Showing 9001 words to 12000 words out of 69481 words
sahalewar ubangiji wajen mallakarki cikin sauqi"_
Murmushi tayi ta duba lkc 1:24:am yayi Mat
a wannan saqon ta sauke ajiyar zuciya tace “na gde" ta sake bude wani ya rubuta _"ina addu'a Ina qara samun qwarin gwiwar fitowa takarar neman wannan babbar kujera da zata zamomin fahari a duniya tabbas idan na samu Rafi'ah matsayin Mata nasan Allah ya gam
a yimin arziqin duniya ko iya hakama yabarni na gode masa"_
Dariya tayi tana toshe baki tace “au haba da gaske?" Sake bude wani tayi _“Iya wuya zan jure kowacce kalma daga bakin duniya domin cikar burina kedin ke nakeso Kuma ke na faraso Rafi'ah meyesa b
akizomin a farkoba kikazo a qarshe?"_ murmushi tayi ta bude wani Wanda dagashi sai na qarshen ya rubuta _“indai na kasance ni dake bana iya yaqar zuciya My Raf inada naci akan duk abinda zuciyata ta aminta tanaso
Ina fatan bazan dameki ba kuma bazaki qosa
dani ba ni namiji ne na gaske inada naci My Wife....."_
Murmushi tayi ta bude na qarshen _“Hi Assalamu alaiki Qurrah ki shirya tarata yau zan kawo miki ziyara yau bazan iya barin Bauchi banganki ba"_ zaro ido tayi tare da miqewa zaune tace “nashiga
uku aa wlh yau inada lecture tun safe har magrib banida Interval" miqewa tayi ta fada wanka ta shirya cikin doguwar riga me masifar kyau dayi rolling kusan shigarta kenan ta dan gyara fuskarta tasa lipstick ta dauki littafanta ta fice ta nufi hall din da z
asuyi lecture din mamakine ya kusa sata faduwa batayi nisa da tafiyar ba ta fara hango Ja'afar Wakil tsaye jikin mota shida wata budurwa ta duba agogo 8:30am taka zuciya yanda ya kafeta da ido bata Isa ta wucce ba dole jikinta a sanyaye zuciyarta a jagule
ta matsa gabansu tace “Mr Wakil lfy da sassafe haka azare da Bauchi da nisa Ina Bestie na?" Kallonta yake yakasa qiftawa ganin yanda yake kallonta yasata duba jikinta tace “lfy Mr Wakil?" Murmushin gefen baki yayi ya kalli yarinyar ta matso gabanta ta Kam
a hannunta tace “morning princess Aunty Rafi'ah gsky Masha Allah sunana Fiddausi Muhammad Wakil ni qanwace a gurin Yaya Ja'afar Kuma autarsu....."
Katse Fiddausi yayi da cewa “ki manta kawai Little zata sanku a hankali ai tunda suka shigo fam dinmu wato a
dmission nake nema Mata a makarantarnan shine mukayo sammako akwai wani abokina da mukayi zamu hadu yau bayan tafiyata jiya yacemin Nazo yau yanzu dai ya kk ya bacci?"
Wani mahaukacin numfashi tayi tace “fine Allah ya gida?" Lumshe idonsa yayi ya k
ada Mata Kai suka kalli juna da Fiddausi sukayi murmushi tace “yanzu yana Ina Mr Ja'afar Wanda zaka gani din muje na rakaku kasan makarantar tamu saimu" kallonta yake yanajin dadin yanda ta nuna kulawarta gareshi budar bakinsa yace “kinci abinci?" Dagowa t
ayi da sauri ta zuba idonta a nasa tare da basarwa tace “ah haba likita ai baya karyawa da wuri saboda tsaro"
Ga mamakinta sai taga ya daure fuska yace “for wht?" Shiga tayi taitayinta abinka da saraki badai kwarjini ba qasa tayi da kanta yayi murmushi ya
ce “da wasa nake Miki muje Nima yunwa nakeji sosai" dagowa tayi arhar hawaye a gurin Rafi'ah kamar baure har idanunta sun kawo ruwa ta duba agogon hannunta Tara saura Kuma Tara zasu shiga lecture, zatayi mgn ya sake daga Mata zara zaran yatsunsa yace “muje
banason musu.
