Showing 108001 words to 111000 words out of 172372 words
ranta, koyaya ra chanza fuska saiya shiga taitayinshi.
Irin wadannan yaran ne da suke tsoron 6acin ran iyayensu ko yayane, basu qaunar suga 6acin rai a tattare dasu komai qanqantarshi.
Wataqila she's so harsh on him,
wataqila ta tsauraramashi dayawa.
Amma kuma ko menene tayimashi shi yaja, tasan yanada kwakwarar hujja na daukar fansa kan Alhaji shamsu saidai bataga hujjarshi na hadawa da innocent diyarshi ba.
Bataga dalilin dayasa zai jata a abinda batada masani
ya akai ba, ya lallatamata rayuwa da wani banzan dalili nashi.
Ta tausayawa halin daya shiga amma hakan bazaisa taso kanta dayawa ba, bazata ta6a bari sucigaba da zaman cutarwa ba, bazata tilastawa saudart zama dashiba koda kuwa hakan na nufin zai wahal
a fiyeda haka.
Tasan yafara sonta, tun a reaction dinshi sanda ta nemi ya kawomata takardarta.
Tasan be iya son abuba kuma yana matuqar wahala idan ya kwallafama abu rai besamu ba.
Saidai hakan vazai sa taso kanta ba ta tauye haqqin diyar wasu.
Yadda takejin son nata dan da tausayinshi haka suma iyayen nata sukeji koma fiyeda hakan.
Ajiyar zuciya tasake saukewa tana qara kallon face din ashraf zuciyarta na saqa da warwara....
✍
Manage
🙏
Ummin fasihu ce
🧚🏻
♀
️
🤵🏻👰🏻
AUREN KWANGIL
A
🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Story written by Ashaanty love
💖
(Ummin fasihu)
072
Ahankali yafara bude idanunshi dayaji sun qaramashi extra nauyi.
Dishi dishi yafara gani dafarko sannan yafara ganin clearly.
Bin dakin y
ashiga yi da kallo yanason gane a ina yake.
Idanunsu suka sarke dana Ummy dake kallonshi shima.
Gabanshi ne yafadi wanda hakan yasashi yunkurin tashi da sauri.
Saurin tashi ummy tayi itama tana dafashi.
"Easy, kabi sannu you're still weak" tafa
da cikin kulawa tana jingina mashi pillow abaya don ya jingina.
Ahankali ya jingina da pillon yana bin ummy da kallo kamar yanason tabbatarwa kanshi ita dince.
"Ya jikin?" Tafada softly
Gyada kai kawai yayi yana kallonta
Shafa kanshi tayi tana
dan murmushi
"Allah ya qara sauqi kaji? Bari nakira Dr" ta tashi tanufi waje yabita da kallo harta fice.
Ajiyar zuciya ya sauke yanajin kamar anyi lifting wani qaton dutse daga saman qirjinshi.
Bin dakin yashigayi da kallo wanda ya tabbatarmashi h
ospital yake.
Ajiyar zuciya yasake saki yana komawa ya jingina sosai da pillon dake bayanshi yana tuna abinda yafaru jiya.
Shi kadai yasan abinda yakeji jiyan nan don qirjinshi inbanda zafi babu abinda yake, jiyake kamar ana iza wutane a qirjinshi am
ma yanzu alhamdullilah yarage sosai sai dan abinda ba'a rasa ba.
Bude kofar da'akayi yasashi dagowa yana kallon kofar.
Baby ce tashigo riqeda basket din abinci abayanta kuma sadeeq ne cikin wasu kayan da alamun yayi wanka ne riqeda qatuwar leda dake
shaqe da kayan itace.
Da sauri baby ta qaraso bakin gadon ta ajiye basket din ta kamo hannun ashraf murmushi fall fuskarta.
"Yaya you're awake?" Tafada cikin murna
Guntun murmushi kawai yayimata yana dan lumshe idanu.
