Showing 63001 words to 66000 words out of 69481 words
dago tace “amma Alh ya kamata abawa babie wani Abu yaci akwai alamun yunwa a yanayinsa Kuma k
amar ma Bai cika lkcn haihuwarsa ba aka haifesa" Shiru yayi yana tunani can ya dago yace “ok bari asiyo mishi madara" ficewa yakumayi nurse din tanata kallon Mahir kyakkyawa dashi ji takeyi kamar ta saceshi haka dai tayita zaman kula dasu har Alh Hashim ya
dawo ta hadawa Mahir madara tabashi yasha taci gaba da kulawa dasu.
Kwanan Rafi'ah biyar a asibitin tana samun sahihiyar kulawa inda Alh Hisham ya rasa ta inda zai bullowa Bari'ah matarsa da batun kawo Rafi'ah gdan da yaga yana neman haifarwa da kansa da
muwa saiya share tunanin kawai yaci gaba da kulawa dasu domin ya daukarwa kansa alqawarin bazai taba bari Rafi'ah ta qara shiga wani gararin ba duk abinda Bari'ah zatayi saidai tayi.
Ranar da Rafi'ah ta kwana biyar ana gobe zaa sallameta da yamm
a ta farfado ta Jima tanajin kanta nayi Mata wani yammmm ta kasa bude idonta sai bakinta da take furta “la'ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalumin" sautinta baya fita sosai hakan yasa Alh Hisham bai lura da wuri ba Saida ta bude idonta taja ajiy
ar zuciya ta zuba Masa ido tana kallon yanda yaketa yiwa Mahir wasa, dagowa yayi da sauri ya sauke idanunsa akanta saiya miqe da sauri ya iso gareta yace “kin farka alhmdllh yanzu inane yake miki ciwo?" Zuba Masa ido tayi tanason tuno inda tasanshi Amma ta
kasa zama yayi a gefenta yace “sannu ya jikinki Ina fatan dai Babu inda keyi Miki ciwo?"
Motsa bakinta tayi da niyyar yin magana Amma ta kasa maqogoranta ya kasa motsawa ya sake bude idonsa akanta tsoro da mamaki ya kamashi ya kwantar da Mahir agadonsa
ya taimaka ya dagata ta jingina da bango yayi Mata murmushi yace “dama ba kowacce kalma kike iya furtawa ba kenan sannu Allah ya qara Miki lfy hakanma mun gode Masa" itadai idonta nakan Mahir dinta sai yaga tayi murmushi ta daga hannunta alamun a bata yaro
n, a hankali yaji tace “Ja'afar" sai ya juya da sauri ganin shi take kallo ya ankarar dashi shine take nufi Kuma ta Kira da Ja'afar numfashi ya sauke ya miqa Mata Mahir ta karbeshi tayi kissing dinsa ta fara kiciniyar fito da nononta tasawa yaron sai ya fi
ce da sauri daga dakin
Bin bayansa tayi da kallo tanason tuna wani Abu Amma Babu hali da gaske ta rabu da ciwon hauka da qarfin addu'ar da iyayenta da mijinta da Hajiya Innah da kuma wacce Alh Hashim yasa akeyi Mata Amma fah ta kasa tuna komai Kuma bakint
a ya kasa furta komai sai Mahir da Ja'afar sai addu'a da koyaushe take furta duk wacce takeson furtawa tana bawa babienta nono tana wasa da gashin kansa kyakkyawan yaron nata Kama yakeyi Mata da wani data sani Amma ta rasa tuna wanene Saida ya qoshi ta zar
e nononta taci gaba da kallonsa daidai lkcn da Nuraiba Nurse ta shigo tace “Masha Allah madam kin farka cikin hayyaci yanzu Alh yace kiyi wanka kafin su dawo bari nakai Masa Babien kafin mu gama"
Batace komai ba ta miqa Mata Mahir ta fita bata Ji
ma ba ta dawo ta Dagota suka shiga bathroom ta rinqa nuna Mata yanda zata gasa jikinta tare da tayata sun Bata kusan awa guda sannan suka fito ta miqa Mata Mai ta shafa ta bude wani akwati da Alh Hisham ya hadawa Rafi'ah ta dauko Mata doguwar riga mara nau
yi ta bulawus ta Bata tasa yanda bazata rinqa Sosa Mata aikin cikinta ba sannan ta hada Mata shayi ta rinqa Bata suna kallon juna Nusaiba tayi murmushi tace “meye sunanki?" Itama murmushin tayi tace “Rafi'ah” numfashi Nusaiba ta sauke tace “kinyi saar miji
yanasonki tunda aka kawoki ya daina zuwa kasuwa balle aikin yananan tare muke jinyarki har kudi ya yankemin na kula dake da babienku nayi Miki murna wlh samun miji irin mijinki sai an tona Allah ya qara muku qaunar juna"Kallonta takeyi da rashin fahimta i
tama kallonta takeyi a hankali cikin sanyin muryarta tace “Ja'afar?" Girgiza Kai Nusaiba tayi tace “aa Hisham dai" sake itama girgiza nata kan tayi tace “Ja'afar" to ganin bazata fahimta ba yasa Nusaiba binta da eh Ja'afar.
