Showing 45001 words to 48000 words out of 69481 words
muradi ba sai kinzama doctor din da zaayi alfahari da ita a fadin Nigeria ki shirya yau zamu wucce Abuja gobe saimu tafi kinji amaryata?"
Yar qaramar dariya takeyi tana shafa qirjinsa ya sanya hannu ya b
alle bottle din rigarsa yajata suka zube a kujera ya sanya bakinsa ya Kama ZIP din rigarta na gaba ya zuge ta tsorata da inda taga ya nufa amma bata Isa nunawa ba yanzu sai rai yazo yana baci hakanan tanaso bataso suka bata lkc wajen romance din juna suna
a haka sukaji ana buga qofar da qarfin gaske kallon idonta yayi itama shi take kallo ya janye yana mayar da numfashi yace.
“Uban waye zaizo yanamin bugun nan da sassafe?" Bude qofar yayi yana huci kawai sai ganin Hajiya Fatsum yayi tsaye tanata huci sauri
n saita kansa yayi yace “da safennan Hajiya sannu shig...." Daukeshi tayi da mari tace “da saikamin iso zan shiga munafuki Koda yake zama ka iya korata kace bacci zakasata sallamamme asararre" shigewa tayi daidai lkcn Rafi'ah ta gama zura hijjab dinta dan
batamasan inda ya cilla Mata rigarta ba a dan darare tace.
“Hajiya sannu da zuw...." Tsawa ta daka Mata tace “dakata irin tsiya barden goyo karki kuskura wannan bakin naki na gadon maita ta ambaci sunana na lalace kamar yanda wannan dan asarar y
a lalace waike makira wacce ta tsotsi kirsa a nonon uwa kinzo daga zuwa kwana hudu kin kanainaye komai wato har tafiyar da aka dade da shiryata da yarinyar nan yar albarka kin hana yanzu dake zaayi ko aikuwa indai nice na haiheka bakai ka haifi kanka ba to
baka Isa ka tafi da yar iskar yarinyar nan ba saidai ka tafi da Ni'imah itace ma ta dace da tafiyar domin ita tayi kalar turawan wannan me baqin jiki da baqar zuciyar bata dace da zuwa canba ka bari idan zaka Niger ko Africa ta kudu ko Kenya saika tafi da
ita nanne ya dace da ita, sannan Abu na gaba wannan cikin dake maqale a mararta ban yarda dashi ba ba naks bane dashi tazo dan bazance a waje kayi Mata ba domin kanada Mata inda kanada rabon a kusa da tuni kasashi a inda ya dace"
Tunda Hajiyan ta
ambaci cikin suka kalli juna tana rufe baki sukace “ciki?" a tare kallonsu tayi da sauri domin tayi subutar baki saita waske da cewa “eh jiya Ni'imah take cemin tana kwance batada lafiya to inba ciki ba menene?" Ajiyar heart yayi ya taka ya qarasa gaban R
afi'ah dake durqushe ya dagota yace “ok babu mamaki ai abin rabone Hajiya am ki manta kawai dama ita Ni nayi Mata dole bason tafiyar takeyi ba
saboda haka kowacce ta zauna kawai zanje na dawo lfy dama wata kwangila ce da zanyi da wani campony so shine nak
eson zuwa na gama komai kafin tsakiyar shekara Amma tunda abin ya zama haka zanyi qoqari na dawo nanda 2 mouths insha Allah"
Harara ta watsa masa tace “ba haka nace ba cewa nayi ka tafi da Ni'imah" qasa yayi da kansa yace “nifa wlh bazan tafi da itaba bat
ada wani amfanin da zatayimin mace sai rakin masifa daka tabata tace ta gaji Hajiya babu ruwanki fah da harkar cikin gidana abinda ya shafi matana kowacce nasan amfaninta saboda haka babu me tsaramin yanda zan rayu da iyalina"
Fuuuu ya juya ya hay
e sama yana masifa muqus Hajiya Fatsum tayi saboda sanin halinsa ba mutunci ne dashi ba ko kadan juyawa tayi ta kalli Ni'imah dake tsaye riqe da qugu tama manta da Rafi'ah a gurin tace “wannan shegen yaron bayajin bari saidai Kai ka bari Kinga muje kawai w