Qarasowa shima sadeeq yayi
yana fadin
"Inyee gawa taqi rami? Ai harna fara cinikin gero shine dan baqinciki ka tashi?" Yafada shima yana ajiye ledar hannunshi kan locker dake kusada gadon ashraf.
Murmushi kawai ashraf yayi don haryanzu beda kuzari sosai.
"To saika fasa don
yayana ko turwa ta shafa mashi lfy a taurin rai, sai yafara shan naka gumbar kafin asha tashi" inji baby tana murgudamashi baki.
Dan waro idanu sadeeq yayi yana rufe bakinshi da tafin hannu
"Iyee? Dama fatan dakike mani kenan? Kodayake ke zaki kwan
ciki, kizama bazawara nabarki da maray..."
Waro idanun da baby tayi yasashi saurin sakama zancenshi full stop yana wulwulga idanu cikin rashin gaskiya.
Ashraf dai kallonsu yake kallon tuhuma, ganin haka yasa baby saurin duqawa ta ciro flask din ciki
n basket din tana yaqe.
"Yaya bari ba hadamaka tea" tafada tana dorawa kan dayan lockern dake dayan 6aren
"Nikuma na hadama fruits" inji sadeeq yana satan kallon baby dake antayamashi harara qasa qasa yana qumshe dariya.
Shidai ashraf bece komaiba
sai binsu kawai dayake da kallo
Suna haka kofar ta bude ummy da Dr suka shigo.
"A'a? Tare kuka dawone?" Inji ummy tana qarasowa
"Eh wlh, zuwa nayi nai wanka na shirya nakoma na daukota" inji sadeeq yana dan sosa qeya.
"To yayi, tea kike hadaw
a?" Ta tambayi baby dake riqe da mug din shayin tana jujjuya tea din da spoon
"Eh ummy" tafada tana kallon Dr dake duba Ashraf.
Saida yagama yan gwaje gwajenshi sannan ya ciromashi magungunnanshi yace abashi yasha idan ya karya sannan ya ciremashi em
pty drip din yafita.
Bowl aka fara kawomashi yayi brush aciki don beda qarfin dazai tashi yaje toilet sannan aka bashi tea din don yasha.
Kauda kai yayi kawai yana satan kallon ummy qasa qasa.
Itama kauda kai tayi don tasan abinda yake nufi.
Ga
nin haka yasa jikinshi yin sanyi ganin kamar still tana fushi dashi.
Dagowa yayi yamiqa hannu zai amshi mug din ummy tarigashi amsa taja kujera ta zauna gabanshi ya debo a spoon tadan hura sannan takaimashi a baki.
Dagudu ya bude bakin yana bin fuska
rta da kallo, harara ta gallamashi tana sakamashi spoon din abaki, murmushi ya su6ucemashi yayi saurin sunkuyar dakai yanayi.
Agefe kau baby sai antayama sadeeq harara take shikuma yana dariya marar sauti harda gwalo.
Haka ummy taita feeding dinshi h
arya qoshi sannan ta dago dan cewa sadeeq yabata magungunnan sai gani tayi yanata dariya marar sauti kamar sabon kamu.
Kallon baby tayi ganin direction dinta yake kallo taga ashraf ma ita take kallo wanda itama saida taga ummy zata waigo tayi saurin mai
da kallonta kan ashraf din.
Maida kallonta tayi ga sadeeq daya nutsu yanzu sai muzurai yake.
"Kaikuma lafiyarka?" Ta tambayeshi
Dan sosa kanshi yayi a kunyace
"Lfy lau ummy" yafada yana satar kallon baby dake qumshe dariyarta
"To allah yasa,
miqomin magungunnan kekuma miqomin ruwa"
Duk juyawa sukayi su aiwatar da abinda tace baby sai danne dariyarta take.
