Showing 24001 words to 27000 words out of 50822 words
Yana jin kanshi Yana taku irin na masu Isa da takama
Ta qura masa ido cikin tsana da kiyayya tana jin tamkar ta zunduma da gudu.
Wani kafirin murmushi ya sakar
mata cikin nuna salo na soyayya ya nemi guri kusa da ita Yana me kama hannun ta Yana fadin"haba my madam ya zaki taho Nan ki kebe ke kadai,meke faruwa ne haka? Ko duk laifin da nai ne na safe da ban tashi da wuri na kawoki ba kike ta fushi Dani,sorry Ina
Neman yafiyarki my wifey,nakasa Nutsuwa plz 4 give me my madam.
Ya tsugunna gabanta guiwa akasa Yana begin ya hade hannaye Yana kallonta cikin wani irin yanayi mai wahalar fassaruwa.
Ta Dan saki ranta tana fadin"tashi ka zauna.
Daurewa ranta tayi tai wan
nan lafazin batason surayya tagano wani abun tunda Taga ita yar fassara ce
Ya zauna dab da ita Yana zuba murmushi
Surayya taji wani haushi da kishi ckn ranta,har ranta tana son gayen Nan haushi da yanda Taga kamar wahalar da kansa yake akanta,Tasha Alwas
hin saita rabasu,saita cure sun zama Abu guda dashi saita Dandani dadinsa inhar me bayarwa ne kai ko baya bayarwa saiya Bata Dadi.taja ajiyar zcy ckn kissa da dauriya tace"kai masoyan Nan Kuna burgeni,Allah ya Kara muku kaunar juna.
Da sauri Haidar yace"A
min surayya,nagode da kokarinki,dole na Baki tukuicin nemar min itan Nan ma da kikai.
Ya zura hannu ckn aljihu ya debo kudin da Baisan yawansu ba ya mika mata.
Da rawar jiki ta karba tana jin wani farin ciki aranta don dama 1k ce kadai a Jakarta gashi ta
na son zuwa joint anjima gashi tana son yin supt dama ba kanta ita Kuma intayi awa guda Bata hau tictok ba jinta take ba lafiya.
Godiya tahau masa tana fadin"in yanzu zaku tafi ma kwa saukeni a hanya.
Labiba ta kalleta tana murmushi tace"to mutafi kawai
tunda antashi ko.
Haidar ya Mike Yana kallonta cikin so da kauna yanajin tamkar ya dauketa Dan ya hutar da ita ganin kamar batajin dadi ko duk yauqi da wulakancin da take masa ne,Amma ganin surayya agun dai ya samu sake.
Dole ya ringa son kasancewar sura
yya agurinsu don ganin sakin fuskar sahibar tasa.
Gurin motar suka koma surayya ta shiga gidan baya shikuma ya shiga gurin tukin driver ita Kuma ta shiga gaban tana fadin "wash!
Da sauri yace"ya dai madam?!
Ta yatsina fuska tace"nifa kaina ke ciwo ga bac
ci da nakeji Dan Allah karka kunna kidan komai a motar Nan.
Ya murmursa yace"Angama,girman ki ne ai abi umarnin ki,sannu ko chemist zamuje ne?
Ta girgiza kai tana fadin"muje gida da nayi bacci zan wartsake ai.
Suna tafe ahanya surayya tana jeho musu Hir
a,shike amsa mata Yana Dan Bata amsa duk son sa ko gwanar zata tsoma musu Baki,Amma tayi musu tsit duk haushi suke Bata.
Taji dadi da sukazo inda surayya zata sauka,suka ajiyeta a gefen titi akusa da wani gidan Mai wai wani zata Jira anan zaizo ya dauketa
zai kaita anguwa.
Sukai sallama yaja motar ya haura titi Yana me kallon labiba Yana fadin"Nifa kawar Nan taki kamar a tictok nake ganinta tana Raye Raye da abubuwansu na Yan social media dai.?
Ta kalleshi ta watsar batai niyyar cewa komai ba Amma don ka
da ya dameta da tambaya sai tace masa"hhuumm kai da kake kallon tictok din kenan,Amma ni da Bai dameni ba,ai banma San tanayi ba.
