Showing 45001 words to 48000 words out of 50822 words
komai idan ka dawo zan nuna maka dakin nawa domin gujewa irin haka,
hankalina ya tashi sosai da na duba naga baka nan."
Ji yayi hawaye suka zubo mashi tunda mahaifinsa ya rasu ya rasa wannan kulawa, a yau shine don ya fita ake nemansa, uwa rahama ce, before koda zai shekara ya shekare babu wanda zai damu da rashin ganinsa
.
Ya saka hannuwa ya share hawayen yace, "To shikenan momcy, hakan bazai sake faruwa ba, zan kiyaye ko domin farin cikinki."
Taji dadin kalaminsa tace, "Allah yayi albarka." Ya amsa da, "Amin."
Bayan sallar Isha'i Yana boys Quarters gun yusuf ya kira Mo
mcy ya sanar da ita ya tsaya hira wajen Yusuf, aijuwa m nan aka kawo masu abinci suka ci tare, suna ta hirar duniya sai around goman dare sannan Aliyu ya koma ciki yana shiga dakin babu jimawa Momcy ta shigo tare da Alhaji. Ya gaishe dashi,
"Ina wuni?"
"
Lafiya lau. Ya jikin?"
"Da sauki."
"Ashe kuma wani tsautsayi ya faru? Allah ya kiyaye gaba, Allah ya ƙara tsarewa."
"Amin."
"Na samu labari mai dadi na kasancewarka yaronta da yake Kano, abu yayi dadi, Alhamdulillah, Allah shine abun godiya."
Sun juya
zasu fita, Aliyu yace, "Momcy." Ta juyo tace, "Kayi barci zuwa da safe sai muyi zaman har da Alhaji. Kada ka manta da addu'ar kwanciya barci ka kuma kashe wuta."
Daga haka ta juya tabi bayan Alhaji.
Aliyu ya kwanta babu jimawa bacci yayi awon gaba dashi
, barci mai dadi wanda ya jima bai yi irinsa ba.
Adaren yanata tunanin idan sun zauna da momcy da Alhaji ko ma yace da Yan gidan gaba Daya harda Yusuf ma daya boyewa asalin waye shi da sana,arsa ya zaiyi kenan agobe da momcy tace ya fada musu labarinsa na
bayan rabuwa,To shin kuwa ma zai iya fitowa yace da Amminsa cewar shi Dan fashi ne!yayi fashi abaya sannan still dai ba wani tuba yayi ba? Ya Bata labarin Labiba ko ya boye?
Muje zuwa
[01/10, 9:09 pm]
: https://chat.whatsapp.com/Fuo3XSrIYYTLrK01nb8MV9
?mode=ac_t
*LABIBA....*
🏵
️
🏵
️
🏵
️
Page
37 and 38
Nabilancy Love
💘
(Auntyn S and S)
A darennan Soja boy yayi bacci cikin jin dadi me tattare da mafarkai masu dadi,ko farkawa baiyi ba cikin dare Dama Rai fes! Ya kwanta sbd yayewar damuwarsa sh
iyasa yai bacci da saleb'a.
Shikuwa a bangaren Yusuf a wannan dare sam bai rumtsa ba sai faman juyi yake tunanin ahalinsa ne cike a zuciyarsa, yana jin kewarsu tana taso mashi musamman uwarshi mahaifiya, uwa mai dadi, haduwar Aliyu da Momcy ya saka mashi
Shima son haduwa da tashi mahaifiyar wacce bata gaza da basu tarbiyya da saka albarka ba, yana mai jin haushin kansa na gudu da yayi daga gareta ya tuna ya ƙara tunawa amma ya kasa tuna abun da yayi mashi togaciya da qin zuwa wajenta a tsayin wadannan she
karun.
Yana ji lallai lallai dole ya koma ga ahalinsa a wannan satin ya nemi gafara a wajen mahaifiyarsa da mahaifinsa na gudunsu da yayi tsayin wadannan shekarun akan dalilin da ya saka gane shin ma miye dalilin?, amsar itace asiri kamar yadda Aliyu ya
sanar dashi tunda har zuwa wajen malami yayi ya fa
ɗ
a mashi dukkanin abubuwan da suke faruwa, ya bashi addu'a ya shawarceshi da yawaita karatun Alk'ur'ani mai girma wanda duk daga ranar da ya fara zuwa yau yaga cigaba sosai, before ko tunawa da gida ba yayi
amma a wannan takin yana yawan tunawa dasu, tunaninsu manne a ransa.
