Showing 30001 words to 33000 words out of 69481 words
ba har azahar tana sama dake litinin cema azumi takeyi sai a lkcn ta bude wayarta text din Ja'afar kusan biyar bata duba ba kiransa ya shigo kamar karta daga tadai danni zuciyarta ta daga suka gaisa ya tambayeta lfyrta
ta amsa yace “ina jiranki a waje" kashe wayarsa yayi tabi wayar da kallo tafi 20 minutes a zaune ya sake kiranta yace “sauri fah nakeyi kina batamin lkc"
A hassale tace “to ka tafi uzurinka mana ko na nemeka ne?" Ransa ne ya baci Ja'afar akwai baqar zuc
iya yace “ok" kawai ya kashe wayarsa ya juya motarsa ya fice zuciyarsa na tafasa unguwa zashi Amma wannan abinda tayi masa yasashi juyawa ya nufi Fam house nasu tun daga shigowarsa Hajiya fatsum take kallonsa yayi parking ya fito a fusace ya shiga bangaren
nata domin tun safe tace tanason ganinsa bai samu
fitowa ba sai yanzu yana shiga ta daukesa da mari ya tsaya cak tare da dago kansa a kasalce ya zuba Mata ido yana cije lebansa.
Shaqarsa tayi tace “nice na mareka magaji ko zaka ramane dan iska maci Amana
kaikam kayi asara meye laifin yarinyar nan Ni'imah daga aurenku ko wata uku baku cikaba zakayi Mata kishiya kishiyarma aminiyarta wannan debabbiyar yarinyar yar gdan Haj Amina sangartacciya lalatacciya aini bansan lalacewarta takai haka ba wlh da ko zaka
mutu bazaka aureta ba..."
Ji yayi daga bayansu an cafe da cewa “wlh Barebari fadawa kowa Shahararriyar yar iskace ta gaban kwatance duk ATBU babu Wanda bansanta ba ke qarewa ma fah Prettyn Lecturori akece mata duk wani lecture daya kwana ya tashi a
ATBU yasanta ansha kamata da lectures......" Rintse idonsa yayi cikin qaraji yace “qaryane Dijah wlh qaryane Rafi'ah ba haka takeba Kuma ku tambayi Ni'imah tafi kowa sanin halinta....." Duka Haj Fatsum takaiwa bakinsa tace “Ni'iman ubanka da uban waye ya f
adi wannan din tun jiya ta kirani ta fadamin na tashi jakada yaje yayomin bincike akai aka tabbatarmin saboda haka tun kafin ka gurbata zuri'arka ka sawwaqe Mata kowa ya Kama gabansa
Komawa yayi ya zauna jikinsa yana rawa sai huci yakeyi tsawa Hajiy
a fatsum ta daka masa tace “Mgn fah nake maka Magaji" iska ya furzar ya miqe yace “bazan iyaba" yana fadin haka ya fice da sauri suka bisa da kallo yana fita mota ya shiga ya nufi gdansa inda Salma da Dijah suka kalli mahaifiyarsu sukace “kinji fah Hajiya
ai dama Hajiya Sahura ta fada sun tsafaceshi a kishi irin nasa wlh da qalau yàke da sai yayi abinda kikace kigafa yanda yake dakama mana tsawa dan tsoron nakima ya daina an cire mishi wlh idan kika sake rabaki zatayi dashi gabadaya kamar yanda ta rabashi d
a matarsa"
Dunqule hannu Hajiya Fatsum tayi ta daki tafin dayan hannunta tace “aa Basu isaba wlh Kaltume ma da take tsafi ta qyaleni ballesu dole ma su barmin dana ba mace na haifawa ba kaina na haifawa" mayafi ta figa tace “ku biyoni" miqewa sukayi suka
bita mota suka shiga driver yajasu suka fice Kai tsaye sukayiwa gdan Alh Nuhu tsinke lkcn Rafi'ah ta sauko tana kwance a parlourn saboda azumin baqar wahala yake bata Ammi tana gefenta tanayi Mata tsifar baqin dogon gashinta saiji sukayi an shigo ana dure
duren ashariya da sauri Rafi'ah ta wuntsulo cikinsu babu Wanda ta sani har garama Dijah suna yanayi da Ja'afar saidai ita baqace a sanyaye ta dubesu tace “haba bayin Allah yada shigowa babu sallama kamar ba musulmi ba....."
