Showing 48001 words to 50822 words out of 50822 words

Chapter 17 - LABIBA Complete

/>
*LABIBA....*



🏵





🏵



🏵



Page

39

and 40

Karshen Book 1

Nabilancy Love

💘

(Auntyn S and S)

Matuƙar farin ciki da Alhaji Sadi yake ciki ya saka ya kasa tuki saidai Labiba ce taja masu motar zuwa adireshin, suka samu magina suna kaiwa da komowa wajen gyaran

ɗ

ay

a bangaren gidan inda Mama Nana zata zauna, da Nutsuwa Labiba ta shiga ciki zuwa

ɗ

aya bangaren inda mutanen gidan suka koma temporary.

Alokacin Soja boy Bai Dade da fita ba,yaje gidansa don ya gyara,sbd su momcy zasu dawo gidan itada ALH Aminu zasu Dan z

auna kafin su tafi,Akwai yaran makwabta da suke bashi girma zai basu kudi don su tsaftace koina na gdn tunda dole zaiyi qura tunda ba me gyarawa gida shiru,shikuma gashi da tsafta.

Labiba Tayi sa'a ta samu har Alhaji Aminu da Momcy suna nan, ta gaishe das

u suka amsa da sakin fuska duk da basu wayeta ba amma masu iya magana suka ce shimfidar fuska tafi ta tabarma, tunda ta shiga falon Yusuf ya kafeta da idanu yayinda yake jin wani yanayi wanda bai san ta yadda zai misaltashi ba.

Ta rusuna tace, "Tare nike

da mahaifina idan kunyi min izini sai in shigo dashi, akwai magana mai muhimmanci da take tafe damu."

Da mamaki suke kallonta babu wanda ya kawo sunzo ne akan maganar Yusuf domin abu ne da basuyi tsammani bayyanar iyayen nasa a kusa ba duba da shekarun da

ya dauka da

ɓ

acewa.

Alhaji Aminu ne yayi karfin hali yace, "Okay, babu damuwa kije ki shigo dashi."

Kafin su dawo har Mama Nana ta saka

ɗ

aya daga cikin kannen Yusuf ta shimfida masu tabarma, suka zauna aka gaisa a mutunce, Alhaji Sadi yayi masu bayanin

yadda lamarin ya faru shekarun baya da suka shude. "Mahaifiyarsa ta fito dashi aka nemeshi aka rasa, tunda ya

ɓ

ata muke nemansa amma babu wani labari." Ya zaro hoto ya mika masu, "Wannan shine hotonsa kafin bacewarsa daga wajenmu."

Mama Nana ta amshi hoto

n tana gani, tabbas shine, Alhamdulillah Allah shine abun godiya, Yusuf ya hadu da danginsa, ya rungume Alhaji Sadi yana mai sakin kuka mai tsuma rai, Labiba ta ƙarasa wajen ya ha

ɗ

e har da ita ya rungume yana mai jin kewarsu.tareda godiya ga Allah Daya kaw

o masa danginsa har gida ckn sauki.

Alhaji Aminu, Momcy, Malam Mamuda, Mama Nana da k'annansa na gidan Shamsiyya, Madiha da Zainab babu wanda bai zubar masu da hawaye, hawaye ne na tausayinsu da tayasu farin ciki na haduwarsu bayan shudewar wadannan sheka

run.

Yusuf Kome ya tuna sai kuma ya sakesu yace, "Mamana!, Ina mamana."!! Ya fada da zazzafar murya me cike da damuwa.

Ji Labiba tayi hawaye sun zubo mata ta share hawaye tana girgiza mashi kai, tace, "Allah yayi wa mahaifiyarmu rasuwa, saidai muyi mata

addu'a Allah ya jikanta da rahama, Allah ya gafarta mata."

Ta karasa fada da sanyin murya tana tuno musabbabin rasuwarta,kuma Bata manta Aliyu Haidar shine silar rasuwar mamanta ai.

Shikuma

Muryarsa tana rawa yace, "Mama, Mama na babu." Sai kuma ya fas

he da kuka gwanin ban tausayi.

