Showing 1 words to 3000 words out of 50822 words
[01/10, 9:06 pm]
: *LABIBA*......
🏵
️
🏵
️
🏵
️
_The Emotional Story_
😰😰😰😰
*By Nabilancy luv*
💘
_Auntyn S and S_
*wannan Page din Sadaukarwa ne ga dukkan members na cikin group din TASKAR Nabilancy Ina tayamu murnaf cika Shekara biya
r atare da juna yau group ya cika shekara biyar da kafuwa munfaro cikin hadin kai da kaunar juna haka mun kawo a yau Cikin Kaunar juna da mutuntawa Ina muku fatan Alkairi Allah ya bar kauna..*
👏🏽👍🏽
Ga masu son shiga Taskar Nabilancy group don samun no
vels da nawa Dana sauran Writers ga links Amma mata zalla plz.sannan masu yin comment Ake bukata.
https://chat.whatsapp.com/IrSkOTTMgyXLstYDBfzGJk
Page 1
and 2
Sanyin safiya ya lullu
ɓ
e unguwar iska mai laushi da
ɗ
a
ɗ
i na ka
ɗ
awa, tana hura ƙamshin turaren
ruwan da aka yayyafa a harabar gidan. Labiba ta fito daga
ɗ
aki tana sanye da hijabi mai laushi, tafin ƙafafunta suna dukan ƙasa cikin nutsuwa wanda ya kasance yanayinta, itan mai sanyin rai ce da nutsuwa.
A cikin zuciyarta tsoro ne fal, ta san yau akwai
babban ƙalubale a kanta zata bada hadda a Islamiyya, kuma har yanzu bata tsaya a kanta ba, ta maimaita sau ba adadi, gashi tana cikin matsala ta cikin gida, damuwa da ayyukan gida da matar uba take ta'azzara mata da su kamar tsohuwar jaka ya saka karatun y
a gagara tsayawa a cikin kwanyar kanta. Ayyukan zatayi ko karatun? Gajiya tayi mata yawan da karatun ba ya shiga. Hajiya Hakima ta tsani ta ganta zaune tana hutawa. Kiris take jira ta tusata gaba da aiki, aike wannan tana iya rabashi ukku, dama ka'idarta b
ata aike
ɗ
aya koda kuwa a waje
ɗ
aya ne, sai tace dauko min plate, sai ta kawo tace ha
ɗ
o da cokali, dauko kofi, daban-daban haka zata raba aikin ta tara mata gajiyar jiki, shiyasa duk dare idan LABIBA ta kwanta jikinta yake azabar ciwo na zirga-zirga da tak
e sha a gidan. Anya kuwa matar nan tana da imani? Amsar a bayyane yake, babu digonsa ko ka
ɗ
an a zuciyarta sai tarin zalunci, isa da mulki.
Ta fitar da mahaifiyarta daga gidan ta tusata gaba da mafitar ayyuka bayan mahaifinta yana da kudin da zai iya
ɗ
auka
r masu aiki, saida tasan kitimurmurar da ta kulla ta kori ƴar aikinsu ta rataya ayyukan akan LABIBA. Koda tausayinta bataji koda yake bata san zafin haihuwa bane shiyasa, da ace ta ta
ɓ
a haihuwa watakila ta sassauta mata wannan wahala, koda yake mata nawa n
e a wannan karni namu da suka haifa sannan kuma suka wahalar da yaran wasu, wato sun tattala nasu sun wofantar da na wasu, lamarin mutanen wannan zamani yana da
ɗ
aure kai matuƙa gaya, son zuciya da mugunta yayi masu ƙatutu da ƙaƙagida suna aikata wasu abub
uwan da idan mutum ya gani yayi ta mamaki da tu'ajjibi.
Tunaninta ya karkata islamiyya saidai ma ba haddar ka
ɗ
ai ke damunta ba. Akwai wani abu daban da ya fi tada hankalinta: Malamin su, Ustaz Haroon. Idan tana gabansa, wani irin kallo yake mata da yake s
aka tana rasa nutsuwarta, ya kafeta da idanu kamar yana so ya karanta abun dake a cikin zuciyarta. Tana jin nauyin kallonsa, tana jin kamar yana da wata manufa da bata fahimta ba.
