Showing 18001 words to 21000 words out of 50822 words
ta hanyar zuba maganin a shayi, kada wannan ma akwai wani mugun abun a ciki, wanda aka yi wa hankali yafi wanda aka haifa dashi, tayi ƙasaƙai tana tunanin taci ko kuma kada taci.
Wata zuciyar tace mata, 'Labiba kici ciki ne ta riga ta
zubar dashi shikenan, duk iya shegen Hajiya ba zatayi yunƙurin kasheki tunda ta sani ku ukku ne a gidan idan kuwa hakane dole zargi zai bi ta kanta'
Da wannan tunanin ta saki jiki taci abincin kuma Alhamdullilah taci sosai, lokaci zuwa lokaci tana tunawa
da cikin da Hajiya ta zubar mata, saidai ta girgiza kai kawai bata tunanin akwai digon tausayi a zuciyar Hajiya, Matar ta cika makirci ta kin kari, miye cikin ya tare mata da zata zubar, abun har
ɗ
aure mata kai yake, koda yake mai daki shine yasan idan yak
e mashi yoyo, ita da ta zubar tasan dalilin. Bata san dalilin ba kuma bata damu da ta sani ba, kawai abun da ta sani shine an zalunceta.
BAYAN KWANA BIYU
Ta fito daga bandaki kenan Hajiya Hakima ta bamko kofa tana mazurai, da gadara tace, "Ke ubanki yana
kira," ta juya ta fita.
Labiba ta bita da kallo tana mamakin wannan kira mai kama da zagi, ta zura hijab ta fita ta sameshi a falo, ogar tana daga gefe tana ka
ɗ
a kafafu tana jiran rohoto.
Alhaji Sadi ya dubeta yace, "Labiba kece kika sha maganin zubar d
a ciki ko kuma wani ne ya saka maki ba tareda kin sani ba."
Wannan tambaya ya saka gaban Hajiya ya fara dukan ukku-ukku, tayi tsuru-tsuru da idanu, Labiba ta juya ta kalleta sukayi kallon-kallo, kallon da saida Hajiya ta razana domin ta sadakas asirinta y
a tonu kawai.
Labiba ta maido da dubanta akan Alhaji Sadi tace, "Tun da safiyar ranar nike jin ciwon mara da ciwon ciki, ina ganin shine ya janyo
ɓ
arewar cikin."
Duk da bai gamsu da amsarta ba amma bai zurfafa ba, ya dora da ainihin maganar da ta saka ya
kirata.
"Labiba na kiraki ne inyi maki godiya, na gode biyayya da kikayi min, nayi maki miji kin kar
ɓ
a ba tare da jayayya ba duk da kuwa abun da yayi maki, sannan ina son inyi maki albishir da cewa bayan zubewar cikin nayi nufin fasa aurar dake in turaki
kasar waje karatu amma daga baya nayi shawara na gamsu da cewa auren shine mafi cancanta da inyi maki idan yaso sai kiyi karatun a nan, na fara ciku-cikun nema maki admission shima Aliyun nayi mashi magana ya amince koda zuwanki gidanshi babu
ɗ
a
ɗ
ewa admi
ssion ya fito zaki fara zuwa, idan kuma ya fito ne kafin auren zanyi maki komai sai ki fara karatun a nan bayan auren ki ƙarasa a gidan mijinki... Labiba ina sonki ina tausayinki, ina sone rayuwarki ta inganta tayi kyau, ban ha
ɗ
aki aure dashi domin in kunt
ata maki ba, nayi ne saboda shine masalaha da muke dashi, naji da
ɗ
in biyayya da kikayi min, na gode, na gode, Allah yayi maki albarka, kema Allah ya baki masu maki biyayya, Allah ya albarkaci rayuwarki, dukkanin abun da kika saka a gaba Allah ya baki sa'a
a kai, dukkanin abun da kika saka a gaba Allah yasa albarka a cikinsa, Allah ya hadaki da dukkanin wani abu da yake alheri ne, ya tsareki da dukkanin abun da yake sharri ne, ina rokon Allah ya albarkaci karatun da zaki fara."
