Showing 6001 words to 9000 words out of 50822 words
ruwan cikinta a gaban mahaifanta yayi mata
fyade kana ya bawa sauran dama akan suma suzo suyi test
Abin baƙin ciki da takaici tana kuka haka su uku suka hayeta Amma da yake bazata iya aikata musu komai ba tunda sun cimmata jikinta ya saki gashi na farkon yaji mata ciwo sosai, kuka take tana neman
agaji amma Inaa sun kukkulle hannu da kafar mahaifinta sannan sun tokare mahaifiyarta da bindiga haka Hajiya Hakima ta kasa motsawa agun saboda tsoron abinda zasuyi mata don sunce dukkanin wanda ya motsa sai sun tarwatsa kansa da bindiga.
Mamanta ta taho
da gudu tayi kanta bayan sun gama sun fita suna masu yi musu warning akan zasu ƙara dawowa. Mama saude kafin ta ankara, da ta zo ga ƴarta da ta Suma dan tallafa mata ina zuciyarta ce ta buga! Ta tsaya cak! Da Aiki ta Fadi a gun ta sume.
Abu
ɗ
aya Hajiya H
akima ta iya yi, tayi saurin isa gurin firji ta dauko ruwa tazo ta hau shafa musu dukkansu
Labiba ce ta farfado ta hau kuka
Da ta tuna abun da ya faru, ta tashi zaune daƙyar tana hango Mamanta kwance magashiyyan tayi gunta a guje tana kuka tana Jin wani
zuqi a kasanta haka ta
ɗ
aure ta RUNGUME mamanta tana kwalla mata kira a rikice.
"Mamaaa!"
Numfashinta ya dauke, idanunta sun rufe, alamun babu rai a cikinta, ta rasu.
Wayyo Allah, Mahaifiyarta ta rasu a nan take.
Abun da suka fahimta dai wato mahaifi
yar Labiba hadiyar Zuciya tayi saboda baƙin cikin wannan abu, lallai ashe dawowarta bai tsinana mata komai ba sai zuwan ajalinta.
Alhaji sadi kuka kawai yakeyi, don me gadi ya kunce masa kullin da sukayi masa, hankalinsa ya bar jikin tabbas acikin ransa w
ata nadama ce ta shigeshi, yasan da gayya aka yi masa Hakan, wannan wani sirri ne acikin ransa, harma wata zuciyar take ce masa KAI KAJA....
Da alamun akwai wani sirrin dake
ɓ
oye kenan, idan babu rami miye ya kawo rami.
Tofa muje zuwa fans
[01/10, 9:06 p
m]
: *LABIBA*.......
🏵
️
🏵
️
🏵
️
_The Emotional Story_
😰😰😰😰
Na _Nabilancy love_
💘
*Auntyn S and S*
______________________________
🌈🇰
AINUWA
🇼
RITER'S✍
🏼
*
🇦
SSOCIATION
🤝🏻
*
```{Unit
ed we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
______________________________
Page
5 and 6
Labiba ta saketa tana ja da baya tana girgiza yayinda hawaye ya wan
ke fuskarta, tana kuka kamar idanunta zasu fa
ɗ
o, shin mi ya saka aka yi mata haka? Fya
ɗ
e na taron dangi, shin su wa
ɗ
anda sukayi mata basu tunanin zasu haifa, idan ba su da ƴaƴa mata ba zasu rasa ƙanne ko ƴan uwa ba, shin idan aka yi masu kwatankwacin abun
da suka aikata a gareta ya zasuji, shin basuyi tunanin hakan ba a lokacin da suke keta mata haddi? Ko kuma gani sukeyi sunci bulus a wannan baƙin zaluncin da suka aikata mata da yayi sanadin rayuwar mahaifiyarta.
Labiba ta rarrafa ta isa gaban gawar Mama
Saude tana jijjigata tana kuka kamar zata shi
ɗ
e, saboda tsabar kuka lumfashinta har sama-sama yake. Da muryarta wacce ta dusashe saboda tsa
ɓ
ar kuka tace, "Mamaaa ki tashi, Mamana ki tashi, yanzu ne nike da buƙatarki a kusa dani fiye da kowane lokaci, a wan
nan bugiren da na shiga halin rayuwa mai tafiya da farin ciki, na shiga gagari da taskon rayuwa."