Shikam Alh Hashim gida
nsa ya nufa cike da fargaba yayi parking ya fito ya nufi cikin gidan rungume da Mahir a qirjinsa hadiman gdan sai kallonsa sukeyi da tsananin mamakin inda ubangidan nasu ya samo danyen jariri kafin ya Isa ciki har saqo ya ishe Hajiya Bari'ah cewar ga mijin
ta Nan dauke da abin al-ajabi hakan yasata saukowa daga saman ta zauna a qasa ya bude qofar ya shigo ya mayar ya rufe ya juyo sukayi ido hudu ta miqe da sauri qirjinta nabada wani daram.
Ya lura da yanayin data shiga shikuma sai yayi Mata murmushi ya zaun
a a kusa da ita ya bude fuskar Mahir ya dago ya dubeta yace “uwargida bani ruwa do Allah" jikinta a sanyaye ta nufi freezer ta bude ta sauko ruwa me Sanyi ya taba yace “yayi sanyi mara sanyi nakeso Mahir zanyiwa addu'a" batayi gardama ba ta sake daukowa da
qaramin cup na glass ta rusuna ta bashi yaja ajiyar zuciya yayiwa yaron addu'a ya dago kansa ya guntsi ruwan a bakinsa ya hada Dana yaron ya rinqa basa a hankali Bai cire bakinsa ana yaron ba saida yaga ya shanye yayi hamdala yace “kinga wani kyakkyawan b
abe Bari'ah Yana burgeni sosai" numfashi tayi ta zauna qirjinta na dokawa tace “ina ka sameshi?" Murmushi yayi yace “ina ranar da naje Dambam karbo Miki magani to ranar Allah ya hadani da uwar yaron nan cikin wani mawuyacin hali abin tausayi da alamun sihi
ri akayi Mata aka kadota daga gdan mijin kinsanni da tausayi saina daukota muka taho nan har Nan gidan mun shigo fah nace ta fito kawai sai ta riqe ciki Ashe aiki akayi Mata aka cire wannan babien a cikinta Kuma aka samu azzaluman da suka haukatata hauka f
ah tuburan, so shine na dauketa muka tafi Gombe General Hospital anan aka rinqa kula da ita nikuma nasa malamai suka rinqa yimata addu'a har Ubangiji ya kawo sauqi yau yanzu haka ta farfado cikin hayyaci saidai fah ta manta kowa da komai sai danta kadai Ba
bu abinda zata iya fada daya faru a baya"
Zuba Masa ido tayi ta kalleshi ta kalli yaron zuciyarta bata yarda da abinda ya fada Amma batason sanya Masa tuhuma da kanta zata tabbatar da abinda qawarta Rahila ta sanar da ita tagani a asibiti shirun
nata ne yabashi damar cewa ki tsayar da zuciyarki Bari'ah bazan cutar dake ba kuma bantaba munafurtarki ba Am Baiwar Allan nan zatazo gidannan ta zauna kafin binciken da nasa akeyimin ya bincikomin inda danginta suke na sadasu da ita so ki nutsu don Alla
h ki taimaka Mata wajen kula da yaron nan ta dalilin taimakonta sai muma kiga Allah ya bamu namu"
Jinjina Kai tayi tana qara kallon Mahir zuciyarta na Bata cewa Raina Mata hankali Hashim yakeyi fah yaje yayiwa yar mutanen ciki ta haihu iyayenta sun koret
a ya dauko zai kawo Mata gidanta ko Kuma auranta yayi a boye yayi Mata ciki shine yanzu yakeson hadasu saboda idanunta daya rufe har Kama taga Mahir da Hisham sunayiMiqewa tayi ta shigewarta dakinta ya bita da sauri yana kiranta don dama ya hasaso faruwan
hakan Kiran duniya ta bude taqi budewa bayason Bata Mata saboda itadin amanarsa ce Amma akan wannan jahadin saidai tayi duk abinda zatayi Allah shine zai fitar dashi.