Labiba Ta kwanta a jikinsa tana mai fashewa da kuka na kewar mahaifiyarsu da kuma quna da take ji na dalilin da ya kai mahaifiyar tasu kushewa yayinda sabon tsanar Haidar ta durar mata a zuciya. Anya kuwa zata iya manta fyad

e da yayi mata a gaban mahaifanta wanda shine dalilin bugawar zuciyar Ummarsu.

Mahaifinsu shine sanadi amma zatayi shiru da bakinta domin ba zata so yayanta ya dandani bakin cikin da ta k'unsa akan wannan lamari ba, shirun yafi fadar kasancewa alheri. Ba

zata bari yayi wannan mummunan jin ba.

Alhaji Sadi ya hadesu ya rungume, ban da uba yana uba da babu abun da zai hana ta tureshi, ji take komai ya dawo mata sabo kamar jiya ne ya faru, damuwa da bakin ciki sukayi mata rubdugu a cikin zuciya saidai haduwa

da yayanta

ɗ

an uwanta ya sakata a farin ciki marar misaltuwa, a karshe ta samu wanda zai ciyar da ita halal kafin aurenta da Dr Haroon.

Wuni sukayi a gidan an zanta, an taya juna murna, Alhaji Sadi bai gajiya da godewa su Malam Mamuda ba, "Na gode, na go

de, Allah ya saka maku da alheri, yadda kuke rikeshi da amana kamar dan jikinku Allah ya biyaku da gidan Aljanna. Har gobe har jibi har ranar da abada Yusuf yana nan a matsayin

ɗ

anku."

Malam Mamuda da Mama Nana sunji dadi matuka na wannan karramawa da Alh

aji Sadi yayi masu.

Yusuf ya bisu suka wuce saidai kwana

ɗ

aya yayi ya koma gida yafi sabawa da can saidai zuwa da yake a kullum gaishe da mahaifinsa.

Shikuwa Haidar lakur yayi ajikin mominsa Yana matuqar jin Nauyin Labiba da mahaifinta,gashi basu kai gar

esu ba su sunzo akan wata bukata tasu data biya,Wanda Hakan yasa Yaja bakinsa yai shiru bazai taso da maganar Aurensa da Labiba a gun yadauki shawarar zcyrsa data ce masa gara yabisu har gida,farin cikinsa Daya ganta lafiya qlau saidai zallar tsanarsa Daya

hanga ackn idanunta abin ya firgitashi,take Yaja mahaifiyarsa zuwa gefe Dan su tattauna akan lamarin Yana Neman Mafita da shawarar ta akai....

*****. ******

Haj.Hakima bakin ciki kamar ya kaita kasheta har wani zazzabi-zazzabi tayi tana wa Labiba kallon

kishiyarta ashe akwai wata kishiyar tana zuwa, yadda Alhaji yake nunawa Labiba da Yusuf kulawa ba karamin kona mata rai yake yi ba. Ta ha

ɗ

a tuggu da makirci tayi asiri amma babu riba domin daga Labiba har Yusuf basu wasa da azkar.

Daga tafiya hutu gidans

u Yusuf Labiba tayi zamanta, Alhaji Sadi ya fahimci shine take gudu saidai baice komai ba, dukkanin abin da ya faru shine ya janyowa kansa, ya biyewa son duniya da kyale-kyalenta ya fa

ɗ

a harkar fashi da makami, ya biyewa son zuciya yayi fyade wanda lamari

ya juye akan diyarsa, baiga laifinta ba komai ya faru shine ya janyowa kansa, yaga kokarinta da ta rufa mashi asiri a wajen dan uwanta.

Tunda Labiba ta rabo gidansu taci ta sakayau kamar wacce ake cirewa ƙaya, ta huta da cin haram da saka suturar haram da

takeyi a bisa lalura, tana da labari har yau mahaifinta bai daina fashi ba kuma tana mashi addu'a Allah ya shiryar dashi.

