Showing 159001 words to 162000 words out of 172372 words

Chapter 54 - AUREN KWANGILA BOOK1 COMPLETE

hakane gwara suzo Susan inda dare yayi masu, bata iyawa

J

in qauri ya turnuke kitchen din yasata saurin tashi ta kashe gas cooker din tana bude tukunyar dake akai

Ganin abin ciki yafara kamu yasata jan tsaki ta dauko wurin kwashewa ta kwashe tana ayyana dolene ma suzo su kama gabansu bazasu maidata uwar banza

ba

Tana cikin jiqa tukunyar datayi kamun a sink taji motsi abakin kofa

Waigowa tayi suka hada ido da ashraf da saika rantse da Allah ba shi ta kamaba ya saka Yar mutane a corner don yawani maze kamar babu abinda yafaru

Dauke kai tayi tacigaba da a

binda take

Qarasowa ciki yana cewa

"Ummy yau ke ke breakfast din? Ina maid din?"

Bata ko dagoba tace

"Na aiketa" a gajarce

"Ayyah nashiga dakine naga ban gankiba shine nace bari nazonan Ashe kina ciki ma"

"Hmm" kawai tace don ita bawai son f

irar takeba ita in so samune ma yatafi yabata wuri

"Ummy to nidai zan wuce office munada aiyuka masu yawa baxan iya tsayawa yin break ba, nayi a office"

Cikin zuciyarta tace

"Jikayi nace katsaya dama?"

Amma a zahiri tace

"To Allah ya tsare, take

care" batareda ta juyoba

Da amin ya amsa yafice yana mammakin wannan tsare gidan na ummy, watsar da tunanin yayi tinawa dayayi aidama haks take yan kwanakin nan dukdan saudart amma yasan maganinta Ai idan tasan wata Ai batasan wataba

Koda yafita s

aida ta jima sosai a kitchen din kafin tafito tayi shahadar komawa saman

Kamar yadda tazata bata taddataba dakin hakan yasa ta maido dakinta ta rufe tana sauke Ajiyar zuciya

Bin dakin tayi da kallo taganshi tsab tsab. Kada kanta tayi ta wuce toilet t

ana ayyana dolene ma su tattara subarmata gida

😆

A bangaren saudart tana samu ashraf yafita tayi sauri ta ida gyara dakin, batajin tana iya hada ido da ummy dukda batasan meya faruba amma gani take data kalleta zata gano abinda yafaru, hakan yasa ta

na gamawa ta lalla6a tabar dakin takoma na baby

Ummy kau maid dinsu takira akan taje tasamu saudart dakinsu tayimata maganar breakfast don ahalin yanzu batajin zata iya facing dinta

Saudart kau bata kawo komai aranta ba ta sauka tayi break dinta abub

buwan dasuka faru dazun naqara dawomata a qwanya, dolene tadan ja dabaya da ashraf idan ba hakaba watarana kunya za'aji, yanzu ace dazu ummy tashigo ta gansu ahakan ina zatasa kanta? Dolene ta takamashi birki tunda taga kamar kunya be isheshiba (ruwa kike

yarinya

😒

)

Yinin ranar ummy bata fitoba bare su hade, gwara gwara ma da baby tadawo sun shigo tareda saudart dakinta akan lunch sai cemasu tayi suje suci kawai she's busy

Ba wanda yakawo komai aranshi suka fita don zuwa suci, baby na bata labarin yad

da exam din yau yayi zafi.

***

Zaune take a dakinta tana dudduba wasu kaya da za'a kawomata sari daga China aka bubbugo kofa

Saida tadanyi jimm sannan tabada izinin shigowa

Ashraf ne yashigo cikin shigarshi ta jallabiya ash colour da alama da

ga massallaci yake don dama ba'a dade da idarda isha'i ba

Kallo daya tayimashi ta dauke kai tana amsa sallamarshi

Qarasowa yayi ciki ya zauna qasa kusada qaffafunta yadora kanshi à cinyarta

Saurin ture kanshi tayi afusace tana cewa

"Meye haka?"

Shagwa6a fuska yayi kamar zaiyi kuka yace

"Kai ummy"

Tsaki taja tacigaba da abinda take

Kumbura fuska yayi yana hura hanci wai nan yayi fushi besan dama ciki take dashi ba

Tsaki tasake ja ta dago daga abinda take tace

"Kana jina? Jibi ka dauke

matarka kabarmin gidana na gaji da ganinku fatan kajini dakyau? Jibi jibin nan kaji na gayamaka, tom" tafada tanajan kunnenta daya alamun yajita dakyau sannan tayi kwafa tacigaba da abinda take

Wara idanu ashraf yayi cikin tsagwaron mammakin kalamanta

"Ummy jibi?"

