Showing 54001 words to 57000 words out of 69481 words
ya
nda take hadiyar yawu sukayi dariya shida Hajiya Kaltume yace “ta koma kamar mayya komai tagani tanaso tunda mukaje Mexico take sani barnar kudi a Rana sai tace tanason abu kusan kala talatin"
Zaro ido tayi sukayi dari dukansu Hajiya Kaltume ta kirawo Ja
kadiya Indo tace “ki dauki wannan kayan ki kai bangaren magaji" gdy Rafi'ah tayi Hajiya Kaltume tayi murmushi tace “Ah haba babu komai ai dole mu kula dake haqqi ne akanmu am don Allah Ja'afar duk abinda ya faru baya a manta dashi ya wucce har abada Rafi'a
h duk abinda kikeso ki aiko a karba Miki bani da wani amfani sai hidimarku"
Jinjina Kai Ja'afar yayi yanajin dadi a ransa idan aka nuna anason Rafi'ah da cikin jikinta ji yàke kamar yayiwa mutum kyautar duniya, miqewa yayi ya kamo hannunta yace “b
ari mu qarasa ciki mun gode da kulawa" fita sukayi tanata zubawa Rafi'ah sannu" suna fita ta kwashe da dariya tace “zakuci ubanku waikai ne Mata ita Kuma me ciki har wani godiya kakemin kamar ka mantani nice dai Ummu kursumu yar mage baki dadin goyo sai ba
qin naci har wani proud akeyi Wai batada sabo tunda ta samu kwadayayyen ciki ai dole ta saba dani zan shekara yi Mata hidima domin Rana daya tak yahudu tuba babu hhhhhhhh" ta qara kwashewa da dariya.
Bangaren Hajiya Innah suka shiga anan ya tafi yabarta s
aboda Hajiya Fatsum batanan anan ta kusan yini ita da Karimah qanwarsa yar wajen Hajiya Innah sunata hirarsu dake dama basufi sa'anni ba sai yammaci ta tafi bangarenta ta shiga hadimai sai hidimarsu sukeyi tayi wanka ta baje a qaramin parlour Dija ta kawo
Mata kunun da gurasar tayi Bismillah taci tayi hani'an sauran tasa a freegde tayi alwala tayi sallar magrib ta kunna kallo anan yazo ya isheta shima yabiyeta sunata hirarsu abin da yakebashi tsoro da mamaki idan baya tare da ita sai kewa da tunaninta ya da
mesa Amma idan yazo sai ysji duk ya gundura duk wani motsi da zatayi maimakon birgeshi da yakeyi da yanzu haushi yake bashi,
Sai darema da sukaje kwanciya yini yayi yana feeling nata Amma yanzu sai yaji duk haushinta yakeji gashi shi baiga wani la
ifi da tayi masa ba balle yayi fada yaji dadi duk wani Abu da tasan zai sanyashi farin ciki shi takeyi, itakam batajin komai a ranta kawai dai yanayinss ne yake bata mamaki sai ya kwanta ya tashi ya sake kwanciya ya tashi Saida yayi haka sau uku tanajinsa
batace komai ba taji ya miqe itama saita tashi
ta rungume pillow a qirjinta yakai ya kawoya tsaya a gabanta yace “na rass meye yake damuna wani haushinki nakeji Rafi'ah Kuma wlh bakiyi min komai ba" Allah sarki sai kawai tayi murmushi ta miqe ta dauki qur'
ani ta dawo ta rusuna ta miqa Masa yasa hannu ya karba tace “a duk lkcn da najini a irin wannan yanayin nakan bar duniya da abinda yake cikinta ta na koma ga Allah ta hanyar ambaton sunayensa tsarkaka da Kuma karanta zancensa me dadi da sawa zuciya haske m
ijina kaima kayi haka nasan zakaji sauqin abinda kakeji...."
