Showing 57001 words to 60000 words out of 69481 words
yayi sanyi tabbas akwai alamun nasara wata biyu an tafi uku ita kanta baya kiranta tunda ta kirashi tayi masa nasiha tare da fada masa halin da matarsa take ciki na yawan
damuwa da kuka ga ciwon Kai daya sata a gaba ko abinci tasa a gaba saita kasa ci idan ta tambayeta sai tace ita ba damuwarta yazo gareta ba damuwarta ya daga wayarta taji lfyrsa Amma yayi block contact nata kota Kira baya shiga.
Sake katse Mata tunani y
ayi da cewa “don Allah Inna kibani ita wlh inajin idan banjita ba komai zai iya faruwa Inna ko wani abu ya farune?" Numfashi ta sauke tace “akwai damuwa me tsanani a tattare da Rafi'ah yanzu dai ma kar naja maka zance bata gidannan tana babban asibitin Bau
chi suna treatment nata sakamakon jininta da ya hau yaqi sauka yau kwana uku batasan waye akanta ba Amma sunankia take ambata dazu ma da mai martaba yazo sunce indai jininta bai sauka zuwa wayewar gari ba to zasuyi Mata Cx su cire cikin jikinta me watanni
bakwai saboda idan aka basshi zaa iyayin biyu Babu ba itan babu shi...."
Katseta yayi da cewa “Wht Innah Amma shine baku fadamin ba" murmushinsu tayi na manya tace “ai Wai da mukaga ba sune a gabanka ba Ja'afar duk da nasan wani abun bayin kanka b
ane Amma yana ishe hali nidai banga abinda yarinyar nan zatayi maka ba ka dauki wannan matakin akanta kafi kowa sanin yanda akayi auren nan bataso iyayenta basaso rabone kawai me gaggawa ya baka saar mallakarta Amma tazama abar wulaqantawarka kada ka sake
kakai hqrn mutum me haquri da zurfin ciki qarshe idan ya kwance maka rawani duk duniya babu Wanda ya Isa ya daura maka so ka kiyaye"
Kashe wayar tayi ta shiga dakin da Rafi'ah take kasancewar itace a gurinta taqi bari a fadawa iyayenta abinda yake faruwa
koda sukazo asibitin kafin jikin ys rikice tace kada a fadawa Abbanta idan yaji akwai matsala, hakan tasa sukayi Shiru Mai martaba da Hajiya Innah da Karimah sune suketa jele sai Badi'ah yar Hajiya Kaltume ce Amma itama zakkace batayo halin uwa ba zuba Ma
ta ido tayi cike da tausayi duk ta kumbura ta dashe kamar bayan hawan jinin ma akwai wani abin dayake damunta daidai lkcn ta wani zabura alamun allurar ta saketa idonta a rufe Amma sai bige bige takeyi ta qarasa da gudu ta riqeta abinda ya janyo hankalin K
arimah ta shigo da sauri ganin yanda matar yayan nata ta datse harshenta tana make make jikinta yana jijjiga yasata fita a sukwane ta Kira likita ya biyota da sauri suka shigo daqyar ya samu yayi Mata allurar kashe jiki sannan ya Kira sauran ma'aikatan ya
dubesu yace.
“Wannan bazatakai gobeba a yau ayi Mata aiki arabata da cikin nan idan ta qara awa daya zata farka alamominta sun nuna zata iya kamuwa da ciwon jijjiga Wanda zai iya haifar Mata da depression domin kuwa akai damuwa danqare a zuciyarta
" Babu bata lkc suka sanya Mata kayan theater suka turata suka shiga da ita dakin theater sai a lkcn ne Hajiya Innah ta Kira Mai martaba ya daga take fada masa halin da ake ciki tare da cewa “Ranka ya dade fah abinnan yafi qarfin Shiru a fadawa iyayen yar
inyar nan likitoci sun shiga da ita dakin aiki Amma sunce sai wani shaqiqinta ko mijinta ko mahaifinta yasa hannu sannan zasu tabata" miqewa yayi daga kishingidar yace “to bari yanzu zan fito" dakansa ya tuqa mota hankalinsa a tashe sai office din Abba ya
rakitosa suka tafi asibitin Abba baisan meye yake faruwa ba Saida sukaje likitan yayi masu bayani ya shiga rudu da tashin hankali ya dago yace “ina mijin nata to ranka ya dade ai huruminsa ne wannan" qasa Abba yayi da kansa yace “bayanan yana Abuja baimasa
n abinda yake faruwa ba Amma zamu sanar dashi yanzu dai kasa hannu a ceto rayuwarta yafi komai muhimmanci.