LABIBA ta kutsa kai cikin kicin da saurinta don
ɗ
aukar ruwa a firij kafin t
a kai ga fita, sai ga matar babanta Hajiya Hakima ta fito daga
ɗ
aki, tana riƙe da mayafinta.
"Ina kuma zaki da sauri kamar wadda ba ta da gaskiya?" Ta fa
ɗ
a tana kallonta daga sama har ƙasa tana yatsine fuska kamar wacce aka yi wa dolen jefa mata tambayar.
Labiba ta tsaya cak!, tana ta
ɓ
e le
ɓ
e. "Islamiyya zan tafi. Ina da hadda." Ta fa
ɗ
a babu yawo babu fallasa.
Hajiya Hakima ta
ɗ
aura hannu bisa ƙugu, fuskar nan a daure kamar an
ɗ
aura dutse a kai. "To ai sai kin gama aikin gida! Ko kin fi kowa son karatu ne
? Ko nufinki ni ce zan dukrkisa inyi aikin, sanin kanki ne ayyukan gidan nan a kanki suka rataya don haka ki tabbata kin gama min aiki kafin ki saka ƙafa ki fita."
"Amma Hajiya ai…"
"Ke rufe min baki! Idan ba kiyi wanke wanken kwanukan nan ba, wallahi ba
zaki ko’ina ba!."
Hankalin Labiba ya ƙara tashi, hankalinta ya dugunzuma, komi ya jagule mata, ta rasa abun da yake mata
ɗ
a
ɗ
i. Ta san idan ta tsaya tana jayayya ba za ta gama da wuri ba hakazalika idan tayi bata da tabbacin zata gama da wuri duba da tulu
n wanke-wanken kamar na gidan biki. Ta ha
ɗ
iye numfashi, cikin sanyinta ta nufi fanfo ta kunna ta tara bokiti nan ta zage ta fara wanke kwanukan da suka taru tun jiya. Hannunta na jijjigar sanyi, zuciyarta na cike da damuwa da tarabbabi.
Sanyin ruwan da ta
ke tsoma hannuwanta tana daurayar wanke-wanken ya rinƙa ratsata yayin da take cigaba da wanke kwanukan da suke da yawa kamar ba za su ƙare ba, jiya hajiyar tayi baƙi shiyasa suka tara uban kwanuka, kawayenta ƴan bariki sunzo.
Haka take tarasu a gidan suyi
girkin
ɓ
arna suna ci suna gulmar mutane, waccen tace, waccen tayi, a zagi waccen, a kushe waccen, maganar kenan gulmar mutane, kina tashi kika
ɗ
aga za'a dasa taki gulmar ana fa
ɗ
in halayenki na ƙarya da gaskiya, zagi da cin mutunci. Ga zagi kamar a bakinsu
ake kirkiri domin wasu samfurin zagunan a bakinsu Labiba take fara jinsu.
Idanun Labiba sun cika da ruwan hawaye, jikinta ya cika da gajiya, jikinta na ƴan hutu ne bai saba da wahala ba amma hajiyar na son sabar mata, karfi da yaji tana neman mayar da it
a boyi-boyi. Sau da yawa ayyukan gidan ne suke sakata makara islamiyya amma bata da za
ɓ
i, idan ta kuskura ta ce zata fita ba tare da ta gama aikin ba, sai Hajiya ta hana ta fita gaba
ɗ
aya ko ma ta hukuntata.
Tana wanke kwanukan, zuciyarta na ta lissafin y
anda zata ƙarasa shi cikin sauri, gani take kamar ana ƙara masu yawa ne tsabar ƙagara da tayi ta gama ta wuce Islamiyya.
A can cikin zuciyarta, tana jin nauyin ranar yau ta asabar, ta san idan ta yi latti Ustaz Haroon ya rinƙa tsareta da kallo kenan, kall
on da ta kasa banbance na tuhuma ne ko na soyayya, watakila ma ya saka ta zauna kusa da shi kamar yadda ya saba mata a wasu lokuttan. Hakan na sanya ta jin tsoro, duk da cewa bata da wata masaniya game da dalilin kulawar da yake nuna mata.