Dauketa Hajiya Fatsum ta
yi da mari tace “kaji sabuwar mara kunya Koda yake kyayi ai nasamu lbrnki dana uwarki me daure miki gindin iskanci da bin maza an fake da karatun likitanci ana karuwanci ruwan jiki ya qare an sihircemin dana an liqa masa to bamaso bamason irin tsiya irin j
araba wannan kyaun dan macijin shine yake dada rudarsa to wlh bazamu kwashi jarfaba"
Rafi'ah sai jikinta ya dauki rawa ta rinqa ja da baya suka rinqa tujararsu da zage zage babu Wanda ya tankansu sun jima sunayi itadai sai tsumar jiki takeyi data zuci Wai
karuwa an fake da karatun likitanci ana karuwanci wannan kalma ta girgizata tunda
take bayan Ja'afar babu namijin daya taba riqe ko hannunta Amma gashi uwarsa tana kiranta karuwa, Ammi ma kalmomin sunyi Mata ciwo Amma bazata biye musu ba tasan duk sharrin
Sahura ne miqewa tayi ta Kama hannun Rafi'ah tajata suka haye sama suka barsu a tsaye sai lkcn Aunty Raziqa ta miqe tace “ashe yan iskan da yawa kema kin haifi dan iska domin kuwa babu yanda zaayi idan shi nutsattse ne yayi sha'awar auren karuwa..." Aunty
Murja ce ta katseta da cewa “wai dama wannan itace uwar Ja'afar din kayy Amma albasa batayi halin ruwa ba dan bai tsotsa a nonon uwaba karuwa kuwa saidai ki gani a dakinki" Suma ficewa sukayi daga parlourn suka barsu tsaye kamar dashe sun jima suna rarrab
a idanu sosai suka Raina kansu ashe Suma iyayen Rafi'ah ba faqirai bane sunma fi na Ni'imah Koda yake ita dama Haj Fatsum tasani baqin cikine ya hanata tunawa wani gwauron numfashi ta sauke tayi qwafa ta fice tana cewa “kunyi da yar halak indai nice na hai
fi Magaji wlh bazai zauna da wannan makirar mara kunyar yarinyar ba matarsa yar arziqi daya tilo ta isheshi..."
Tunda su Ammi suka shiga ciki take aikin rarrashin Rafi'ah ta sake botsarewa tanata kuka tana cewa wlh bazata zauna da Ja'afar ba ita baz
ata iya masifa ba kowansa masifaffe shima masifaffe ita bazata iya masifa ba bata sababa, duk yanda ammi take tunanin shawo kanta taqi shawuwa saima qara botsarewa da takeyi tana maimata “Wai nice karuwa Ammi wlh bazan iyaba ni bazan iya masifa ba"
Shikuw
a gogan gdansa ya shiga yana shiga yaci karo da Ni'imah duk ta fashe komai na parlourn hatta show glass dinta bata bariba baiko saurareta ba ya haura saman ya bude wani daki dake kulle ya debo takardunsa ya fito har yaje bakin qofa ya tsaya yace “sannu da
aiki Allah ya qara lfy" Bai jira cewarta ba ya zaro raffers na 100k ya ajiye Mata yayi gaba abinsa ya fice ya tare adaidaita ya fada masa inda zashi airport ya nufa ya hau jirgi sai birnin tarayyah gabadaya Bauchi tayi masa zafi.
