Showing 21001 words to 24000 words out of 50822 words

Chapter 8 - LABIBA Complete

/>
Kamshinsa ya fara yi mata sallama kafin muryarsa a yayinda yayi mata sallama, ta amsa da murya marar sauti, ya

zauna a gefen gadon ya janye lullu

ɓ

i da aka yi mata, tayi kasa da kai tana jin kunyarsa matsananciya.

Kamshinta ya tafi dashi ya tura kansa a gefen wuyanta yana shakar kamshi mai

ɗ

an karen

ɗ

a

ɗ

i na mutanen Maiduguri, ya susuce. Da hanzari taja da baya gaba

nta yana dukan ukku-ukku, ya

ɗ

an yi murmushi yace, "Uhmm muyi sallah."

A wannan daren taga kulawa da tarairaya a wajensa, salo ne da yanayi mai tsayawa a rai, a jikinsa tayi barci.

Washegari tun da safe ta shiga kitchen tayi girkin breakfast, a kunya ce

ta tayar dashi bayan da ta kammala komai. Ya bu

ɗ

e idanu ya kafeta da wani salon kallo mai kashe jiki, "Kin tashi lafiya?"

Tayi kasa da kanta murya kasa-kasa tace, "Lafiya lau."

"Miye?"

"Na gama ha

ɗ

a breakfast ka tashi kayi wanka muci."

Ta miƙe ya kamot

a, "Miye kunya ake ji ne." Ba ta ce komai ba sai murmushi da tayi.

Bayan sun gama breakfast ya fita ta shiga bedroom dinsa tana gyarawa taci karo da wani ƙaramin littafi mai kama da diary, tana bu

ɗ

ewa taga diary dinsa, sai ta samu kanta da zaunawa tana ka

rantawa duk da a sakaye da

ɓ

adda yare yake rubutawa amma ta gane yaren.

Abun da ya bata mamaki da tu'ajjibu shine labarinsa da ya bata yasha banban da abun da ta gani, illai kuma ashe fashin da yazo gidansu ba fashi bane kawai, ramuwar gayya ne, lamarin d

a ya burkita mata lissafi, a rana tsake tana ganin abun da yake nuna mata mahaifinta

ɗ

an fashi da makami ne.

Abun ya doketa, Aliyu da take ganin aurenta zai saka ya shiryu ashe rufeta yayi, ba Aliyu bane, H.D SOJA BOY ne, HAIDAR SOJA BOY ne, wannan yankan

baya da wani suna zata kirashi, shock ya hanata kukan hawaye saidai na zuci a yanayin da ake lugude a cikin zuciyarta da kwanyarta.

Tana ji tamkar ta kwala ihu da dukkanin karfinta, tayi zaman ƴan bori a parlour tana jiran ya fito taji ba'asi. Ƙarar bu

ɗ

e

get ne ya sanar da ita dawowarsa ta miƙe zumbur idanunta akan kofa hawaye suna zuba daga idanunta.

Da fara'arsa ya shigo yayi turus ganin sauyawar yanayinta daga yadda ya barta kafin fitarsa, ya kama hannunta da kulawa yace, "Miye yake damun Matar Oga in

magance mata?" Ta kafeshi da idanu tace, "Idan na fa

ɗ

a maka zaka magance min."

"Eh Labiba ki fa

ɗ

a min, yanzu kiga aiki da cikawa."

Tayi murmushi mai ciwo tace, "Haidar SOJA BOY ne yake damuna, nace H.D SOJA BOY ne ya yaudareni."

Aiki ya kwana, ji yayi

zufa ta fara karyo mashi yana mamakin a inda taji sunan, ta fizge hannunta ta jefeshi da diary din tace, "Ashe ƙarya kayi min, ka fa

ɗ

a man akasin abun da yake gaskiya, ban sani ba an rufeni na auri

ɗ

an ta'adda

ɗ

an fashi da makami."