Ballar mashi magungunnan tayi tabashi yasha yanajin sanyi a zuciyarshi don abubuwan datake mashi sun nuna tabar fushi dashi.
Excus
ing kanshi sadeeq yayi ya fita waje yana hararar baby ta gefen idanu itakuma tamashi gwalo ta gefen baki tana murmushi.
Juyowa dazatayi suka hada idanu da ashraf tayi saurin kauda kai gabanta na faduwa.
Ta6e baki kawai yayi shima ya janye idanunshi.
Riqesu akayi asibitin ganin yanayin rashin qarfin jikin nashi.
Da yamma saiga matar kawu zaharadini da shi kanshi kawun nashi sunzo ganinshi.
Anan ne suka ke6e da ummy tabashi labarin komai.
Yayi mammaki shima matuqa don shi rabonshi dajin
ko labarin shamsu qolo tun suna mutunci da margayi Alhaji Auwal.
Saida suka tattauna sosai sannan suka tafi can gab da magrib.
Saudart kau a 6angarenta abin yayi affecting dinta itama sosai.
Takoma wata shiru daita ranta kodayaushe a jagule
.
Duk yadda daddy yaso wartsakar daita yagaza don wannan karan takasa controlling din kanta.
Haka zata wuni a daki ba uhm ba uhm uhm, abinci saidai abiyota dashi kuma dakyar yake samu taci.
Idan ya takuramata da tambayoyi sai taita mashi kuka.
A cikin kwana biyu duk ta chanza tafita hayyacinta.
Saida yayi kwanaki uku sannan aka sallamashi daga asibiti, lokacin yaji sauqi sosai.
Direct gidan ummy suka wuce.
Sosai Ashraf ya wartsake saidai haryanzu cutarnan ta son Saudart babu abi
nda ya ragu saima abinda yaqaru.
Kwana daya da sallamoshi Kawu ibrahim ya diro garin kano don shima tuni labari yakaimasu a wudil.
Sudai su baby basusan dalilinshi nazuwa ba amma sunsan baya rasa nasaba da case din Auren Ashraf.
Ranar sun hadu
da Kawu zahradini da ummy da kawu ibrahim sunyi heart-to-heart discussion akan yadda zasu 6illowa al'amarin.
*WASHEGARI*
Bayan azahar suka shirya dukkansu wato Kawu ibrahim, Kawu zahradini, Ummy, baby da Umma suka nufi gidan *MAMY*
💖💖💖💖💖💖💖💖
Jin ringing din doorbell yasa su dagowa daga cin abincin dasuke.
"Habeeb, jeka duba" inji Abba yana sipping din juice.
Ajiye fork din hannunshi yayi yana goge bakinshi da tissue sannan ya sauko daga dining din yanufi kofar.
Budewa yayi yayi tozali da maigadi
"Baba Audu" inji habeeb yana murmushi
"Na'am habibullahi" shima ya amsa yana washe baki
"Kashigo" yafada yana matsawa
"A'a dama baqi kukayi"
"Baqi? Ina?" Yafada yana leqa bayanshi.
"Suna can garage, s
una neman iso ne" yabashi amsa
"Ok inazuwa" yakoma ciki yafadawa su mamy.
"Baqi? Jeka ka shigo dasu" inji mamy
"No, kaisu falon baqi seems harda maza tunda kikaga sun fara aikowa" inji Abba.
Wucewa habeeb yayi don aiwatarda yadda yace din.
T
are suka tafi da maigadin har parking space din.
Ganin baby cikinsu yasashi washe baki yana qarasawa wajensu da sauri
"Laa aunty?" Yafada yana washe baki
Shafa mashi kai tayi tana murmushi
"Sheikh habibullah" tafada cikin sigar tsokana kamar yadd
a tasaba kiranshi a dan zamanta gidan lokacin biki.
Murmushi yayi sannan yajuya gasu ummy ya duqa har qasa yana gaidasu.