Haka kwanaki suketa
turawa a bangare ukun duka babu kwanciyar hankali hauka sosai Ni'imah takeyi duk wani Abu me amfani na gdanta ta lalatashi Yusrah ce tazo gdan taga yanda ta mayar dashi take ta fadawa Hajiya Sahura aikuwa tayo tattaki tazo ita da Hajiya Fatsum nan suka ha
uta da fada suna nuna Mata illar haukanta Hajiya Fatsum tace “ina mijin naku kwana bakwai banganshi ba?" Hawaye ta share tace “nima kwana bakwai bansashi a idona ba nikadai naketa haukana" murmushi Sahura tayi tace “ya hadaki da hawan ruwa ya tsallake ya t
afi yabarki garama ki canza salon kishi wannan haukan bazaisa ki samu abinda kikeso ba"
Hajiya Fatsum taja numfashi tace “ni bantaba ganin jaraba irinta Magaji ba ita kanta Rafi'an ba son auren takeyi ba jiya Muhseen yakemin bayani ni saitama bani tausayi
tun ranar da mukaje mukaci mutuncinta da iyayenta tanacan ana bala'i da ita akan ita saiya saketa bazata zauna dashi ba gashi Yama kashe wayoyinsa gabadaya duk neman duniya an kasa samunsa balle asan inda yake" hararar Hajiya Fatsum Ni'imah tayi tace “qar
ya takeyi munafukace wlh tanasonsa ni nasanta fiye da yanda uwarta tasanta inda batajin sonsa aranta da bai isama ya rabeta ba ranar fa da aka daura aurensu fah da ya dawo yayimin hawan qawara bayan ya gama cemin yayi itace ta tada masa da sha'awa wlh idan
da batasonsa ko ystsanta bazai riqeba tujararriyace ta masifa akan abinda takeqi"
Numfashi Hajiya Fatsum ta sauke tace “malam me hawainiya yace dole sai ta shigo gdannan abinda nakeso dake ki sanyawa zuciyarki salama ki barmu dasu wlh daga ita harsh
i tunda suka taboni saina tashi hankalinsu suda zaman lfy saidai idan anayi a lahira suyi ta shigo din Fatsum cefa" kuka Ni'imah tasa tace “kuma fah itama kwanciya zaiyi da ita kwanciyar aure ko?" Tsaki Hajiya Fatsum tayi tace “to meye don ya kwanta da it
a ke kin cika shashanci dukkanku ya isheku indai Magaji ne" numfashi Hajiya Sahura tayi tace “nidai zan koma gurin na gangare ayi yanda bazai kwanta da itaba don nima banason ya hada shimfida da ita irin Haj Amina jarabane idan namiji ya dandanasu baya iya
rabuwa dasu kinsansu da tsafin tsiya ke yakamata ki fadamin haka tunda kece kike bani lbrn matar babanku buzuwa" haka suka rinqa saqawa da warwarewa basubar gdan ba sai dare sukace Mata gobe ta fito da wuri zasuje gurin Mal na gangare zasu gabatar da ita
sai Rafi'ah ta zama yar kallo Haj Sahura tayi Mata alqawarin gobe zatasa Dad ya canza Mata komai na parlourn ta, sunanan suna saqa da mugun zare Hajiya Innah da Karimah da Hafsatu yayan Hajiya Kaltume da sauran dangin ango sukakai kayan lefen Rafi'ah tare
da sanya lkcn biki sati biyu abinda akayi zaayi wata guda Ja'afar ya murza kambu yace shi yagaji da ajiyar Mata a gidan wasu abashi abarsa kawai haka Mai martaba da Dad suka taushi Abba ya yarda a hakan Dad ne yace shi ya daukewa Abba komai da uba yakeyi
shi zaiyiwa Rafi'ah nan fah gidan Alh Nuhu ya hargitse aka shiga shirye shirye babu Kama hannun yaro ana bikin auta sha lele dinner kuwa Saida aka shirya hudu tun saura kwana biyar bikin ya dawo wani salo harda Prince Day wasu abubuwa da yawa baiyi a aure
nsa na farko ba hatta rawar jikin da yakeyi baiyi a bikinsa na farko ba duk abinda akace yana barin jiki zai zaro ya bayar kowa yasan cewa wannan aure na musamman ne a gurinsa Amma fah baisan halin da amaryar take ciki ba tun ranar da yaje tace bata buqata
rsa ko waya Bai qara kiranta ba balle yaje itama kuwa ta watsar dashi dama baa gabanta yakeba.
Sai dare yaje gidan ya tarar da hakimar tasa a zaune a parlour sai karkada qafa takeyi bai kulata ba ya haye sama yayi wanka.