aini wannan lemon kuwa kinbawa shegiyar nan Tasha?" Harara Ni'imah ta watsawa Rafi'ah ta waske da cewa jiya fa saboda wannan snatcher din yace na zauna a gidanmu ni wlh Hajiya na fara gajiya da wulaqancin danki idan bazaki iyaba ki qyaleni na tafi Mana sai
kace dole"
Ranqwashi ta zuba Mata tace "babu inda zaki kinanan Wai an dorawa kwado tanki wato so kike kibarwa baqar ashana gdan ta qoneshi ta qone me gidan ai kece mafitarsa idan ba hakaba kuwa to ganinsa ma saiya gagareni am ki barni da yar shegiyar nan
da qafafunta zata tafi ai duk Wanda yaci tuwo Dani miya yasha ba Amina ba ko Niger ce gabadaya qarewar buzu shegiya me idon aljanu wlh a gidan dana dai baki Isa ki haihuwa saidai kita asarar qwayaye su lalace a banza"
Saukowarsa ne yasa su saurin
juyawa suka fice tananan durqushe inda yabarta ba maganar Ni'imah ce ta batanta Raina ta Hajiya Fatsum ita a komai nata tana hqr Amma batason ana taba Mata martabar iyaye domin batada na biyunsu a duniya, sosai kuka takeyi harda shassheqa tana tambayar ka
nta ita wannan wanne irin aurene takeyi kowa baya qaunarta meyesa qaddararta tazo da wannan simatsin?"
Jitayi ya dagata cak ya nufi saman da ita bai direta ko inaba sai gado ya lullubeta da qirjinsa ta sakarwa kukanta jiniya tana cewa “don Allah ka qyale
ni banaso Ja'afar wlh banason...." Rufe Mata baki yayi yana tsotsa yana sauke numfashi yana tura Hannunsa cikin sumarta tare da dora dayan a qirjinta ta rintse idonta ta tureshi ya fadi gefe kafin ya taso ta tashi a guje kamar walqiya ta shige bandaki shi
dariya ma ta bashi yayi dariyarsa me isarsa ya miqe ya fice daga dakin sake shiryawa yayi ya hade abinda yasan zai buqata ya dawo ya ajiye Mata kudi masu yawa a saman bedside ya fice bangaren Ni'imah ya shiga tananan zaune sai chat takeyi daure da towel da
alamun daga wanka ma ta fito murmushi yayi yace “kinji dadi ko kin hadani da mahaifiyata to meye ribarki don kinsa ta hanani tafiya da Rafi'ah?"
Tashi tayi zaune tace “ko banza munyi biyu babu ai Kuma sai aje a rungumi pillow abinda akewa bazaa samu ba
saidai aci na kwararo" badan ya shirya tsiya ba da kwade bakinta zaiyi Amma dake yasan meye ya taka sai kawai yayi murmushi ya zaro kudi ya doranta a jikinta yace “kinyiwa kanki"
_Sorry yau banida charge shiyasa bakujini ba kuma banyi long typing
ba_
*_Continuation 35-36_*
____________________________
____________________________
*_Cigaban na jiya_*
Ficewa yayi ya koma bangaren Rafi'ah dakinta ya shiga ya dauki qaramin akwatu ya zuba Mata kayanta bai bita kanta
ba yaje yasa a mota ya dauki wayarsa ya kirata Saida tayi ring sai uku sannan ta dauka yace “ki fito Ina jiranki a parking space" yana fadin hakan ya kashe wayarsa yabarta tsaye sake da baki zuciya na raya Mata kartaje sanin da tayi cewa hakan zai bata ran
sa yasata daukar mayafinta ta zura takalmi riqe da wayarta ta fita bude Mata yayi ta shiga yatada ta kalleshi da sauri tace “hajiya fah tace kada ka tafi dani" Saida suka fice a get din ya waiwayo ya dubeta suna hada idanu sai hawaye sharr.
Tsuke fuska ya
yi yace “ikona ne hakan ba ikon Hajiya ba bata Isa ta yankamin yanayi da iyali na ba" daga haka Bai qara cemata komai ba itama taja bakinta ta tsuke sukayita sharara tafiya sune har Abuja a mota kafin sukai Abuja tayi bacci yakai sau hudu ita da kanta tana
mamakin yawan baccin nata cikin sati guda da bikin nasu data zauna sai gyagyadi sai bacci.