Amsawa duk sukayi cikin jindadi ummy na kallonshi tana hango kammaninshi da saudart sosai.
Iso yayi musu suka bishi har falon
baqi suna tafe baby na tsokanarshi shikuma yana murmushi don dama shi becika maganaba ko a lokacin data zauna gidan idan ta tsokaneshi saidai ya sunkuyar dakai yana murmushi hakan yasa take kiranshi sheikh ko ustaz.
Saida suka zauna sannan yajuya yafita
, chan saiga aminullah yashigo da kayan motsa baki.
Shima yadda habeeb ya gaidasu haka shima yayi amma banda baby sai harararta dayayi yana murmushi.
"Inyee lallai ka riqu, ni bazaka gaidani ba?" Tafada tana harararshi don dama shine abokin fadanta.
Gwalo yaimata yafice da sauri ganin tayi kamar zata tashi.
Duk dariya sukasa don sosai yaran suka burgesu.
Ana haka sukaji sallamar Abba, hakan yasa suka maida kallonsu a qofar dukkansu suna amsa sallamar.
Cikeda nutsuwa da dattako Abba yashi
go Mamy abayanshi suka shigo suna sakeyin sallama.
Amsawa duk suka sakeyi suna murmushi.
Saida suka zazzauna sannan aka shiga gaishe gaishe cikin girmamawa.
Sai anan Mamy ta lura da baby lokacin da itama ta zamo tana gaidasu.
"Laa kamar baby"
inji mamy
Murmushi baby tayi
"Nice mamy"
"A'a wata sabon gani, yau kece gidanmu?" Tafada cikin raha tana bin kingin mutanen da kallo tana mammakin su wanene? Agefe guda kuma gabanta nadan faduwa.
Ummy kau tunda Mamy tashigo take binta da kallo
don sosai take hango kammaninta nada dukda ta chanza sosai, gashi kammaninta sak na saudart sai mammakin yadda takasa ganin kammanin ada tayi.
Saida suka gama gaishe gaishen cikin raha da dariya sannan aka nutsu don tattauna abinda yakawosu.
Ganin ha
kan yasa baby miqewa ta barmusu dakin tashige cikin gida....
✍
Ummin fasihu ce
🧚🏻
♀
️
🤵🏻👰🏻
AUREN KWANGILA
👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
073
"Hajiya khadija, ashe rai
kan ga rai?" Inji ummy cikin murmushi.
Itama Mamy murmushin take mayar mata sai kallonta take don she looked familiar
"Aikaudai yaudai allah yayi mun hadu, munata saka ranar zuwa gashi kun rigamu zuwa" mamy tafada cikin fara'a
Murmushi ummy taq
arayi ganin haryanzu bata ganeta ba.
"To yaya bayan rabuwa? Ban ta6a tunanin zamu sake hadewa ba, gashi Allah yasake hadamu a matsayin in-laws"
Sai alokacin mamy tafara mata kallon rashin fahimta don bata gane abinda take nufiba, su dai du Abba nasu
ido.
"Erm... sorry, dama munsan juna ko?" Inji mamy tana kallonta sosai tana qoqarin gano inda ta ta6a sanin fuskar.
Murmushi mai sauti ummy tayi tana kada kai
"Sosaima, nasanki kema kin sanni wataqila dan an dade ba'a haduba shiyasa kika kasa gan
eni, shekaru Ashirin ai ba wasaba"
Kallon juna Abba da Mamy sukayi sannan suka maida kallonsu kanta
"Fateema ce, matar aminin tsohon mijinki Shamsu... Matar Alhaji Auwal"
Tsit dakin ya dauka, kowa yazuba masu idanu yayinda ita mamyn tazuba ummy i
danu babu ko kyaftawa tanason tuna inda ta ta6a jin wannan sunan.
"Auwal aminin mijinki dakika sameshi lokacin dakuka fara samun mtsl da tsohon mijinki" ummy taqara fada ganin mamy ta antaya kogin tunani.