Ya Jima cikin tunanin abinda ya dace kafin ya juya ya sake ficewa ya koma asibit
in lkcn Rafi'ah ta samu bacci ya zubanta ido yana kallonta a ransa yanajin ninkin
tausayin ta damuwar loosing memories ai ba qaramin abu bane dole tana buqatar kulawa ta musamman sake fita yayi ya samu likitan ya nema Mata sallama suka sallamesu tare da do
rata akan magunguna sannan ya koma da Nusaiba aka had a kayan suka tafi yanata zuba mata sannu suka shiga gidan tanata bin gdan da kallo tana son tuna tasan wani Abu kwatankwacinsa Amma ta kasa Kama hannunta yayi har cikin gdan bangaren da yass aka gyara N
an ya kaita ya kwantar da Mahir yace “ki huta sosai sosai zuwa anjima sai nazo nabaki magungunanki" zama tayi ya juya ya fice ita Kuma ta kwanta bacci ya sake dauketa har yanzu akwai baccin gajiya akanta.
Ranar kwana sukayi shida Bari'ah suna rigima kuka
takeyi sosai wai yaci amanarta Babu wani taimako matarsa ce Rafi'ah saboda yaga Bata haihu ba shine yayi Mata wannan sakayyar yaso fahimtar da ita Amma taqi ganewa shikam da yaji haushi ya dawo parlour yayi kwanciyarrsa cikin dare yaji Mahir na kuka yaso y
a qyaleshi amma yaji bazai iyaba saboda qaunar yaron yakeyi da gaske ya miqe ya bude qofar bangaren a parlour ya tarar da Rafi'ah tasa yaron a gaba itama sai kuka takeyi.
Mamaki ya kamashi yayi dariya shi baitaba ganin wannan rigima ba ki haifi da
a cikinki Yana kuka maimakon ki rarrasheshi Wai sai kema kisashi a gaba ki Kama kuka karbarsa yayi ya zauna yana hura Masa kunne har yayi shiru ya koma bacci ita Kuma Bari'ah ta fitto ta nemansa bata gansa ba zuciya tabata yana dayan bangaren ta nufa a fu
sace ta bude ta shiga sai tayi turus ganinsa kwance a parlourn farko Mahir na qirjinsa suna baccinsu cikin kwanciyar hankali qwafa tayi ta juya ta fice ta kwana zaune tana kuka Wai ya tsallaketa ya tafi gurin shegen dansa.
Da asuba ya farka ya miqe ya kwa
nkwasa dakin Rafi'ah da take zaune tana lazumi ta miqe ta bude ta karbi yaron tare da jinjinawa alamun godiya yayi Mata murmushi ya fice, yana fita masallaci ya nufa lkcn daya dawo ya tarar da Bari'ah ta hade kayanta a akwatu tanata kukan Wai anaci Mata mu
tunci duk yanda yake tunanin shawo kanta ta dadi ya kasa qarshe yace idan ta fita bai yafeba dole tayi hqr bata fitan ba Amma ko abinci ta rantse bazata rinqa bawa Rafi'ah ba bai wani damu ba hakanan ya amince kullum da kansa yake shigar kitchen yakewa Ra
fi'ah girki tea ne zai dafa Mata ya soya Mata qwai da duk wani Abu da yasan zata buqata har tayi sati uku a gidan lkcn tayi qwari sosai ta murje Amma Babu baki sai ido yanajin dadin yanda yaga ta saki jikinta dashi abu daya dake neman wargatsa lissafinsa s
hine yanda take mu'amalantarsa yayi Kama da tanayi masa kallon mijinta sannan taqi karbar sunansa Hisham kullum Ja'afar take kiransa
Yayi iyakar yinsa yaga ta gane ta kasa ganewa inda Bari'ah take qara samun hujja da yanda Rafi'ah take mu'amalanta
r mijin nata da Kuma irin son da yake nunawa Mahir kullum sai yayiwa Mahir shopping idan ya fita takanas Bari'ah da taga bashida niyyar saukowa ya sake Mata bayani tayi tattaki har gidan surukarta tana kuka ta fada Mata cewa Hisham ya kawo Mata mace gda ya
ajiye Kuma harda
ɗ