Cikeda masifa ta zaburomashi tace

"Eh jibin! Dan wlh karma ka kuskura kuwuce..."

Kasa ida maganar tayi jin ya qanqameta yana ihun murna

"Kai ummy amma Allah ya tsundumaki a aljannar fiddausi, insha Allah ga kofar gidanki gana anna

bi (s.a.w), Allah ya baki duk abinda kikeso, Allah ya hadaki kema da Abba a aljanna"

Wani dundu takai mashi abaya tana tureshi ajikinta

"Dan gidanku zoka fitarmin a daki, marar kunyar banza kawai"

Dariya yake yana Sosa baya inda tazuba mashi qulli

yace

"Babu komai ummy, dukda haka Allah ya saka da alhairi ya kuma farantamaki yadda kika faranta Mani"

Pillow din gefenta ta dauka ta jefeshi dashi tana cewa

"Bazaka fitaba nace?"

Saurin ficewa yayi yana Dariya harda dafe ciki

Kwafa ummy tayi t

ana kada kai, can kuma tayi murmushi tana girgiza kai tana fadin Allah ya shirya

Shikau qasa ya sauka yana cigaba da kaka6a dariyarshi don har kwarewa yake tsabar Dariya

Aqasa suka hade da saudart datayo hanyar sama itada da baby

Tsayawa sukayi

kallon ikon Allah ganin yadda yake dariyar kamar sabon kamu

Ganin saudart yasa ya tattakura ya fashe dawata dariyar yana nunata yana tafi

Sororo sukayi suna kallonshi suka kalli juna sannan suka qara maida kallonsu kanshi

Dakyar ya iya hadiye dari

yarshi yace

"Congrat *MRS ASHRAF AUWAL*" saikuma yaqara fashewa da Dariya yana tafi yawucesu yana cewa

"Well play momma, well play"

Daga saudart har baby binshi da kallo sukayi baki bude har saida yafice daga falon sai a sannan suka kalli juna

Fa

shewa da wata mahaukaciyar Dariya baby tayi harda rintse idanu

Sororo saudart take kallonta itama tanajin gabanta na dan faduwa, kodai sun haukace ne?

Qarfin halin cewa

"Kekuma lafiya?" Tayi tana danja baya kartaji saukar bugu

Qara kecewa da Dari

ya baby tayi kafin tace

"Wlh mijinki ya haukace, Allah ya zare, shikenan Yaya ya zare"

Takuma fashewa dawata dariyar tanayin sama dagudu

Binta da kallo saudart tayi adan tsorace zuciyarta na ayyana mata kodai dagaske basuda lafiyar ne?

Ita bataga

abin Dariya ba anan, shi ya sauko yana Dariya marar dalili itakuma tana Dariya wai ya haukace, idanma haukacewar yayi aiba Dariya ya kamaceta ba, kuka ya kamaceta.

Ta jima atsaye tana jujjuya abin aranta sannan ta fara hawan saman jiki a sanyaye

Asa

ma kau dakin ummy baby tafada tana cigaba da dariyarta mai kamada ta mahaukata

Kafin ummy ta dago harta fado Kanta tana cigaba da dariyarta

Tureta ummy tayi tana cewa

"Lafiyar ki lau kuwa?"

Cikin Dariya baby tace

"Wlh ummy yanzu muka hadu da yay

a qasa yana gagga6a Dariya kamar sabon kamu, wlh harda tafi" takuma fashewa dawata dariyar

Wani dogon tsaki ummy taja bayan tagama binta da kallon takaici

Kofa ta nunamata tana cewa get out

Ba musu ta tashi tafita tana cigaba da dariyarta

Sa

udart na zaune a dosane gefen gado tana tunane tunane tajiyo dariyar baby na tunkaro dakin

Saurin dago Kai tayi tana kallon kofar.