Turo baki tayi gaba taja da baya tana harararsa tace “to waikai Ina ruwanka da cikina ne nagadai banice Bestie ba da zaka ce sainabar lecture na nabika yawo nikam aa gask....." Numfashintane ya dauke jin qamshin jikinsa ya kusanceta
sosai kafin ta gama bude idonta kawai saijin wani dumi tayi akan bakinta ji tayi wani Abu na yawo cikin bakinta daya sanya numfashinta daukewa cak na tsayin lkc daqyar ta tattaro qarfinta domin tureshi ta kasa kawai sai hawaye sharr jikinta ya dauki wata
muguwar rawa.
Sai lkcn ya saki bakinta yana sauke wani nishi ya tura hancinsa kan wuyanta yace “zakije ko bazakiba..." Yayi maganar muryarsa na shaqewa kawai saita saki kuka me sauti tana tureshi shikuma yaqi sakinta tace “ka taimakeni ka sakeni don Allah
ana ganin mutuncina a makarantarnan Meye hakanne Ja'afar meye hakanne banason haka don Allah wannan ai iskanci..." Saurin sake hada bakinsu yayi ya dagata cak yasata a mota ya kulle ya janye bakinsa daga nata ya juya ya dubi Fiddausi da itama jikinta yake
rawa bata taba ganin wannan tantiranci ido da ido ba sai yau ita gabadaya yayan nata ya firgitata musamman yanda taga jikinsa yana rawa,
Tsawa ya daka Mata yace kin wani kafeni da ido kizo ki shiga muje mu dawo lkc yana tafiya" shiga tayi yaja mota
r da gudu ya fita daga makarantar itadai Rafi'ah tsoro da fargaba sun hanata Motsin kirki sai hawaye da takeyi tace “mijin aminiyata..." Batasan maganar ta kufce Mata ba yaci gaba da tuqinsa ya bude baki yace “kinsan cewa daga kallon farko a gurin dinner k
ika hadani da aiki kika jefani a komarki Rafi'ah kinsan cewa “kallon dana dameki dashi a ranar ba kallon rashin sani bane kallone na karbar saqo daga zuciya zuwa zuciya, kinsan cewa tun a ranar kika hadani da aiki bana cikakken bacci bana iya komai Saida t
unaninki hatta qawarki idan ba hirarki takeyimin ba bana iya doguwar Hira da ita rafi'ah Hira idan har bataki bace gara abarni na zama kurma, shin ya kike tunanin zan kasance idan nace zanyiwa aminta biyayya na bijirar da abinda ya shiga zuciyata a karon f
arko?"
Tunda ya fara mgnr ta kafesa da ido hawayen ma da take fitarwa ya tsaya cak sai rawar jiki da bugawar zuciya da kawai takeyi, dauke idonsa yayi daga kanta yace “bandamu da mgnrki ba Rafi'ah buqatata itace ki yarda Kuma kiji cewa Ja'afar Wakil yanas
onki so bana abota ba na aure aurenki zanyi Rafi'ah"........
_Mgn ta Allah comment yayi qasa nima zan aje alqalami na na huta_
*_Ummuh Hairan_*
[1/2, 9:19 PM] Mrs AA Fansah: *_My Bestie's husband_*
*_Ummuh Hairan_*
*_Wat
tpad-realfauzahtasiu_*
*_Free book_*
*_7-8_*
_Masu Bina suna cewa na turo musu daga farko kuyi hqr bazan iya bane duk groups din da kukaganshi to ku tambaya zaku samu abun zaimin yawa nayi typing nayi Post sannan nazo na rinqa bink
u one by one Ina tura muku please kada wata tace banida da mutunci wlh ko kin bini bazan turaba Amma fah kuyimin uzuri nima inada uzurirrika na na qashin kaina sannan wannan book din kyautane sadaukawa ga duk wani masoyina dake fadin duniya nasan addu'ar k
u ke samamin kariya gurin Ubangiji Kuma Allah ya kareku daga bakin duniya
😘
_
____________________________
____________________________
Batare da yayi aune ba ko ya zata yaji saukar yatsun hannunta akan kyakkyawar fuskarsa me cike da saje abi
nda ya haddasa masa cin wani uban birki ji kaki qiiiiiiy! Abinda yasasu wata girgiza hakan baisa Rafi'ah ta daina tsumar da takeyi ba idanunta har yanzu na kansa ya saki baki yana kallonta rabon da asa hannu a mareshi har ya manta.