Abun ya ha
ɗ
e mata biyu, ga kuka da takeyi kamar idanunta zasu zazzago ƙasa, ga kuma azabar ciwo da ƙasanta yake mata. Kanta ya sara tayi luu, komai ya dauke
mata kamar
ɗ
aukewar ruwan sama.
Hajiya Hakima tayi karfin hali zuba mata ruwa, taja dogon lumfashi ta miƙe zaune tana bin wajen da kallo. Ta fashe da kuka hango gawar Mama Saude, tayi fatan ace mafarki ne saidai kash ba mafarki bane, zahiriyya ce ƙaddarar
rayuwa mai tafiya da farin ciki da walwala.
A dare
ɗ
aya rayuwa ta juye mata daga sama zuwa ƙasa, farin ciki da walwalarta ya tafi, bata tunanin akwai wani abu a nan kusa da zai dawo mata da farin ciki da wannan lamarin ya shafe daga tarihin rayuwarta.
W
annan dare ya zame mata wani irin
ɗ
are da ta rasa sunan da zata kirashi dashi, ba zata ta
ɓ
a mantawa da mummunan abun da ya faru da ita a cikinsa ba. Ina ma itama ta ha
ɗ
iyi zuciya ta mutu, da ta huta da wannan kuncin rayuwa mai dagula lissafi ta rasa mahaif
iyarta da budurcinta a rana
ɗ
aya. Keta mata haddi da aka yi na fya
ɗ
en taron dangi yayi sanadin rayuwar mahaifiyarta.
Wata shari'ar sai a lahira, bata tunanin akwai abun da za'ayi masu da zai shafe tarihin cutarwar da sukayi mata a rayuwa saidai ya rage ma
ta wani bangare na ra
ɗ
a
ɗ
in da ya wanzu a cikin zuciyarta na cewa abun da suka aikata mata basu ci bulus ba.
Saidai shima bata tunanin zata samu, shin ina aka gansu da har maganar hukunci zai biyo baya.
Duk da tsaurin idanun Hajiya amma saida ta tausaya m
ata saidai kash ashe tausayin bai kai har ƙasan zuciyarta ba, tun ba'a je ko'ina ba ta fara wa kanta tufka da warwara, tana sakin kwafa tana ta
ɓ
e baki tana mitar an ishesu da kuka kamar gidan mutuwa. To idan ba gidan mutuwar bane ina ne, ga gawa a kwance a
gabansu.
Har ta iya bu
ɗ
e baki tace, "Idan banda rashin daukar ƙaddara miye na ha
ɗ
iyar zuciya daga faruwar wannan ƙaramin abun, ke kuma kin ishemu da kuka kamar wacce aka aikowa sako uwarta ta mutu."
Labiba ta kafeta da idanu, Shin ta fahimci abun da tak
e furtawa kuwa ko kuma izgilanci ne na idan jifa ta wuce kaina. Idan ba haka ba, tana mace amma tana kiran fya
ɗ
e karamin abu, shin bata da labarin tambari mai girma da yake bari a zuciya da rayuwar wa
ɗ
anda aka aikatamawa, yake tafiyar masu da farin ciki ko
kuma ta sani ne take takewa tunda ba'a kanta jefar ta fa
ɗ
a ba.
Kai duniya, ibtila'in rayuwa ya fa
ɗ
a mata amma maimakon ta nuna mata tausayi sai ta buge da ya
ɓ
a mata maganganu har take iya kallon tsabar idanunta tace tana kuka kamar wacce aka aikowa sako
uwarta ta mutu, ga gawar mahaifiyarta a gabanta amma take iya fa
ɗ
a mata haka.
Har ta iya kiran fya
ɗ
e da karamin abu, koda yake ai duniya ce tafi gabaruwa iya jima, idan har izgilanci akan kuncin wasu halinta ne to kuwa aje a dawo wata rana zata ha
ɗ
u da na
ta kuncin da tasko idan yaso sai mu gani idan zatayi wa kanta izgili da kanta.
