Showing 15001 words to 18000 words out of 50822 words
na tabbatar da cikin ya zube inga karshen iskanci."
Koda A
lhaji Sadi ya miƙe upstairs ya wuce zuwa dakinsa yana tunanin mafitar da zata kawo daidaito a rayuwar Labiba, ya cire hannu ya janyo waya ya lalubo lambar da sukayi musayar tes da H.D SOJA BOY.
Saida yayi kira biyu sannan aka
ɗ
aga, muryarsa da damuwa yace
, "Sadi ne, ka tsaya ka saurareni akwai maganar da nike son muyi."
Daga
ɗ
aya bangaren H.D SOJA BOY yace, "Wata magana kuma? Ai takaddama ta ƙare a tsakaninmu, kayi min na rama shikenan..." Alhaji Sadi ya katseshi da fa
ɗ
in, "Ramakon gayya da kayi akan
ɗ
iya
ta yabar baya da kura, ciki ne da ita shiyasa nike son mu zauna mu tattauna."
A take jikin H.D SOJA BOY yayi sanyi, ya nisa sannan yace, "Babu damuwa mu ha
ɗ
u a zoo road amma ka sani idan wata kitumurmurar kake kullawa karonmu ba zaiyi maka da kyau ba, kod
a a wancen karon banyi maka ta
ɗ
a
ɗ
i ba." Daga haka ya tsinke kiran.
Alhaji Sadi ya suri makullin mota ya fita yaja motarsa ya nufi zoo road, Hajiya Hakima tana ganin fitarsa ta suri mayafi ta fita yawon gidajen bokaye.
Labiba ta girgiza kai kawai, ta
ɗ
au
ko Alƙur'ani mai girma ta zauna a harabar gidan tana rera karatu a cikin Suratul Nisa'i, a take nutsuwa da kwanciyar hankali ya saukar mata.
Alhaji Sadi ya samu zama da H.D SOJA BOY, bai
ɓ
oye mashi komai ba, ya fayyace mashi komai akan ƙalubale da take fu
skanta tun kafin faruwar wannan al'amarin.
Ya
ɗ
ora da fa
ɗ
in, "Tana cikin damuwa akan abun da kayi mata, kayi min alfarma ka aureta tunda dama kaine ka aikata mata hakan."
H.D SOJA BOY ya ware idanu yace, Dama ana aure da ciki ne?" Alhaji Sadi ya girgiza
kai yace, "A'a, ina nufin bayan ta haihu, amma ina neman alfarma da ka rufa min asiri kada tasan sana'ar fashi da nikeyi."
H.D SOJA BOY ya kafeshi da idanu, "Idan har kana tsoron taji har haka saboda gudun kunyar duniya to ka tuba ka daina domin kunyar du
niya ƙarama ce akan abun da zaka tarar a gobe ƙiyama. A wancen lokacin nayi niyyar shiryuwa amma abun da kayi yayi min togiya."
Ya miƙe yana fa
ɗ
in, "Ko ma miye zan shigo in gana da ita." Daga nan bai ƙara magana ba ya juya ya wuce inda motarsa ya ha
ɗ
e kan
sa da sitirayi yayi zuru ya jima a hakan kafin yaja motarsa ya wuce.
Daga nan Alhaji Sadi ya wuce gidan Baba Malam ya sanar dashi akan yayi wa Labiba miji. Baba Malam ya ja fasali yace, "Saidai abun da ban gane ba shine ƙin bayyana min waye mijin." Alhaji
Sadi yayi kasa da kai yace, "Nayi bincike a kansa kuma bashi da damuwa." Baba Malam yayi jim sai kuma yace, "To shikenan." Suka ƙara tattaunawa kafin Alhaji ya kama hanyar gida.
Alhaji Sadi yana komawa gida ya nemi ganin Labiba ta sameshi a falon sama. "
Labiba na gana da wanda ya aikata maki wannan lamarin." Ta
ɗ
ago da sauri ta dubeshi idanu a waje, "Abba me kake jira dashi, a
ɗ
amkashi a hannun hukuma a bi min kadina."