Ajiye qur'ani yayi ya matso gabanta yana huci kamar wacce ta zagi uwarsa ya dago kanta kawai saiji tayi dauketa da Mari ya hankadata a gado ya hau bala'i yana cewa “wato saboda kin rainani har
ni zaki fadawa yanda zanyi idan Ina cikin yanayi ai ba duniya ce tayimin zafi ba kece kikayimin Kuma wama yace Miki banayin karatun qur'ani ko yau da asuba saida nayi nifa banson kirsa waike ta Allah to fadamin wanda yake bautar ubanki..." Fuuuu ya fice da
ga dakin yana cewa haba nima da jarabata in Banda qaddara ma mezanyi dake nifa baa hakicceni domin wahala ba ke kika rasa ba yar iskar da zata doramin hawan ruwa sakarya kawai" miqewa tayi da sauri ta leqa ta window jin tashin motarsa agogo ta duba 1:49am
kawai saita dora hannu a ka ta rushe da kuka ita ba cin mutuncin ne ya bata Mata raiba aa fitarsa a wannan lkcn gashi gda basu kadai ba kowa da abinda zai fassara ta jima tana kuka ganin bazai kaita ba ta tashi tayi alwala ita ta rungumi qur'anin da aka ma
reta dominshi tana karatun tana hawaye tunda take baa taba wulaqantata irin wannan wulaqancin ba harda zagin ubanta wai JM da bakinsa yake ce Mata yar iska, sake rushewa tayi da kuka tare da daukar wayarta ta fara kiransa Kira daya tayi masa ya daga shassh
eqar kukanta yasashi saurin cewa “kinga don Allah kiyi Shiru wlh bazan iya kwana a gidannan ba zuciyata tafasa takeyi kaina kamar zai tarwatse Rafi'ah bansan meye yake damuna ba na kasa jurewa idan na cika takurawa cutuwa zanyi"........
_More Co
mments_
_More Typing_
*_41-42_*
_____________________________
_____________________________
Numfashi ta sauke tana qoqarin shanye kukanta tace “amma me nayi maka JM don Allah kayi hqr tun kafin ka fadamin laifina inasonka bazan iya
jurewa wannan sauyin da kake neman wanzarwa tsakaninmu ba" numfashi shima ya sauke yace “calm down please ki kwanta ki huta babienmu nason hutu da safe zamuyi mgn"
Bata iya jayayya ba hakance tasata cikin sanyin murya tace “shikenan kayi bacci cikin ami
nci Allah ya tsaremin Kai" kashe wayar tayi ta koma ta takure a saman gadon tana saqe saqe ta rasa tuno abinda tayiwa mijin nasu kwanciya tayi tana shafa cikinta da ya fara motsi jiya ta sauke ajiyar zuciya tanajin qaunar abinda ke cikinta a wannan daren d
ai daga ita har Ja'afar babu wanda yayi bacci shima din daya fita bai iya nufar gidansa ba asibitinsa ya nufa yayi parking a mota ya qarasa kwana saida yayi sallar asubz sannan ya juyo ya dawo gidan sarautar, a fada ya tsaya akayi zaman fada dashi sannan y
a shiga gidan tana kitchen sanda ya shigo ya shige ciki yayi wanka ya canza kaya ya dawo parlon ya zauna,
Saida ta gama shirya breakfast dinta ta fito tana jerawa a dinning taji gyaran murya juyawa tayi da sauri suka hada ido ajiyar heart tayi ta fadada
murmushinta ta nufishi duk wata gaba ta jikinta tana rawa tana zuwa ta zube a qasan carpet din ta Kama kyawawan yatsun qafarsa tace “barka da safiya mijina" janye qafarsa yayi yace “ki bani abinci yunwa nakeji" miqewa tayi ta nufi dinning din ta hado masa
kunun gyadar da tayi ta dauko masa doya data soya sai farfesun kifi tarwada ta kawo masa ta ajiye a gabansa ya sauko qasa cike da zumudi ya faracin abincin, cokalinsa uku a kunun ya ture ya sake Kai doyar bakinsa ya furzar tana kallonsa gabanta na faduwa
ya ja farfesun yakai bakinsa kawai sai taga ya ture plate din yaja tsaki ya miqe ya shiga ciki.
A mamakance Kuma a tsorace ta miqe tabi bayansa ta bude dakin ta shiga ya juyo ya kalleta itamma shi take kallo ta matsa a hankali dan nesa dashi sa
boda har yanzu tanajin Marin da yayi Mata jiya tace “kace kanajin yunwa naga Kuma bakaci abincin ba ka tashi" a hasale ya dago yace “me kikasawa abincin nan yake daci..." Da sauri ta kalleshi ya dakanta tsawar da Saida tasa dan cikinta ya dunqule yace “mag
ana nakeyi Miki kin kafeni da ido" idonta ne ya cicciko da ruwa tace “wlh bansa komai ba...."