a a wata majiyar ma ance dansa ne yayi Mata ciki ta Haifa Masa shine iyayenta suka koreta shikuma ya aureta,
Sosai hankalin tsohuwar ya tashi duk da ta yarda da ingancin danta Amma mgnr Bari'ah abar dubawa ce dubanta tayi tace “kije zan
zo anjima idan ya dawo" haka
kuwa akayi da magariba ya dawo daga aiki yayi wanka ya zura doguwar rigarsa ya nufi bangaren da Rafi'ah take domin dauko dansa Mahir da ya qara ku
ɓ
ul
ɓ
ul dashi a parlour ya isheta tana sallah shikuma Mahir na kwance a kusa da it
a yanata kallon sama yasa hannu ya daukesa ya zauna a kujera yana cillashi sama yaji an bude qofar an shigo ya dago da sauri sai yaga Hajiya Rakiya mahaifiyarsa ya shafa kansa tare da cewa “Ahhh Hajiya kece da daren nan?" Zubawa Rafi'ah ido tayi tana tunan
in inda taso sanin fuskar yarinyar tana cewa “ashe haka ka zama Hashim dan shege a zuri'ar mu...." A gigice Rafi'ah ta dago ta dubi Hajiya Rakiya sai hawaye sharr a idanunta shima Hashim saurin kallon mahaifiyarsa yayi yace.
“Hajiya nasan cewa baki yanke
hukunci da ka a mafi yawan lokuta ma baki amsar hujja saman yaqini wlh tallahi banida wata alaqa ta kusa da wannan baiwar Allan bayan taimako, Nan ya kwashe komai ya fada Mata tayi shiru tana nazarin kalamansa ita kanta Bari'ah sai jikinta yayi sanyi ya sh
are qwallar idonsa yace “ke daga ganin nutsuwa da kamalar wannan baiwar Allan bata cancanci wofintarwa ba duk inda ahlinta suke sunanan suna haqilon nemanta jiya nabada hotonta a kafafen yada labarai da jaridu domin a cikitomin ahlinta ko Ubangiji zaisa a
dace"
_Comment_
_Share_
_Vote_
*_Ummuh Hairan_*
[2/1, 7:44 PM] Real Oum Hairan: *_Mbh_*
*_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
*_Telegram Link_*
👇🏻
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7
*_51-52_*
_____________________________
_____________________________
Jinjina Kai Hajiya Rakiya tayi ta dubi Rafi'ah ta miqe ta Isa gabanta lkcn ta idar da sallah ta zauna kusa da ita ta Kama hannunta kuka takeyi sosai, cikin yanayi n
a tausayi Hajiya Rakiya tace “kiyi hqr kinji yata Allah yasan komai Kuma shine yakeda maganin komai" kwantar da kanta tayi a kafadarta ta sake rushewa da kuka cikin yanayin da batasan ya akayi ya wanzu ba ta bude bakinta da cikin watanni hudun baya iya fur
ta komai tace.
“Wlh banida wata alaqa da Hisham a baya ne ma yakemin Kama da uban Dana Ja'afar amma yanzun ya daina...." Miqewa Hisham da bari'ah sukayi tare suka Isa gabanta yakai hannu zai tabata sai ya tuna da mgnrta uban danta Ja'afar tuni ya dawo nut
suwarsa yaja fasali yace “dama bakinki Yana mgn kikaqi yimin mgn tsayin wata hudu?" Cikin kuka tace “aa yaune naji Ina iya furta wasu kalmomin sannan inajin kamar inason tuno wani abu game Dani Amma na kasa don Allah wacece ni ya akayi nazo nan Kuma inane
nan?"
Hawayen tausayinta Alh Hashim ya goge ya fice daga dakin saboda zuciyar Mata ke gareshi abin kuka bayayi Masa wuya Kuma yin kukansa zai qara karya mawa Rafi'ah zuciya, zama yayi yana tunanin abubuwa da yawa da bashu da amsarsu bai ankara ba
yaji Bari'ah nayiwa Hajiya Rakiya magiya akan kada ta tafi da Rafi'ah tayi alqawarin kulawa da ita tare da dauke Mata kewa taci alwashin taya mijinta ida wannan kyakkyawan aiki da yayi niyyar aiwatarwa.