Suna Isa gdan yayi parking ya sabi abarsa a kafadarsa ya shiga da ita ciki ya kwantar da ita a kujera ya zuba Mata ido lkcn da take bude idonta akansa murm
ushi ya sauke mata yace “baccinki yayi yawa saikace kasa Anya kuwa bansa babyn ba ta mafarkin na Hajiya" turo baki tayi tace “ni banida komai kawai gajiyar bikincan ne" ya bude baki zaiyi mgn tace “wayyoh kaina..." Saurin riqe Mata yayi yace “meye ya samu
kan?" Harararsa tayi tace “ina ka kawoni?" Tambayar taso bashi dariya ya gimtse tare da daure fuska yace “au bakisan Ina satar mutane ba ai satoki nayi zanyi camping naki nayita baki aiki bazaki koma Azare ba saida kyautar babie"
Duka takai masa da pillo
w ya goce yana dariya ta miqe suka fara zagaya parlourn shammatarta yayi ya fada wani daki ya maqale jikin qofa tabisa ya kuwa rufe yace
“masha Allah abani abinci na ko nayi aiki da qarfin da ilahi yabani na qwata" kukan shagwaba ta fara harda su dire dire
n qafa ya cafketa sama ya watsata gadon yabita ya turmushe sosai sukaba sama hayaqi suka jiyar da junansu dadi inda kowa yake baje fasaharsa wajen sarrafa dan'uwansa duk da bajin dadin abin takeyi ba har yanzu wuyar budurci bata barta ba Amma takan daure t
unda ta fahimci mijin nata bamai takura bane indai kabashi yayi yanda yakeso to kaima zaka samu sauqi hakan yasa take sakar masa jiki tare da tayashi duk abinda ya dauko wannan Abu yayi mugun qara Mata martaba a idanunsa soyayyarta take qara narkewa a ruhi
nsa ta yanda take batattakar duk wani diso na son wani Abu bayan ita.
Wannan dare an more sosai washegari tashin asuba jirginsu yayi zuwa Mexico itadai bazata iya Dorar da tsayin tafiyar ba saboda wani irin yanayi da take a ciki ita ba me lfy ba i
ta ba mara lfy ba, sosai sun qoshi da tafiya tunda suka fara keta sararin samaniya take lefe a jikinsa shikuma sai shafa bayanta yakeyi inda suka bawa na kusa dasu aikinyi sukayita kallonsu suna shauqin jin dama sune, lkcn da suka sauka suka hau mota zuwa
masauki sanyi kamar ya kasheta bata tabajin sanyin azaba irin na qasar ba ganin yanda take rawar sanyi yasasa kunna Mata room hitter.
Tare da bata wata Madara tasha ta haye gadon dake kusa da ita ta qudundune shima shiga yayi saboda ba qaramar gajiya yayi
ba suka Kama bacci tsayin lkc sannan suka tashi tare sukayi wanka suka shirya ya bata wasu kayan sanyi da aka Basu a hotel din tasa shima yasa yabata coffee sukasha tare da cin abinci ya dauketa suka fice darene Amma kamar Rana tsirarun mutane sunata hark
okinsu ta dade da lura da qasashen turawa da larabawa sunfi harkokinsu da dare,
Wani shagon siyayya suka shiga ya lodo Mata kayan sanyi suka fito ya sake biyawa wani gurin ya siya musu hot coffee sannan suka nufi masauki suka fara sabuwar rayuwa dakanta
ta fahimci Ashe sunso suyi ganganci subarshi ya taho shikadai itama da take mace yanayin azabar sanyin yana sata shiga yanayi bare shi namiji lafiyayye dole ya buqaci dumin mace a jikinsa aikuwa tanacin ubanta babu qarya danma yañada tausayi idan yaga ta
shiga yanayi yakan qyaleta.
