman.. take control tafada tana daukar purse dinta tayo waje suka hade da baby suka nufi waje cikin sauri.....
✍
Ummin fasihu ce
🧚🏻
♀
️
👰🏻🤵🏻
AUREN KWANGILA
🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Story written by Ashaanty love
💖
(Ummin fasihu)
071
Zaune yake jigum ya zubamashi idanu yana kallon yadda yake sauke numfashi ahankali na barci.
Sosai jiya cikin dare ya tsoratashi don giggicewa yayi da ganin yanayinshi.
Tunda Dr yayimashi allurar barci be tashiba sai wajajen takw
as na dare.
Lafiya lau ya tashi yaci abinci ya rama sallolinshi yasha magani sannan yakoma ya kwanta.
Shima sadeeq ganin hakan yasa hankalinshi kwanciya har yasamu damar kwanciya shima.
Can cikin barci yaji sautin tari babu qaqqautawa wanda haka
n yasashi watsakewa ba shiri.
Ashraf yagani zaune yana tari tafin hannunshi dafe da qirji yanata tari babu qaqqautawa.
Bashiri ya duro daga gadon ta zagayo wajenshi yana riqeshi ganin yadda jikinshi ke rawa.
Sosai hankalinshi ya tashi nan yaita je
ramashi sannu.
Ganin tarin yaqi tsayawa yasashi sakinshi ya nufi dan qaramin fridge din dakin yaciro ruwa ya tuttula a cup yadawo da sauri ya samashi abaki yasha ko tarin zai lafa.
Cikin ikon allah sai tarin ya lafa sai sauke ajiyar zuciya dayake dak
yar idanunshi sun kada sun tara ruwa.
"Sannu Ashraf" inji sadeeq kamar zaiyi kuka
Dagowa yayi a kasalance ya kalleshi batareda yace komaiba yakoma ya jingina da kan gadon.
"Sannu Allah yabaka lfy" yasake cewa cikin tausayawa.
Lumshe idanu kaw
ai ashraf yayi yana sauke ajiyar zuciya
"Meke damunka yanzu?" Inji sadeeq.
Bude kod'add'un idanunshi ashraf yayi ya kalleshi sannan ya dafa saitin zuciyarshi yana dan shafawa
"Za..fi" yafada ahankali cikin muryarshi da baya fita sosai
Kamo ha
nnun daya dafa qirjin dashi sadeeq yayi yana dan murzawa cikin tsananin tausayinshi.
Idan da wani zai ta6a gayamashi abokinshi kuma dan uwanshi zai ta6a fadawa cikin irin wannan halin saboda mace da ya qaryata amma gashi yana gani da idanunshi.
Shi s
haidane, iya zamanshi da rayuwarshi da ashraf yasan komai gamedashi.
Ashraf mutum ne da idan yanason abu yana sonshine da dukkanin zuciyarshi haka zalika idan yaqi abu yana qinshine da dukkannin zuciyarshi ataqaice dai be iya son abu ba, be iya qallafar
abuba haka allah yayishi.
"She... hate..me" ashraf ya katsemashi guntun tunaninshi
"Nima...na... tsani...kaina" yafada yana sake lumshe idanunshi
"No ashraf, please kabar wannan maganar, you're ill"
Bude jajjayen idanun yasakeyi ya kalleshi a
gajiye
"Na cancanci tsanarta, don't I? Kullum saina sata kuka..."
"It ok ashraf, nace kabar magana" sadeeq yasake katseshi
"I want..to die" yafada yana sake murza qirjinshi dake mashi zafi kamar ana hura wuta.
"Ashraf please kabar magana nace,
haba? Kanason..."
Tarinshi ne ya katseshi wanda yasake tasomishi yacigaba dayi babu qaqqautawa wannan karon ruwa be lafarmashi dashi ba.
Hankalin sadeeq yakai qololuwar tashi.
Ganin abun nayine yasashi kiran Dr wanda saida yajeramashi kira biyar
kafin ya daga kasancewar cikin darene don har uku ta gota.
Cikin daren Dr din yafito yazo gidan suka dauki ashraf dayayi matuqar galabaita suka sakashi mota sai hospital.
Dakyar suka samu suka shawo kanshi sai gab da asuba barci ya figeshi sanadiyar
allurar barci da aka sake danna mashi.
Sai a sannan sadeeq yasamu hankalinshi yadan kwanta yaje yayi sallar asuba, gari na ida wayewa yakira baby ya gayamata.