Alhaji Sadi ya girgiza kai yace, "Ya sameni ne yana kuka sha
ɓ
e-sha
ɓ
e yace yayi nadama
zai aureki, yayi min alƙawari akan shiryuwa. Labiba idan kika aureshi kinyi jihadi kin tsameshi daga halin banza ya koma mutumin kirki."
Wannan kalami da Alhaji Sadi yayi ya saka jikinta yayi sanyi, "To shikenan Abba, zanyi maka biyayya, na yarda zan aure
shi." Alhaji Sadi ya sauke ajiyar zuciya yace, "Tashi ki tafi, Allah yayi maki albarka, yadda kikeyi min biyayya kema Allah ya baki wadanda zasuyi maki." Ta shafi cikinta sannan ta amsa da, "Amin." Duk da yadda aka samu cikin amma bata ji ta tsaneshi ba.
A daren an ta
ɓ
a fa
ɗ
a sosai a tsakanin Hajiya da Alhaji Sadi fa
ɗ
a take tana ƙarawa, "Shikenan sai mu biye mata mubarwa kanmu abun kunya, ka fiye son ƴaƴa, ka biye wa yarinya zaka tafka kuskure, idan kayi mata ta dole ai dolenta zata haƙuri." Ba wai fa
ɗ
an ci
kin bane kawai ta buge da karsana ne domin ta harbo guzuma tana kwada karfin maganin da ta amso wajen bokanta ne da ya tabbatar mata da cewa idan tayi amfani dashi koda icce ta ajiye Alhaji Sadi bai isa ya tsallaka ba saidai karfin addu’a da karatun Alƙur'
ani mai girma da Labiba takeyi ya hana asirin yayi tasiri.
Alhaji Sadi ya taso mata, "Ina ruwan ki, diyarki ce ko diyata, yaushe ne har kika fara nuna damuwa a kanta, yarinyar da a kullum kike cikin azabtar da ita, kiyi hankali da kanki tun ban saitaki ha
nyar gidanku a wannan daren ba."
Hajiya tana jin haka tayi lakwas bata ƙara furta kalma koda daya ba ta fice fuu ta wuce dakinta tana kudura a ranta cewa sai ta rama abun da Alhaji Sadi yayi mata akan Labiba kuma akan cikin zata huce haushinta.
Kwatsam w
ashegari saiga Ustaz Haroon zuwansa yazo mata da tarnaki, ta jima tana tsumayin zuwansa saidai KASH yazo a daidai lokacin da bakin alkalami ya bushe, tayi fatan yazo ne kafin wancen alƙawarin da tayi wa mahaifinta, da kuwa ta karbeshi hannu biyu-biyu, said
ai kaddara ta riga fata, ya makaro, me yasa tuntuni bai fa
ɗ
a mata ba, gashi yanzu an bata wani, taji kaunarsa ta ƙaru ina ma yazo kafin zuwan wancen zancen da hakan bai faru ba.
Lokacin da yake fa
ɗ
a mata yana sonta hawaye suka wanke fuskarta ta kasa magan
a saidai kuka kawai saida tayi mai isarta sannan tace, "Kayi haƙuri nayi fatan kazo ne kafin wannan lokacin amma yanzu bakin alkalami ya bushe, akwai alƙawarin aure a kaina, ina maka fatan alheri a rayuwa."
Ta miƙe ta wuce dakinta tana mai fashewa da kuka
, a ranar wuni tayi tana kuka, tayi kwanan bakin ciki abun yana cinta, duk da aurenta ga waccen zai saka ya shiryu amma inda gizo yake sakar shine shin zata iya jure zama dashi bayan tasan shine yayi sanadin mutuwar mahaifiyarta, anya kuwa zata iya? Kamar
ta dauko dala ne tace zata aza a saman kanta abu ne da bazai yiwuwa ba amma zata zuba idanu ta tsumayi zuwansa tunda dole zaizo, a yadda yayi mata zata yanke shawara akan ko ta aureshi ko kuma ta nemi alfarma a sauya mata da wani koda kuwa ba Ustaz Haroon
ba.
Idan taji ba zata jure zaman ba zatayi magana domin gujewa auren da zata dawo tana nadamar yin sa.
