Showing 27001 words to 30000 words out of 69481 words
sannan yaji alamun shigowarta saman ta hau ta kalli qofar a rufe ganin hakan yasata fara dukan qofar da dukkannin qarfinta tana cewa.
“Tunaninku zakuci amanata ku hutane qarya kake Ja'afar Wakil tabbas baka fara
shiga damuwa ba wlh ka zubar da farin cikinka tunda kaci amanata macuci mayaudari maci Amana azzalumi, Ashe dama abinda yasa kullum bakada Hira saita Rafi'ah kenan Ashe da gaskene saqon da aka taba turomin cewa kullum sai anganka a makarantarsu ka dauketa
ni Ina tunanin saboda nine macuci Ashe kanka kake ginawa to wlh dole ayi dayan biyu dole ka saki daya cikinmu domin baa fada daya sarki biyu Ja'afar ka budemin ka fadamin laifin da nayi maka da zakayimin wannan sakayyar...."
Yanajinta yayi Mata ban
za tayi bugun duniya yaqi budewa zagin duniya tayi masa ya shareta saboda dama ya shiryawa zuwan wannan lkcn baizaci ma haukan nata zai tsaya iyanan ba a yanda ko a Hira take nuna masa ita zata iyayin komai akan kishiya, yanajinta ta gaji ta zube a gurin t
aci gaba da kukanta tana cewa “Allah dama mafarki nakeyi na bude idona naga ba gaske bane Allah ka mayarmin dashi tunani na shaidan Allah bazan daukaba wlh kasan bazan daukaba bazan iya zama da Bestie na matsayin kishiya ba Allah ka kashe wannan azzalumin
Ja'afar na huta Allah ka hada hardani nikam na shiga ukuna Allah...."
Maganganu takeyi kamar zararriya yanajinta yaqi budewa saboda shi kansa zuciyarsa a cunkushe take bada damuwar Ni'imah ba aa damuwar halin da Rafi'ah take ciki shine yake addabarsa gas
hi Kiran duniya yayi taqi dagawa ya tura Mata saqo taqi replying dabara ce ta fado masa ya Kira number Ammi don dama tun ranar data kirashi tayi masa warning yayi saving ring biyu ta daga da sallamarta ya amsa tare da cewa “Ammi barka da Rana" jin muryarsa
yasata hadiyar wani takaici Amma dake dattijuwa ce saita dake tace “lfy Ja'afar ya gdan"
Shiru tadan ratsa kafin ya ja numfashi yace “inata Kiran wayarta taqi dagawa Ammi Allah yasadai lfy?" Iska ta furzar tace “yo wanne lfy Ja'afar dama kanasonta da lfy
ne ai da sauqi ma da bata hadiyi zuciya ba tanacan tana fama da zazzabi" miqewa yayi zaune yace “ya Salam bari nazo na dubata" yana fadin haka ya kashe wayar ya tashi shi kansa idan zaa dubashi din so yake bai Saba da tashin hankali ba shi tashin hankali
fitar dashi a hayyaci yakeyi.
Doguwar riga yasa ya dauki key ya fice a hanya ya kira Muhseen yake sanar dashi ya daukeshu suka tafi daqyar megadi yabarsu shima Saida Ammi tayi masa mgn suka shiga sukayi parking Rashid dake fitowa yazo suka gaisa y
ayi masa ya hannu saboda yaga aika²r da qanwar tasa tayi, shine yayi musu jagora har parlourn baqi suka qara gaisawa ya dauki wayarsa ya kirayi Rafi'ah ta daga lkcn ta tashi tasha magani tayi salla yace “kizo ki sameni maza a parlourn baqi" bai jira cewart
a ba ya kashe wayar ta kalli Ammi Ammi ta kawar dakai tace “
“Kidaibi a sannu kada ki zafafa kiyi biyu Babu ba mijin babu aminiyar ita rayuwa baduk abinda kakeso kake samu ba iyakar saninmu munayi Miki addu'ar samun miji na qwarai Kuma kema munsan kinayi
tunda Allah shi ya zaba ya zaayi dama shi muka miqawa zabin Kuma yayi abinda ya dace"
Ficewa tayi tabarta da sassanyar gwiwa wasu hawaye suka zubo Mata wayar Yaya Rashid ce ta sake shigowa cikin kuka ta daga tace ”gag ganinan Yaya" miqewa tayi ta za
ri hijjab saboda sanyin da takeji ta fice ta sauka ta nufi parlourn baqin ta tura qofar ta shiga da sallamarta idanunsa na kanta suka amsa Yaya Rashid ya miqe shida Muhseen suka fice tare dajan qofar ya rage daga ita saishi ganin taja ta tsaya yasashi shar
eta yaci gaba da danna wayarsa kawai takaici yana cika masa ciki Wai kawai laifinsa don ya sota ya aureta ne take basa wannan ciwon kan jibi yanda ta wani tsaya masa aka kamar sa'anta.