Tsaurin idanu da rashin tausayin Hajiya Hakima ba ƙarami bane ba, ta jima tana ganawa Labiba aya a hannu, ta
ɗ
a
ɗ
e tana gana mata azaba a wannan gidan.
TUNANI
Da safiyar wata r
ana ta tashi da matsanancin ciwon ciki da na mara na gabatowar zuwan al'adarta, tana kwance a dakinta tana nukurkusu na azabar ciwon ciki da yake tuƙarta.
Ji take baƙi daya duniyar tana juya mata ta rasa abun da yake mata
ɗ
a
ɗ
i amma hakan bai saka Hajiya H
akima ta tausaya mata ba. Ta bamko kofar dakin tana tujara, "Da kika zo kikayi kwance, waye kike tunanin zaiyi ayyukan gidan nan ni ko kuma mahaifinki?"
Labiba ta
ɗ
aga kai daƙyar ta kalleta tana magana muryarta tana katsewa na azabar ciwo da takeji tace,
"Kiyi.. haƙuri Hajiya.. bani.. da lafiya ne." Hajiya ta ƙarasa shiga
ɗ
akin tana fa
ɗ
in, "Kika ce baki da lafiya? To ƙarewar rashin lafiya ko asibiti baki
ɗ
ayanta ne take a saman kanki sai kinyi ayyukan nan, zaki tashi daga wannan nuƙurƙusun iskanci na lambo
da kikeyi ko kuma sai na laka
ɗ
a maki dukan tsiya idan yaso sai kiyi lambon mai dalili."
Labiba ta
ɗ
aga idanu tana kallonta daƙyar, ƙirar samudawa da matar take dashi idan tayi gigin da ta bari ta
ɗ
aura hannunta a kanta sai
ɗ
an buzunta, don kuwa watakila
saidai a yayyafa mata ruwa a sadata da makwancinta na gaskiya. Ta maida dubanta akan hannuwan Hajiya da sunyi biyun hannuwanta ko ma ukkunsu, maganin kada a yi kada a fara, yadda Abba ba ya gidan idan ta sake Hajiya ta rufeta da duka ko bata kasheta ba sai
ta kusa kaita lahira gwara kanta a likafa ta rarrafa tayi ayyukan, ƙaƙari ba zasu kasheta ba saidai wahalar shima wata rana sai labari, zalunci ba ya
ɗ
aurewa.
Da muryarta da take fita daƙyar tace, "Ba sai kin
ɗ
aura hannuwanki a kaina ba, zanyi, da mi da
miye ne ayyukan?"
Hajiya ta fashe da dariya har da sakin gu
ɗ
a tana fa
ɗ
in, "Kika ce ke ƴar iska ce, ashe rashin kunyar naki bai kai tsaiko ba, ai da kin tsaya yi min gardama in laka
ɗ
a maki dukan tsiya babu mai kwatarki."
Labiba bata bi takan wannan magana
r ba tace, "Ki lissafa min ayyukan inje inyi maki in dawo in kwanta ko na samu cikin ya lafa min ko na samu inci wani abun, rabona da abinci tun daren jiya." Hajiya ta ta
ɓ
e baki, "Masu iya magana suka ce yunwa ba ƙanwar uwa bace ba, ita yunwa bata da hanka
li, ciwon iskanci ne shiyasa har kike maganar kin kasa cin abinci, ni kuwa miye nawa don bakici komai ba, gaba ta kaini abincin gidan ya ƙara auki, mun huta da
ɓ
arnar ciyar da wacce ba'a gani a cikinta."
Labiba bata cikin jerin mata da za'a kira duma-duma
hakazakila ƙaryar mutum ya kushe zubin halittarta haka take zube da zubinta mai kyau, babu kiba sai halittar kugu da nonuwa sa
ɓ
anin Hajiya Hakima da take a tsaye sai shegen tsawo da kauri amma nonuwa da kugu wala haka take tsaye kamar muciya da zani.
Lab
iba tace, "Miye ayyukan da zanyi?" Hajiya ta juya ta fita tana fa
ɗ
in, "Ki sameni a parlour in fa
ɗ
a maki, ni ba gantalalliya bace da zan tsaya ina ta
ɓ
a
ɓ
atu."