Saida ya huta sannan ya sau
ko sanye da kayan bacci ya zauna yana danna wayarsa Rafi'ah ya Kira har tayi Ring ta katse bata dagaba ya sake Kira saboda sosai yake azabtar da kansa da rashin jin nata ta daga tayi sallama ya dube Ni'imah yace “ranki ya dade saraki sai Allah wai bakisan
kin sosa raina ba ko?" Banza tayi dashi yayi murmushi yace “shiyasa kullum kike qara mamaye zuciyata kin iyabada hqr sorry My luv wow! Sunan ya hau nikam na gama sa'ar Mata a duniya, am nace ba me kike shiryawa game da shagalin bikin nan ne kinsan fah wann
an bikin na musamman ne banason a samu matsala"
Mamaki ya hana Rafi'ah mgn taji yayi dariya yace “kinada basira ok karki damu zanyi qoqarin naga na daidaita komai...." Qit ta kashe wayarta ita tsoroma yabata saikace zararre shi kadai sai zance yake yana
bawa kansa amsa, kissing din wayar yayi ya kalli Ni'imah ya tashi ya matsa kusada ita yace “uwargida sarautar Mata ke me kike shiryawa ne?" Dannan zuciyarta takeyi saboda hudubar da Haj Sahura da Haj Fatsum sukayi Mata amma qarshe yakaita zuciyarta tafasa
takeyi murmushi yayi yace “mgnr tarihin amarya kece zaki gabatar dashi ranar dinner saboda ke kikasan komai game da ita...." Zabura tayi ta miqe shima ya miqe ya daga Mata hannu yace “baki Isa kice aa ba dolene ramawa kura aniyyarta a gdannan dole kema kiy
i Mata abinda tayi Miki bazata rasa wannan gatan ba wlh Kuma banason son zuciya gaskiya nakeso na rantse
da Allah kikace aa yau saikin koma gdanku Kuma kikayi son rai wajen gabatarwa sai na tsinke igiyoyin aurena akanki"............
_Hmmm uhmm t
ab Allah ya qarawa Bestie's hqr wannan tantirin miji naku ya shirya
🤔
_
_Vote_
_Comments_
_Share_
_Please_
*_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
*_23-24_*
____________________________
___________
_________________
Hayewa sama yayi yana yan waqoqinsa tabisa da idanunta daya kawo ruwa wai itace zata gabatar da tarihin amarya Kuma har yana iqirarin idan taqi zai qara sakinta zubewa tayi a gurin zuciyarta na hantsilowa tace “allah wannan wanna
n irin dan iskan mutunne" ta jima tana kuka kafin ta tashi gwiwa a salube ta shiga dakinta Hajiya Sahura ta Kira take fada Mata abinda yake faruwa ta danna Mata ashar tace
“ke me kikace masa?" Shiru tayi tana tsiyayar hawaye tace “idan nace zanyi mgn Mom s
akina zaiyi nikuma wlh bazan tashi a banza wata tazo taci bulus ba"
Shiru Hajiya tayi daga bisa taja ajiyar zuciya tace “Hakane Kinga bari na Kira uwarshi naji ko zata iya wani Abu" ajiye wayar tayi ta zauna tayi sukuti saida wajen awa daya ta wucce ta ki
rata tace “ki kwantar da hankalinki kije kiyi idan kin tashi ki zagesu tsaf dagashi har ita wannan shawarar uwarsa ce Kinga ko banza kin bata musu taro...." Katse Mom tayi da cewa “mom bakisan Ja'afar ba itama Barebari batasanshi ba wlh duk abinda ya furta
baya masa wahalar aiwatarwa saura fa igiya biyu auren idan na kuskura nayi abinda kukace nasan biyun zai tsinke a bainan nasi"
Tsaki Mom tayi tace “to kiyi abinda ya dace nikam wannan tujararren mijin naki ya fara kaini qarshe wallahi idan na waiw
ayeshi saiya Raina kansa ace aure ko wata uku baayi ba tashin hankali ya cikashi daga wannan sai wannan kayy wannan Ja'afar din jarfa ne gsky Hajiya Fatsum ta haifo mugun iri irin tsiya irin jaraba" haka suka hadu sukayita zaginsa bata ankara da yana tsaye
akanta ba Saida suka gama tana juyowa taganshi harde da hannu a qirji.
Saida taji qirjinta kamar zai tsage tsabar tashin hankali ya shafa gashin bakinsa ya juya ya ficeTsaki taja sosai yaji tsakin amma dake miskili ne bai juyaba ya bude dakinsa ya shiga
ya kwanta yanata juyi babu mataimaki takaici ya cikashi ya sake gyara kwanciya kawai yaja pillow ya rungume.