Ya matsa kusa da ita ya

na kiran sunanta, "Labiba!." Ya ƙara da cewa, "Let talk, I can explain." Ta fusata tayi ihu tana ball da filon kujera dake kusa da kafarta tace, "Explain what? Talk about what? Ashe zuwanki gidanmu ramuwar gayya ne, ka kashe min Ummata domin ka dauki fansa

na mutuwar budurwarka da Abbana ya haddasa. Kayi min fya

ɗ

e ka saboda ramuwar gayya na fya

ɗ

e da Abbana yayi wa Fatimarka har ta mutu, uhmm, ashe raina kin wayo aka yi."

"Please Labiba ki saurara mu tattauna mu samu daidaito."

Ta daka mashi tsawa tace, "W

ani daidaito kake magana, har kana iya furta min daidaito, babu laifin Ummana dani akan abun da shi yayi maka, mi ya saka ramuwar gayyar ya sauka a kanmu. Da kace daidaito Ummana da ka kashe zaka maido min, ko kuma fya

ɗ

e da ka saka yaranka sukayi min da ka

i da damuwar da kuka saka min zaka kwashe. Ai saidai magana ta fatar baki amma wanda aka cuta an riga an cuceshi."

Ta buga tsaki ta ƙara da cewa, "Sai nayi magana kace you can explain let talk, bayanin ƙarya da gaskiya ko? An shani na warke babu abun da z

ai fito daga bakinka da zan yarda dashi. Kana yi kamar na gari ashe mage ce mai kwanciyar

ɗ

aukar rai, da na tambaya kace Aliyu ashe H.D HAIDAR SOJA BOY ne, ashe

ɗ

an fashi ne

ɗ

an ta'adda... Zan zauna a gidan nan ne kawai saboda bazan iya komawa gidanmu ba,

zuwana Maiduguri kuma tamkar tonon asiri ne ni kuma bazan tonawa kowa asiri ba, amma da ni da kai ta ƙare, ka gama ganin fara'ata, bana son ganin fuskarka na tsaneka, naji ina nadamar yarda da nayi na aureka tun asalin farko."

Ta juya ta koma daki ta murz

a makulli tana ji yana kwankwasawa tayi burus har ya gaji da jera mata magiya ya tafi.

Tun daga ranar suka fara takon saka a gidan, bata bari su ha

ɗ

u, sai ya fita take fitowa tayi girki, ko rutsata yayi bata saurara mashi, tsanarshi ta kamata, bata son ga

ninsa, makashin Ummarta.

Wata rana tana tsaka da girki ya rutsata ta

ɗ

auka zai da

ɗ

e, saidai bai jima ba ya dawo da wuri ta kashe girkin ta koma

ɗ

aki, ta gwammace kwanan yunwa ya fiye mata ha

ɗ

uwa da makashin Ummarta.

Damuwa tayi mata yawa, komawarta makar

anta ya rage mata yawan zama gidan, sai kuma ya tsiri binta makaranta tunda ba zata yarda su ha

ɗ

u a gida ba, sun fito daga lectures taji karo dashi jingine da motarta, kallo

ɗ

aya tayi mashi ta watsar, sa'arsa

ɗ

aya tana tare dasu Aysher, da ta gwammace ta k

oma inda ta fito har ya gaji da jira yasan inda dare yayi mashi.

Ta ƙaƙaro murmushi da iyakarsa akan fuskarta ne tace, "Sannu da zuwa." Ya kama hannunta hannunta yace, "Nayi kewarki." Ya janyota jikinsa yana sauke ajiyar zuciya, jinta take kamar wacce aka

jona akan garwashi.

Aysher ta gaishe dashi daga nan ta shige mota ta barsu, amma Surayya ƴar neman wajen zama tana nanuke dasu tana shige mashi tana faman kiransa take 'Yayana'

Labiba ji take kamar ta zunduma ihu ta lura da Surayya irin ƴan kwacen mijin

ne, koda yake miye zai dameta, indai H.D SOJA BOY ne gashi gata ya isheta riga da zani har da fallen yafawa.

Ji tayi yace, "Muje."

"A'a a motata fa."

"Ki barta za'a maida maki."

Ba don ranta yaso ba tayi wa su Aysher sallama ta bishi, ganin ya dauki h

anyar gidansu ta murtuƙe fuska tace, "Kada kayi wannan gangancin kafata na dura a gidan ubana saidai kayana su biyoni idan kana ji wasa nike ka kwatanta ka gani."