Figarta yayi yace “qarya kikeyi kice bakisa komai ba kinsa komai muje kici kiji" a gaban abincin ya dangwarar da ita yace “kici kiji" daukan kunun tayi takai ba
kinta tasha ita bataji dacinba ta dago tace “ni banji ba" masifa ya rinqayi ta inda ya shiga ba tanan yake fitaba itadai babu abinda takeyi sai kuka ya juya zai fice tabishi da sauri ta riqoshi ta fada jikinsa yasa hannu ya rungumeta sukayi Shiru na dan lk
c kafin ya dagota yasa bakinsa yana lasar hawayenta yajata zuwa ciki ya zaunar da ita yace “me kikewa kuka?" Kwantar da kanta tayi a jikinsa tana shafa bayansa ya gane abinda take nufi hakan yasa ya dagata cak ya nufi ciki da ita ya kwantar da ita ya kwant
a a gefenta ya zubawa fuskarta ido.
Murmushi yayi yace “meyesa ne Rafi'ah" a hankali ta bude idonta tare da janyo jikinta ta hade bakinta da nasa ya sukaja numfashi tare sun dade a haka tana shafa sumarsa shima yana shafa nata sosai suka tsuma jun
a kafin su Kai ga cimma burinsu sun jima sosai sannan suka saki juna suna mayar da numfashi ya shafa fuskarta yace “so sweet babe" murmushi tayi masa a rayuwarta batason fada balle mara dalili irin nasa hakanan dai babu wata walwala suka yini Abu qalilan y
a rufeta da fada hatta Hajiya Innah data shigo duba lfyrta Saida ta fahimci akwai matsala Amma bata
zurfafa ba dake dama tasan fadan halinsa ne, da dare suna zaune duk ta takura saboda Motsin kirki idan tayi rufeta zaiyi da fada wajen Tara na dare wayarsa
tayi ring ya wani zabura ya miqe ya Kara wayar a kunnensa bataji me akace ba taji dai yace “to angama ganinan 20 minutes" miqewa yayi ya fice batare da ko ya kalleta ba taja ajiyar zuciya.
Miqewa tayi ta gyara gurin ta shiga daki tayi wanka ta sh
irya cikin kayan baccinta ta sanya hijjab ta dauki hisnul muslum tana dubawa tana daukan addu'o'i ta Jima zaune sannan tayi addu'a ta kwanta, Shiru goma sha daya har daya bataji Motsin Ja'afar ba wayarta ta dauka ta danna numbersa ta kirasa har tayi ring B
ai dagaba sake Kira tayi.
Taji an daga taja ajiyar zuciya tace “Allah yasa dai lfy kake najika Shiru...." Jitayi anyi murmushi sannan akace “dake zama kikayi kina jiran dawowar abinda aka baki aronsa to ai dama kwanciya kikayi kikayi bacci zaifi Miki sau
qi Ja'afar kam yayi nisa saidai Kuma gobe idan naga dama na baki aronsa, sorry fah babie"
Qit aka kashe wayar taja numfashi tare da tashi tsaye cike da al'ajabi a ranta take tambayar kanta to dama ana haka kenan? Batada me Bata amsa hakan yasata ta koma
ta sake kwanciya kishi na azalzalar zuciyarta hawaye nabin idonta tana karanto addu'ar annabi Yunus “ La'ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalumin" dahakadai daqyar bacci ya saceta itakam tana ganin rayuwa to me tayiwa Ja'afar haka ne daya fara ju
ya Mata baya yana kantafi da mutuncinta.
Washegari har hudu bai shigo gidan ba batayi zuciya ba ta Kira wayarsa akayi rejected takaici ya kamata Amma saita dake saboda kullum Amminta tana fada Mata ibada batada sauqi aljanna ce me sauqi idan ka
iya sarrafa zuciyarka tare da naiman daukin Ubangiji a duk lkcn da wani Abu ya kulleka.