Ahankali mamy tafara ware idanu tana kallon u
mmy daketa murmushi yayinda take nunata da yatsa bakinta na rawa
"Ummyn muhammad?!" Tafada tana ware manyan idanunta sosai
Murmushi kawai ummy tayi tana kada kai.
Dasauri mamy tanufi wajen ummy suka rungumi juna
"Ummyn muhammad? Kece or am dre
aming? This is unbelievable" tafada cikin alhini.
Murmushi duk mutanen dakin sukayi suna kallonsu.
Nanfa akayita firar yaushe gamo, haryanzu mamy takasa yarda ummy ce surukarta, jinjinama ikon Allah takeyi, ko a mafarki bata ta6a tunanin zata sake ga
ninta ba sai gashi cikin ikon allah sun sake haduwa kuma wannan karon da strong bond atsakaninsu.
Sun dade suna fira suna dariya suka dan ta6a kayan motsa baki da aka kawomusu sannan suka nutsu suka dawo serious don tattauna abinda yakawosu, ummy sai
kallon mamy take tana jin badadi don tasan dole hankalin mamy yatashi idan taji dalilin zuwan nasu.
Ciki hikima da iya tsara zance Kawu ibrahim ya gabatarmusu abinda yakawosu wanda saida yafara basu labarin abota da amintar dake tsakanin margayi Auwal d
a Shamsu sannan ya gangaro zuwa yadda suka samu matsala dajuna suka koma basa ga maciji da juna zuwa yadda aka kame mottocin margayin da yadda labari ya iskesu nacewa aikin tsohon amininshi ne sanadi harzuwa jinyar dayayi wanda sanaddiyar girgizar dayayine
dajin cewa tsohon abokinshi ne sanadin karayarshi wanda wannan jinyarce sanadinshi.
Ya gangaro kan yadda rayuwa ta sauyamusu da yadda suka siyarda gidansu suka samu allah ta tallafamusu zuwa inda Ashraf yasamu scholarship yayi karatunshi a Uk xuwa inda
yagama yabude company na A.A ENTERPRISES.
Tsit falon yayi, kowa shiru kamar ruwa ya cinyesu, mamy kau idanunta sun kada sosai mood dinta ya chanza
Abba kau he is expressionless, baxaka iya gane awane yanayi yake cikiba.
Ajiyar zuciya kawu ibrah
im ya sauke sannan yacigaba daga inda yatsaya yafara magana akan abinda ya tarasu.
Tunda yafara magana mamy takafamashi idanu tana kallo babu ko kyaftawa harya kai aya.
Daga mamy har Abba rasa mai kwakwarran motsi akayi, they're all dumbfounded.
K
wakwalwarsu kasa daukar zancenshi sukayi.
"I don't understand, i don't really understand" inji mamy tana girgiza kai hawaye na taruwa idanunta, kallo daya zaka mata kasan hankalinta yayi matuqar tashi.
Kama hannunta ummy tayi kasancewar dama kusada i
ta take asanyaye tace
"Khadija, nima i was shocked danaji wannan zancen, it's unbelievable banta6a jin makamancin wannan yafaruba ko a tatsuniya amma it's real" tafaxa asanyaye.
" *AUREN KWANGILA?* contract marriage? Dama akwai irin wannan auren? Am co
nfused" tafada kaida gani kasan she's not herself.
"But how? Tayaya Saudart da hankalinta zata yarda da irin wannan shirmen? This is unbelievable" inji Abba shima cikin alhini
"He forced her, bada son ranta bane, shiya tilasta mata" inji ummy
"Shi
ya tilasta mata?! Ni meye amfanina? Why can't she come over to me and tell me! Daqiqancinta harya kai takasa confiding in me as her mother?.... dama nafada! Babu yadda banyiba akan kar amayar mashi daita tun farko akaqi saurarata, ga irinta nan, ya siyar d
aita akan kudi, ya musayata da kudi! Kagani ko Alhaji? Kaga abinda nake fada? Allah kadai yasan me da me yakoyamata, Allah kadai yasan tarbiyarda ya dorata akai, ya maidamani yarinya cash worm..." kuka ne ya kufce mata ta toshe bakinta tanayi sosai.