******
Washegari tunda asubar fari Hajiya Hakima ta gama kitsa zaren mugunta na ta'asar da zatayi wa Labiba, tana fatan shegen cikin ya zube ko ta fus
he haushin abun da Alhaji yayi mata a gaban yarinyar har itace Alhaji zaiyi wa tsawa sannan ya koma yana lalla
ɓ
a Labiba ashe kuwa bai nemi zaman lafiya.
Saida ta fakaici lokacin fitowar Labiba wanke-wanke yayi ta dauko ruwan kubewar da ta ajiye ta zuba ak
an hanya, baiwar Allah Labiba da bata san wainar da ake toyawa tana zuwa ta saka kafarta a ciki saidai jinta tayi a ƙasa, kugunta ya bugu, ta turgude kafa saidai babu karaya. Tana kuka tana kiran sunan Allah.
Alhaji Sadi ya fito yana jera mata sannu, ciki
n bai samu damuwa ba saidai gurdewa da kafarta tayi, ya kira masu daurin gida suka
ɗ
aure mata. A ranar ya kira ya sanar da H.D SOJA BOY abun da ya faru da ita, ya bukaci da ya zo ya sameta suyi magana ta fahimtar juna, sun ajiye magana akan zaizo da marece
n ranar.
Saida ya cire aski dake a saman kansa sannan ya wuce masaukinsa ya shirya cikin dakakkiyar shadda dinkin zamani ya murza hula dara, ya feshe jikinsa da turare, ko shi da ya kalli kansa saida gabansa ya fa
ɗ
i na matukar kyau da yayi, kyaukyawan nam
iji fari dogo mai suffar jarumai. Ya feshe jikinsa da designer turaruka masu kamshi, ya
ɗ
aura agogo kirar rolex a hannunsa ya suri makullin mota ya fita yana baza.
Bata san da zuwansa ba har saida yazo Alhaji Sadi ya shigo da kansa ya sanar da ita, ta ras
a wani tunanin zatayi, hawaye suka zubo mata ta saka hannu ta sharesu ta zura hijab ta fita tana dogara sanda.
Saida gabanta ya yanke ya fa
ɗ
i a lokacin da tayi arba dashi, ta kafeshi da idanu tana al'ajabi, kyawunsa, kamalarsa, yanayinsa, shigarsa, zata i
ya rantsewa tace bazai iya aikatawa ba saidai ganinsa da tayi a falon ya tabbatar mata dashi, cikin ranta tace, "Mugu bashi da kama."
Ta zauna a kujerar da take gefensa kamar yadda take kallonsa da mamaki shima hakan yake kallonta yana al'ajabin zubin kya
wunta, yadda take da ni'ima haka take da kyawun fuska duk ba tayi kwalliya ba amma wannan bai
ɓ
oye fasalin kyawunta, yace, "Ya jiki?" Ta amsa da, "Lafiya lau."
"Allah ya kawo sauki, Allah ya tsare gaba."
Ta amsa da, "Amin."
Ya
ɗ
an yi jim yaja fasali san
nan yace, "Labiba ina mai baki haƙuri..." Da sauri ta katseshi, "Dakata, tsaya a nan, ai gangarar tamu ba ta zo nan ba, tukunna." Ta nisa tace, "Miye sunanka?" Ya dubeta ya jima rabonsa da a kirashi da Aliyu saidai H.D, Soja Boy ko Kuma Haidar H.D amma sai
ya samu kansa ya furta, "Aliyu." Ta jinjina kai tace, "Da kayi halin mai sunan da baka aikata abun da kayi ba... Abbana ya fa
ɗ
a min ka sameshi ka sanar dashi ka tuba ka nemi alfarma akan zaka aureni, kayi alƙawarin daina fashi da kwace da dukkanin wani ha
li marar kyau."