Ji tayi hawaye sun ciko mata,
hawaye ne na farin ciki akan addu'ar mahaifinta a gareta. Ta amsa da, "Amin." Tana jin farin ciki a ranta.
Fuu Hajiya ta bar falon bakin ciki fal a ranta, ta rasa abun da yake mata
ɗ
a
ɗ
i, yarinya ƙarama tana nema ta zame maka karfin kafa, tayi asirin tayi
tuggun amma komai ya daina amfani, ji take kamar ta fasa ihu.
Da shigar Labiba daki ko dakika biyar ba'a yi ba Hajiya ta banko kofar har wannan bankowar tafi waccen don saida ta razana ta
ɗ
auka wani abu mai cutarwa ne, ta dafe kirji idanunta a waje, gani
n Hajiyar ce ta sauke ajiyar zuciya.
Hajiya ta kalleta ta watsar tace, "Nazo ki fa
ɗ
a man dalilin da ya saka kika rufa min asiri a wajen Alhaji bayan nasan kin gane abun da ya faru akan zubewar cikinki."
Labiba ta girgiza kai, halayen Hajiya suna matuƙar
shayar da ita giyar mamaki, ace har yanzu matar bata hankarta ta daina bakin halin mugunta da bakin ciki ba, koda yake wasu mugayen haka suke da ƙeƙesasshiyar zuciya.
Tayi murmushi mai ciwo tace, "Na rufa maki asiri ne saboda kina maki fatan shiryuwa, ida
n kina da rabon shiryuwa wannan zai zame maki izina, idan kuma kince sharri zaki cigaba da kullawa to ga fili ga mai doki, akwai ranar kin dillanci."
"Sai inyi maki dukan tsiya nan har ni zaki datsawa baƙar magana, da
ɗ
in abun bani bace nace kiyi min alfar
ma ballantana ki hura hanci kina ƙafafa a kai, kuma koda zanyi yawo tsirara sai na tabbatar da na nakasa rayuwarki kin tashi aiki."
Labiba tace, "Allah ya fiki."
Hajiya ta figi jiki fuu ta fita tana jin takaicin da bakin ciki sun tokare mata wajen lumfas
hi, tana tafe tana mita ita
ɗ
aya, ta kwara kofar da karfin da saida Labiba ta ƙara razana.
Dama karatun Alƙur'ani tayi nufin tayi sai kuma ta samu kiran Abba, ta shiga bandaki ta
ɗ
auro alwalla ta fito ta shimfi
ɗ
a sallaya ta bu
ɗ
e Alƙur'ani mai girma tana r
era karatu a cikin Suratul Maryam, tana jin nutsuwa da kwanciyar hankali suna saukar mata.
Wayarta dake a ƙasa tayi haske alamar kira ya shigo, Aliyu ne, ta
ɗ
aga ta cigaba da karatun har saida takai aya sannan ta saka a amsa kuwwa tace, "Ina kwana ranka y
a da
ɗ
e?"
Daga daya bangaren yace, "Lafiya lau Malama, kin wuni lafiya?"
Ta amsa da, "Lafiya lau."
"Sai kuma wannan abun ya faru, Allah ya saka hakan shine yafi zama alheri, Allah ya ƙara sauki, Allah ya tsare."
Ta amsa da, "Amin."
Tayi shiru yayi shir
u, ita ce ta kawo karshen shirun ta hanyar cewa, "Yaushe zaka zo ina son magana da kai?"
Ya
ɗ
an yi shiru sai kuma yace, "Gobe idan Allah ya kaimu sai inzo."
"Allah ya kaimu."
"Amin."
Shiru ya ratsa a tsakani, shine ya kawo karshen shirun yace, "Ƙira'ar
ki tayi min
ɗ
a
ɗ
i da fatan zaki rinƙa rera min a gidana idan munyi aure." Tace, "Allah ya kaimu."
"Amin."
Daga nan sukayi sallama ta tsinke kiran.
Tayi mamakin kiran duk da yana kiranta jefi-jefi amma ba kamar haka ba, kuma basu doguwar hira, har wani sa
'in tana ji kamar ta kirashi sai kuma ta tuna abun da yayi mata sai ta fasa.