Bude qofar takai hannu
zatayi yayi saurin danna pin din ta juyo cikin bala'i tace “zanci kutumar ubanka Ja'afar zan yaga alfarmarka da mutuncinka matuqar baka budemin motarnan ba...." hannu ya sa ya toshe kunnensa ta sake daga murya cikin qaraji tace “ka budemin mota nace stupid
man kawa...." Bata rufe bakinta ba ya cafki bakinta da nasa ai baigama Kama harshenta ba ta gasa masa cizo a harshe dake cikkaken dan air ne ido kawai ya rintse ya sake tura harshen nasa cikin bakinta yana qoqarin sanya qarfi ya janyota jikinsa ta cure ji
kinta ta banqara ta kwace ta zame daga kujerar ta rushe da kuka tace “nashiga uku ni Rafi'ah wannan wacce irin baqar ranace Jama'a meye yake faruwa danine...." Bude motar yayi ya dube fiddausi yace “jeki little jirani...." Kafin ya ankara Rafi'ah ta bude q
ofar ta dire waje kamar wata mahaukaciya ta kwasa da gudun bala'i ta runtuma cikin daji.
Cikin tashin hankali ya fito yabi bayanta a guje dake dogone ita Kuma tsayin ba sosai ba sai gashi yacin Mata da taimakon bishiyar da tayi karo da ita ta caki g
oshinta tayi baya taga taga zata fadi ya tareta ta fada hannunsa ga matsanancin mamakinsa sai yaga ta fado hannunsa sumammiya abinda ya qara fitar dashi a hayyacinsa ya dagakai ya kalli Fiddausi data dafe qirji tanason mgn Amma tsoron jizginsa ya hanata ya
ce “meye hakan Fiddausi saboda nace inasonta shine harta suma"
Cije lebe tayi tace “yaya abinda girma ka taimaketa ka kaiyi Mata urgent treatment" sabarta yayi a kafadarsa ya sata a mota ya shiga cikin garin Kai tsaye wani asibintinsa ya nufa sabone bai d
ade da budeshi ba ya dauketa kamar beby ya shiga da ita har dakin da zai dubata ya cire babbar rigarsa duk likitocin dake asibitin ya hanasu tabata dakansa yayi treet nata ya cire Mata iccen daya shiga goshinta ya wanke gurin da magani, yana tsaka da dress
ing din gurin wayarsa ta fara ring ya daga ganin number Ni'imah ya danna ok Bai bata damar mgn ba yace “naje cikin Bauchi ne inada wani petiant bama lallai tafiyar nan yau ba saboda yanada muhimmanci a gurina" yana Shirin kashe wayar yaji tace “sweet kaje
gurin Bestie kace nace tabani abin dadi" duk da damuwar dake cinsa Saida yayi murmushi yace “insha Allah zanyi qoqari" yana fadin haka ya kashe wayarsa yaci gaba da abinda yakeyi.
Yana gama dressing din ta farka ganinta daure da drip yasata miqewa
ta fincike allurar ta watsar juyowar da zaiyi yaganta tana daye dressing din da yayi mata ya nufota a guje yana cewa “kewai meye hakanne baki da hankali ne jibi yanda kika jiwa kanki ciwo kina tunanin hakanne zaisa na janye qudurina" wani matsiyacin kallo
tayi masa ta nufi qofa ya nufota da niyyar hanata fita ta juyo tace “wlh tallahi ka qara matsata sai nayimaka ihu na tona maka asiri fajiri maci amanar qauna ka dauka ni yar iskace da zakazomin da wannan games din to kayi gaggawar lashe amanka kafin ka fu
skanci qasqanci a gurina Ja'afar bana zama inuwa daya da maci amana maha'inci dan uwan shaidan me burin shiga tsakanin qauna,
Sakin baki yayi tare da rungume hannunsa a qirjinsa shi masifar tata ma burgeshi takeyi baitaba ganin mutumin da yake fada yana
kyau ba sai ita yana wannan tunanin ta fice da sauri cikin saa tana fita ta fada napep ta fada masa inda zai kaita Koda ya fito baiga alamarta ba ya tambaya akace tahau napep kafin yaje ya dauko rigarsa ya nemo Fiddausi har takai school tana zuwa ta nufi h
ostel tanata wucce mutane bata gane su waye har ta Isa dakin ta fada gado ta rushe da kuka tana furta “ Innanillahi wa Inna ilaihirraji'un Allahummah ajirni fih musibati wa'akalifni khairin minha" ta jima tana kuka me dafa zuciya bata taba shiga tashin han
kali irin na yauba ji tayi anzauna a gefenta ta tashi firgigit.