Da wannan ya sauya hanya zuwa gidanshi, yana parking mota tayi nufin fita ya rufe motar yana

mata magiya akan ta saurareshi, "Please muyi magana." Tayi relaxing akan kujera ta lumshe idanu, taji lumfashinsa kusa da wuyanta, idanunta a rufe tace, "Ko abun da kayi min a ranar da muka fara ha

ɗ

uwa zaka maimaita min a nan."

Maganar ta shige, ya bu

ɗ

e

lock da ya saka motar yace, "Zaki iya tafiya." Ta bu

ɗ

e idanu ta fita, ta shige dakinta ta murza makulli.

Tun daga ranar da ya rutsata ta fasa girkin ta kwana da yunwa ta tantance wahala, tun daga ranar koyi dakewa miye zai saka ta cuci kanta akan wanda ya

cutar da ita.

Zuwa yanzu idan H.D SOJA BOY ya ƙure mata bata

ɓ

uya, dakewa takeyi tana zuba mashi na mujiya kawai, idan zai shekara yana magana ba zata ce mashi ci kanka ba, saidai ta zuba mashi idanu tana zargin zuciyarta da ta kasa yakice sauran

ɓ

ur

ɓ

ush

in sonsa da ya rage mata a zuciya.

A wajen course mate dinta take samun labarin wani sabon lecturer Dr. Haroon, kyakykyawa mai kamun kai, bata damu da sanin waye ba saidai hirarsa da surayya takeyi mata yana tado mata mikin dake binne a zuciyarta, yana tu

na mata da Ustaz Haroon, tana ji dama bata yarda da auren wannan

ɗ

an fashi da makamin ba.

Ranar bikin yaye dalibai, tunda suka isa makaranta Surayya take fa

ɗ

a mata zata nuna mata Dr. Haroon, bata tankata ba ta samu kujera ta zauna ta maida hankalinta akan

wayarta, har an kusa gamawa baizo ba, tana ji Surayya tana jaje.

Babu zato babu tsammani sai gashi yadda Surayya tayi mata maganar saida ta kusa razana tace, "Please bini a sannu, ban tuna munyi dake ina son ganinsa ba..." sauran maganar ta makale mata a

makoshi a sanadin tozali dashi, ta waro idanu waje.

SHIN WAYE TA GANI?

MUJE ZUWA

[01/10, 9:08 pm]

: *LABIBA*.......



🏵



🏵



🏵



_The Emotional Story_



😰😰😰😰





Na _Nabilancy love_

💘

*Aunt

yn S and S*

______________________________

🌈🇰

AINUWA

🇼

RITER'S✍

🏼

*

🇦

SSOCIATION

🤝🏻

*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________

___________



Page

15

and 16

Ido Labiba ta Kura masa tana tantamar shine ko ba shine ba.

Take ta hau murza idanunta tana kokarin mikewa tsaye bakinta na motsawa ahankali ta furta..Uztaz Haroon!!!

Surayya Taga rikicewarta haka zalika Taga yanda bakinta

ya furta sunan Haroon a saboda suna kusa da kusa sai tayiwa canjin yanayin labibar fassara tunda batasan meke akwai atsakanin Haroon da labibar ba.

Murmusawa tayi tana me kama hannun labiba tana fadin"zauna kawata! Zauna ki samu nutsuwa,nima aranar Dana

fara ganinsa rikicewar nayi fiye da taki ma,Kinga ke kina da Aure dole ki sawa zuciyarki salama inta kamu ki tausheta,nima da nake son sa Hakurkurtarta nake Dan gurin ba Wajen wargi bane,sam bashi bada fuska ga kowacce mace a ckn sch dinnan duk kwantar da

kaina gareshi nakasa samun gurbi agunsa.

Labiba takalli surayya cikin takaici tace"karkiyi min fassara akansa surayya,canjin yanayin da kika gani atare dani akansa kamanni ne yaimin da Wanda nasani,Dan haka koma meye kikeji akansa wannan ke ta Shafa,kinsa

n inada Aure,Kuma ko banida Aure ni namiji irin wannan Bai D'ad'ani da kasa ba,bare wannan da Bai kai.... "Kai haba Dakata da fadin haka!! Surayya ta katsewa labiba hanzarin maganar da Bata karasa ba.