Bayan Abba ya dawo ta sameshi ta sanar dashi zuwan Aliyu a washegari, da mamaki yace, "Amma mi yasa kike son ganinsa?" Tambayar tazo mata a bazata domin ba tayi tunanin zai tamba
ya ba, tace, "Ina mamaki ne wace sana'a yake yi a yanzu, Ina son in tambayeshi, gidan ya nuna inda zai ajiyeni baka ganshi babba katoto gari guda, motoci yau yazo da waccen gobe yazo da wata daban, yana saka min shakku da kokonto, ina son cire shakku da ko
koton da nikeji a kansa, nayi ƙoƙarin tambayarsa a waya amma sai yayi ta kaucewa maganar hakan yana ƙara saka min shakku, ina son in tabbatar da yabar fashin kada inje yana ciyar da ni haram.
A cikin Alƙur'ani mai girma a Suratul Baqara aya ta dari da sab
a'in da biyu 172 Allah Subhanallahu Wata'ala yana cewa:
"Ya ku wa
ɗ
anda sukayi Imani ku ci daga cikin tsarkakan abubuwan da muka arzuta ku da su, sannan kuma ku nuna godiya ga Allah in har kun kasance Shi kuke bautawa."
A aya ta dari da saba'in da ukku 17
3 Allah yana cewa:
"Haƙiƙa an haramta maku mushe da jini da naman alade, da kuma abun da aka yanka da nufin wani abin bauta sa
ɓ
anin Allah ba. Amma duk wanda dole ta tilasta mashi ba don sabawa Allah ba, to babu laifi a kansa. Haƙiƙa Allah Mai gafara ne ku
ma Mai rahama."
An kar
ɓ
o daga Abu Huraira (RA), ya ce: Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gareshi) ya ce:
"Ya ku mutane! Lallai Allah tsarkakke ne, kuma ba ya kar
ɓ
a sai mai tsarki, Allah ya umarci muminai da irin abun da ya umarci Ma
nzanni. Sai ya bada labarin wani mutum matafiyi, gashin kansa mai kura (ya wahala saboda tsananin tafiya), ya
ɗ
aga hannuwansa izuwa sama yana addu'a yana fa
ɗ
in: 'Ya Ubangiji! Ya Ubangiji!' alhali abincin sa haram ne, abun shan sa haram ne, tufafin da yake
sanye dasu na haram ne, guzurinsa na haram ne, Annabi (Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gareShi) yace, shin ta ya ya za'a kar
ɓ
i addu’arsa?"
An kar
ɓ
o daga An-Nu’man Bin Bashir (RA), ya ce:
"Lallai Halal a bayyane take, Haram ma a bayyane take, amm
a a tsakaninsu akwai wasu al'amurra masu rikitarwa (shubuha) wa
ɗ
anda da yawa daga cikin mutane basu sansu ba, wanda ya nisanci abubuwan da ake shakka (shubuha), hakika ya kiyaye addininsa da mutuncinsa. Amma wanda ya auka cikin shubuha ya afka cikin haram.
.."
Bukhari da Muslim ne suka ruwaitosu
Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gareshi) ya ce:
"Dukkan jikin da aka gina shi da haram, wuta ce makomarsa." (Tirmidhi 172)
Alhaji Sadi ji yayi jikinsa yayi sanyi tausayinta ya kamashi, tu
n tana jinjira yake ciyar da ita da haram na ku
ɗ
a
ɗ
en da ya samu a fashi. Jinjina kai kawai yayi ya miƙe ya haye sama.
WASHE GARI
Tafiyar tasa ta samu tsaiko saida da marece gab da Sallar Magrib ya iso, ta saukeshi a babban falon baki bayan sun gaisa ya ƙ
ara yi mata sannu da jiki.
"Sannu, Allah ya ƙara sauki."
"Amin."
Saida ta nisa sannan tace, "Akwai abin da ya da
ɗ
e yana min yawo a kai shiyasa na nemi ganinka."
H.D SOJA BOY ya gya
ɗ
a kai yace, "Ina sauraronki."