Shigowa tayi tana cigaba da dariyarta saidai yanzu tadan rage saboda cikinta daya fara amsawa

Bata ko kalli saudart

ba ta fada kan gado tana qara dafe cikinta daya fara mata ciwo Dom Dariya

Itadai saudart na zaune tana kallon ikon Allah tana ayyana duk yadda akai baby bata rasa ingilmu akanta

Saida ta huta sannan ta tashi ta wuce toilet saudart tabita da kallo

Bata dade ba tafito daure da towel da alamu wanka tayi

Kallon saudart datayi zugum tana kallonta tayi tace

"Aunty ke ba yanzu zakiyi wankan ba?"

Ajiyar zuciya ta sauke tace

"A'a yanzu zanyi"

Daga haka ta tashi ta wuce itama toilet din tana qara

mammakin abinda yasamesu

Koda tafito har baby tayi barci

Chanza kaya zuwa na barci tayi tazo ta kwanta gefen baby tana kallonta

Saida ta tottofamata addu'o'i sannan itama tayi addu'ar barci ta rintse idanu

Ta dade tana jujjuya abinda yafaru daz

un kafin wani barci mai dadi yazo yayi awon gaba da ita...

✍

️

Ummin fasihu

🧚🏻

‍♀

️

🤵🏻👰🏻

AUREN KWANGILA

🤵🏻👰🏻

(Contract marriage)

Story written by Ashaanty love

💖

100

A bangaren ashraf kau he is super happy, shi bema wani lu

ra da baby ba daya sauko qasa kodayake ga yadda yakeji alokacin koda ya gantan hakan ba zai hanashi bayyana farincikinshi ba.

Yau ummy ta sashi farincikin da be ta6a yiba arayuwarshi, haryanzu ganin abin yake kamar wasa

Koda yashiga dakinshi, saiti y

ayi kamar a wasan tsere ya falfala da gudu yayi wani qundunbala akan gado yana Dariya, jiyake kamar yayi hauka don farinciki.

Harya dauko wayarshi zai kira amininshi saikuma yayi tsaki ya jefar da wayar can gefen gado yakoma ya kwanta rigingine yana qiy

asta yadda zasu shimfida sabuwar rayuwarsu su biyu a matsayin ma'aurata

Ranar dakyar barci yasaceshi can tsakiyar dare wanda ke cikeda da mafarkan saudart

Yau tunda yatashi da asuba be komaba, gari na danyin haske yafice daga gidan ko shiga gaida umm

y beyiba

A bangaren su baby kau yauma da wuri ta shirya don yauma sunada exam na safe saidai dawuri zasu dawo don paper daya garesu

Tare suka shiga gaida ummy wanda ta amsamusu as usual cikin fara'arta ko kadan bata nunama saudart komaiba shiyasa i

tama bata kawo komai araiba

Baby tayimusu sallama ta tafi while saudart tahau gyara dakin ummy kamar yadda tasaba

Sai wajajen 10 tagama gyare gyaren dakunnan nasu sannan ta sauko qasa tayi break tana gamawa ta hayewarta sama don hutawa

1:30pm ba

by tadawo daga school, saida tayi wanka sukayi sallar zuhr sannan suka sauko yin lunch

Anan ne ummy kecewa idan sungama zata basu kudi suje saloon suyi gyaran kai da Kunshi

Zokaga murna wajensu, musanmman saudart da tunda tazo gidan bata sake leqa wa

jeba

Cikin zumudi suka qarashe cin abincin sannan suka haye sama don shiryawa baby sai tsokanar saudart take wai ba sabon ba yau akuyar daure tasamu sake, itadai saudart bata biyemata ba don a qagare take sutafi kafin ummy ta chanza shawara

Wajajen u

ku suka fito cikin shirin su ta kamala don duk hijabai sukasha har qasa, da baby gyale taso sawa amma ganin saudart ta zumbula hijab yasata fasawa itama ta zira tata har qasa

Tare sukaje suka amshi kudin ummy sai yaba kyawun su take sannan sukayi mata s

allama suka fita zuwa parking space inda driver ne zai kaisu.