Amarya Rafi'ah kuwa tananan kullum cikin quncin zuciya take ta kasa karbar auren Ja'afar a qasan ranta kowa dai daya shafeta a salube y
ake hidimar bikin saboda damuwar da tayiwa amaryar tasu yawa duk wata kwalliya da akewa amare taqi yarda ayi Mata hatta lalle da wankin Kai qememe taqi duk wani daya Isa ya fada Mata taji ya fada tayi kunnen uwar shegu shikuwa Abba dama da aka fada masa ce
wa yayi a qyaleta kukanma kansa yakeyi babu meyi Mata maganin damuwarta sai Allan daya jarabceta, ranar ranar alhamis akayi kamu juma'ah takanas Hajiya Innah ta turo me kwalliya akan ayiwa amarya nanma tayi tsalle ta dire itafa bazaayi Mata ba dole haka ak
a qyaleta da yamma likis aka turo wasu arnan motoci domin daukarta wai Prince's day tana kuka tana komai Aunty Murja da Aunty Raziqa suka fito da ita cikin alqabbar da Saida akasha dambe sannan ta yarda ta saka suka sanyata cikin daya daga cikin motocin.
A cikin gidan Sarautar aka ware wani bangare aka kashe masa manyan nairori aka tsara gurin dinner tunda suka shigo sautin sarewi da algaitu ya cika Mata kunne suna busawa da bugun zuciyarta daqyar ta samu ta fara kamo addu'o'i tanayi wasu matane su hudu s
uka nufo matar da take suka bude suka fito da ita suka kamata anata yi musu ruwan kudade da turare itakam sai ruwan hawaye takeyi da shassheqa.
Wani bangare suka nufa da ita suka shiga Basu tsaya ba Saida sukakai qarshe suka qwanqwasa wani daki aka
bude musu suka shiga Saida sukayi Mata guri a gefen
gadon sannan suka russuna suka kwashi gaisuwa suka fice matsowa yayi gabanta ya jima yanajin sautin kukanta tanata shassheqa yanajin diran gunjin kukan nata har tsakiyar ruhinsa ya tsugunna a gabanta ya s
anya hannu ya dage hular alqyabbar.
Babu kwalliya a fuskarta ga hawaye ya bata fuskar Amma bai hana asalin kyaunta fitowa ba, yaja ajiyar zuciya yana qara sauke injin idonsa akanta idanunta a lumshe suke sosai kukanta yake tabashi ya miqe ya zagaya dakin
ya dawo fuskarsa a daure ya sanya hannu ya miqar da ita ya fara qoqarin zare Mata alqabbar ta riqe da sauri ya furzar da iska me zafi ya bude baki yace “ance rabonki da wanka tun shekaran jiya tunda bazaki iyaba ni zanyi Miki yanzu saboda banson qazanta"
Batasan sanda ta bude idanunta akansa ba yaci gaba da qoqarin cire mata rigar ta sake qanqame jikinta tana kuka tace “don....don Allah ja'....." Rufe Mata baki yayi ya dago kanta yace “ki roqeni wani abun Banda wannan tunda Ammi da Abba Basu Isa
su saki kiyi ba ni na isa nayi miki"
Baijira cewarta ba ya faketa ya dagata cak tana kuka tana shure² yaqi sauketa Saida ya dangana da ita bathroom din dama ya shirya terming dinsa kawai ya tsomata cikin ruwan alqyabbar kawaiYa cire Mata nanfa suka Dora
kokawa kowa naji da taurin kai takaici ne yasa baisan sanda ya keta riqar sabuwar atamfar sharratone din ba ta rintse idonta da qarfi jikinta na rawa ganin ta saki Masa tanata ajiyar zuciya yasashi kunce zanin ya zare Mata komai na jikinta pant da bra ka
wai yabar Mata ya fara wanketa tayi tayi ya qyaleta tayi yaqi.
Aikuwa ta Raina kanta ta dirzu miqewa yayi ya bare sabon towel ya miqa Mata fuskarsa kamar Bai taba dariya ba yace “ki tashi jiranmu akeyi ki fito banson sakarcin nan naki" yana fadin
haka ya fice daga bathroom din yama fice daga bangaren gabadaya qarasa wankan tayi jikinta har yanzu rawa yakeyi tana jera masa Allah ya Isa dama Wanda ya fada mass batayi wanka ba, towel din ta dauro ta fito ta ishe wannan matar da taje yimata kwalliya t
aqi da wata me