A yayinda take
wanke-wanken, zuciyarta ta rinƙa bugawa da tunanin yadda Ustaz Haroon zai kalleta idan ta yi latti. Kuma idan ya tsare ta da tambayoyi game da haddar da bata gama rikewa ba fa?
Muryar Hajiya taji tana mai bata umarnin wai ta tabbatar kafin ta fita ta shar
e mata falo. "Ki share min parlour ya fita tsaf kuma idan kika sake kikayi cuwa-cuwa sai kin tusa koda kuwa zamu shekara kina maimaitawa domin ni ba ƙazama bace ba." Kuji fa! Matar da idan ba Labiba ce ta share falon ba zata iya barinsa yayi sati a haka sa
boda ganda da son jiki, ita a dole ƴar hutu bata son hayaniya, matar da idan suna gulma da kawayenta ƴan bariki muryarta sama-sama kamar wacce take sanar da duniya.
Labiba ta gyada kai kawai, duk da cewa zuciyarta na ƙaraji da tuƙuƙi. Tana saurin gama wan
nan sai kuma ga wani an kitso daban. Hawaye suka taru a gurbin idanunta suna zuba akan fuskarta ta saka hannuwa ta share. Ba shiri tana gama wanke-wanken kuwa ta dauko tsintsiya don sharar falon, aikuwa dai tana share falon da saurinta tana kallon agogon d
ake kafe a bangon falon, zuciyarta cike da fargaba da tunanin watakila kafin ta gama ta ƙara kirkiro wani aikin, ta gama tayi mopping tiles din ta kammala, saidai ina tuni lokaci ya kure mata!
Tayi hanyar dakinta cikin azama, ta
ɗ
auki jakarta ta fito da s
auri, tana jin zuciyarta na bugawa. Yanzu ta tabbata Ustaz Haroon zai tsareta da tambayoyi kuma hakan ne take gudu.
Kwana biyun nan, yana nuna mata wani irin kulawa, yana tsayawa a bayanta fiye da sauran
ɗ
alibai, yana nuna mata wasu abubuwa kamar na Soyay
ya, Amma ita fa? Ita ko ma’anar soyayya ba ta san ta ba, ballantana ta fahimci abun da yake nufi da kallon da yake mata.
***** ******
Hajiya Hakima masifaffiyar mace ce bata saurarawa idan tana fada, hatta mahaifin Labiba Alhaji Sadi yana shakkarta, Abb
an Labiba yana da gudun Rigima shiyasa baya biyewa Hajiya idan tana masifarta.
Shine mai gida amma takan bugi kirji tace itace da gida, karfi da yaji so take ta mayar dashi mijin Hajiya, shekararsu goma tare amma bata ta
ɓ
a haihuwa ba watakila shiyasa bat
a san darajar haihuwar ba da har take wulakanta
ɗ
iyar miji.
LABIBA itace ƴa
ɗ
aya tilo da yake da ita, abar sonsa abar faharinsa, akwai wanta wanda ya
ɓ
ace a duniyar bat! Tun yana da shekaru biyar a duniya yayi ta
ɓ
an dabo tun suna saka ran samunsa har sun
fitar da rai, anyi duba anyi bincike har an hakura, malamai da dama kance yana nan a raye, zai bayyana a garesu watan watarana.
Zuciyar Alhaji Sadi ta kan lafa tayi sanyi idan aka ce masa a hannu na gari gudan jinin nasa yake.
Mahaifiyar LABIBA Mama Saud
e macece itama me hakuri da yakana ga kawaici.
Sun rabu da Alhaji Sadi a sanadin ta daki LABIBA saboda son da yake yiwa LABIBA yasa ya fusata yayi mata saki
ɗ
aya.
Sakin da ya gigitata ya tsayar da lissafin kwakwalwarta, ta rinƙa tambayar kanta miye na sa
kin akan haka, ita ce ta dauki cikin Labiba tsayin watanni tara ta haifeta ta kula da ita har ta girma, aikuwa koda tana mugunta zaiyi wahala tayi wa gudan jininta ballantana ba wani duka ne na azo a gani ba, duka ne wanda tayi shi domin ladabtarwa, sosai
a dangi anyi mamaki matuƙa gaya saboda yanda sukayi auren soyayya sukayi mugun shaƙuwa sannan yake kaffa-kaffa da lamarinta, ba'a jin kansu amma sai gashi akan abu kalilan she
ɗ
an yayi rinjaye akan su har ya kai ga saki.