Labiba ta miƙe daƙyar tabi bayanta tana tafiya tana ha
ɗ
a hanya ta sameta a parlour ta hakimce ta
ɗ
aura kafa
ɗ
aya akan
ɗ
aya suna gulmar ƙawarsu ta voice chat.
Labiba ta gaji da tsayuwa tace, "Hajiya gani." Hajiya ta dubeta a wulakance tace, "Sai kuma aka ce maki ban ganki bane da zaki tusani a gaba da mita, ina da idanuwa kuma na ganki sarai sai ki ji
ra in gama abun da nikeyi tukunna, sai na gama in lissafa maki kuma karki sake ki zauna min a kujera ki
ɓ
ata shi da jini, koma haraba ki jirani ina zuwa."
Saida ta mula tasha iska ta gama maida yadda aka yi na gulmar da suka kitsa da ƙawayenta wacce ta za
me mata jiki sannan ta fito ta zayyana mata ayyukan da zatayi, "Ki fara min jajjage ƙawayena suna akan hanya." Fitinar gulmar ya tashi kenan.
Labiba tace, "Inyi maki da blender?" Hajiya ta dubeta sororo tace, "Nasan akwai blender nace kiyi min jajjage, da
man katon gidan mai ku
ɗ
i kamar wannan ba za'a rasa blender ba saidai bana blender nike so ba na hannuwa nike so." Ta tsareta da idanu tace, "Ko kina da magana ne?" Labiba tace, "A'a babu wata magana da nike da ita, jajjage da mi zanyi?" Ta tambaya.
Hajiya
ta ta
ɓ
e baki tace, "Idan banda rashin ganewa ace har sai na maimaita maki ayyukan da kika san sun rataya maki a gidan nan, ina ji sai na fara maimaita maki da bulala sannan zaki riƙe ya zauna maki a doron kwanya. Ki share min gida kiyi min wanke-wanke ki
gyara parlour, idan kin gama min ayyukan, ƙarewar ciwon ƙarya idan ma mutuwar ƙarya zakiyi ke ya shafa." Ta juya ta koma
ɗ
aki.
Labiba ta lalla
ɓ
a ta shiga kitchen ta fara da jajjage har ta gama, Hajiya tayi tsaye a kanta ta saka ta tusashi, abun har da gay
ya da zalunci. Ta
ɗ
auki wahala ta
ɗ
aurawa
ɗ
iyar miji ta manta da cewa
ɗ
a da dukiya ba'a masu mugunta. Ita
ɗ
iya mace don kin musguna mata da ayyuka da nufin cutarwa sai kiga idan taje gidan miji hakan ya zame mata tamkar training ke kuma zunubin cutarwa da
kikayi mata yana nan yana bibiyarki.
Daƙyar Labiba ta kai kanta wajen fanfo ta tara bokiti ta fara wanke-wanken mai yawan tsiya kamar na gidan gandu, ko jiya saida Hakima ta tara ƙawayenta sukayi girkin
ɓ
arna da ta saba masu, suna ci suna gulma da zage-za
ge.
Har tausayinsu Labiba takeji yadda suka san surrukan zagi sannan suka mayar dashi kamar wani yaren magana idan suka mutu dashi a bakinsu sai ya kenan. Ta kawar da wannan tunanin ta cigaba da wanke-wanken shima saida ta gama aka sakata ta tusashi, abun
har da gayya domin ya wanku iyakar wankuwa aikuwa kafin ta gamashi ta gaji ainun har wani jiri-jiri take gani, ALLAH ne kawai ya tsareta daga fa
ɗ
uwa ƙasa warwas a lokacin da take mopping, ta jingina da bango tana maida lumfashi.
Hajiya ta leƙo, "Uwar mi
kikeyi a nan ko nufinki idan ƙawayena suka zo sai sun jira kin gama nawa da lalaci sannan su samu matsugunni a falon, zaki cigaba kiyi da jikinki ko kuma sai nayi maki da yaren da zakifi ganewa."