Run
gumota ummy tayi asanyaye tana rarrashi.
"But how come tun farko baku ganeshi ba dakukazo?" Inji Abba da duk jikinshi yayi sanyi.
"Alokacin nida Nura mukazo tareda yan uwan ummy, lokaci yaja gashi dama ni sau daya nata6a ganinshi lokacin rasuwar mall
am, shi zahradini daya sanshi sosai bayanan lokacin yayi tafiya, kuma munyi bincike mun samu gamssashiyar shaida gamedashi tun kafinma muzo din" inji kawu ibrahim.
"Innalillah waina ilaihi rajiun, wannan abu beyi dadiba samm" inji Abba yana girgiza kai.
Dagowa mamy dake kuka haryanzu tayi tareda cewa
"Dama nasani, that greedy man can do anything don yasamu kudi, gashi greediness dinshi yaja zai lallatama diyata future, koko ince yama lallata tunda gashi itama saboda kudin ta yarda tayi auren"
"No
mamy, he forced her ne" inji umma da tundazu batace komaiba.
Kallon umman mamy tayi tace "bawani forcing, nasan saudart ciki da bai, idan batayi niyyar yin abuba babu wanda ya isa yasata, besides baganiba? Ni meye amfanina idan bazata iya gayamin damuwa
rta ba? Am her mother for goodness sake, dama i smell something fishy gameda auren nan don everything come all of a sudden ne, now yayi nasarar maida diyata kwadayyaya irinshi" tafada bitterly.
Rarrashinta akai tayi don kuka take sosai, banda zafi babu
abinda zuciyarta keyi.
Ajiyar zuciya Abba ya sauke sannan ya kalli su kawu ibrahim dakyau ya bude baki calmly yace
"Now meye abin yi? Aikin gama dai yariga da yagama, sai samun solution yarage, yanxu ku me kuka yanke?"
Kawu zahradini da shima tund
axu beyi maganaba yadan muskuta sannan yafara cewa
"To yanxu dai two things are involved, na farko case din shamsu nabiyu kuma auren nan.
Mudai bamu riqe shamsu araiba akan abinda yaima margayi, wannan tsakaninsu ne da margayi da Mahallicinsu, Allah za
ima kowa sakayya daidai dashi.
Batun aure kuma Ashraf yanuna yanason matarshi kuma ya janye contract din tsakaninsu, idan so samune sucigaba da zama a matsayin ma'aurata saidai wani hanzari ba gudu ba.. *saudart!*.... dole yadda tun farko auren yarjej
eniya ne a tsakaninsu yanxuma yarjejeniya zamansu zai zama, ma'ana dole saida amincewar dukkansu, bazamuso mu cutar da daya ba don farantama dayan. Idan saudart ta amince zata cigaba da zama dashi to fallilahil-hamd don muma bazamu so yankewar wannan alaqa
r tamuba, munason saudart kamar yar cikinmu, abinda mahaifinta yayi can baya bazai ta6a shafanta ba don kwata kwata babu kamanceceniyar hallaya tsakaninsu, saudart yarinyace mai nutsuwa da tarbiya wanda samun irinta ayanzu yayi wuya, ladabi da biyyayarta y
asa tunfarko ta yarda da qudurin babanta wanda ita tausayamashi tayi ganin halin dazai fada idan bata aminceba, saudart macece mai amana da zuciya mai kyau don ba don itaba da yanzu company don A.A ya fuskanci mummunar asara da karaya, muna sonta amma haka
n baxaisa idan taqi yarda da cigaba da zama