Showing 3001 words to 6000 words out of 172372 words
zuba a kamfanin? Kashi ba wasu qadarori nataraba, zan shiga chakwakiya ba kadan ba"
"Kabar fadin haka dad, insha Allah hakanma bazai faruba. Kaidai ka dage da a
ddu'a insha Allah komai zai warware cikin sauqi" tace cikin sigar lallashi.
"Allah ya yarda shalele, kidai dinga tayani addu'a"
"Insha Allah"
"So ya bakery, Mrs chef?" Yafada cikin sigar tsokana
"Kai dad, bakery alhamdulilah, komai na tafiya da
idai..."
Nan tashiga bashi lbrin yadda bakery din, ahaka har suka gama cin abincin, sannan sukayima juna saida safe kowa yawuce makwancinshi.
Tuesday was uneventful a 6angaren Dad, while Saudart a 6angarenta yauma she's busy, bata samu kant
aba saida yamma liqis.
Haka takoma gida tasamu Dad dinta cikin tarradadin yadda gobe zata kasance.
Kamar koda yaushe kwantar masa da hankali taitayi har saida ta tabbatar hankalinshi yadan kwanta, haka ta raya Rabin Daren tana yimashi addu'ar samun n
asara.
WEDNESDAY
Dayake yau haduwar marecene sa6anin na ranan, yau Saudart kadai tafita dasafe, saida ta tabbatar yaci abinci kuma ta qara kwantar mishi da hankali sannan tafice bakery dinta.
**************************************
"Wannan kwalailaita ko mace sai haka, please Ashraf kayi da jiki mutafi, Wai halan Baka duba time ne?" Inji sadeeq cikin qosawa.
Ko nuna alamun yajishi beyiba bare ya tanka.
"Ni wlh narasa gane kanka, kaida bakada Africa time Amma akan wannan mutumi
n kazama wani.."
"Ohhhh! Please sadeeq
🙏
Wai kai bakinka baya zugine sbd surutu? Dan Allah free me, Dan Allah" ya fada kamar zaiyi kuka.
"Oh nine.."
"Dalla shut up mallam, nace shut up, mgnarce bana so, zaka samun headache, idan bazai iya jiraba t
hen off he go, bani nakawoshiba so bazan hanashi tafiya haka zalika bazai hanani harkan gabana ba, idan ka takuramin sai in Daga appointment din zuwa next month, try me and see" yafada daringly.
Daga hannaye sama sadeeq yayi alamun surrender sannan yaju
ya yacigaba da kallon t.v sbd yasan qaramin aikinshine ya aikata abinda yace din.
Saida yaqara wasting kusan 30mins sannan yagama shirya wa, izuwa yanzu qiris yarage sadeeq yafashe don haushi.
"Shall we?" Inji Ashraf yana gyara necktie dinshi.
Ban
za yayi dashi saima tashin dayayi fuuu yawuce waje.
Ta6e baki Ashraf yayi sannan shima yabishi abaya.
Mota daya suka shiga da sadeeq dayan kuma bodyguards dinsune aciki suka cilla kan kwalta.
**************************************
"Sir munyi nazari akan buqatar ka, kuma mun yarda zamu Baka adadin daka buqata ko fin haka, Saidai da sharadi Bamusan idan ka amince" inji sadeeq
Murnar Alhaji taso komawa ciki, kallon sadeeq yayi sannan ya maida kallonshi kan Ashraf dake faman jujjuya
wa kan kujera idanunshi lumshe.
"Inaji, wane sharadi kenan?" Inji Alhajin
"Bansan yadda zaka dauki zancennan ba but believe me, it's just business, bamuda wata manufa akan hakan, zamu Baka loan na 30 million Naira ko fin hakan na shekara daya za
ka maidosu ciff babu d'ori babu ragi Saidai kamar yadda kasani bakada abinda zamuyi holding akan idan Baka biyamuba zamu fanshe ta wajen, koba hakaba?"
"Hakane" inji Alhaji
"Shine mukayi shawara why not muyi haka, muyi trade by barter, mubaka kudin k
aikuma kabamu wani abun dazamu riqe harsaika maido kudin sannan mubaka" yafada cikin nutsuwa.
"Me kenan?" Alhaji ya tambaya cikin rashin fahimta.
Kallon Ashraf sadeeq yayi Wanda haryanzu yana jujjuyawane akan kujera sannan ya maido dubanshi ga Alha
jin.
"Diyarka" ya bashi amsa ataqaice.
"Diyata?" Ya tambaya cikin rashin fahimta.
"Eh ina nufin kabamu diyarka saimu Baka kudin.."