Dagowa yayi ya dubeta tama kawar da kanta gefe daga facing dinsa idanu
nta ya balle da ruwan hawaye miqewa yayi a ransa yana dannan zuciyarsa dole ya koyi rarrashi don alamu sun nuna masa Kuma yaji a bakin Ni'imah amaryar tasa yar shagwaba ce a
sangarce take kuka bayayi Mata wahala idan Kuma akaqi bata hqr sai tayini tanayi k
amar wata qaramar yarinya shikuma gashi ba gwanin iya rarrashin mace ba to ta inama zai iya shida ko rakiyar zance baitabayi ba Saida yazo kansa Kuma itadin daya kamata su daidaita su fahimci juna taqi bashi hadinkai da tuni sun wucce babin kansu saidai su
ji da Ni'imah yar tujara, Hannunsa yakai ya kamo hannunta ta fincike kamar wacce akayiwa allura ta balle da bala'i tana nunashi tace “zan zagi babanka idan ka qara tabani mara zuciya kawai Wanda aka dafa zuciyar kare aka bashi ya ciny....."
Wata
tsawa ya daka Mata me hade da ihu data sanyata ja da baya yayi saurin dukan qofar da qafarsa ya fara matsarta tana janyewa Saida sukaje qarshen dakin ya damqi wuyanta idanunsa sun kada sunyi jawur jikinsa sai rawa yakeyi ya bude bakinsa dake tsuma yace “ba
na umarni sau biyu wannan shine na uku ki rinqa sanin kalmar da zaki fadamin duk so bazan dauki raini da wulaqanci ba ni ba qasqantaccen bawa bane da zaki rinqa jana a qasa kamar karenki dole ne Rafi'ah dole kisoni kiyimin biyayya domin Ni nan mijinki ne b
a yaronki ba kuma ba dan iska baneni nida kike ganina bana daukar raini raini ma a gurin macen da nakeso kawai don nace inasonta wlh idan kika bari kikakai zuciyata qarshe zan wahalar da ruhinki Rafi'ah zaki kasa samun jin dadi ta ko Ina ni a gurina zaki s
amu farin ciki to nima nema kike ki qureni"
Sakinta yayi ya koma ya zauna yana huci taja ajiyar zuciya me qarfi iya tsorata ta tsorata dashi ta shiga taitayinta guri ya nuna Mata a hassale yace “ki zauna naceee!" Da sauri ta zauna yaja numfashi
ya sauke muryarsa ya sauko gabanta ya Kama hannunta yana murza cikin a hankali ya dago kanta idonta a lumshe yace “karki qara fadamin irin wannan mgnr kinji?" Da sauri ta daga masakai bakinta na rawa ta fada jikinsa ta rushe da kuka tace “me kakeso yanzu d
ani ni kadaina zuwa gidanmu ka daina zuwa gurina ka daina Sona nima bana sonk....."
Bata idaba ya wawuri bakinta yasa a nasa ya fara aika Mata da wani zazzafan kiss me gigita yanayi qoqarin qwacewa takeyi shikuma yana qara shigar da ita jikinsa yana danna
kanta tare da hura Mata iskar hancinsa da ta hadu ta sakar Mata wata kasala, a hankali ya dagata cak ta fara tureshi tanason qwacewa shikuma ya riqeta a qirjinsa suka zube a kujera bakinsa na cikin nata ya tura hannunsa cikin hijjab dinsa tsoro ya lullube
ta don ko riga babu a jikinta saga ita sai bra.
Taushin fatarta ya kidama masa lissafi ya qara tura hannunsa tayi nasarar zame bakinta ta fashe da kuka tace “please ka bari don Allah banas...." Mgnr ce ta maqale lkcn da ya sauke hannunsa kan bra dinta ta
rintse idonta jikinta ya dauki tsuma ta saki gunji a cikin kukanta tayi saurin girgiza masa Kai tace.