Ajiyar zuciya tayi ganin Nina ce tace “meye Kuma pretty?" Kukanta ta qarawa qarfi tanasa tisue tana tsane jinin da Bai daina zuba a ciwon ba Nina ce ta dauko wani dan qaramin akwati ta bude t
a dauko auduga da magani tayi Mata dress na gurin tace “yanzu Mutuminnan na jiya yazo yabani magunguna yace na kawo miki garinyaya kikaji ciwo?" Dora Mata magungunan tayi a cinyarta tayi watsi dasu tace “kije kice masa banaso bana buqata ki hada masa da ka
yansa na jiya duka banaso ya fadi meye yakeso bayan wannan na fadawa abbana ya biyashi nidai roqona ya janye furucinsa, kwanciya tayi tace “Nina meye yasa mutane basusan girman aminta ba meyesa basusan darajar alaqa ba ? Meyesa Ja'afar zaiyimana haka wlh b
antaba zatoba Koda wasa nayi tunanin duk abinda yakeyimin saboda Bestie na yakeyi min meyesa zaiyimin haka me yake nufi dani Nina ya cutar dani ko iya haka kalamansa suka tsaya na rantse da Ubangijin da yake rayani bayan ya kasheni a kowanne lkc nayi bacci
bantaba jin tsanar wani mutum araina ba sai yau naji tsanar Ja'afar Wakil ta darsu a qoqon zuciyata natsani mutum maci amana"
Ta qarashe maganar tana shigewa jikin Nina tace “ko iya haka da wanne ido zan kalli Bestie mijinta yace yana Sona har ya
hada bakinsa da nawa innanillahi wa Inna ilaihirraji'un Hasbunallahu wani'imal wakil wannan masifa dame tayi Kama nikam na shiga ukuna Nina qaddarorina sunada wahala"
Miqewa tayi kamar zararriya ta kalli gabas tama manta da ciwon dake goshinta tayi sujja
da tace “Allah inhar ka qaddara yankewar alaqata da Ni'imah alaqar daka sardata tun bamusan kanmu ba Allah kada ka yanketa ta wannan hanyar ka karbi rayuwata na tafi na barta da mijinta abin qaunarta farin cikinta Allah nafi kowa sanin cewa Bestie na tanas
on mijinta Allah kada kabashi ikon cutar da ita Allah ka cire masa so da sha'awar duk wata ya mace a ransa bama niba ya Allah idan kayimin haka ka gamamin koma...."
Ji tayi an rufe Mata baki ta dago Nina tace “meyesa kike roqon farin cikin wata ha
r kike roqon Allah ya kasheki akan farin cikinta?" Share hawayenta tayi tace “ba wata bace Bestie nace wlh tafi gaban haka a gurina zan iya bata rayuwata matuqar zata rayu cikin farin ciki meyesa mijinta zaice yanasona Nina meye bambamcina da Ni'imah mutan
e suna cewa saboda aminta Kama mukeyi toshi meye yasa yakeson raba amintarmu?"