"Wait, nufinku inbaku diyata sbd kudi? Ko nufinku son kudi zaisa in lallata rayuwar 'yata? This is unbelievable!"
Alhaji ya katseshi cikin tsananin mammaki.
"Calm down Alhaji, ba nufina kenanba, you misunderstand us, abinda nake nufi shine zakaba Sir Ashraf auren diyarka bisa yarjejeniyar daka biyashi kudin shi zai sakoma ita, babu abinda zai shiga tsakaninsu, kaw
ai sunan an daura aurene, zai Baka bashin har zuwa 50million idan kana so, all you'll do is sign a contract with him, Amma fa bawai tilas bane, Mr shamsu remember kanada option, this is just...Business" yaqarashe zancen yana mai stressing din business din.
Shiru Alhaji yayi don kanshi yayi mugun kullewa, contract? Aure? AUREN KWANGILA fa kenan? To meye ribarsu? Shikuma meye ribarshi? Tambayoyin daketa mashi kara kaina akai kenan.
"Alhaji kayi shiru" inji sadeeq dake kallonshi.
Dagowa yayi yana ka
llon Ashraf, yes he's handsome, damn hot! Irin namijin da kowacce mace zataso samu a matsayin miji, ga kuma uwa uba kudi, he's damn rich, zaici riba idan Ashraf yazama sirikinshi koda na kwana dayane, gaggarumin riba kuwa, Amma shi Ashraf din meye ribarshi
idan yayi hakan? Dolene yanada manufarshi nayin haka, meye manufarshi to?
"I'll take your silence as NO" Inji sadeeq.
"No, bawai nayi rejecting bane, Saidai shi meye ribarshi idan yayi hakan? Nasan akwai wata manufa akai" inji Alhaji shamsu.
"Goo
d. Kayi tunani mai kyau, dolene yanada manufa, eh yanada ita, as you can see, Ashraf matashine mai ji da kudi da kyau, he's clocking 28 yrs wata mai zuwa, iyayenshi sun tasoshi gaba da mgnr aure har suka bashi wasu adadi lokuta na idan be kawo mataba zasu
hanashi da wadda sukeso, shikuma wacce yakeso na schooling ne, sai nanda shekaru 2 zata gama, so shine daya bincika yaga kanada 'ya yaga why not ya aureta, AUREN KWANGILA, Inyaso daka biyashi saiya saketa at that time kuma yarinyar dayakeso is over sai kaw
ai ya aureta, this is just a CONTRACT MARRIAGE, kamar yadda nafadama babu abinda zai shiga tsakaninsu, yadda ka kawota haka zaka amsheta"
Shiru Alhaji shamsu yayi yana sauraronshi, yana kuma hada kalmominshi yana rarrabawa, abunka da businessman harya
fara
hango hanyoyin samun ribarshi na sosai ma, yes akwai riba, huge riba, babba ma kuwa.
"Kai muke sauraro, ka amincene? Koko musami wani?" Inji sadeeq.
Qara kallon Ashraf yayi Wanda a wannan karon shima shi yake kallo yana jiran amsarshi, nima nay
i kasaqe da Biro a hannu ina jiran amsarshi.
Bakajin komai a office din sai qarar A.C
Sauke ajiyar zuciya yayi sannan ahankali ya bude baki yace......
✍
Ummin fasihu ce
🧚
♀
🤵🏻👰🏻
AUREN KWANGILA
👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka
yayemana wannan cuta (covid19)
🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu karka barmu da kanmu
🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
006
Sauke ajiyar zuciya yayi sannan ahankali ya bude baki yace
"Idan nace kubani lokaci in
yi tunani fa?"
Wannan karon Ashraf yayi magana cikin husky cool voice dinshi
"You can have your time to think, is not as if tilastama akeyi, wannan deal ne kawai Wanda bazai yiwuba sai duka 6angarorin sun amince kuma sunyi sign, ni, kai sai daughtern k
a, kanada ikon janyewa it's your right, Saidai remember millions of people are outside waiting for opportunity irin
wannan, idan beyimaba karka ji kunyar fada. Am good with any of your answer" ya qarashe zancen yana qara balancing a kujerarshi.
Ajiyar z
uciya Alhaji yayi.
'Thank God. At least fargabana na aurama diyata kurma ya kau' yafada cikin zuciyarshi.
"Babu matsala insha Allah, kawai dai kubani time inyi tunani"
"Zuwa yaushe?" Inji sadeeq
"Nan da Monday insha Allah"
"To Allah yakaimu"
"Amin thanks, I'll get going"
"Alright mungode sir"
"You're welcome" yafada yana miqewa tsaye tareda miqama sadeeq hannu sukayi musabaha sannan ya d'an sack kallon Ashraf sannan yafice.