Surayya taci gaba da fadin"gaye har wannan tsulele da

shi kice baikai ba,? Haba gyara kalamanki yarinya wannan hadaden gaye dai fari kawai mijinki yafishi Amma kyau iya kyau Dr Haroon yakai inkinji ana fadin Bakin balarabe to shine larabci tamkar zubar shayi....

Kabbarar da akai agun da tafi da aka dauka ne

ya katse surayya da zubar gadon da takeyi.

Dr Haroon Yana me kai karshen maganarsa da Jan Aya da yayi bayan Dan guntun lokaci na mintina Daya dauka atakaice yayi Wa,azi da nasiha ga daliban da aka yaye 'yan gaban su Labiba na bangaren Arabic da sukai gra

duation me CAPACITY Dan guri yayi guri MANYAN Baki sun bayyana ta koina haka zalika dalibai sun hadu kaf na cikin sch din kwansu da kwarkwatarsu har Wanda suka fita ba dadewa sun zozzo.

Ba Dan dai Dr din ya gabatar da kansa a bayaninsa da Labiba taji ba d

a tabbas zatace bashi bane,sbd yanda ya Kara kyau ga wata Kamala data sake rufuwa akansa,da alamun Kuma ya Kara samun kudi a lamuransa,shigar dayai ta burgeta jallabiya ce me hade da wandonta, milk colour ce me aiki agaban rigar har kasa ga hirami Daya na

de kansa dashi fuskarsa dauke da glass siriri sai agogon Rado dake daure a tsintsiyar hannunsa Shima fatarsa milk ce.

Ya koma ya zauna a mazaunin da malamai masu capacity suke zaune wanda ake ji dasu acikin Sch din ankawata gurin an Saka VIP section tare

da MANYAN kujeru akusa data MANYAN Baki.

Labiba kasa sakat tayi agun,ta nemi nutsuwarta ta rasa,duk ta sukurkurce tanajin inama zata samu damar kebewa da Dr Haroon ta fashe masa da kuka ta gaya masa damuwarta koya rarrasheta ya Bata Baki ko zcyrta tayi sa

nyi.

Sulalewa tayi ta bar gurin Bata yarda surayya ta biyotaba Dan hankalinta ma na can tana kallon ana bawa dalibai kyauta, ta fice agun.

Can bayan capteria ta bayan classes da aka ware aka kawata gurin akai gurin shakatawa an zuxxuba kujeru farare agun

taje ta nemi guda daga cikin kujerun ta zauna tana fidda ajiyar zuciya.

Tabbas ganin Dr Haroon ya tada mata daddad'an Miki, sai taji inama Kaddarar Haidar Bata hau kantaba,tabbas sai yanzu ta yadda da cewa ma ashe So Daya tak! Dr Haroon takewa dama!

Soy

ayyar dole ce ashe takewa Haidar, soyayyar da a yanzu take me nadamar nuna masa da sauri da tayi na accept tun a fari..

Da tayi shiru tana nazari da tunanin baya sai Taga ai soyayyar Neman Mafita ce ashe ba ta Allah da Annabi ba.

Lokaci yayi daya kamata

ta bijire tayi bore akan rabuwa da Haidar bazata ci gaba da zama da Wanda baisan Annabi ya faku ba,makashin mamanta tabbas kallon da zatai ta masa kenan Rabuwarsu itace Mafi masalaha....zuciyarta ce ta tuno mata da zaman qunci da rashin 'yancin da tayi ag

idan mahaifinta.

Saita runtse idonta tana wani irin Nishi me kama da bukatuwar sunkuto katon Kashi a masai.

wani Abu ne takeji Wanda ya kime mata aciki take son Kuma ta turoshi ya fito ko ta iskar tusa ce ko Hakan zai Saka taji sararin dadi acikin Ciki

nta.

Zcyrta ce tahau mata tuni da tsawatarwa akan cewar"Ke labiba kada ki sake ki kashe Auren Nan na Rufin asiri da kikai,tabbas zamanki gaban Mahaifinki fa ba dadi bane kema kinsani,don kuwa a yanzu yanda Hajiya hakima ta Kara jin haushinki na ganin kin

samu cigaba to inkika koma gidan zakiyi nadama marar Amfani,za kuma ki gasu ahannunta fiye da baya.