Daqyar Hajiya Rakiya ta yarda tabar Rafi'ah a gidan
tun daga wannan ranar zaman Bari'ah da Rafi'ah ya koma gwanin sha'awa komai tare sukeyi Bari'ah macece me surutu amma tanada hqr da Kuma sanyin hali wannan abin ya dawwamar da qauna tsakaninsu, yauma kamar ko yaushe suna parlourn sunata hirarsu Bari'ah ta
nayiwa Rafi'ah koken matsalarsu ta dubeta tace “akwai wani magani da wani Malamin mu ya sanar damu idan akayi amfani dashi indai da rabo zaa dace ki bani bero da takarda zan rubuta Miki mu fita pharmacy mu nemeshi insha Allahu idan kikayi amfani dashi Alla
h zai dubemu ya bamu babie"
Murna ce ta cika Bari'ah ta tashi ta dauko biro da paper Rafi'ah tayi rubuce rubucenta da rubutunta na likitawa mamaki ya cika Bari'ah ta dubeta tace “dama kinyi karatu ne Rafi'ah?" Murmushi tayi tace “jiya na tuna cewa
Ina da medicine certificate a garinmu Amma na kasa tuna a makarantar da nayi karatu Ina takurawa zuciyata akan tuno wani Abu game dani nakasa kawai abinda brain dina take fadamin ni matar aure ce Kuma ni ba matar qaramin mutum bace"
Shiru Bari'ah tayi t
ana nazarin kalamanta kafin ta miqe tace “idan ance asiri akayi Miki aka haukataki aka baroki da garinku da Mijinki sai kice aa ke ba asiri bane Mijinki
ya mutu Kuma a kalamanki kina bayyana ke matar aure ce na rasa wanne zamu dauka a ciki to Allah dai muk
e fadawa Kuma munsan zai amsa bari na Kira Yallabai idan yana kusa sai yazo yakaimu
Shigewa dakinta tayi ta canza kayanta zuwa doguwar riga tayi rolling mayafin ta fito lkcn da Alh Hisham yake shigowa ya dubeta ta rusuna tace “barka da dawowa" mu
rmushi yayi yace “kun dawo dani ku dole da kukeso to Wai inama kuka samo sunan maganin?" Sunkuyar dakai tayi Bari'ah tace “gulma itane ta rubutamin...." Kallonta yayi da sauri yace “ina kika samoshi?"
Qasa ta sakeyi da kanta tace “akwai wani lecturer din
mu da yake yawan yimana bayani akan abinda ya shafi matsalar haihuwa dayake a bangaren daya shafi matsalolin Mata nayi degree na..." Shiru tayi Alh Hashim yana qare Mata kallo yasan daganan bazata iya sake tuna komai ba shi tausayi na sosai take bashi musa
mman idan tace Ja'afar dinta ya mutu. Ficewa sukayi kowa jikinsa Babu qwari suka inda suke sakaran zasu samu Basu samu ba sukayi Shiru a mota na tsayin lkc kafin yatada motar yace “na tuna a titin government house naga an bude wani sabon katafaren Pharmacy
R&J naji ance na wani babban doctor ne Kuma kamar ance dan Bauchi ne akwai yuwuwar zaa samu acan"
Nufar Pharmacy din sukayi sukabar Rafi'ah a cikin mota Bari'ah na riqe da Mahir a hannunta yaron kyakkyawa dashi Masha Allah fari tass kamar ubansa ta ratsa
jininsa ta fito yanda duk Wanda yasan ubansa yana ganinsa zai iya shaida hakan, suna shiga pharmacy din suka miqa takardar da aka rubuta maganin wani matashin saurayi da alamun shine mamallakin gurin ya karba ya dago ya sauke idonsa akan Mahir gabansa ya
yanke ya fadi.
Miqewa yayi da sauri yana kallon yaron, itama Bari'ah sai tabishi da kallon mamaki kawai sai taga ya miqowa Mahir hannu duk qwuiyar Mahir da baya daukuwa gurin kowa sai taga ya miqa hannu shima yana bangale Masa baki mamaki ya cika
Bari'ah