Kallon juna Ashraf da Sadeeq sukayi Bayan sun rakashi d
a idanu.
"Did you think the jerk will accept?" Inji Ashraf cikin yamutsa fuska.
"Ina jiyo qamshin nasara dai, he won't afford to loose this opportunity, besides wazai the whole SIR ASHRAF?"
Murmushin gefen baki yayi yana sake balancing a kujerar.
"It better be" yafada yana shafa sajenshi ahankali murmushin still a fuskarshi.
****************************************
Tuqi yake Amma kwata kwata hankalinshi na wani wajen.
AUREN KWANGILA? Contract marriage? Da familyn A.A? diyata
tazama daya Daga cikin familyn A.A?
Wow! What an incredible opportunity! Ni? In-law din A.A family?
As for me banda problem but Saudart...
Shiru yayi yana tuna aqidar Saudart na tsanar mutuwar aure, koyaya taji aure yamutu saita shiga damuwa da 6ac
in rai, musanmman idan antara iyalai.
Tashin datayi cikin broken family yasa ta tsani mutuwar aure, lokaci da dama takan gayamishi ra'ayinta na son yin auren MUTU-KA-RABA, Akoda yaushe maganarta baya wuce
"Dad katayani da addu'a Allah yabani miji na ga
ri, ko bashi da kyau bashida arziqi ya kasance mai kyan hali, Wanda zamu Gina ingantacciyar zuri'a nan gaba, Wanda zamu hadu muba 'ya'yanmu tarbiyya, Wanda mutuwace kawai zata rabamu"
Wani sa'in ya kan tsokaneta da marar kunya tana fadamashi irin wannan
mgnan a matsayinshi na mahaifinta.
Takan yi dariya lokuta da Dama tana rufe fuska sannan tace "Dad, ai gaskiyane, Aure wajibine ga dukkan musulmi Duk cikarka bazaka ta6a zama cikkake mai darajaba saikayi aure, name zanji kunya Bayan nasan koba dade koba
jima saina yi auren?
Hakan daya tuno ba qaramin tada mashi hankali yayiba.
Me zaice mata? Zan hadaki AUREN KWANGILA da A.A sbd farfadowar company na? Impossible!
Bazai iya kiyasta tashin hankalin fasata shigaba idan taji hakan, aure? Na Wanda bata
saniba kuma bata ta6a ganiba? Kuma qarin gishiri a ciwo Aure na taqaittacen lokaci? Kai da kamar wuya.
Haka yaita tunane tunanenshi harya iso gida jikinshi yayi matuqar la'asar.
Shidai abinda yasani no matter what, bazai bar wannan damar ta wuceshiba
.
WAIWAYE (Adon tafiya
🕴
)
Manage please
🙏
Ummin fasihu ce
🤵🏻👰🏻
AUREN KWANGILA
👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan cuta (covid19)
🤲
Ya Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu
🤲
Story wri
tten by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
007
WAIWAYE (Adon tafiya
🕴
)
Alhaji shamsu d'ane tilo ga Mallam yahya.
Su yan asalin garin kanjiyane dake jahar katsina.
Tun yana Dan shekara shida mahaifinshi yakaishi cikin birnin
katsina almajiranci.
A makaranta wani babban malami wato mallam Ballo.
Haka suke rayuwa a wannan makarantar Wanda yawanci abincin dazasuci sai sunje bara suke samu, wani sa'in idan basu samuba haka suke haqura su kwanta kasancewar iyayensu basu wani ha
d'osu da abincin kirkiba, gashi shima malamin ta kanshi yake don bazai iya daukar nauyinsuba kasancewar shima bamai wani hali bane ga d'aliban dayawa.
Haka rayuwa ta kasance basa komawa qauyensu saiga damina don taimakawa iyayen da noma, da kaka tayi sa
i asake turosu da guzurin dabe taka kara ya karyaba.
Rayuwa suke irin na sakakku wadanda babu mai tsawata Masu sai malaminsu shima a lokacin karatu, wani sa'in karatun ma ba dauka sukeyiba saboda ai sai ciki ya dauka sannan za'a maganar karatu, wani sa'
in saisun yi aikatau sannan zasu sami abinci.
Haka rayuwarsu ta kasance wani sa'in tufafin dazasu sa sai sunyi bara suke samu shima dakyar, wasu kau Kayan jikinsu sbd
tsabar datti ko zanen Kayan ba'a gani, wasu kuma kaya sun 6e66ere Masu ajiki Amma babu
halin dinkawa.