Labiba ta muskuta tace, "Ina son sanin g
askiya akan shin ka daina fashi da gaske ko kuma a fatar baki kawai ka fa
ɗ
a min, kuma idan ka daina shin wace sana'ar ta Halal kakeyi a yanzu."
"Labiba na daina sana'ar fashi da gaske, a yanzu haka ina sana'ar mota, mahaifinki ne ma yake dorani akan hanya
."
Taji sanyi a ranta tace, "Allah ya taimaka." Ya amsa da, "Amin."
Yana a gidan har bayan sallar Magrib yana mata hira ta dauka shiru-shiru ne, sai a lokacin ta fahimci ashe oga ne a fagen soyayya, da ya tashi tafiya har mota ta rakashi.
Ya dubeta da k
ulawa yace, "Sai yaushe kenan Matar Oga?" Tayi siririyar dariya tace, "Sai kazo kenan." Ya ware idanu yace, "Ko gobe da safe ne?" Ta rausayar kai tace, "Koda asubahin goben ne ana maraba da kai."
A tare sukayi dariya, ya juya ya shige mota tana tsaye har
saida taga fitar motarsa sannan ta juya ta koma ciki tana mai sakin murmushi duk da har a lokacin Ustaz Haroon ne a ranta amma taji Aliyu ya kwanta mata a rai kuma zata iya rayuwar aure dashi, aurenshi ya fiye mata zaman gidan.
Daga ranar kullum suna mann
e a waya ana zuba soyayya, duk bayan kwanaki yana zuwa, har gidan Baba Malam sukaje ya gaishe dashi daga nan suka wuce Malam Sabo (Mariƙin Mahaifiyarta Marigayiya Mama Sauda).
Alhamdullilah ta samu Admission a Northwest University Kano, a lokacin da Abba
yake mata albishir har hawayen farin ciki, tana lura da yadda Hajiya take ka
ɗ
a kafafu tana ta
ɓ
e baki.
Labiba cikon ranta tace, "Aniyar kowa ta bishi, Allah ya shirye ki idan mai shiryuwa ce, bazan gajiya da nema maki shiriya ba domin shiriyar taki tafi la
lacewar alfanu."
Tana komawa
ɗ
aki ta dauko wayarta ta kira Aliyu (H.D SOJA BOY) tana fa
ɗ
a mashi wannan dadda
ɗ
an labari.
"Amma na tayaki murna, Congratulation."
"Na gode."
"Ki tsumayi kyautata zuwa gobe."
"To shikenan, godiya nike."
Bata kawo komai a
ranta ta dauka wani ƙaramin abun ne, washegari sai ga mota sabuwa dal Mercedes benz kalar ruwan toka, bakinta ya kasa rufuwa saboda farin ciki kamar yasan motar tana matuƙar burgeta, ta kira tayi mashi godiya.
"Babu komai ai yi wa kaine, Matar Oga ta canc
anci fiye da haka."
Muje zuwa
[01/10, 9:06 pm]
: *LABIBA*.......
🏵
️
🏵
️
🏵
️
_The Emotional Story_
😰😰😰😰
Na _Nabilancy love_
💘
*Auntyn S and S*
______________________________
🌈🇰
AIN
UWA
🇼
RITER'S✍
🏼
*
🇦
SSOCIATION
🤝🏻
*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
______________________________
Page
13
and 14
Duk abun nan Hajiya
tana a balcony tana kallon komai baƙin ciki da hassada sun taso mata sun tokare mata zuciya tana kwafa tana ji dama motar ta ƙone kowa ya huta. Kishin da takeyi da marigayiya Mama Saude ta daukoshi kacokan ta mayar akan Labiba.
Washegari gari sai ga wata
motar Jeep daga wajen Alhaji Sadi zuwa ga tilon diyarsa Labiba, a lokacin hauka ne kawai Hakima ba tayi ba har ta saka
ɓ
oye bakin cikinta, ta tada bori akan lallai idan yana son zama lafiya da ita saidai ya barta taje wajen siyar da motocinsa ta za
ɓ
a ta da
rje wacce tayi mata ita dai Labiba bata san yadda ta kaya a tsakaninsu, amma dai har aka kwana ukku da maganar bata ga Hajiya da sabuwar mota ba wanda yake nuni da Alhaji bai amince da wannan kudirin ba.