Ya meleye Baki Yana fadin"To ai shikenan.
Sun karasa gida yai hon me gadin ya Bude musu ya gangara parking lot Yana tsaida m
otar tayi kokarin fitowa daga ciki da zafin nama yaiwa motar lock.
Taja taji murfin motar yaqi buduwa saita juyo ta kalleshi fuska a cukule tana turo Baki tace"Ni ka Bude min walh bani da lokacinka.
Ya rike hannayenta duka Yana fadin"walh karya kike,nasa
n rashin Shan romanki da banyiba ne yasa kika rainani,kike min kallon ban Isa ba ko?to walh ki shirya bani hakkina Babu ruwana da fadanki akaina...
Cikin tsiwa da fada tace"Allah ya tsareni,walh Babu ni Babu kai,na baya ma da ka kusanceni Allah ya isana,a
yanxu nake nadama da ganin bakinka,mutum mara kishin kai,mutum mara Imani irinka Bai cancanci zama da macen kwarai ba walh....
Ya rintse idonsa Yana jin qunar abinda take yab'a masa.
Ya gaji da muggan kalamanta agareshi wai ko ta manta ta gefe guda aiki
nsu Daya da mahaifinta halinsu guda Shima ya aikatawa 'yar wasu abnda yai matan? Son kanta yai mata yawa dole ya dau mataki akanta dole ya hukuntata da tsauraran kalamai don kawo togaciya akan wannan fadan na ba gaira ba dalili.....
Muje zuwa.
[01/10, 9:
08 pm]
: *LABIBA*.......
🏵
️
🏵
️
🏵
️
_The Emotional Story_
😰😰😰😰
Na _Nabilancy love_
💘
*Auntyn S and S*
______________________________
🌈🇰
AINUWA
🇼
RITER'S✍
🏼
*
🇦
SSOCIATION
🤝🏻
*
```{
United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
______________________________
Page
17 and 18
Dukkanin wannan abun da yake faruwa Labiba tana a daki tana ku
ka, tana duniya tayi mata zafi, tana ji ta tsani zamanta a wannan gidan tare da wannan
ɗ
an fashin saidai idan ta bar ina zata ce dukkanin inda taje da kukanta kamar ta fallasa asirin mahaifinta ne, za'ayi tur da Allah wadai dashi ya zama abun yamudidi itam
a ba zata tsira ba ai diyarsa ce kuma mutanenmu na yau sun dauki dabi'ar
ɗ
aura laifin wani akan wani sun manta da cewa ba'a gadon hali.
Ji tayi baki
ɗ
aya garin Kano ya fita daga kanta tana son tayi nisa daga garesu, Haidar ya lalata mata rayuwa ta hanyar
ɗ
aukar fansa akan mahaifinta da kuma shi kanshi mahaifinta wanda ya duba gobensa ba, bai duba haramci na zaluntar mutane ba ya dauki sana'ar fashi da makami ya
ɗ
aurawa kansa akan kudin da a duniya aka samesu a nan kuma za'a barsu, lahira itace matabbata.
Ina zata saka kanta?
Ubanta mahaifi
ɗ
an fashi mai fya
ɗ
e sannan shima mijin da ta aura shima
ɗ
an fashi da makami kuma mai fya
ɗ
e, mazinaci.
Ji tayi kanta ya fara sara mata, ta
ɗ
an kwanta koda zata samu sassauci na damuwar da take damunta, ciwon kanta ya sa
uka saidai damuwar tana nan a zuciyarta, abu ne mai wahalar mantawa ga wanda ya faru dashi musamman ita da abun ya ha
ɗ
e mata biyu, uba
ɗ
an fashi miji ma
ɗ
an fashi, mahaifiyarta da take kallo tana jin sanyi a ranta wannan mugun
ɗ
an fashin ya janyo tsinkewar
Numfashinta.