“ Innanillahi don Allah Ja'afar ka bari banaso nashiga uku Ammi na wayyoh Abbana wayyoh Yaya Rashid....." Rufe Mata baki yayi jikinsa yana rawa y
ace “Calm down bazanyi Miki komai ba" tureshi ta farayi tace “Zaz....zafi kabari nipples dina zafi" hakan dama yakeson yaji yayi murmushin mugunta yace “kinason na bari?" Saurin
dagansa Kai tayi tana zubar hawaye yasa bakinsa ya fara lashe hawayen bai dain
a motsata ba yace “kicemin kayi hqr My Bestie kabari akai makani gdanka tukunna sai kayi komai"
Rintse idonta tayi kunya hade da tsoro suka qara shigarta yasa hannunsa ya janye hijjab din ya zubawa qirjinta ido wani kyaune dasu na musamman yaja numfashi
yana Shirin Kai bakinsa ta riqe kansa tanayi masa magiya ya dago qananun lumsassun idanunsa yace “Kinqi kice waike kunya ki fada ki tsira banajin kunya akan halal kema shaidane bazanji kunyar taranki gajiya anan ba wlh ke kinsani" ganin abinnasa na canza s
alo yasata saurin maimaita masa abinda yace,
Sakinta yayi yana murmushi sosai yakeji a jikinsa don da gaske yau feeling dinta yakeji, hijjab dinta yaja Mata ya rufe Mata jikinta ya kwantar da kansa yace “daga yau na soke sunan Bestie akan kowa ni kadaine
na cancanci sunan nan karna qarajin Ja'afar a bakinki Bestie shine sunan da nakeso ki fara kirana dashi a gaban kowa harda Mai martaba"
Matse qwallarta tayi ta miqe zaune har yanzu qirjinta dukan tara² yakeyi ya dubeta yace “ammi tacemin bakida
lfy Kinga nima ciwon da kikajimin ya jikin naki" Shiru tayi masa wani haushinsa takeji da ninkin tsanarsa ta tsani mutum mayaudari kalaman Ammi ne kawai suke danne zuciyarta da tuni ta qara illatashi, miqewa tayi tabi ta gefensa yana kallonta tunaninsa wa
ni abin zata dauko sai yaga ta bude qofa ya miqe da sauri Amma kafin yayi wani yunquri harta fice ya daki bango yanajin abin aransa dukkan wasu alamu na bayyane sun nuna hikimarsa bazata jawo masa hankalin Rafi'ah ba saiya hada Mata da addu'a.
Dole miqewa
yayi ya fito suka fita da Muhseen tunda suka taho ya kife kansa a cinyarsa har sukaje gdan bai dagoba Saida sukayi parking Muhseen ya taboshi ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi ya kalleshi murmushi yayi yace “abinda kowa yake jiye maka kenan kaqi yard
a gashinan tun baaje ko inaba ka fara ciwon Kai" bude motar yayi ya fice ya nufi cikin gdan yanajin wani qauri yana dukan hancinsa da sauri ya qarasa shiga yaga wani baqin hayaqi yana tashi ta sama ya kwasa da gudu a step na qarshe yaja yayi turus ganin N
i'imah tsaye gaban wutar da takeci da sauri yakai dubansa ga wutar abin mamaki suturunsa ne da takalmansa tasawa wuta Kuma take tsaye a gabansu tana jiran su cinye...
Sosai abin ya girgizashi Amma dake qwallon dan duniya ne sai kawai yayi murmushi ya shig
a cikin dakin wata suit dinsa da sauran wasu kayan da bata dibaba ya debo ya miqa Mata yace “kin manta da wadannan"......