Satinsu biyar a qasar Mexico ta fara rashin lfy ta gaske da farko ya zaci weather dince ta dameta ya rinqa lodo mata kayan sanyi yana siyo Mata duk wani nau'in abinci da zaisa ta rage jin sanyi Amma daga bisani saiya
fahimci ita sanyin ma takeso batada aiki sai kwanciya a qasa shan ice da sauran abubuwan sanyi ga rashin cin abinci sai tayi kwana uku bataci abinci ba saidai ice ki jus sosai ya shiga damuwa,
To yauma tun safe ya fice sha'anonin daya kawosa qasar ya mat
su ya gama su tafi shi tunaninsa duk wannan yanayin ne yasata shiga ha'ula'iYana wajen harkokinsa yaji hankalinsa yayo wajenta ya dauki wayarsa ya kirata bugu kusan biyar bata dagaba abin ya tsumashi dole ya ajiye komai ya nufo hotel din da sauri ya haura
saman ya bude dakin ya shiga bata parlourn hakan yasashi fara kiranta Amma Shiru bude qofar dakin yayi gabansa ya yanke ya fadi hangota da yayi kwance a qasa a sume bakinta sai fitar da kumfa yakeyi,
Da mugun gudu ya qarasa gareta ya ciccibota jikinsa yan
a Kiran sunanta a gigice yana jijjigata cikin tashin hankalin dabai taba shigaba, dagata yayi cak ya fito waje da gudu da ita ya nufi emergency care din cikin asibitin suna ganinsa suka tareta aka dorata a gadon tura marasa lfy suka shiga da ita wani daki
suka dorata a gado tare da jorner Mata na'urori shikuma sai danna qirjinta yakeyi, jinyeshi likitocin sukayi duk da kasancewar bangarensa ne tashin hankalin da yake ciki bazai barshi ya bata taimakon da take buqata ba,
Duk wani taimako na gaggaw
a Saida suka gama batashi ta fara sauke numfashi sukayi ajiyar zuciya tare da likitocin dashi ya matso yana zana musu irin sign din da ciwon ya fara bayarwa kafin ta kwanta hakan yasasu fara bincikarta cikin saa kuwa bincikensu ya nuna musu ai shigar ciki
ke gareta na wata daya da awanni goma sha daya.
Wani ihu Ja'afar ya saki tare da yiwa Allah godiya ya rungumeta sai hawaye sharr ya sumbaceta yace “ni...Ni dama nasan aurena dake akai wani Abu me qarfi Allah baya hada lamarinsa a banza Allah na gde maka
daka azurtani da samun qaruwa da mace mafi soyuwa a Raina Allah ka kareminsu ka tsareminsu daga sharrin duk wani abinqi" sake matseta yayi a jikinsa hawaye ya kwaranyo mata tun dirarsa ya tasheta taja ajiyar zuciya tare da qara gasqata girman Ubangiji tabb
as Allah buwayi ne gagara misali burin Ni'imah kenan da anyi aurenta da Ja'afar ta samu ciki ta haifi Lil Prince Ashe ba haka Allah ya shirya ba ita da bata taba zataba bare ta kawo ita qaddara ta zaba a lissafin da likitan yayi ma ranar farko daya Santa m
ace ranar cikin ya shiga tabbas girman buwayar Allah abar jinjinawa ce.
Dagota yayi jikinsa cikin sanyin murya yace “har yanzu bakya sona Rafi'ah meyesa kika kasa koyawa zuciyarki son mijinki me sonki da qaunarki uban yayanki Ja'afar haba Rafi'a
h me nayi Miki da kika kasa yafemin ne" rungumeshi tayi ta saki wani Kuma me ciwo tace “ni...nifa ba sonka ne banayi ba inajin tsoron Hajiya ta gane da gaske inada cikinka a jikina JM kasheni zatayi bata qaunata...."
Rufe Mata baki yayi da nasa ya lumsh
e qananun idanunsa itama ta lumshe nata sun jima a haka kafin su saki bakin juna yaja numfashi yace “bandamu da kowa ya tayani sonki ba nidai inasonki Kuma nine zan rayu dake matata ki cire kowa a ranki don Allah ki manta da kowa kinji?" Dagansa Kai tayi y
ayi murmushi yace “bari nayiwa Hajiya Innah albishir nasan zata tayamu farin ciki" da sallama ya fara wayar suka gaisa yace “wlh tananan da sauqi muna asibiti ma batada lfy Lil Prince yana wahalar da ita" dariya yayi yace “aa Innata kawai dai na fadane ko
Prince ko Princess duka Wanda Allah yabani Ina murna" sun jima suna waya tanayi masa fadan rage zafin zuciya me ciki batason yawan fada da fushi hakan yana dabi'antuwa ga yaron dake cikinta idan San samune ma zaifi su yawaita karatun qur'ani hakan zaiyi ta
siri wajen halittar yaro zai dabi'antu da hakan sosai.