Murmushi Nina tayi tace “ai jiya dana fada Miki baki yarda ba Rafi'ah tun ranar bikin da kika gayyacemu na fahimci sinadarin dake fita a idonsa sone da zallar qauna Amma wanne
mataki kika dauka?" Shiru tayi nadan lkc kafin ta dago tace “zan yanke mu'amala da matarsa na dan lkc idan burinsa kenan" girgiza Mata Kai tayi tace “kada ki fara hakan zaisa ta zargeki kici gaba da mu'amala da ita shikuma ki take Masa dogon burki kiyi duk
meyuwuwa kiga kinsa masa tsanarki ta yanda dakansa zai janye Rafi'ah jiya dana fada Miki haushina kikaji har kina cewa bazai yuwuba to gashi dai kin gasqatani" Jinjina Kai tayi ta miqe ta fada bathroom tayi wanka ta dawo ta kwanta ranar duk wata lecture b
atayi ba tanajin wayarta tana ring taqi ko dubawa balle ta daga Nina ce ta zauna tanata rarrashinta tare da nuna màta bafa wani Abu bane latsine irin na mazan zamani yanzu haka ma bazai qara mgn ba tunda ta nuna masa batada mutunci,
Da wannan ta da
n samu kanta harta dauki wayarta ta fara duba kiraye kirayen kiransa yafi hamsin da layin data sani saina dayan daya rinqa turo Mata saqo jiya Wanda shima yakai talatin saqonni kuwa sunyi ashirin batako dubaba tayi delete all ta watsa layukan a black list
kiran Ni'imah ta gani har hudu tayi kamar ta share sai Kuma taga rashin dacewar hakan yau gabadaya basuji junaba zatayi tunanin ko ba Lau ba hakance tasata kiranta dagawa tayi cikin muryar kuka tace “inata Kiran wayarki kinqi dagawa Bestie kinsan Kuma bana
samun nutsuwa idan banjiki ba har na fara tunanin ko wani abune ya sameki na kiraki sosai da wayar Sweet ma baki dagawa I hope fine dai?"
Ajiyar zuciya tayi tace “banji dadi bane Bestie kaina na ciwo sosai Amma nasha magani na samu relief Ina fatan kina
lfy Ina unborn dina?" Dariya tayi tace “waye yace Miki inada ciki wlh banida komai yanzuma period nakeyi in fada Miki jiyama Saida mukayi fada da sweet wai saina bashi nutsuwa Wai Ashe akwai yanda akewa namiji ya samu nutsuwa ko ana halin haila?" Dariya R
afi'ah tayi tace “matsalace dake
babba Bestie Ina littafin dana zauna na rubuta na baki harfa buga mikishi nayi saboda kinsan rubutunmu na likitoci ba kowa ke ganewa ba, idan kika duba book din Zaki samu komai har addu'o'in da zaki samu daukaka da soyayyar
mijinki nabaki sannan ki cire ganda Bestie ki tallafi mijinki namiji da kike ganinsa bashida tabbas don Allah kada kibani kunya wlh a shirye nake na baki taimako ta kowanne bangare indai akan mijinki ne inason Kuma Ina burin ki zama tauraruwa a gurin miji
nta"
Tabe baki Ni'imah tayi tace “ke nifa duk dare fada mukeyi dashi banason nacinsa shiyasa naso kizo kinqi zuwa wlh idan ya fara baya gajiya a dare sai yayi sau biy....." Katseta tayi da cewa “sheeet! Bestie banson ji don Allah haramun ne sirrinki
ne ke dashi ki daina fada mijinki nakine ke kadai kiyi Masa komai babu komai Bestie your are educated meyesa kike Abu kamar tashin qauye duk wani farin ciki fa yana tare da aure duk da cewa aure ba dadi gareshi ba tsanani ne Kuma kinsa dama ita aljanna sa
munta ba abune me sauqi ba Ashe kuwa hanyar samunta bazata zama me dadi da sauqin biba please ki cire ganda Bestie don Allah ki tarairayi mijinki kinji?"
Numfashi Ni'imah ta sauke tace “nifa na rasa meye yasa wlh banason wahala kinsan ban sababa shi ya c
ika tsurfa wai bazaici abincin kuku ba saidai nayi masa Kuma idan nayi sai yace yaji ko yace magi yayi yawa shi komai baayi masa gwaninta ga izza da Isa kamar wani sarki Bestie Ja'afar fah inaga kamar ma yafi Muhammad Wakil Izza" murmushi tayi tace “haka z
akiyi hqr baki bishi inda zaku daidaita bane komai yakeso bakiyi bakya dauke buqatarsa a bed baki kashe masa yunwar cikinsa baki zama kuyi Hira dasshi kina fama da waya Ina gani fah 24 hours datarki a bude kina online da anyi Miki mgn ki amsa why Ni'imah w
hy da bazaki raba lkcnki ba kibawa mijinki kaso mafi rinjaye Ni'imah namiji zuciyar jariri gareshi Wanda yaje tattalinsa yake kula dashi dashi yake sabawa dashi yake tashi kibi a sannu ki fahimci mijinki ki haqura da chat matuqar kina