Text ta rubuta Masa da zafafan kalamai da tasan zasuja hankalinsa Amma har dare babu reply hakan yasa ita da kanta ta fara zargin ko wani laifi tayi masa ta sake rubut
a Masa saqon ban haquri ta tura Masa bai biyota ba har wayewar gari idan barawo ya rintsa itama ta rintsa.
Da sassafe saiga Hajiya Kaltume suka gaisa tace “ina me gidan ko ba anan yake bane?" Qaqaro murmushi tayi tace “Eh ba anan ya kwana ba" murmushi tay
i tace “nikam Rafi'ah Anya bazan baki shawara ba a zaman da nayi dake na fahimci kinada tsayawa akan addini sosai alhmdllh Zaki dace a rayuwa Amma fah sai kin tashi tsaye, in baki wani lbr Mana surkarki da tatafi Damagaran bafa kowa take dashi ba neman asi
ri ta tafi na mallakarwa kishiyarki mijinku ta yanda da quruciyarki da komai zaki zama bora bance kiyi shirka ba Amma ki dan tashi tsaye ki tallafawa kanki rayuwarnan ta yanzu baa zama wlh duk wanda kikaga yana fantamawa to ya miqe"
Kallonta take
yi da rashin fahimta tace “ban gane ba Hajiya" miqewa tayi ta rufe qofa ta dawo ta zauna tace “saboda munafukai masu fakar ido am Rafi'ah da Hausa nayi
Miki bayani ki miqe ki dage ki zama tauraruwa a gurin mijinki ta hanyar yan shige² nifa bance ki fita ba
aa ki barmin komai zanyi Miki nidai hadin kanki nakeso"
Saurin girgiza kai tayi tace “astagfirullah Hajiya aa bazan iyaba nikam babu wanda nake dashi daya wucce Allah shine zai iyamin" Shiru Hajiya Kaltume tayi tana nazarin mgnrta kafin tace “Eh hakane
kam kin Kama dahir Allah yasa mu dace" miqewa tayi tace “zan wucce kidai duba maganganuna akwai gyara a rayuwarki idan ba hakaba kinaji kina gani Zaki zama yar kallo" sallama sukayi ta tafi Rafi'ah ta tabe baki tace “dama Hajiya Innah ta fadamin ba Allah n
e take kawoki ba kaji mace yar kalan masifa zata liqamin tsiya ta jamin raba tsaba da mahalicci na" shigewa tayi daki tayi duk abinda zatayi dare yayi tayi addu'o'inta kamar yanda ta saba ta kwanta tanajin cikinta yanata motsi tasan harma da yunwa kasancew
ar damuwar rashin mijin nata ta hanata cin abinci.
Ita burinta bai wucce ko a waya taji lfyrsa ba inda ya kasance duk Kira ana rejected haka ta wanzu idan taga dare yaqi tafiya takan tashi tayi alwala ta nufi mahaliccinta da, da yamma ta gama duk
wani shirinta na karbar miji har dare tana tsara girkinta ta kashe lkcnta wajen shirya masa abinci tagama ta dauki wanka ta harde tana duba agogo takwai Tara goma sha daya Shiru.
Cikin tsananin mutuwar jiki ta dauki wayarta ta katsa numbersa gabanta na fa
duwa ta Kira cikin saa ya daga batare da yace komai ba taja fasali tace “barka da yini" qaramin tsaki yayi yace “inajinki" a sanyaye tace “lfyrka nakeson ji kwana uku bamu gaisa ba" wata qaramar dariya yayi yace “idan banida lfy nan nake jinya saboda haka
indai Ina wajen gdannan kikajini Shiru to qalau nake" Shiru tayi maganganun nata suna hautsina nutsuwarta ta hadiye wani Abu me ciwo tace “ba nufina kenan ba gani nayi baka nemana idan na kiraka ma sai kayi rejected don Allah ka yafemin Best wlh nakasa tun
a kuskurena gareka iyakar sanina dakai cikin watannin da mukayi baka iya barin Abu a ranka wannan ba dabi'arka bace tawace nima Kuma kullum Ina addu'ar Allah ya sassautamin nauyin baki saboda gudun kamuwa da wani ciwon akan matsalar da zan iya maganinta da
harshena"
Maimakon yaji kalamanta sunyi tasiri a zuciyarsa saima tafasa da yaji zuciyar tasa tanayi yace “saime idan kin kamu da ciwon bake kika dorawa kanki ba kwanane yau ban shirya yinsa anan ba ni bama na Bauchi Ina Abuja Kira Kuma banaso ki
daina idan kinqi kuwa ranki ne zai baci a banza sakarya kawai...."