"Anya kuwa saude ba shegen duka kik
ayi mata ba irin na hukuncin huce haushi domin da yawan uwaye a wannan zamani sun daukarwa kansu fushi na hukuncin dukan yara duka na wuce misali, duka ba don ladabtawa ba, duka na huce haushi, hukunci na huce takaici." Tsohuwa Kaltume mahaifiyarta ta tuhu
meta.
Mama Saude ta girgiza kai fuskarta dauke da damuwa tace, "Ko
ɗ
aya ba haka bane, tsa
ɓ
ar son da yake mata ne da kuma kulafucin
ɗ
a, shi a dole komai tayi a zuba mata idanu. Shin Inna ta ya tarbiyyar yaro zata kasance a haka? Idan ta lalace har da ni za
'a ha
ɗ
a a zaga. Har sai anfi ganin laifina duba da nice nike tare da ita a kullum."
Tsohuwa Kaltume ta jinjina kai tana tu'ajjibin wannan lamari, tace, "To Allah ya kyauta amma idan ta tabbata hakane to kuma Alhaji Sadi bai kitsawa kansa abun kirki ba."
Mama Saude ta gya
ɗ
a kai kawai ba tare da ta furta komai ba.
Mariƙinsa Baba Malam yayi mashi dole akan ya dawo da ita bayan anyi sulhu tsakaninsu sannan yayi musu fa
ɗ
a akan zaman aure ba wasa bane kada a sake wasa da Aure ayi irin wannan rabuwar mara dadin
ji.
A yanda Alhaji Sadi yake da haƙuri ba ya da hayaniya anyi mamakin ma da har hakan ta kasance a tsakaninsu. Babban abun mamakin shine dalilin yin sakin.
Tun bayan sulhun Hajiya Saude take kaffa-kaffa da lamarin Labiba musamman idan tayi mata laifi ya
na nan takan bari sai ya fita sannan tayi hukunci idan yaso kafin ya dawo tayi kukanta ta bari watakila har ta manta.
Alhaji Sadi
ɗ
an kasuwa ne yana da kudi sosai wanda ba kasuwancinsa da yake yi bane ka
ɗ
ai yake kawo masa kudin, akwai wata
ɓ
oyayyiyar sana
'a da yake gudanarwa ta karkashin kasa wacce babu wanda yake son ya san da ita. Wannan sirrinsa ne da a kullum yake nadamar tsundumarsa a ciki, yake kuma da burin ya fita a cikin harkar.
Bayan dogon zama a tsakaninsa da mama saude, LABIBA ta kawo ta zama
budurwa saidai tana shiga makarantar sakandire mahaifin nata ya ƙara aure.
Ƙ
arin auren da ya zamo na ƙaddara domin shigowar Amarya Hajiya Hakima ya zamo tamkar sinadarin gishirin tashin hankalin mama Saude, don kuwa tun da ta shigo cikin gidan farin cikin
maman ya tsaya cak! Ya juye zuwa bakin ciki da damuwa mai tarin yawa, Hajiya Hakima mace ce makira ga kissa gashi kuma ta iya kitimurmura, ƴar zaqon kasa ce da ha
ɗ
a tuggu da makirci.
Hajiya Hakima takari ce don ta
ɗ
a
ɗ
e a saudiyya tana neman ku
ɗ
i, a can m
a aurenta biyu yana mutuwa, ta auri baƙar fata
ɗ
an Nigeria sukayi zaman shekara guda acan sannan ta auri balarabe, kuma duk idan sun rabu takan aikata musu sata na kudade ne ta tsallake ta barsu, kowannensu ta fisu girma takan musu duka har azo a kwacesu a
hannunta, ita din irin matan nan ne ingarma guda, doguwa ga jiki ga kira ga muni kamar duhu, baki
ɗ
ayanta bata da fasali ko sisin kobo, akan ce mata suna fin maza kyawu amma ita kam dukkanin namijin da tafi kyawu to kuwa a jinjinawa muninsa domin ba ƙaram
i bane ba.