*******
SHIN ME YA FARU DA YUSUF NE WAI? MIYE MAKASUDIN DALILINSA NA BARIN KANO NE?
Yusuf ya tashi cikin so da kulawa na mahaifi da mahaifiya kasancewarsa babban d'a a gidan da kuma h
alinsa na jajircewa akan dukkanin abun da ya saka a gabansa, ga kwakwalwa da son kannansa wannan ne ya ƙara wa mahaifinsa sonsa.
Yana da kananan shekaru mahaifinsa malam mamuda ya auro ladiyo matar da tunda ta shigo gidan ta dauki karan tsana ta daurawa M
ama Nana uwar gidan Malam Mamuda sannan kuma mahaifiyarsu Yusuf, a haka rayuwa ta cigaba da wakana, Ladiyo ta shigo gidan ne da zummarta da kudurin ta fitar da Mama Nana saidai hakurin Mama Nana yayi mata togaciya da cin nasara abun bai yiyu ba dolenta ta
hakura ta koma kulla tuggu da makirci a gidan ta hana malam mamuda da Mama Nana zaman lafiya a gidan, kullum cikin ha
ɗ
a kitimurmura take tana ha
ɗ
a kansu amma da yake Allah baiyi zasu rabu ba sai shirinta ya kara faduwa kasa warwas.
Yusuf yayi karatu tun d
aga primary har zuwa degree ta farko har aikin hidimtawa kasa yayi a garin Jos na jihar pilato, bayan dawowarsa ya samu babban aiki tunda aka samu aikin har ya fara zuwa sau daya Ladiyo ta taya murna daga nan bata sake bi takan maganar ba hakanan danginta
babu wanda yazo tayasu murna.
Ashe tuggu take ha
ɗ
awa ta karkashin kasa, karshe tayi nasarar da Yusuf ya rasa aikinsa akan tuggu da aka ha
ɗ
a mashi a wajen aiki saboda gaskiyarsa da amana su kuma abokan aikin suna son ayi almundahana shi kuma ya hana suka h
a
ɗ
a mashi makirci har saida suka saka aka koreshi.
A wannan karon ne fa Ladiyo ta samu bakin magana saidai muryarta ta kere ta kowa tana masu jaje tana nuna ta samu amma a zuciyarta nishadi takeji da farin ciki, washegari saiga danginta sun zo jaje, kuji
wani lamari an samu aiki basuzo taya murna ba amma da aka rasa sai sukayo gayya suka zo (kaizo munafunci baiyi ba, sai abun arziki ya samu mutum ya kasa nuna ka damu amma kuma abun banza yana faruwa sai kayi fuska biyu kana nuna ka damu bayan kuma a zuciya
ba haka bane, Allah ya kyauta).
Da yake babu mugunta a zuciyar Yusuf bayan wata biyu ya fara kasuwanci a kasuwar wambai kuma Alhamdulillah yana samun cigaba sosai saboda gaskiya, rikon amana da iya tarbar kustomomi.
Bakin ciki da hassadar ladiyo suka mo
tsa, kiyayyar da takeyi wa mahaifiyarsa ta shafeshi ganin tunda yaron ya tashi babu abun da yake faruwa a rayuwarsa sai nasara, komai ya taba sai yayi albarka, tana kyashin jinin Mama Nana ya zama mai kudi a rayuwa wannan ya saka ta hada tuggu tayi asirin
da ya rabo Yusuf daga mahaifarsa ya shigo legas ya manta da komai.
******
A haka Yusuf yayi ta tunane har
ɓ
arawon barci yayi awon gaba dashi wanda yake cike da mafarkan gida.
Da asuba Aliyu yayi
ɗ
aya
ɗ
aya yana sharar barci Momcy ta shigo ta tayar dashi
sallar asuba yana ta turo baki saying, "Ayyerh Momcy zanyi da safe." Ta dan kalleshi tace, "Subhanallahi miye nikeji haka babu dadin ji babu dadin saurare, ka tashi kaje kayi sallah, Aliyu ka zama mai yin sallah akan lokaci a cikin jam'i koda kana wani abu
n sai kaga with time ka daina. Allah yayi albarka." Ya amsa da, "Amin."