_Vote_
_Comments_
_Share_
_Please_
*_Ummuh Hairan_*
[1/6, 10:46 AM] Mrs AA Fansah: I think you'd like this st
ory: "MY BESTIE'S HUSBAND" by realfauzahtasiu on Wattpad https://my.w.tt/lgobFTY2Ocb
*_My Bestie's Husband_*
*_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
*_21-22_*
*_Dedicated to Real Ladingo and Feedyn Bash_*
_Wa
nnan page din nakune kuyi yanda kukeso dashi
🤗
_
_____________________________
_____________________________
Wani matsiyacin kallo tabisa dashi ya matseta sosai ya cafki hannunta yajata qasa bayan ya kwarawa wutar ruwan dispenser suka sauka q
asa tana turjewa tana kaimasa duka baiko saurareta ba ya cillata daki yabita gadon ta zame jikinta na rawa tana wani irin kuka ya qarayin murmushi ya shammaceta ya janyota qasa ta fado rikicaa yabita ya dannan dukansa takeyi tana yaqushinsa shegen qarfine
dashi takasa tureshi saima qara luguiguiceta da yakeyi duk ihun da takeyi Masa bai qyaleta ba Saida ya wahalar da ita sosai sannan ya janye tana kuka me tafasa zuciya yayi murmushi tare da shafa gemunsa yace “Qawarki ce ta motsani Kuma ta tsorata shiyasa n
a hucce akanki ni ai naga hankalinki ma wlh banzaci iyanan kishin naki ya tsayaba aurene dai anriga an daura suna daya kuke amsawa idan Kinga dama ma ki qone gdan babu abinda zaa fasa jahila kawai" ficewa yayi daga bangaren ya shiga daya bangaren kasacewa
r shima a gyare yake ya haura saman yayi wanka ya dawo yayi kwanciyarsa tunanin Rafi'ah ya dameshi ta dauko wayarsa ya bude hotunan da
sukayi dazu kamar masoyan gaske yayi murmushi ya danna numberta ya kirata lkcn Aunty Murja tana dakin tana bata lbrn tuja
rar da Hajiya Sahura da Ni'imah sukazo sukayi musu abin ya wucce tunaninta shiyasa kukanma ta kasayi Ja'afar ya cucesu ya raba musu zumunci shi ko tsoron Allah ma bayaji kawai burinsa yake cikawa baruwansa da damuwar wani.
Kiranne yasasu duban wayar g
abadaya ganan an rubuta My Bestie's husb yasata jan tsaki dubanta Aunty Murja tayi tace “ki daina wannan abun da kikeyi zai iya rabaki da Ubangijinki Allah babu ruwansa da mijin aminiyarki tunda ya qaddara ya zamo mijinki to dole kiyi takatsantsan sosa mas
a ran da zakiyi ke Kuma Allah saiya sosa naki kinsan kuwa radadin dake cikin ace Allah ya sosa ranka Rafi'ah?" Girgiza Kai tayi Aunty Murja tajata jikinta ta shafa bayanta tace “duk wani farin cikin duniya zai iya hanaki ya hanaki kwanciyar hankali saboda
wannan abinda kike rainawa Rafi'ah ki taushi zuciyarki Ja'afar Wakil bazai taba janyewa qudurinsa ba tun kafin kukawo yanzun ma ya kafe balle yanzu da kike amsa sunan matarsa idan kika cika matsawa wahala zakisha"
Kawar da kanta tayi tace “nifa banasonsa
ne Aunty banajinsa a ko saman halshena bare zuciyata don Allah ki qyaleni" daquwa tayi Mata tace “kin dade baki tsaneshi ba yanda ya nace Saida kika zama matarsa zai nace saikin soshi har kinyi kishinsa namiji irin mijinki shigarai gareshi wlh namiji me na
ci tsayawa araine dashi garama kibi a sannu kada kizo kema ki rifta harma ki fishi ruftawa" sake tsuke fuska tayi daidai lkcn da wayar Ni'imah ta shigo gabanta ya fadi ta kalli Aunty Murja itama kallonta tayi tace “daga Mana kiji abinda zatace"
A t
sorace ta daga tare dayin sallama bata amsa sallamar ba sai wata uwar ashar data lailayo mata girjin Rafi'ah yabada wani dam ta miqe jikinta na rawa kuka ya balle mata tace “wlh Bestie bantaba son mijinki ba na fada masa yaqi amincewa abinda kikeji nafiki
ji ke kishine yake damunki da tunanin naci amanarki nikuwa qiyayyace Ni'imah na tsani mijinki banasonsa wlh bantaba mafarkin kasancewar wannan gwamutsin ba bantaba mafarkin zuwan wannan cukurkudadiyar ranar ba...."