Acikin wannan rayuwar wasu suke kauce hanya su fada munanan hali batareda an ankaraba tunda babu Masu sanyamusu ido, sai aga ba'a samo karatunba kuma 'ya'ya sun kangare sun gaggari al'umma.
Shamsu shi Allah ya tsareshi da fadawa irin
wadanan halin Saidai yataso da kwadayin abin duniya, kudi ko ta hanyar haram ne yanabi yasamesu, gashi da tarin karatu Saidai be amfaneshiba.
Duk buga bugan dazaiyi yasamu kudi saiyayi don a tunaninshi kudi shine komai, idan kanada kudi to kowama kana i
ya takawa.
Tun yana komawa kauyensu Duk damina don taya babbanshi noma har ya daina.
Alokacin dakowa ke komawa kauye sai shi yashige cikin gari yana buga buganshi na Neman kudi, wani sa'in ya kwana a tasha wani sa'in a massalaci.
Babu yadda babans
hi beyi dashiba don ya dinga leqosu koda sau dayane a shekara Amma firr yaqi, don aganinshi baya iya zaman kauye kuma, yasaba da riqe kudi da cin Abu mai maski mezeje yi kauye?
Abun ba qaramin damun mallam Yahya yayiba gashi shine d'a talin qwal nashi.
Haka ya haqura yazuba mashi idanu don yariga ya kangare bawai maganar kowa yakejiba.
Shamsu likafa taji gaba, Tun yana buga buganshi a katsina harya koma kano jin can anfi kasuwanci kuma anfi samun kudi.
Wani babban shago yasamu aiki na yaron shag
o inda ake siyarda Cosmetics Kala kala.
Sosai yake samun kudi don shagon shahararene kuma mai shagon na sallama mai tsoka.
Dayake Shamsu Allah yayimashi farin jinin mutane, cikin d'an qanqanin lokaci yasan kwastamomi dayawa, kusan kowa yasanshi sabod
a barkwancishi da iya mu'amala.
Ahankali ahankali yafara yiwa ubangidan nashi cuwa, yana mashi rinto, wani sa'in idan aka aikashi saro kaya saiya Dora nashi Asama kokuma wurin Saidawa ya qara akai.
Dayake uban gidan nashi ya yarda dashi kuma becika s
a ido sosaiba, beyi saurin ganewaba, saida yayi mashi mummunar
6anna, sbd Duk kusan customers dinshi sunbar zuwa sbd yadda kayanshi suke tsada.
Ataqaice dai shago yarushe babu riba kullum sai faduwa, Daga qarshe Saidai ya sallami yaran shagon gabadaya y
arufe shagon sbd rashin jari.
Shamsu daketa Tara kudaden dayake samu wajen rintonshi, yasamu wani qaramin shago cikin kasuwar yabude shima yazuba irin Kayan da oganshi ke Saidawa ada.
Ahankali ahankali, kasuwancinshi yadinga ha66aka, Allah yasa mashi
albarka a kasuwancinshi.
Abu qarami yakoma babba Tun yana sari garuruwa harya fara fita qasashen waje.
Cikin shekara biyar ya bude wani qaton company mai suna A.S GALLERY
Duk abinda akeso na Kayan alatu yana Saidawa. Company nashi yazama shaharar
e Wanda ake tutiya dashi garin kano.
Wata shekara yadai runtse ido yayi aikin hajji shima sbd matsa mishi da abokan kasuwancinshi kemashi na yaqi aikin hajji.
Haka dukiyar Alhaji shamsu yacigaba da bunqasa Wanda Duk yawanci na ha'incine don sosai ya
kware wajen ha'intar mutane.
Saidai abinka ga Dan kauye, Duk tarin dukiyarshi beta6a marmarin sayan kadaroriba sbd gaba kokuma yabude reshe awani wajen, Shidai Duk abinda yasamu ya narkawa company dinshi.
Ana haka rasuwar mallam yahya ta riskeshi,
sosai ya girgiza don rabonshi da kankiya harya manta, yana dai yimusu aike bakin gwargwado.
Ba shiri yanufi qauyen, yayi kuka sosai jin baban nashi yadade kwance ba lfy, haka yaita Neman gafarar inno (mahaifiyarshi) harta yafe mashi.
Bayan Arba'in ya
tarkata inno sai kanon dabo don acewarshi bazai iya cigaba da zama a kauyeba.
Shekara daya da rasuwar mallam inno ma tabishi, babu laifi mutuwar ta girgizashi na Dan lokaci sannan yacigaba da rayuwarshi.