Saida taga shigarsa bandaki sannan ta juya ta fita, saida yayi wanka sannan ya dauro alwalla ya fito ya zura jallabiya ya fita, a matakalar bene ya hadu da Alhaji Aminu suka hadu da Y
usuf a compound suka wuce masallacin a tare, suna a masallaci suna azkar saida gari yayi haske sannan suka kamo hanyar gida.
Aliyu yabi lafiyar gado bacci yayi awon gaba dashi, Momcy ta shigo mashi da breakfast ta samu yana barci ta koma dashi a zuwan ida
n ya farka ta girka mashi wani (uhmm uwa mai dadi, Allah ya saka masu da alheri, wadanda kuma suka rasa nasu Allah yayi masu rahama).
Sai wajen karfe goma sannan ya farka ya mike zaune yayinda idanunsa suka sauka akan farar takardar dake ajiye akan bedsid
e drawer a kusa da wayarsa.
Ya dauka ya duba rubutu ne da harshen Hausa: 'Idan ka tashi ka kira ka fa
ɗ
a min abun da kake sai a girka maka kayi karin kumallo.'
Murmushi ya su
ɓ
uce masa uwa kenan, uwa mai dadi, ya kira numbarta, ya rusuna kamar tana a gab
ansa yace, "Momcy ina kwana?" Ta amsa da, "Lafiya lau. Ka tashi lafiya." Yace, "Lafiya lau."
"Miye za'a girka maka?" Ta tambaya daga
ɗ
aya bangaren.
Ya dan yi jim kafin daga bisani yace, "Komi Momcyna ta girka min zanci." Ta murmusa tace, "To shikenan."
"Maganar ta jiya?" Ya tambaya. Ta dan yi dariya tace, "Idan kayi breakfast sai muyi maganar Alhaji yana nan." Ya gya
ɗ
a kai yace, "To shikenan." Tace, "Allah yayi albarka." Ya amsa da, "Amin." Yana jin wani dadi marar misaltuwa da nishadi yana shigarsa. Mah
aifiya kenan, uwa mai dadi, wanda yayi rashin ta yayi babban tashi.
Momcy tana ajiye wayar ta mike ta shiga kitchen ta zage ta girka mashi lafiyayyen breakfast, delicious one, ta saka a kwando ta nufi bedroom dinsa.
Ya gama shiri yana zaune a gefen gado
yana kallon hotunan Labiba, Momcy ta shigo, ya ƙara gaishe da ita ta amsa da kulawa, yana cin abincin yana mata santi tana dariya har ya koshi, abincin yayi dadi ba ka
ɗ
an ba, yana ta kwasar loma zuba santi (Ni Nabilancy na ce kodai su nemo wagi ne).
A ta
re suka sauko kasa suka samu Alhaji Aminu a falonshi, Aliyu ya gaishe dashi da girmama ya amsa da kulawa.
A wannan lokacin ne suka samu zaman duk da Aliyu yaso zaman ya kasance daga shi sai Momcy domin yana da kudurin bude mata komai na rayuwarsa ko ya sa
mu ta tayashi da addu'a, wanzuwar Alhaji Aminu yaso ya zame mashi babbar togaciya saidai ranar wanka ba'a boyon cibi don haka bai boye masu komai ba ya fede mashi daga biri har wutsiya akan rayuwarsa har zuwa rabuwa da labiba da yayi ya shigo duniya neman
Momcy har sana'arsa ta fashi bai buye masu ba.
Babu abun da Momcy take sai zubar da hawaye, ta rasa furta komai, tana zaune dai a wajen a yanayi na damuwa da alhini da jin haushin kanta da kanta na sakaci da tayi ta guje
ɗ
anta har ya koma haka.
Ya share
hawayen dake akan fuskarta tana fa
ɗ
in, "Kaicona da na guji dan cikina har ya koma haka amma babu komai zan gyara kuskuren da nayi a baya su kuma wadanda suka ha
ɗ
a kitimurmurar da suka rabaka da aikinki da yan uwan mahaifinka da sukayi wasarairai da lamurra
nka babu komai, ai da
ɗ
a da dukiya ba'ayi masu mugunta domin baka san wanda zakaci gajiyarsa ba."