Ko a Nijeriya ma aurenta biyu idan har da na Alhaji Sadi ukku kenan, babu wanda ta ta
ɓ
a haihuwa dashi gwara-gwara aurenta na fari ta ta
ɓ
a yin
ɓ
ari a lokacin da ganiyar ƙuruciyarta, abun mamaki rashin haihuwar da ba tayi bai sakata a cikin damuw
a tunda tana kama ƴan canji, kaunarta da ku
ɗ
i ba ƙarama bace ba.
Baƙa ce mai idanuwa ƙwala-ƙwala ga babban baki ga katoton hanci kamar shantu, kunnuwa kamar na zomo. Tana da ƴan canjinta a banki tana buga kasuwanci, ba'a cin bashinta a riƙe a zauna lafiya
har gida zata zo ta nada maka duka ko kuma ta kaika a kulle har sai ka biya a fito da kai, bata da mutunci akan bashi. Ta kance ko ciki
ɗ
aya ta fito da mutum idan yaci bashinta sai ya biya ko kuma a ji kansu.
Tunda ta shigo gidan Alhaji Sadi ta mallakesh
i take zuba iko da mulki a gidan, ga isa ko girki za'ayi sai an tambayeta ta fa
ɗ
i abun da take da ra'ayi, ta kame komai tana zuba mulki yadda ranta yake so, komi za'ayi na harkar gidan sai ta amince, idan muguntar ta motsa tayi ta abubuwa da gayya domin Ma
ma Saude ta kwashi takaici.
Mama saide me haƙuri saidai ta zuba ido kawai, hakurinta da rashin maganar da take idan taga abu ya saka take zaune ƙalau a gidan, ba'a taba yi da ita ba, saidai tagani tayi kurum, takanyi mamakin yanda Hajiya Hakima ke saka Al
haji gaba da fa
ɗ
a da masifa tamkar Ɗanta, baya iya katabus.
Bata ƙara yin mamaki bama sai watarana ana kan hakan Hajiya Hakima ta daki LABIBA saboda ta sakata jajjagen kayan miya LABIBA ta ƙiyi ta shirya ta tafi islamiyya abunta, saboda tace gara mata mas
ifar Hajiya Hakima akan dai tayi latti saboda suna gab da shiga Babban aji, a lokacin ƴan sauka suna yin sauka sune next, kuma Uztaz Haroon ya matsa musu ba ya bari suyi latti ko fashi su kwashe ta
ɗ
a
ɗ
i suna mugun tsoronsa a ajin dama makarantar baki
ɗ
aya.
Aikuwa da ta dawo daga islamiyya Hajiya ta kama ta da duka, abun mamakin Alhaji yana nan yana sama dakinsa yana jiyo ihu da kukan LABIBA ya fito da sauri, Amma me!? Ganin Hakimar tashi ce take dukan LABIBA yasa ya kasa aiwatar da komai sai ma juyawa da y
ayi ya koma ya kasa yi mata fada ko ya tsawatar, amma a cikin zuciyarsa yaji ciwon abun ba ka
ɗ
an ba, ihun da labibar takeyi yana ta
ɓ
a zuciyarsa.
Mama Saude tasha mamaki anan ta ƙara tabbatar da abun da zuciyarta take ayyana mata na cewar Hajiyar ta shanye
Mijin nasu ta kuma fi ƙarfinsa tunda ita da ta tsugunna ta haifeta amma akan ta doketa yayi mata saki guda to gashi wacce bata san zafinta ba ta doketa dukan da yafi wanda ita tayi mata kuma akan abu kalilan amma ya gagara yayi magana. Wane mutum ya doki
LABIBA a zauna lafiya, da walakin goro a miya. Akwai lauje a cikin nadi, ba banza Hakima ta barshi ba.
Ita kuwa dama a kara da kawaici irin nata bazata iya ce mata kanzil ba, kawai dai ta tashi a falon ne ta bar mata gun ta shige dakinta, dama irin mu had
u a falon nan ne, babban falo ne da aka ƙawatashi da manyan kujeru masu tsada set biyu wanda Alhajin ne ya siyesu ya gyara dakin kafin Auren Hajiya Hakima.
Ƙ
afar benen ata cikin falon yake me matakalar silba Wanda idan ka hau zai sadaka da bedroom din Alh
ajin.
Tun daga wannan duka da hajiyar tayi mata LABIBA take