Yana Dan shekara 32 yayi aure ya auri wata sh
uwa Arab Wanda suka hadu da ita awata tafiya dayayi Maiduguri.
Mace mai kyau, hankali da tarbiyya.
Bayan shekara ta sulu6o Masu da kyakyawar baby mai kammaninta sak masha Allah.
Saidai Tun Daga sannan suka fara samun sa6ani dashi a dalilin sata da
yayi Wai tacire mahaifarta beson haihuwa diya daya ta isheshi.
Wai 'ya'ya babu abinda suke jawowa sai talauci.
Itakau firr taqiya Wanda hakan yaja mummunan sa6ani tsakaninsu Wanda Daga qarshe suka rabu da Abu yaqi dadi.
SAUDART Nada shekara biyar Al
haji shamsu ya amsota sbd yaji mahaifiyarta zatayi aure acewarshi 'yarshi baza taje wani gida agolanciba.
Saida aka kai ruwa rana sannan suka bashi ita da sharadin sai ta dinga zuwa Duk sati suna ganinta kuma yasata both islamiya da boko.
Soyayya sos
ai Alhaji shamsu ke nunama Saudart, wata irin shaquwa ke tsakaninsu na qin qarawa don sunfi shaquwa dashi bisaga mamanta.
Ya sakata both islamiyar da boko, Duk wani gata da diya zata samu wajen iyayenta tana samu don Saudart tadauko dukan halin iyayenta
.
Kyaun fuska da hali na mamanta sai farinjini da siye zuciya irinna bbanta.
Tun tana yar shekara sha biyar tasauke Al qur'ani mai girma, a fannin boko kau tanada kwalin degree a fannin economics.
Saudart Tun tana yarinya ta tsani mutuwar aure, don
shine silan rabuwanta da daya Daga iyayenta.
Tsanar yaqara karfine dataji a islamiya malaminsu ya gayamusu babu abinda Allah ya tsana kamar mutuwar aure don har sama girgiza take.
Tin alokacin take addu'ar Allah yabata miji nagari Wanda mutuwa kadai
zata rabasu.
Tana gama degree dinta ta matsama daddynta ya bude mata bakery, sbd tsananin son datakema girki, da farko yaqi yarda don yafison tayi aikin office Amma data matsamashi dole yabude mata Wanda nan da nan Allah yasamata albarka a harkar har ta
yi fice a garin, babu Wanda beson ALHAIRI BAKERY ba.
Ana haka wannan cuta (covid19) tashigo duniya harta 6illa Nigeria Wanda hakan baqaramin rushe tattalin arziqin qasa
yayi, cikin wadanda abun yashafa harda Alhaji shamsu don komai ya karye sakamakon
rufe border da akayi.
Ga tarin basussukan da ake binshi na banki haka yasa dole yanemi taimakon shahararen kamfanin nan na A.A ENTERPRISES.
Saiga kuma yadda abun ya kasance...
✍
Sorry babu dai editing
🙏
Ummin fasihu ce
🧚
♀
🤵🏻👰🏻
AUREN K
WANGILA
👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Allah ka yayemana wannan cutar (covid19)
🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu
🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
008
Cigaban labari
📖
Yau
Saudart tafi zama busy saboda ita dakanta ke tsara cake din bikin Sir Wilson, abubuwa take cikin qwarewa while wasu tsirarun ma'aikata na gefe suna qara daukar kwas.
Aiki take Amma hankalinta na wajen daddynta.
Tun dazu take jiran kiranshi Amma shir
u, Allah Allah take ta ida ta dawo gida, abindama yaja delay rashin samun kalar colouring dasukeso dawuri da tuni angama an hada da kingin snacks da akayi delivering dazu.
6:30pm ta kammala cake din, sai tashin wow! Wow!! Kakeji a dakin kamar jiniyar
motar ambulance sbd haduwar cake din.
"Wow ma'am! This is the best cake I've ever set eyes on" inji wani mai suna Farouq yana tafawa.
Nan kowa yabi sahu sunata tafa mata.
Yar dariya tayi sannan tad'an dramatically tana cewa "thank you, thank you".
Ba ita tabar bakeryn ba sai 7:00pm Duk hankalinta yayi gida.
'Meyasa dad be kiraniba? I hope all is well' tafada acikin zuciya.
Da sallama tashiga parlourn, can ta hango daddy a dining yana sipping din coffee.
Dadi taji ganinshi cikin ni
shadi babu damuwar komai.
Amsamata sallamar yayi cikin fara'a saikuma yasha mur yana kai dubanshi ga wall clock.
Dan Waro idanu tayi tana Dan dariya ciki ciki yayinda