Idan ta koma gidan mahaifinta babu abun da zata tarar sai bakin ciki da tashin hankali, idan har zata ga mahaifinta sai ta tuna dashi
ɗ
an fashi ne kuma fya
ɗ
e yayi aka zo aka yi ramuwar gayya a kanta, ai wannan gidan ya fiye mata koma gidan A
bbanta wanda haj. Hakima kawai ta isheta, gwara nan Soja Boy ne idan ya fa
ɗ
a mata ciwo daidai take da fa
ɗ
a mashi magani, yace Cas tace As.
Dama tsoronta
ɗ
aya dashi kada ace mai duka ne amma tunda ta lura a cikin rashin imaninsa babu dukan mace ta saka a r
anta ba zata bari bakin cikinsa ya kaita kushewa ba saidai ayi ta zuba bala'i an
ɗ
a
ɗ
e ba'a shekara ana tijara, ita aka cuta ya rufeta da halinsa da gaskiyarsa asalinsa ta aureshi auren da take nadamar yarda dashi da tayi, da tasan abun da zai faru kenan da
ba ta yarda da aurensa ba amma Allah shine masanin daidai watakila akwai alherin da ita bata hango ba. Idan jarabawarta ce tazo mata a haka na auren wannan
ɗ
an fashi zata amsa da hannu biyu domin ta sani Allah yana sane da ita.
Ji take kamar tayi tsuntsu
wa daga Kano ta ganta a Maiduguri wajen dangin mahaifiyarta a can zata samu sauki da sassauci na wannan abun da yake damunta a zuci, jinjina kai tayi ta kai hannu ta share hawayen da suka zubo mata, ta lumshe idanu sauran hawayen da suka maƙale a gurbin id
anunta suka samu damar fitowa, shima zuwan Maiduguri kamar da wuya, ba zata fita daga gidan ba tareda izininsa ba domin ba'a gyara
ɓ
arna da
ɓ
arna kuma ta sani bazai ta
ɓ
a lamunce mata ta tafi ba, watakila dama wata hidimar ce ta taso na can idan ta lalla
ɓ
as
hi watakila ta samu ya yarda ya barta ta tafi duk da shima bata da tabbas.
Ba wannan ba koda ya barta ta tafi din ko kuma ta biyewa zuciya ta gudu shin lamarin Ustaz Haroon fa, tana jinsa a ranta, kai an cuceta da ta kori mutum kamili mai kamun kai mai il
imin addini wanda yake da ilimi na abun da addinin Musulunci ya koyar na zamantakewar aure, auren namiji mai ilimin addini babban dace ne a wajen mace domin yana da ilimi da sani akan yadda addini ya koyar da zamantakewar aure amma ina amfanin auren
ɗ
an fa
shi wanda babu abun da ya sani sai zafin zuciya da sha'awarta da take damunsa, da wannan ta rushe maganar zuwa Maiduguri.
Amma dai kam ya kamata ta fesar da abun da yake a zuciyarta ko ta samu sassauci na damuwar dake cinta a zuciya, da haka ta bu
ɗ
e jakar
ta da ta dawo da ita daga makaranta ta lalubo numbar Auntynta salima (Yagana) ta Maiduguri da nufin ta sanar da ita halin da take a ciki, ƙanwar mahaifiyarta ce kuma gwaggonta, uwa take a wajenta, zata fahimceta kuma zata bata shawara na abun da ya dace ta
yi, aikin mai shawara ba ya kwa
ɓ
ewa.
Saidai kira na shiga zuciyarta ta karye kuka yana neman yaci karfinta tayi saurin mayar dashi ta daidaita nutsuwarta tace, "Assalamu Alaikum, Barka da dare Aunty, ya Maiduguri, Aunty nice Labiba daga Kano."
Ta
ɗ
aya ba
ngaren Aunty Salima tayi dariya tace, "Ɗiyata Labiba shine har da wannan dogon bayani, ai ni ina da numbarki kuma kina magana na
ɗ
auki murya, wace ni in manta da muryar
ɗ
iyata."