Kanta ne ya Sara mata,taji tana jin wani irin Jiri daga zaunen da take.

Ta dafe kanta tana kiran sunan Allah.

Adduar datake ta karantowa ne cikin zcyrt y

asa ta fara jin wani Nutsuwa tana shigarta.

Bayan tsahon wani lokaci tana gurin Bata San iya adadin mintinan data kwashe agun ba, ba,a haiyacin ta ba,har aka tashi a Taron nan

Acan surayya tana ta nemanta don H.D Soja boy ne yazo yaji wayarta akashe gash

i yaga batazo da MOTA ba ta barta agida tayarta ta gaba ta sace da kansa ya gyara mata yasaka mata wata tayar kana yaje gdn Mai yasha Mai me yawa don yaga na ciki yai kasa.

Dama baiga fitarta ta ba yanatason ya kaita sch don yasamu kebewa da ita sui magan

a,sai dubawa yayi yaga harta fice,don ya burgeta yai mata wannan lamarin sai gashi Kuma yazo sch ba,a gantaba.

Yana jingine jikin motar tata dayazo da ita sch din yaji surayya na ce masa"bari naje can capteria na duba maka ita ko can taje don mutuniyar ta

ka Bata son hayaniya da damu zata iya guduwa can din.

Ya gyada mata kai Yana fadin"okay tank you.

Ta farfara idanunta da sukasha eye lashesh ta juya ta fara tafiya tana kad'a mazaunanta masu Fadi Babu tudu

Ya kalleta kawai ya dauke kansa don sam Bata bu

rgeshi sbd rawar kanta da rashin kamun kai.

Taku Daya biyu saita dawo gunsa da sauri tana fadin"in bazaka damu ba ka bani nambarka intana can zankiraka ne inhadaku ko insanar maka kazo can din sbd kasan ta da taurin kai zata iya qin tahowa akan lokaci.

T

ayi hakane Dan dabara na son samun nambar tasa.

Baiyi mata gardama ba ya Bata kuwa Dan Bai kawo komai ba.

Tayi save tana fara,a da godiya ga Allah ckn ranta.

Labiba na zaune dafe da kai ta zurfafa a ckn kogin Tunani taji an dafa kafadarta ana fadin"ke k

awata kiyiwa kanki kiyamul laili da Tunani marar Amfani,walh akwai abinda yake damunki,karfa kije ki kashe kanki a banza ato,Maza tashi muje ga mijin ki can yazo daukar ki ma.

Cikin mamaki labiba take kallon Surayya ranta ya Baci dataji abinda tace

Saita

yi mata mirsisi taki motsawa Bata ma sakar mata fuska ba don kada ta sake mata wata fassarar ta daban.

"Waike lafiyarki kuwa? Nace ga mijinki can yazo daukar ki naga bakiyi farin ciki ba,walh ki raga masa kiringa tausayinsa mana naga alamar kina wahalar d

ashi saboda Kinga Yana rawar kafa akanki ko,?to walh kibi ahankali saboda yammatan zamani tsaf za,a iya Miki kwace saboda kin masa rikon sako sako.... Labiba ta dakatar da ita da fadin"Kinga surayya Dan Allah ki tafi ki bani guri,bana son damu, bana son ha

yaniyarki marar Amfani,kije kice masa Baki ganni ba ma.

Kama Baki surayya tayi tana fadin"walh Baki isaba,baza,ai haka Dani ba Yana ganin mutuncina,bazanyi karya Dan asoni ba ma.

Ga mamakin labiba sai ganin surayyar tayi tasa waya akunne tana fadin"Eh na

ganta,Muna tare Amma tace bazata iya zuwa ba saidai kazo,to ka tambayi inda capteria take ka biyo ta baya akwai garden agun zaka ganmu.

Sosai Labiba ta cika da mamakin surayya ayau,wato dama tana da nambar Haidar ne ko yanzu ya Bata,kai Anya ba wayar kary

a take ba kuwa?

Kafin ta gama mamakin lamarin sai hangoshi tayi ya taho a sukwane Yana tafe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login