Aysher kawarta ta makotansu itama a makarantar ta s
amu Admission course
ɗ
aya da wanda Labiba ta samu, a tare sukayi registration wani sa'in Aliyu.
A wajen registration tayi Ƙawa Surayya, da fari kamar tasu zata zo
ɗ
aya sai kuma ta lura yarinyar ta fiye rawar kai, ga gulma da surutun asara, ranar da Aliyu
ya sauketa a makarantar tana kallonshi.
Wannan ya saka ta fara ja baya da ita, sanin halinsu ba
ɗ
aya ba, bata son gulma, ita ko taron mata ƙawaye ne idan har akwai gulma a ciki fita take da fitarta.
Ta fara kakkauce mata, yadda Surayyar take ƙara shigeta
mata ne ya saka take sakar mata fuska kamar babu komai amma tana fara kawo mata gulma zata taka mata burki, tana kawo hirar Aliyu zata sauya akalar hirar, ranar tazo mata gulmar Aysher ance-ance, a take ta taka mata burki.
"Na gaya maki bana son maganar
mutumin da ba wajen, ki bari idan tazo sai ki fa
ɗ
a a gabanta, kinga da gulma da maganar Aliyu bana son kina yi min, idan yazo ganina kawoni ko yazo ganina tsakaninki dashi gaisuwa shikenan, bana son wannan shigewar da kike mashi gaskiya."
Ta
ɗ
auka Surayya
zatayi zuciya kawancen ya ƙare a wajen amma ga mamakinta sai ji tayi tace, "To babu damuwa za'a kiyaye."
Biki yana ta matsowa har saura wata guda, dama ta fa
ɗ
a mashi babu wata bidi'a da zatayi wa'azi kawai ta saka sai Friends Evening shikenan.
Biki saur
a sati biyu mutanen maiguduri suka iso mota guda, da kayansu niki-niki na gudunmuwa, abun sai wanda ya gani, tayi farin cikin zuwansu ta sake a cikinsu saboda kauna da suke nuna mata.
An kawo lefe na azo a gani har mamaki ta rinƙa yi na yawanshi na ku
ɗ
a
ɗ
e
da aka kashe, mutane suna ta shigowa gani, Hajiya babu baki sai ido saidai tayi yake har mutane sun gane mata, saidai kiji ana kus-kus ana fa
ɗ
in bakin ciki takeyi wa marainiyar Allah.
Kamar yadda Labiba ta kudura ba tayi wani tarin programs ba duk da har
dinner yaso ayi ta hana, wa'azi da friends evening kawai tayi, tayi matuƙar mamaki da tunda aka fara hidimar bikin bataga wani danginsa ko lefen maza ne suka kawo abun yana
ɗ
aure mata kai saidai ta saka a ranta cewa sai bayan auren zata tuntu
ɓ
eshi akan ma
ganar.
Ranar Asabar da misalin karfe
ɗ
aya da rabi na rana a Na'ibawa gidan Baba Malam aka
ɗ
aura auren Labiba Sadi da angonta Aliyu Samanja Audu Turaki akan sadaki naira dubu dari biyar, murna a wajen H.D SOJA BOY ba'a magana.
Washegarin walima mutanen Ma
iduguri sukayi haramar komawa guda suna murnar ganin auren diyar ƴar uwarsu, Labiba tasha nasiha sosai a wajensu da shawarwari akan zamantakewar aure.
*******
Har ƙawayenta Aysher, Ummi, da Surayya sun tafi, dama Surayya take ta jan zaman a dole su bari
ango yazo daga karshe da suka matsa ba don ranta yaso ta miƙe ta bisu, gidan ya rage daga Labiba sai kanta.
Takon takalmansa suka fara sanar da ita zuwansa.
Karon farko da taji kunyarsa ta kamata sai kuma ta tuna abun da ya faru a lokacin da kaddara tayi
mata yankan baya, gabanta ya fara dukan ukku-ukku yana lugude, abu
ɗ
aya ne ya saka hankalinta ya kwanta sanin cewa tana kwanakin al'adarta ne.