H.D SOJA BOY ya gya
ɗ
a kai yace, "Ehh haka ne." Ta jinjina kai tace, "To babu damuwa, yanzu manzo gangarar da nike magana a kai." Sai kuma tayi shiru ba tareda ta furta komai ba, ya gane hausarta fuskarsa dauke da damuwa yace, "Labiba ina m
aki ta'aziyya na rashin mahaifiyarki da kikayi, Allah yayi mata rahama, na sani babu wani abu da zan aikata maki da zai goge baƙin zaluncin da nayi maki amma ina ganin aurenki da kuma sauya halayyata zai zame min tamkar wani tsani na kawo gyara. Tun daga r
anar na rasa sukuni, bana iya barci, komai ya fice min a kai, na rasa abun da yake min
ɗ
a
ɗ
i. Labiba alhakinki ne yake bibiyata. Labiba naji ina sonki ina tausayinki ki bani dama in dauki hanyar gyara akan laifin da na aikata a gareki, ki zama mai yafiya, k
i zama mai gyara
ɓ
arna ta hanyar gyara, kada ki zama mai riko na ramakon gayya domin babu komai a cikinsa sai dana sani da kaico."
Hawaye suka zubo mashi, shi kanshi mamakin kansa yake, rabon da ya zubar da hawaye tun rasuwar Fatima.
Hawaye da ta gani a
idanunsa da kuma kalami da yayi mata ya saka jikinta yayi sanyi tace, "Babu komai. Allah ya yafe mamu baki daya." Ya amsa da, "Amin."
Tausayawa da ya nuna a gareta da kuma nadama da yayi ya saka taji cewa zata iya aurensa ko saboda hakan ya zame mata jiha
di a wajen shiriyarsa.
Tayi shiru yayi shiru sun shafe lokaci a haka kafin yayi mata sallama ya miƙe da nufin tafiya har ya kai kofa ta samu kanta da kiran sunansa, "Aliyu." Rabon da a kirashi da Aliyu har ya manta, yadda take kira sunan na musamman ne ya
na jin sautin muryar har a zuciyarsa. Ya juyo yace, "Na'am."
Ta nisa sannan tace, "Idan rayuwa tayi maka ƙunci kayi alwalla ka dauko Alƙur'ani mai girma ka karanta, Alƙur'ani waraka ne." Maganarta ta dokeshi ba ka
ɗ
an ba, rabon da wani ya fuskanceshi ya sa
nar dashi gaskiya har ya manta. Ya gya
ɗ
a kai yace, "Na gode Labibar Aliyu." Ya saka kai ya fita, taji hawaye sun zubo mata, ta miƙe ta koma dakinta.
Tunda Aliyu yabar gidan kalamanta suka tsaya mashi a zuciya musamman tunatarwar da tayi mashi daga karshe.
Rabon da wani ya kirashi ya fa
ɗ
a mashi gaskiya tun mahaifinsa yana da rai, abokan mahaifinsa sune suka kulla mashi kitumurmura su kuwa dangin mahaifinsa tun bayan barinsa aiki suka watsar dashi akan fushi na cewa ba ya
ɗ
aukar shawara suka kasa fuskantar c
ewa ba akan son ransa bane ya ajiye aikin. A daren bai rumtsa ba maganganunta suna mashi amsa kuwwa a kwakwalwa.
*******
Washegari ta kasance ranar da Hajiya ta samu nasarar zubar da cikin Labiba, cikin da Labiba ta dauki damarar rainonsa har ta haifeshi
domin nunawa duniya cewa yaran da aka haifa ba tareda aure ba basu laifi akan abun da ya faru, kuma idan suka samu ingantaccen ilimi da tarbiyya zasu kasance mutane na gari da al'umma zatayi alfahari dasu, mutane da al'umma zata amfana dasu saidai kaddara
ta riga fata.
Da safe ne, tana kishingide Hajiya Hakima ta dungure mata kofin shayi da burodi, bata kawo komai a ranta ba kasancewar jiyan Alhaji Sadi yayi wa Hajiya Hakima gargadi a kanta akan kada ta ƙara bari tayi aikin wahala saidai ashe Hajiya tana
da wani shirin na daban domin a cikin shayin ta zazzage maganin zubar da ciki.
Labiba tana sha jini ya
ɓ
alle mata ta gabaita matuƙa, a karshe ciki ya bare tana kwance tana barcin wahala, Alhaji Sadi ya zuba mata idanu tausayinta ya kamashi, tunda har ciki
n ya zube yana ganin kamata yayi ya warware maganar auren tunda dama mijin ba na gari bane, dama yayi hakan ne saboda cikin, gwara ya warware maganar ya cillata wata kasar karatu hakan sai ya fiye mata auren H.D SOJA BOY.