Godiya yayi Mata ya miqawa Rafi'ah wayar a kunyace suka gaisa tayi Mata fatan alkhairi suka aje wayar ya sake Kiran qaninsa Jamal ya fada masa amaryarsa tanada ciki steel ya sake Kiran Muhseen
ya sanar dashi kafin dai wani lkc mgnr cikin ta cika wannan family Hajiya Fatsum itace qarshen Kira dake taji lbrn gurin Jamal saitaqi daga wayar sai text ya tura Mata tayi tsaki tace _“tsiyar zanwa fatan alkhairi?"_ tura Masa tayi ya duba sosai zuciyarsa
na tafasa cije lips dinsa yayi yace “tsiya! tsiya!!" Numfashi ya sauke ya miqe ya fita bai jimaba ya dawo yana kallonta tayi qasa da kanta yayi ajiyar zuciya kallonta kawai yana kwashe masa damuwar da yake ciki zama yayi a gabanta yace “bansan me bebie na
yakeso ba a fadamin na tafi ns Nemo" Lumshe idonta tayi tace “Abbansa yake feel....."
_More comments_
_More typing_
*_Ummuh Hairan_*
*_37-38_*
_____________________________
_____________________________
Abin
ya bashi dariya sosai yayi abarsa ta zuba masa ido yayi qiba sosai ya qara haske abinka da farin mutum ta sauke ajiyar zuciya tanajin wani yanayi game dashi, batayi aune ba taji ya dagota cak ya dauketa kamar babie ya sunkuyo da kansa daidai fuskarta ya sa
uke Mata kiss me zafi yaja numfashi yace “bansan me zanyi ki gane irin farin cikin da nake cikiba Rafi'ah inason babien nan na cikinki tabbas shine asalin raba gardama ga duk me hankali yasan cewa zafin rabo shine ya rinqa azalzalar zuciyata Saida na malla
keki sonki da sha'awar kasancewa dake suka hanani duba kowace irin alaqa tabbas inajin cewa da wani qaddara ta gifta dana kasa samunki da zanyi Miki fyade Kuma zaki samu ciki to sai Allah ya dubi kyawun niyyata ya qadarta zamowarki matata mace mafi daraja
aguna"
Lumshe idonta tayi yayi murmushi tare da direta a gadon yace “inasonki Rafi'ah kema kinasona?" Rufe idonta tayi da hannunta tana dariya shima dariya yayi ya miqe yace “har yanzu nakasa samun wannan kalmar kina Sona ya gagareki furtawa ko?"
Fic
ewa yayi ta miqe ta shiga bathroom tayo alwala ta dawo tana duba alqibla ya shigo da kaya a Hannunsa ajewa yayi yana kallonta ta tayar da sallar bayan ta idar ya matsa gabanta ya fito da kayan daya shigo dasu tarkacen ciye ciyene ya rinqa bata wanda zata i
yaci ta karba Wanda bazata iyaba ta kawar dakai da haka saida ta qoshi sannan ya qyaleta.
Likitan ya Kira yabasu sallama suka fito tana kwance a jikinsa suka shiga dakinsu suna shiga ta fada gado duk jikinta batajin qarfinsa shikuma ya fada wanka lkcn day
a fito har tayi bacci ya dubi agogo 10:30pm ajiyar zuciya yayi ya haye gadon ya janyota jikinsa ya matseta yana shafa bayanta zuwa mazaunanta ta sauke ajiyar zuciya tare da bude idonta Dora bakinsa yayi saman idon nata yace.
“ke kikace babie na ni yake bu
qata" turo baki tayi tace “aa nifa wasa nakeyi maka banajin feel naka..." Rufe mata baki yayi yace “ni inaji" daga haka Bai qara