Taja fasali sannan tace, "Aliyu abun da ya faru a tsakani da mahaifinka da sanadin rabuwarmu wannan sirrinmu ne, bazan zama cikin sahun maza masu
ɓ
ata mataye
nsu da suka rabu dasu a wajen yaransu ba, a'a yadda nike son ka girmama lamarina haka nike so shima ka girmama lamarinsa. Allah ya jikan sa, Allah ya gafarta masa."
Ta ƙara jan fasali kafin tace, "Abun da ya saka ban nemeka ba fushi ne da zafin zuciya sai
daga baya na gane kuskurena a lokacin da bakin alkalami ya bushe, naje Kano sau ba adadi a wajen dangin mahaifinka saidai babu wata gamsasshiyar amsa, saidai suce rabonsu da kai anfi shekara ukku akwai ma wadanda suka ce tun daga rasuwar mahaifinka basu ƙ
ara ganinka ba, wannan abu ya dade yana bani mamaki da tu'ajjibi, shin idan yaransu ne zasuyi masu haka? Amsar itace a'a, dan uwansu na jini amma bayan rasuwarsa sukayi wasarairai da lamarin
ɗ
ansa kwaya daya tilo, kaico. Allah yasa muci karfin zukatanmu."
Suka amsa da, "Amin."
Ta dubeshi tana mai zubar da hawaye tace, "Aliyu ka yafe min." Ya girgiza kai yace, "Babu komai Momcy, haduwa dake ya yaye min dukkanin wani kuncin dake nike ji a raina."
Wuni sukayi a tare suna hira saida aka yi kiran sallar Zuhr s
annan Aliyu da Alhaji Aminu suka wuce masallaci yayinda Momcy ta haura saman bene domin gabatar da sallah.
Yusuf ya kasa zaune ya kasa tsaye tunanin gida ne cike da ransa, a ranar ya samu Alhaji Aminu da magana akan yana son zuwa gida bayan da ya kwashe l
abarinsa ya sanar dasu, sun tausaya mashi ba ka
ɗ
an ba, Alhaji Aminu yace, "Dama tuni nike maka maganar ya kamata ka koma gida sai kake kauce wa maganar ko kuma sai ka fara shiri rimi-rimi sai ka watsar sai nayi tunanin watakila iyayenka ne basu a raye ko k
uma baka sansu ba shiyasa na daina tada maka zancen amma tunda yanzu da bakinka ya fa
ɗ
a kana son zuwa sai muje har da Aliyu."
Aliyu ya girgiza kai yace, "A'a tukunna ban shirya zuwa Kano a yanzu ba."
Alhaji Aminu yayi jim sai kuma yace, "To babu damuwa a
mma ka zama cikin shirin domin akwai wani abokina zanyi mashi magana akan case dinka domin a ƙara bincike a bankado gaskiya ka koma akan aikinka." Aliyu ya jinjina kai yace, "Na gode, Allah ya ƙara girma." Alhaji Aminu ya amsa da, "Amin."
Alhaji Aminu ya
saka ranar tafiyar kwanaki biyu masu zuwa, ana ta shirye-shiryen zuwa Kano, tunda aka saka ranar tafiyar Yusuf ya dage da tsayuwar dare tareda karatun Alk'ur'ani mai girma yana rokon Allah ya bashi ikon zuwa ga iyayensa ba tareda ya fuskanci togaciyar dake
mashi togaciya before ba. Kuma Alhamdulillah har ranar da za'a tafi son tafiyar yana manne a ransa babu abun da ya sauya.
Momcy, Alhaji Aminu,Soja boy, Yusuf tareda Muniba sukayi boarding flight Abuja to Kano, bayan sun sauka a kano suka kama hanyar gida
nsu Yusuf duk da garin ya sauya mashi amma bai manta gidansu ba, da mahaifiyarsa Mama Nana ya fara cin karo ya ƙarasa da saurinsu ya rungumeta yana mai fashewa da kuka, itama kukan ta saki babu abun da take fada sai, "Alhamdulillah. Alhamdulillah. Alhamdul
illah."
Sunyi sa'a Malam Mamuda shima yana nan, sun samu tarba sosai an karramasu, Yusuf Yana ta zuba idanu yaga inda zai hango makirar amma babu ita babu alamarta, da ya tambaya Mama Nana take sanar dashi kwanaki biyu da suka wuce ta fara wasu sambatu ka
mar mahaukaciya tana tonawa kanta asiri da kanta, dukkanin wani makirci da tuggu da ta ha
ɗ
a a gidan saida ta fada har da asirin da tayi mashi ya shiga duniya, maganar da ake tana can tana hauka bayan da Malam Mamuda ya buga mata saki.