Kaunar da dangin mahaifiyarta suke nuna mata ta daban ce, shiyasa take nadama
r rashin amincewar mahaifinta akan ta bisu, da rikonta ya koma hannunsu da duk haka bata faru ba, kakanta babban malami ne, ƴaƴansa duka suna da ilimi da sani akan addinin musulunci, bata da abun da za'a goranta mata a can, amma a nan Kano kam idan da za'a
yi terere na halin mahaifinta da mijinta ai ko kofar gida bata isa ta leƙa ba.
Tayi nufin sanar da ita zuwanta Maiduguri ko kuma ta fa
ɗ
a mata damuwar da take damunta saidai lokaci guda komai ya kwance mata, kuka yaci karfinta ta fashe mata da kuka tana ma
i jin kewarsu, tana kewar dangin mahaifiyarta mutanen Maiduguri, nisa yayi mata togaciya da zuwa wajensu.
Hankalin Aunty Salima ya tashi tana tambayarta abun da ya faru duk a tunaninta ko wani ne ya mutu.
Ji tayi bakinta yayi mata nauyi akan fa
ɗ
a mata da
muwarta, sai kawai tace, "Bani da lafiya ne," (ta yi ƙarya.)
Daga
ɗ
aya bangaren Aunty Salima tace, "Kuma gashi munyi nisa, ina mijinki ne?"
"Ya fita, ba ya nan," Ta fa
ɗ
a muryar kuka.
Aunty Salima tace, "To ina zuwa bari in kira mahaifinki in fa
ɗ
a mashi
tunda kuna kusa."
Ji take kamar ta dakatar da ita daga kiran Abba, babu abun da kiransa zai janyo mata sai damuwa ƙarƙari yace zaizo ko kuma ya aiko haj.Hakima wanda kowane a ciki damuwa ce da bakin ciki zasu ziyarceta, babu na gwara ballantana tace gwara
wannan da wannan.(duk da ba taba zuwar mata tayi ba ma)
Amma ya ta iya tunda Aunty Salima tace zata kirashi dole ta bari a kira tunda ba gardama zata tsaya tana yi da ita ba.
Aunty Salima tana tsinke kiran Labiba ta lalubo numbar Alhaji Sadi ta kira, su
n gaisa a mutunce cike da girmama juna. Kafin ta fa
ɗ
a mashi dalilin kiran.
"Munyi waya da Labiba tana kuka tace min bata da lafiya, kaji halin da take jiki kuma daga ji kamar jikin yana damunta har muryarta kanshi ya nuna, na tambaya tace mijin nata ba ya
nan."
Hankalin Alhaji Sadi ya tashi jin diyarsa kwaya
ɗ
aya tilo bata da lafiya har ya kai tana kuka, Labiba da ya sani da
ɗ
auriyar ciwo, abun da ya sakata kuka ba ƙarami bane ba
"Kuma bata kira ba, amma bara in kira mijinta inji idan yayi nisa ne sosai
sai inje in dubata idan ta kama sai a kaita asibiti, ba'a zauna da ciwo a gida ba. Ban san bata lafiyar ba tunda bata kira ba, dana sani ko Hajiya ce sai in aika ta rakata asibiti."
Aunty Salima tace, "Hakane."
Daga haka sukayi sallama tana mamakin dalil
in da ya saka Labiba ta za
ɓ
i kiranta akan kiranta mahaifinta da suke a gari
ɗ
aya, anya kuwa babu wani abun, kai akwai abun da yake damun yarinyar amma zata bari sai zuwa nan gaba ta tuntu
ɓ
eta cikin hikima, tausayi yarinyar take bata, rashin uwa babban ciwo
ne musamman a kanta da ya kasance bata da wani
ɗ
an uwa.
*****
A bangare Alhaji Sadi numbar H.D SOJA BOY ya lalubo har zai kira sai kuma ya fasa, ya maida akalar kiran zuwa numbar Labiba saidai har ta karaci tsuwwa kiran ya tsinke bata
ɗ
aga ba, tana gan
in kiran ta share, haushinta takeji tana ji dama ita ba diyarsa bace ba, kira ukku yayi mata bata
ɗ
aga ba, hankalinsa ya tashi ya tura mata tes message.