Ashar ta qara danna Mata sai Kuma ta fas
he da kuka sukayi Shiru kowacce na kuka abubuwa da yawa na dawo musu can Ni'imah ta zabura tace “wai kece kishiyata matar mijina mijin da kinfi kowa sanin irin son da nakeyi masa Rafi'ah kin yaudareni kun cutar dani keda Ja'afar wlh ko zan mutu saina hanak
u jin dadin wannan auren cin amanar gakinan gashi ku zauna nagani muddin Ina raye sai kunyi nadama sai kunsan kunci amanata zaku ganine dagake harshi dagayau zamu fara wasan abun da nakeso ki fara cirewa a ranki shine aminci da zumunci daga wannan ranar na
yankeshi har abada kisa aranki zan iya kasheki da hannuna duk inda kika ganni kiyi qoqarin barin gurin donni maqiyiyarki ce ta gaske akan mijina ko kece Sahura uwar data haifeni wlh sai naga bayanki...."
Tana gama wannan mgnr ta kashe wayar Rafi'ah
ta zube a qasa ta dora hannu akanta ta fashe da kuka tana cewa shikenan abinda nake gudu ya faru Aunty Ni'imah bazata taba fahimtata ba Allah ka fitar dani kasan banida laifi fin qarfina akayi...." Wayarce ta qara daukar ruri Aunty Murja ta dauka ta miqa
Mata tace “ki rungumi mijinki aikin
gama ya riga ya gama" karba tayi ta kara a kunnenta yayi ajiyar zuciya yace “9 misscall sallah kikeyi ne?" Shassheqar kukanta yaji yaja numfashi yace “it's ok na gane wato kuka kikeyi ko ayyah sorry fah Kinga da muna tar
e da na tsotse hawayen na lashe komai Amma Babu komai lkcne banason takurawa Abba ne nifa ban buqatar komai ke kadaice nakeso da zai banike gobe da nafi kowa murna so nake duniya ta shaida da wuri ba laifina bane laifin rabone idan sukaganki da turtsetsen
ciki zasu fahimci hakan"
Gabadaya haushi yake bata qara kwantar dakai yayi yace “kinsan me?" Batace masa komai ba yace “wlh inason komanki kedin dama domin Ni akayiki Rafi'ah zan nuna miki asalin so zakiyi alfahari ki godewa Allah da zabin da yayi miki"
miqewa Aunty Murja tayi ta fice da hikima da dabara Ja'afar akai baiwar kalami idan yaga dama haka ya rinqa kwantar Mata da hankali duk da bata mgn Amma yasan kalamansa suna shigarta ga yanda taketa ajiyar zuciya.
Numfashi taja yace “Inasonki fiye d
a rayuwata My Bestie ki kasance cikin aminci 1:30am ki kwanta ki huta akwai ranar rashin baccin batazoba tukunna" kashe wayar yayi taja fasali tana jujjuya tata wayar a hannunta maganganunsa sunata yawo a kwanyarta lumshe idonta tayi tare da dauke qwallar
idonta da kalamansa dana matarsa sune suka hadu suka saukar Mata da ciwon Kai ta miqe ta dauro alwala tayi sallar nafila raka'a hudu tayi addu'a me tsayi tana roqon Allah alkhairin wannan aure tace “Allah Kai kace mu roqeka zaka amsa mana tabbas baiwarka t
a kasance me kawo duk wani damuwarta gareka Allah na nemi zabin miji a gurinka ka zabamin mijin aminiyata Allah Kai kace Aljannar wadanda sukayi soyayya dominka ma dabance tabbas naso Ni'imah dominka nayi Mata duk wani Abu dominka, Allah Kaine masanin sir
rin fili dana boye Kaine kadai kasan dalilin zabamin mijinta a matsayin mijina Ina roqonka ka haskamin alkhairin abin Allah ka ragemin qinsa a zuciyata idan kabarni naci gaba da qinsa bazanyi masa biyayya ba idan banyi Masa biyayya ba bazan hadu dakai ciki
n aminci ba"
Ta Jima tana hawaye tana fadawa Allah buqatunta tana cikin addu'ar ya kirata bata dagaba daya sake kiranta ta daga jin muryarta wasai yasashi jin dadi yace “kinyimin addu'a?" Shiru tayi yaja fasali yace “ina buqatar addu'arki matata ki roqami
n Allah yabani ikon adalci tsakaninku kinji matata?" Jinjina Kai tayi tace “saida safe" wani dadi ya lullubeshi suka aje wayar ta cire rigar da tayi sallah da ita tasa na bacci ta haye gadon tare da addu'ar ta kwanta.
Washegari tunda ta tashi bata s
auko qasan ba kuma bata bude wayarta