Mama Nana da Malam M
amuda da kannan Yusuf sunyi farin cikin dawowarsa a garesu ba ka
ɗ
an ba, a nan ne kuma Malam Mamuda ya tabbatar masu akwai maganar da yake son yayi, saida ya Numfasa ya Kalli kowa kana ya gyara zama yace, "Hakikanin gaskiya Yusuf ba
ɗ
anmu bane, tsintarsa mu
kayi muka rikeshi tamkar yaronmu...
Yayi shiru kana yaci gaba" kuma har yau har gobe Yusuf kana nan a matsayin
ɗ
anmu, na za
ɓ
i fada maka wannan maganar ne saboda ina ganin ka cancanci ka sani,Dan ka dage ka nemi iyayanka,Kuma watakila ka gamu dasu inkai ad
dua Kuma ka fita neman iyayen na ka." Yusuf ya kadu da jin wannan maganar ba ka
ɗ
an ba, aikuwa dai daren ranar bai rintsaba yana ta juye-juye ya zurfafa Neman mafita.
Yayinda agefe guda Aliyu ya ringa karfafa masa guiwa da bashi shawarar farko akan ya fara
Dora hotonsa a kafar sadarwa don cigiyar iyayansa.
To Zama dai a garin Kano ya kama su Momcy, Alhaji ya bukaci su zauna na yan kwanaki a fara cigiyar iyayen Yusuf tukunna watakila a dace, Aiko dai sun baza hotonsa na lokacin da yake yaro, yana ta yawo a
kafafen sada zumunta da cikakken bayanai akansa.
*********
Labiba tana zaune tana juya hoton yayanta wanda ta samu a wajen Abba, tana jin kewa tana tunanin ko yana ina? Shin yana ma raye kuwa? Inama zata ganshi,to ta wacce hanyar? Ta ajiye hoton kenan ta
hau Instagram taci karo da hoton wani yaro mai kama dashi yana neman iyayensa ta dauko wancen hoton ta duba tabbas shine, ai bata san lokacin da ta mike zaune ba tana fadin, "Alhamdulillah.!Allah maji rokon bawa".
Da sauri ta fice falo gun Abba,Ta samesh
i a parlour Yana duba news paper ,ta zauna fuskarta cike da annashuwa da rawar murya take sanar dashi, "Abba na samu yayana, yanzu naga hotonsa a manhajar Instagram yana neman iyayensa kaganshi" Ta miƙa mashi wayar, kallo daya yayi wa hoton ya gane tabbas
ɗ
ansa ne da ya rasa shekarun baya da suka wuce.
Fuskarsa ta cika da farin ciki da annashuwa, a daidai wannan lokacin haji. Hakima ta shigo falon tana yatsine fuska tace, "Menene wai,meke faruwa ne?" Labiba tayi mata kallo Tara saura kwata ta watsar kafin
tace, "Yayana da ya
ɓ
ata tun yana yaro shine yau Allah ya bayyana manashi"
Hajiya hakima ta zaro idanu A take kuma yanayin ta ya sauya ya koma tsantsar bakin ciki,kana kallonta zaka fahimta, Labiba cikin ranta tace, "hhuumm Aniyar kowa ta bishi Ta Allah
dai ba taki ba."
Abba ya suri makullin mota suka fice shida labiba,domin bin adireshin gidan dake akan cigiyar.
Shikuma acan bangaren Yusuf Yana tare da Soja boy Daya takura masa da maganar matarsa Daya Saka abaya,Amma ayau yanason dukkansu wai suje gid
an matar tashi zai mayar ta agabansu zai nuna mata soyayya da nuna mata ya Daina harka mara kyau ta baya,Yana son ya nuna musu ahalinsa ayau.
Yusuf yace"Naso ace ka bari an Nutsu nima kafin Nan naga nawa iyayan.
Soja boy ya girgiza kai yace "bazaka Gane
ba bros,inason Labiba,inason kasancewa da matata,dole ce fa ta raba mu,Dan Allah ka amince aje ayau pls my bros ga Ammi dai tana jinmu karkai musu....
Muje zuwa
[01/10, 9:09 pm]
: https://chat.whatsapp.com/Fuo3XSrIYYTLrK01nb8MV9?mode=ac_t