_Ina kika kai wayar ina kira baki
ɗ
aga ba, gwaggonki ta kira ta fa
ɗ
a min baki da lafiya, miye yake dam
unki? Ina mijin naki yake? Yayi nisa ne ko kuma ya
ɗ
an fita ne? Ko inzo ne a kaiki asibiti_
Sau ukku tana maimaita karanta sakon duk ya nuna cewa ya damu da ita da halin da take ciki amma wannan bai goge ta
ɓ
on da ya dasa mata a zuciya ba na sirrin da ya
ɓ
oye na sana'arsa ta fashi da makami, kenan tunda ta tashi haram take ci har girmanta gashi yanzu ma tazo gidan miji tana cigaba da cin haramun koda yake bata da yadda zatayi ne amma zatayi ƙoƙari na nemi abun yi domin gujewa kanta kokonto.
Har ta ajiye wa
yar ta share dashi sai kuma ta sauya shawara gwara ta tura mashi sako ko ya rabu da ita da kiransa da babu abun da yake taso mata dashi sai bakin ciki da damuwa da nadama da kasancewarta tsatsonsa, ta tabbata banda ya rufi mahaifiyarta da ba zata yarda ta
aureshi da wannan kazamin halin ba.
_Ba ni da lafiya ne, bazan iya
ɗ
aga wayar ba shiyasa _A'a ba sai kazo ba, ba nisa yayi ba, ba zai
ɗ
a
ɗ
e ba zai dawo sai ya siyo min maganin_
Duk ya karanta sakonta amma hankalinsa bai kwanta ba, ya lalubo numbar H.D SOJ
A BOY ya kira.
******
Haidar Soja Boy ya fito daga wanka zaiyi shirin tafiya watsewar da zaiyi da Surayya a green place yaga kiran Alhaji Sadi, yayi wa wayar kallon raini kamar dai Alhaji Sadi ne a gabansa baiyi yunkurin maida kiran ba ya cigaba da shiry
awarsa na kitsa yadda masha'arsu zata kasance da Surayya.
Kira ya ƙara shigowa ya duba yaga Alhaji Sadi ne still amma maimakon ya
ɗ
aga sai ya mayar da wayar silent, abun da Labiba 'yarsa tayi mashi ya saka har Alhaji Sadin haushi yake bashi bugu da ƙari
tunawa da yayi da Fatima da abun da Alhaji Sadin yayi mata ya saka yake ƙara jin haushinsa, ko kiran miye yake mashi bazai
ɗ
aga ba, daidai yake dashi daga shi har diyar tasa mai taurin kai, abun da take hanashi din gashi nan zaije ya samu a wani wajen. (To
ai H.D ba'a gyara
ɓ
arna da wata
ɓ
arnar, haram haram ce duk yadda aka yi ƙoƙarin langwasashi).
Text message ya turo mashi;
_Ina ta kiranka matarka ce babu lafiya kuma tace baka gida, kana ina? Idan kana kusa kaje ka dubata bata da lafiya_
A lokacin ya g
ama shirinsa ne tsaf, ya karanta amma bai bashi amsa ba, ya kalli sakon kawai ya gogeshi yayiwa kansa wankan turare,danshi mutum ne ma,abocin son qamshi,kan mirro dinsa turare ne fal designer's kala daban daban ga lotion shima masu qamshi masu tafe da show
er gel dinsu,saida ya tabbatar da gamsuwar shirinsa ya fito fes ya murmusa Yana ajiye Dan karamin kum din Daya taje sumar kansa da tayi luf!Tasha gyara tayi wani Shar Baki sidik tana shining.
ya fito har ya wuce sai kuma ya dawo da baya yatsa daf da kofa
r dakin nata yana kallon kofar bedroom din yakai hannu ya rike handle din kofar yai kamar zai Bude ya shiga don ya gantan,sai kawai ya fasa ya
ɗ
auki hanya yyi waje. tunawa da abun da tayi masa yasa yaji baya son ganinta a wannan lokacin,ba ruwansa da wani
rashin lfyrta,gara ya fito mata da halinsa ya