Tana exam lokacin da Yusuf zaije Maiduguri wajen dangin mahaifiyarsu, yaje tare da Dr Haroon. Tunda Labiba ta koma gidan Mama Nana d

a zama abota ta kullu a tsakanin Yusuf da Dr Haroon. Alokacin Soja boy bayanan yabi mahaifiyarsa sun koma Lagos Yana son yabita can na Yan kwanakin kafin yadawo kamar yanda aka tsara inya dawo zaici gaba da yin Aikinsa zai koma bakin daga na fagen aikin So

ja duk wannan bisa taimakon ALH Aminu ne mijin momcy.saida aka gama komai yatafi.

Soyayya ruwan zuma, soyayya sosai take bugawa da ita da masoyinta farin cikinta Dr Haroon, lokaci zuwa lokaci take girki ta aika mashi.

Tare da maryam ake cinye abincin har

tana santi tana yabon gidan abincin da yake siyowa, saidai yayi murmushi kawai, yasan haukan kishin ta na fitina shiyasa ya

ɓ

oye mata har sai abun yayi nisa tukunna.

Yusuf ya gyara gidansu ya mayar dashi babban gida samfurin ginin masu kudi, babu abun da

ahalinsa suka nema suka rasa, Alhaji Aminu ya samar mashi aiki a nan Kano a cewarsa ya zauna ya samu lokaci tare da danginsa idan yaso daga baya ya dawo Legas idan hali ya

bada.

Tunda wayewar garin ranar Yusuf ya sanar da ita abokinsa Dr Haroon yana nan

zuwa zance, har da fa

ɗ

in, "Kuma kiyi mashi kwalliya." Kunya ya bata ta rufe fuska, Mama Nana ta amshi zancen da fa

ɗ

in, "Kada fa a takurawa diyata da magana

ɗ

aya ko kuma in fasa badawa." Ya ha

ɗ

e hannayensa a waje guda yace, "Tuba muke kanmu a kasa." A tare

sukayi dariya, labiba ta dubi yayan nata tace, "Wajen karfe nawa zaizo ne?." Ya ware hannuwa yace, "Ba muyi maganar ba amma dai yace zai kiraki."

Wajen karfe sha biyu na rana saiga kiransa saida ta kusa tsinkewa sannan ta

ɗ

aga, daga

ɗ

aya bangaren yace, "

Ya dai kyakykyawata, ko aji aka tsaya ja min ne har wayar ta kusa tsinkewa." Ta saki siririyar dariya tace, "Kusan haka."

"Amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida kiyi komai ba komai lokacin kine."

Ta dan waro idanu tace, "A'a da wannan don wannan

amma ban da dungurin uwar miji da tabarya, kirarin amarya bakya laifi wannan na amsa amma daga inda aka ce ko kin kashe dan masu gida babu ni a ciki, babu dalili ayi min ingiza mai kantu."

A tare sukayi dariya, da muryarsa dake mata dadi a kunnuwa yace, "

Maganannata.!" Ta murmusa tace, "Na'am maganannena!."(Sunan da suka sawa kansu dashi knn na Raha)

Suka kara dariya, yana matuƙar jin dadin soyayyarsa da Labiba duk yadda Maryam ta

ɓ

ata mashi rai idan ya kira Labiba mintina biyu sunyi yawa zai nemi damuwar

ya rasa a yayinda nishadi da farin ciki yake maye gurbinsa.

Ya kwantar da bayansa da kujera yana jujjuyawa da ita dukkanin takaicin da haushin da Maryam ta kunsa mashi a safiyar yau ya nemeshi ya rasa sai zallar farin ciki, "Ina abokina?" Ya tambaya. Tac

e, "Ya wuce wajen aiki, kafin ya wuce yake fa

ɗ

a min zaka zo har da jaddada min inyi maka kwalliya."

Ya saki murmushi yace, "Alhaji Yusuf kenan, Abokina kuma aminina, Allah dai ya barmu tare." Ta amsa da, "Amin. Yaushe zaka zo?" Ya dan yi jim sannan yace,

"Wajen karfe hudu haka, akwai maganar da nike son muyi."