Ringing din wayarshi yadawo dashi daga duniyar tunanin daya lula.
Dauka yayi ya da
ga ganin ummy ke kira.
Gaisheta yafarayi a girmame, saida ta amsa sannan ta fadamashi gasunan hospital din yazo yashigo dasu.
Tashi yayi yafita don shigowa dasu.
A reception ya taddasu tsaitsaye kallo daya yayima baby yasan tasha kuka don fuskarta
ma ta isa ta baka amsa.
Sake gaida ummy yayi sannan yayimasu jagora har zuwa dakin da ashraf ke kwance yana barcinshi peacefully.
Dagudu baby ta qarasa bakin gadon tana toshe bakinta don hana kukanta fitowa tana kallon yadda fuskar yayan nata yayi
so pale.
Ahankali itama ummy ta qaraso dayan gefen gadon tana kallonshi tanajin wani abu na ta6amata zuciya.
Kallon fuskarshi take datayi fayau tana hango dan fadawar dayayi na kwana biyu.
Ahankali tasa hannu tashafi lallausan gashin kanshi cikin
tausayi da qaunarshi.
"Me Dr yace ke damunshi?" Inji ummy batareda ta daina kallonshi ba.
Sadeeq dake gefe tundazu ya sauke ajiyar zuciya yace
"Damuwa... cewa yayi yana stressing din zucuyarshi da damuwa ne" yafada shima yana kallon sleeping ashraf
din.
Kafin wani yasake magana acikinsu kofar dakin ta bude Dr yashigo.
Juyowa sukayi dukkansu suna kallonshi, ganin ummy yasashi qarasowa yana murmushi.
"A'a Hajiya? Yaushe kuka zo?"
Janye hannu tayi daga shafamashi kan datake tana maida mas
hi martanin murmushin nashi tana cewa
"Yanzu wlh... ya aiki?"
"Alhamdullilah Hajiya antashi lfy" yafada cikin girmamawa
"Lfy lau.. ya mai jiki?"
"Alhamdullilah, as you can see tarin ya lafa, yasamu barci, insha allah lokacin da zai tashi everythi
ng will be ok" yafada yana qarasawa wajenshi yana dafa kanshi.
Gwaje gwaje yadanyi mashi sannan ya gyaramashi drip dinshi sannan ya buqaci ummy tabiyoshi office zaiyi magana daita.
Babu musu ta maramashi baya suka fita.
Bayan fitarsu sadeeq ya dag
o ya kalli baby dake gefen ashraf tana matsar qwalla.
"It ok angel... everything will be ok" yafada a tausashe cikin sigar rarrashi.
Dago watery eyes dinta tayi ta kalleshi sannan ta saddasu tana saka bayan hannunta tana share hawayenta.
"Ha
jiya gaskiya damuwace tayima danki yawa, dagani wani abune yasa aranshi har yake neman illata mashi zuciya don sosai yake stressing din zuciyar... yakamata a kula please, seems he have a tender heart wanda abu kadan zai illatata if care is not taken, yanzu
munsamu komai yadawo normal, munmashi allurar barci kuma munasaka ran lokacinda zai farka zaiji sauqi zamu riqeshi a hospital mucigaba da kula dashi harya warware gabadaya insha allah"
Ajiyar zuciya ummy daketa sauraronshi tundazu tayi sannan tace
"
To Dr mungode qwarai"
"Yanzu yakamata asamarmashi abinda zai dan ci idan yatashi don zai buqaci hakan and please aguji 6atamashi rai hajiya, adinga kwantarmashi da hankali yadda zamu samu ya ida warkewa sumul"
"Insha allah doctor" inji ummy tana kada
kai.
Dakin suka sake komawa inda suka tadda su sadeeq kamar yadda suka barsu saidai yanzu zaune baby take kan wata plastic chair kuma tabar hawayen.
Umarni ummy taba baby kan taje su hadamashi break su kawo nan ta fadama sadeeq shima yaje gida ya
huta hakanan ita zata zauna dashi.
Da to duk suka amsa suka fita inda sadeeq yawuce da baby gida.
Jawo kujera ummy tayi ta zauna kusada gadon tana kallon dan nata abubbuwa namata yawo a zuciya tana tuhumar kanta na tsauraramashi.
Tasan yadda Ashra
f ke taka tsantsan da gudun 6acin