Ajiye wayar tayi da sauri saboda a duniyarta takan hadiye kowacce irin damuwa Amma banda cin mutuncin iyaye shikuma ta lura hakan yafi Masa komai sauqi, zuciyarta suya takeyi sosai nadama
r Kiran nasa takeyi da tasan abinda zai fada Mata kenan, kuka kam har saida taji jijiyar kanta na daurewa ta hqr tasha magungunanta ta kwanta zuciyarta nayi Mata wani irin zafi.
Abu kamar wasa tafiya sai qara miqawa takeyi daga sati antafi wata babushi ba
bu alamarsa waya kam tun ranar da ta kirashi yaci mutuncinta take tsoron kiransa Amma ta wajabtawa kanta kullum saita tura masa saqon barka da safiya dana Saida safe shi kansa abin na damunsa sosai yarasa ya zaiyi ne wani sharadine Ni'imah ta gindaya masa
wai idan ya kuskura taji lbrn yaje inda Rafi'an take sai tasa ya saketa
shikuma tsoro ya shigeshi wani mugun tsoronta yakeji saiya daga waya zai kirata sai ya tuna cewa idan tasan ya kira Rafi'ah cin mutuncinsa zatayi hakan duk zafin kansa zai hqr ya share
, wasa wasa har gashi da wata biyu a Abuja.
Yau tun safe ya tashi dajin wani qwarin gwiwa nason ganin Rafi'ah yana qissima watannin cikinta fitowa yayi daga daki ya tarar da hakimar tasa a zaune tanata fama da tuffa ya dubeta yayi mata murmushi ya
ce “gimbiya yau watanmu nawa rabonmu da Bauchi ne?"
Dagowa tayi ta dubeshi a banzace tace “wata biyu da sati biyu mana wani abune?" Gabansa ne ya fadi yace “aa kawai dai na tambaya ne" yatsina fuska tayi tace “ok na dauka tunanin waccan yar iskar yarinya
r kakeyi" dagowa yayi da sauri sosai kalamin ya tabashi Amma suna hada ido sai yayi qasa dakai yace “ah haba dai kawai dai tunanin cikin jikinta nakeyi"
Wani banzan kallo tayi masa tace “to ko zakaje ne" qasa yayi da kansa yana wasa da yatsunsa kamar wani
qaramim yaron da yaje jiran umarni ta daka masa tsawa tace “tambayarka nakeyi ko zakajene?" Saurin girgiza Kai yayi tare da dagowa kawai sai idonsa ya ciko da qwallah ya miqe da sauri ya haye sama ta sheqe da dariya tace “sakaran banza da kace bakaji saur
a shegiyar baqar kadarar can labarinta ma saiya shafe a duniyar mutane daga ita har cikin jikin nata muga ta tsiya
_More Comments_
_More Typing_
*_43-44_*
_____________________________
_____________________________
Tunda ya shiga dakin ya hade Kai da gwiwa kuka yakeyi sosai kamar yaron goye zuciyarsa na azalzalar sa ya tafi Azare ya gano lfyr matarsa da cikin jikinsa Amma
babu dama tsoro yakeji kada Ni'imah ta fahimci inda ya dosa ji yake kamar idan ya bata Ma
ta rai qonashi Ubangiji zaiyi dabara ce ta fado masa ya miqe da sauri ya rufe qofar ya shige bandaki da waya a Hannunsa ya fara duba number Rafi'ah Amma Babu a wayarsa tsoro ya qara cikashi gami da mamaki duk inda zai duba baigani bs hakan yasashi kiran Ha
jiya Innah ta jima tana ring sannan ta daga daga yanayin muryarta yasan akwai damuwa.
A gaggauce yace “Am Innah Ina Rafi'ah?" Numfashi taja cikin tausayawa halin da dan nata yake ciki tace “anya magaji kana addu'a kuwa" katseta yayi da cewa “inayi Inna p
lease kibani Rafi'ah magans nakeson yi da ita" murmushin qarfin hali tayi duk jikinta