Tace, "Okay ranka ya dade babu damuwa sai kazo, Allah ya kawoka lafiya." Addu'a da take mashi da kuma girma da take bashi, tsaftarta, iya girki da salon iya maganarta ya saka take ƙara shiga ransa,

a rayuwa ba ya da tsarin auren mace fiye da

ɗ

aya amma halayen Maryam sune suka tilasta mashi kara auren, da ace da Labiba ya fara haduwa da bazai kara sha'awar ƙara aure ba saidai kaddara ta riga fata.

Daga wajen aiki ya biya gida ya caba ado ya kure adak

a fito, Ai maryam tana ganin fitowarsa malolon kishi ya tsaya mata a wuya, kada fa zance zaije, kada fa tana nan tana hauka da yaqin kada ƴan aiki sugane mata miji shi kuma yana can yana neman yi mata sakiyar da ba ruwa.

Tasha gabansa tana fa

ɗ

in, "Ina zak

aje?"fuska ahade

Ya murmusa tare da

ɗ

an kallenta Yana gyara agogon rolex ahannunsa yace, "Gidansu abokina Yusuf." Idanunta a tsaitsaye, muryarta fal kishi da gadara tace, "Wai nikam intambayeka Haroona, shi wannan abokin naka Yusuf din,dan gidan uban waye

wannan din da ban sanshi ba a cikin abokanka, kodai raina min wayo kakeyi ne, Yusra ce ta koma Yusuf."? Jiyayi kamar ya kwada mata Mari,Amma sai ya dake yai jarumta.

Yayi Yar Dariya da basar wa yaja tsaki yace, "Kina min kaxanta a gida, baki san ki zauna

kiyi min girki ba shine har kike tunanin zan zauna dake ke

ɗ

aya, ashe kuwa toshewar basira ta sameki, kishiya babu fashi don haka ki zama a cikin shiri."

"Walh baka isaba,indai Ina Raye Babu macen data Isa ta rabeka,ko ni ko ita walh,saina kasheta,macuci

mayaudari,... Bai Kara ce mata uffan ba ya fice yabarta da cizona yatsa.

yana fitowa yashiga GLK new modern 2025 dinsa ta masa kyau ainun yaja motarsa yafice agidan Yana buga kamshi,aguje me gadi ya Bude masa get Yana daga masa hannu Yana Adawo lafiya ub

angida.

Karshe ta ringa masifa ta qunduma ashar kamar Yana gun karshe dai akan Yan Aiki ta fanshe takaicinta

******

Dr Haroon dai Kai tsaye ya wuce gidansu Labiba yana jin zafin maganganun da Maryam ta yaba mashi, ace mace babu ladabin magana a bakinta

saidai ta saki magana a duk yadda tazo mata abin takaicin ma sunansa da Bata sakayawa take kiransa Haroon gatsala,kamar ba miji gareta ba.

Saida ya shiga ya gaishe da Mama Nana sannan ya fito harabar gidan ya zauna yana tsumayinta babu jimawa ta fito tan

a zuba mashi, yana kallonta tana ƙara kyau, murmushinta yana kara karuwa da kowace dakika ta kusanto wajen da takeyi.

Taja kujera ta zauna opposite dashi, "Ina wuni?" Ta gaishe dashi. Ya amsa da, "Lafiya lau Amaryar Haroon." Ta murmusa kawai, ya dubi warm

er da ta fito dashi yace, "Ke baki gajiya." Ta girgiza kai tace, "A'a idan ban yiwa ƴallabaina girki ba waye zanyi wa." Ji yayi ta burgeshi yace, "Speaking of which ina son in turo magabatana a kawo kudin neman aure." Ta murmusa kawai ba tare da tace komai

ba.

Saidai ya ƙara maimaita mata sannan tace, "Allah ya bamu zaman lafiya." Ya amsa da, "Amin." Bai jima ba sosai ya wuce tareda warmer ta abincin da tayi mashi.

Tunda Haidar ya tashi ya kasa zaune ya kasa tsaye ji yake Kano kawai yake son zuwa ya kuma

rasa dalili, ya kamo hanyar Kano, yana sauka ya hau kekenapep ya fa

ɗ

a mashi adireshin gidansu Yusuf.