Labiba ta girgiza kai tana jin jiri-jiri yana
ɗ
ebarta tace,
"A'a zanyi." Ta cigaba har ta samu ta ƙarasa ta zauna a harabar gidan tana hutawa, zuwan ƙawayen Hajiya ya dauke mata hankali daga sha'anin Labiba, tsayin hour
ɗ
aya Labiba ta huta sannan ta miƙe ta dasa sharar gidan kafin ta gama ta kusa fita hayyacinta,
ga ciwo ga azabar aiki.
A daddafe ta isa
ɗ
akinta ta kwanta tana nishi sama-sama na azabar baƙar wahala da tasha a hannun wa
ɗ
annan ayyuka, saida tayi barcin wahala, cikin ikon ALLAH ta samu cikin ya lafa tayi wanka ta fa
ɗ
a kitchen domin samun abun da zaka
sakawa kofar salati, ga mamakinta wayam ta samu kitchen babu abincinta babu alamarsa.
Ta samu Hajiya a parlour suna gulmar da suka mayar sana'a sunyi kaca-kaca da falon kamar yara ƙanana, sai kace dabdala aka yi a ciki. Ta tambaya inda abincinta yake, bu
ɗ
ar bakin Hajiya tace, "Mun cinye, kije ki girka da kanki kuma koda wasa kada inji ko in gani kin zuba nama ko kifi a ciki, ke ko kayan miya kada ki ta
ɓ
a, ki dafa fara da mai da yaji shine ya dace dake."
Ji Labiba tayi hawaye sun zubo mata ita da gidan uba
nta amma har ana kafa mata doka akan kada ta zuba nama, kifi ko kayan miya a abinci bayan ga ƙawayen wacce tayi maganar suna ci har da naman kaji a ciki, ga kifi a gefe, ga miya tsagaga. Idan abun na tarbiyya ne da sauki amma wannan tsagwaron zalunci ne da
rashin imani. Ta dafa shinkafa da miya da nama da kifi tana ci da ƙawayenta amma har tana da baƙin fa
ɗ
awa ƴar masu gida kada ta ta
ɓ
a nama, kifi da kayan miya. Anya kuwa tayi wa kanta adalci?
Labiba ta koma kitchen saida ta ha
ɗ
a shayi mai kauri tasha ta z
auna ta huta sannan ta dafa shinkafa fara da mai da yaji domin a zauna a lafiya, ta zuba mai sosai, yajin ya ha
ɗ
u sai yayi mata
ɗ
a
ɗ
i fiye da shinkafa da miya.
Ba wannan ka
ɗ
ai ba, akwai ranar da Labiba bata da lafiya tana zazzabi, tana kwance tana rawar sa
nyi da makerketa, Hajiya ta kwara mata ruwa masu sanyi tana zazzaga mata bala'i da tujara akan ta tashi tayi mata wanke-wanke, wanke-wanken da ta gama a galabaice kenan, ta koma daki ta kwanta.
Da almuru ciwo ya taso mata gadan-gadan saida tayi jinya a as
ibiti, ruwan da Hajiya ta kwarara mata da wanke-wanken da ta tusata gaba tayi ne ya janyo mata.
A wannan bugiren Hajiya Hakima taga bala'i ganin idanunta, tsakar dare Labiba tana kwance daki taji ihun Hajiya, tana ihu tana kururuwa, ta fito daga
ɗ
aki ko k
allabi babu kamar mahaukaciya sabon kamu.
Daƙyar suka samu ta lafa da kururuwar wahala ta koma
ɗ
aki tana zagaye tana wayyo, wayyo kaina amma da yake zuciyarta ta ƙeƙeshe wannan bai zamar mata izina ba da har yau take izgilanci akan damuwar wasu tana maida
fya
ɗ
e na taron dangi ƙaramin abu saboda ba kanta ya faru ba.
....Labiba ta shiga maraici akan maraici, ga maraicin rasa mahaifiyarta, ga ta
ɓ
on fya
ɗ
en da aka yi mata na taron dangi, da azabar matar uba
😭😭😭😭
...
Muje zuwa
[01/10, 9:06 pm]
: *LABIBA*...
....
🏵
️
🏵
️