A wani qayattacen saloon driver ya ajiyesu, koda ganin yanayin wajen kasan na masu dashi ne

Shiga sukayi cikin sa'a kuma ba jira kasancewar yau alhamis ba mutane sosai ba kamar weekend b

a

Cikin dan qanqanin lokaci aka fara musu gyaran kan wanda saida sukayi zaman tsefeshi sannan aka hau gyaran

A taqaice dai basu suka dawo gidaba wajajen six na marece saboda harda qunshi akayi musu duk jaa both kaffafu da hannaye, sosai qunshin ya fi

to a fararen fatarsu gwanin sha'awa

Agajiye suka dawo gidan, saida suka fara biyawa dakin ummy dake zaune robobin fresheners da turaren qamshi kala kala da humrori agabanta tana packaging dinsu

Sosai ta yaba kyawun dasukayi tana santin qunshinsu sa

nnan ta umarcesu suje suyi sallah kasancewar anfara kiraye kiraye alokacin

Saida sukayi har isha'i sannan suka sauko sukaci abinci suka koma saman

A dakin ma hira suka dasa wanda duk baby ce mai surutun itakau saudart dakyar take amsamata don a matuq

ar gajiye take burinta kawai takai kaffadunta qasa kewar ashraf dake maqale a qasan zuciyarta, rabonta dashi tun jiya, duk yau bata sashi a ido ba saidai hakan yamata daidai don yanzu tsoron haduwarsu take don ta lura bashida self control, idan sun hade du

k abinda yazomashi akai yi yake beko la'akari da inda suke

Tunawa tayi da kissing dinshi na jiya hakan yasata jin tsigar jikinta na dan tashi, ganin hakan yasata yakice wannan tunanin a zuciyarta ta maida hankalinta akan baby dake zuba kamar Yar tsanar

da aka sawa battery

Ashraf kau tunda yafita be dawo gidan ba sai wajajen 10, amatuqar gajiye yadawo hakan yasashi wucewa part dinshi kawai

Yana shiga ya rage kayan jikinshi ya kwanta ko minti goma beyiba barci yayi awon gaba dashi

*WASHEGARI*

Juma'atu babbar rana! Yau kowannensu cikin nishadi ya tashi, kowannensu najin farinciki wanda basusan dalilinshi ba kodayake saudart ce za'ace batasan dalilin farincikin ba amma Oga A.A yasan abinda yataka dama

Yauma kamar jiya tunda safe yafita s

aidai sa6anin jiya yau saida yashiga ya gaida ummy kafin yafita dukda bata amsamashi ba da kyau amma hakan be dameshi ba don bayajin ga yadda yakejin kanshi akwai abinda zai 6atamashi mood dinshi

Koda yafita saida yaje ya qarasa settling din aikinshi na

jiya sannan yawuce saloon shima aka dan saisaye Mashi suma dukda bawani yawa gareta ba akaimashi trimming din sajenshi yafito gwanin kyau, sannan akaimashi gyaran farce da filing nails sannan akaimashi foot bath

Bashi yafito daga qayattacen saloon din

maza dinba saida aka kusan shiga sallar Juma'a

Gidanshi yawuce daga nan ya shirya cikin sabbabin shaddarshi Yar gaske mai shegen maiko kalar golden ya kashe hula kamar wani sabon ango yafice massalaci a gaggauce don karya rasa sallar juma'a

A banga

ren saudart kau tunda tashiga gyara dakin ummy, ummy ta riqeta don abinci ma saidai takawomata nan dakin, ga cimmar datake bata taci ayau din na musanmman don duk dangin fruits ne da farfesu da pure madara dasukaji hadi

Wankama kanshi yau ruwa musanmman

tayi amfani dasu wanda yasha hadin turarrukan wanka masu shegen qamshin dadi

To tun anan saudart tafara shan jinin jikinta don ita ba qaramar yarinya bace tasan ko me akebata, kanta ya kulle sosai yayinda zuciyarta tashiga fargabar Allah yasa ba abinda

zuciyarta ke rayamata bane zai faru

Hakan yasa tanemi dan kuzarinta data tashi dashi ta rasa saita koma wata sukuku daita gashi ummy bata bata fuskar tambaya ba kodayake kota bata me zata cemata?

Hakan yasa takoma wata sukuku daita tanayin duk abind

a ummy tasata.

A bangaren ummy kau tana lure da yanayinta amma tayi kamar bata ganiba

Saida tasata tayi wanka tayi sallah sannan ta fiddomata wani jan danqareren lace mai touches din baqi tabata akan tasa

Ba yadda ta iya haka ta amsa tasaka dinkin

riga da skirt sunmata ciff kamar ajikinta aka dinkasu

Ko ita kanta ummy saida tayaba da kyawun datayi don sosai kalar kayan suka fitoda glowing skin dinta