Dr Haroon bai jima da tafiya Haidar ya duro gidan kusan tare da Yusuf, Yusuf ya rungume abokin nasa yana murna suka shiga ciki, Haidar ya ware ya zama dan

gida yana ta hira dasu Mama Nana.

Yusuf yace, "Wai ina Labiba?" Shamsiyya tace, "Tana dakinta." Yusuf ya jinjina kai yace, "Kira min ita ta gaida Aminina wanda ta silarsa na samu lafiya na dawo Kano."

Gaban Aliyu ya yanke ya fa

ɗ

i jin sunan da ya kira, y

a kasa hakuri har saida ya tambaya, "Wacece Labiba?" Baisan tana gidan ba. Hankalin Yusuf a kwance yace, "Ƙanwata."

Haidar gabansa ya tsanan faduwa tunanin abubuwa yake da dama.

Tana fitowa idonta akansa jiki na akidime tace" tace, "Haidar." Haidar yac

e, "Labiba."ko amafarki bazai manta face din ta ba haka itanma.amma saita jure ta basar

Mamaki ya cika mutanen dake a falon, Yusuf yace, "Kin sanshi ne."

Tace, "Tsohon mijina ne da muka rabu." Daga haka bata ƙara cewa uffan ba ta juya ta koma ciki.

****

**

A bangaren Dr Haroon lokacin da ya isa gida bata a falo ya ajiye warmer din ya haura sama da nufin ya dawo yaci, tana saukowa ta samu abincin, kishi, bala'i da masifa ne suke cin ta ba ka

ɗ

an ba, amma ganin abincin ya tuna mata yunwa da takeji cikin ran

ta tace, "Kwara inci in koshi in samu karfin zazzaga mashi ta cikina, yayi ka

ɗ

an ya auro wata tazo gidan ta zame min kishiya saidai a mutu."

Ta zauna tana tsakurar abincin, ya sauko ya samu tana zuba loma ya

ɗ

an yi turus yace, "Ikon Allah kince baki son k

ishiya amma ta dafo abinci kin zauna kina ci."

Bata san lokacin da ta furzo na bakinta ba tana sakin ashar da ni kaina bazan iya maimaitawa, da bala'i tace, "Kana nufin dama shegiyar ce take baka abincin kake kawo min ina ci, haba shiyasa shegen abincin b

abu dandano ko kadan, tur."

Dariya ta bashi yace, "Anya kuwa? Idan na tuna daidai da kanki kike cewa a kawo saboda yana maki. Mi ya sauya yabonki zuwa kushe."

Saida ta kara lailayo ashar ta durawa Labiba wacce bata san wainar da ake toyawa ba sannan tace

, "Wannan kuma aikin asiri ne kuma gaskiya ta bayyana, shegen abincin sai karni yake babu dandano babu tsafta."

Ya saki dariya yace, "Zaki ma dawo ne ki fa

ɗ

i gaskiyar tsaftar girkin da dadinsa."

Kishi ya kawo mata wuya ta cigaba da zuba bala'i, a wannan

daren babu wanda ya rumtsa a gidan yadda sukaga rana haka suka dare tana zuba bala'i da masifa.(Tab to inaga Kuma tasan cewar ayau yakai kudin Aurensa da Labiba Wanda har an tsaida lokacin Aure biyu me zuwa.)

Muje zuwa kwarban na gaba akwai cakwakiya fa.

ALHAMDULILLAH. A nan muka kawo karshen book 1.

Shin ya zata kaya a tsakanin Dr Haroon da Maryam? Shin masifar kishin zata samu yayyafi ruwa ko kuwa na fetur zata samu a cigaba da wullo wuta

😅



🤣



😂



😅



Haidar ya bayyana, Itama kuma Labiba Haroon take s

o, shin bangaren wa Yusuf zai goyi baya, Haroon ko kuma Haidar?

Ina labarin Hakima?

Book 2 zaizo da zafinsa, akwai cakwakiya, tuggu da kitimurmura, wuta iya wuta

😅



🤣



😂

kudai ku biyoni domin jin yadda zata kaya

Nabila Aliyu (Nabilancy Love)

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login