Ya
ɗ
auki makullin motarsa ya wuce
gidan Baba Malam ya sameshi a parlour yana kallon wa'azi ya gaishe dashi sannan ya zauna yayi shiru. Hakan ya saka Baba Malam ya gane akwai magana, ya maida hankalinsa a kansa yace, "Ina sauraronka Sadi."
Alhaji Sadi yace, "Akan maganar auren Labiba ne."
Da jin haka Baba Malam ya fa
ɗ
a
ɗ
a fuskarsa da murmushi, "Torh.. Torh.. Torh.. An saka ranar auren ne."
Alhaji Sadi ya girgiza kai yace, "A'a fasa aurar da ita nayi, na yanke shawara zan kaita kasar waje karatu."
Baba Malam ya kafeshi da idanu, "Da wa ka
yanke shawarar?" Alhaji Sadi yayi shiru. Baba Malam ya girgiza kai yace, "Wannan ba shawara bace, diya mace ka dauketa ka cillata uwa duniya babu kowa a kusa, daga ita sai kanta, A'a bazan yarda da wannan ba."
Ya tsaya yaja fasali sannan ya
ɗ
ora da fa
ɗ
in,
"Ni ban san miye ka yanke a kanta ba, kace min kayi mata miji na tambayeka waye domin asan asalinsa kace ba sai an bi ba kai ka sanshi to yanzu kuma miye ya kawo maganar cewa ka janye har kana maganar zaka cillata karatu kasar waje, ina mai baka shawara k
a janye wannan kuduri, yarinya ce mace, maraici ne a kanta bai kamata a dauketa a turata uwa duniya ba, bata da kowa a kaita karatu wata kasa, a'a, macece sannan
ɗ
iyarka kwaya tilo, idan kuma wani abun ya sameta sai muyi ya. Ina mai baka shawara ka aurar d
a ita kamar yadda ka tsara a farko, ba amincewata ga kaita uwa duniya karatu."
Haka ya hakura a dole tunda Baba Malam ya nuna rashin amincewa akan maganar saidai inda gizo yake sakar shine makomar maganar auren, tunda har cikin ya zube anya kuwa zai iya d
aukarta ya baiwa H.D SOJA BOY, maganar karatu kasar waje ya haƙura amma har lokacin yana waswasi akan maganar auren.
Muje zuwa
[01/10, 9:06 pm]
: *LABIBA*.......
🏵
️
🏵
️
🏵
️
_The Emotional Story_
😰😰😰😰
Na _Nabilancy love_
💘
*Auntyn S and S*
______________________________
🌈🇰
AINUWA
🇼
RITER'S✍
🏼
*
🇦
SSOCIATION
🤝🏻
*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/k
ainuwawritersassociation
______________________________
Page
11 and 12
A hankali ta bu
ɗ
e idanunta ta yunkura ta miƙe zaune tana mai
ɗ
aga idanunta tana bin
ɗ
akin da kallo daki-daki yayinda take tunawa da komai da ya faru tun daga shan shayin har zuwa z
ubewar da cikin yayi, bata jin karfi a jikinta dakyar ta iya miƙewa zaune ta dafe cikinta hawaye suna zubowa akan fuskarta duk da ta hanyar fya
ɗ
e ta samu cikin amma ta shiga matuƙar damuwa da bakin ciki akan zubewar saidai bata takurawa kanta ba Allah da y
a jarabceta da samun cikin ta wannan hanyar shine ya amshi abunsa, Hajiya Hakima sanadi ce kawai wanda da tayi haƙuri tunda har an rubuta cikin zai zube a yau to kuma sai ya zube koda bata yi gaggawar zuba mata maganin zubar da ciki a shayi ba.
Babu karfi
a jikinta ga kuma yunwa dake nukurkusarta, ta maida dubanta akan teburin dake a dakin nata, kulolin abinci ne ta miƙe dakyar tana takawa sannu a hankali ta ja kujera ta zauna tana bu
ɗ
e kulolin, abincin da Hajiya ta ajiye mata.
Har zata ci ta tuna zubar m
ata da ciki da tayi