Saida tagama shiryawa sannan ummy ta zaunar daita don suyi magana

Tunda tafara magana sau

dart ta tsinci kanta cikin faduwar gaba

Da nasiha ummy tafara mata, nasiha mai kashe jiki da sage gwiyagu

Tun anan saudart ta sadaqat don ko makaho ya laluba yasan mezai faru

Saida tagama mata nasihar sannan tacemata tazama cikin shiri anjima miji

nta zaizo yatafi da ita

Kasa tsaida hawayenta tayi hakan yasa tabarsu suna digowa kanta aqasa, dukda tasan koba dade koba jima saita koma dakinta hakan besata jin wani iri ba, saida ummy ta rarrasheta sosai ta sassamata albarka sannan tabarta ta sauka q

asa don ida shirye shiryen datake tun safe

Haka saudart takoma ta kwanta zuciyarta namata nauyi

Koda baby tadawo a wannan halin ta sameta, tambayar duniyar nan tayimata amma tayi banza daita don bata tata takeba

Ganin hakan yasa baby maida akalar

tambayarta ga ummy inda ummy ta gayamata yau zasu koma gidansu

Sosai itama baby taji ba dadi don yan kwanakin nan ba qaramin dadinsu tajiba tareda ita saboda tana debemata kewa sosai haka itama tadawo dakin ta zauna kusada ita ta zabga tagumi tanajin

kewarta tunma kafin ta tafi

Haka dai suka qarasa wunin ranar jiki asanyaye

*8:00pm*

Wata sabuwar mota baqa wulik mai sheqi tafara horn a bakin gate din gidan

motar qawace take da decorations masu qyalqyali both gaba da bayan motar

Saida

aka gama scanning din motar sannan gate din ya wangale motar tashigo ciki

Maimakon motar tayi parking space saita wuce har gaban entrance din gidan ta tsaya

Saida aka kusan shafe minti daya da tsayuwar motar sannan aka bude driver seat, nanma said

a aka ja daqiqu 20 sannan aka ziro qafa daya mai sanye da half cover farare tass sannan gangar jikin mammalakin kafar yabiyo

Tsarki ya tabbata ga mahallincin wannan kyakyawar hallitar mai cikeda kwarjini da haiba

Wato fadin haduwar A.A a wannan Daren

6ata bakine don duk yadda zan misaltamuku shi ya wuce nan

Sanye yake cikin baqar shadda yan ubansu wanda akaiwa aiki kalar fari

Dinkin Riga da wando ne na samarin zamani rigar da kadan tawuce cinya

Kanshi sanye da hula fara an wani kasheta a gefe

n kai, hannunshi na dama sanye da tsaddadiyar agogon fata itama fara sai takalmin shi half cover suka farare

Sosai yabada kala cikin shigarshi ta black and White ga wani daddaden qamshi dake fita daga jikinshi

Maida kofar yayi yarufe sannan ya za

gayo yanufi kofa fuskarshi na fitar da annuri irinna angwaye

Knocking yayi a kofar falo yasa hannu ya murda handle din kofar batareda ya tsaya jiran isoba

Tura kofar yayi yashiga da sallama.

Babu kowa a falon sai t.v daketa haukanta ita kadai

Hakan yasashi nufar sama direct cikin takunsa na qasaita

Suna zazzaune ummy na ida packing din kayyakin da tasaimata dangin kayan qamshi itakuma baby na yima saudart simple makeup wanda dakyar tasamu ta yarda ayimata

Knocking din kofar da akayi ya

sasu danyin Jim da baby da ummy yayinda zuciyar saudart tabada damm har saida tadan dafe saitin zuciyar

"Baby get the door" inji ummy jin ansake kwankwasawa

Ida shafamata janbakin tayi sannan ta ajiye ta nufi kofar da sauri yayinda saudart taja lif

ayar dake nade ajikinta ta rufe fuskarta

Harzai qara knocking sai yaji alamun za'a bude kofar hakan yasashi fasawa ya zubawa kofar ido

Cak baby ta tsaya tana kallonshi from head to toe baki sake ganin yayan nata ya wani transforming kamar bashi ba

Harara ya gallamata ganin yadda tawani bake hanyar ita bata barshi yashiga ba sai kallon datake binshi dashi kamar yau tafara ganinshi

"Jira kike inyi ball dake sannan?" Yafada yana harararta

Sai a sannan ta wara idanu tace

"Kai yaya! You look so

o takeaway

👌

" tafada cikin murna

Dan yatsine fuska yayi sannan yace

"I know"

Ganin yanufota yasata saurin komawa baya ta ra6e gefe yashige

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login