Cikin sanyi jiki da mamaki ya sanya hannu jikin takardar daidai lkcn da taxi ta tsaya Ja'afar ya fito suka zubansa ido yana sallamar me motar
ya nufosu Mai martaba gabansa ya fadi ganin irin muguwar ramar da dannasa yayi ga wani baqi da yayi qarasowa yayi ya russuna cike da ladabi ya gaida mahaifin nasa da surikinsa suka amsa tare da tambayarshi hanya yace “alhmdllh" Shiru ce ta dan ratsa kansa
na qasa kunyar Abba yakeji tunaninsa ko yasan meye yake faruwa tsakaninsa da Rafi'ah ganin babu wanda yabi takansa yasashi miqewa ya matsa kusa da Innah ya zauna ya rafsa uban tagumi.
Lkc yaja sosai sannan wata likita mace ta fito dauke da jaririn a towel
me kauri tana zuwa ta tsaya tace “Waye Ja'afar M Wakil?" Miqewa yayi da sauri yace “Gag...gani" gabansa na faduwa ya nufi nurse din tayi ajiyar zuciya tace “petiant dinka ta farka tun dazun saidai bata cikin hayyaci sai yanzu muka samu ta dan samu so Kuma
tunda ta farka take sharar hawaye munyi munyi ta fadi me take buqata bakinta baya fita sosai Amma na iya fahimtar tana cewa Ja'afar M Wakil meyesa kayimin haka me nayi maka alqawarin farin cikin da kayimin kenan irin tukuicin da na cancanta gareka kenan?
Wadannan kalaman tuhumar su taketa maimatawa shiyasa naga ya kamata idan kana gurin kaje kaji meye take buqata"
Numfashi ya sauke me qarfi tare da miqa hannu ya karbi bebien dake nade cikin towel ya bude fuskarsa yaja wata qaqqarfar ajiyar zuciya y
ace “barakallahu ahsanal khaliqin" kyakkyawan yaron me muguwar Kama da ubanshi saidai qanqanta kamar an fyatoshi a hanci.
Juyawa yayi ya nufi dakin da yaga nurse din ta fito rungume da dannasu dan qarami kamar yar tsana, tana kwance saman gadon ya tsaya a
kanta yanajin bugawar zuciyarsa da numfashinsa suna neman daukewa Koda bata cikin yanayin lfy da Kuma walwala ya sani Kuma ya shaida shidin rahama ce garesa a duk lkcn daya rabeta sai yaji nutsuwa tana wanzuwa a cikin ruhinsa.
Idanunsa ya sauke saman nat
a da suke lumshe ruwan hawaye na kwarara, tausayinta ysna ratsa gabbansa ya rasa meye yasa ya qaurace Mata har tsayin lkc haka Kuma ya yanke duk wata hanya da zata sanya ta samu sauqi yanada tabbacin duk wannan halin da ta kasance a ciki shine sanadi domin
da ace bashidin bane bazai kasance Abu
na farko da zata bude baki dashi a wannan yanayin me hatsari ba tabbas aikine ja a gabansa ya dawo Mata da farin cikinta fiye da baya.
Miqawa nurse din babien yayi yace “Asashi a Inquivertor" ficewa tayi s
hikuma ya tsugunna a gaban gadon ya riqo hannun Rafi'ah da yake daure da callular ya hada tafin hannunta da nashi ya matsa a hankali ya dora harshensa saman kuncinta yana lasar hawayen da yake zuba a idonta taja ajiyar zuciya tare da daga hannunta dayan ta
dora a kansa sai ta fashe da kuka ta qanqamesa shima hawaye ne suka zubo masa ya janye da sauri yana qoqarin rarrashinta yace “kinga Rafi'ah ki bari kukannan Kinga aiki akayi miki baa buqatar yawan numfashi ma me qarfi balle kuka"
Ajiyar zuciya tayi ta b
ude idonta akansa shima itan yake kallo cike da tausayi da kunya yace “please kada ki tuhumeni wlh bansan ya akayi hakan ta faru ba ki tayani da addu'a kawai" lumshe idonta tayi kawai kamar mai bacci Amma idonta biyu tabbas tuhumarsa takeson yi saidai ya r
iga ya katse Mata hanzari a hankali tace “ina fatan kana lfy ba wani abune yasa hakan faruwa daya shafi lfyrka ba" a hankali take mgnr wanda sai mutum yasa nutsuwa sosai zai fahimci me take fada tausayinta ya qara cika zuciyarsa yace “lfy Lau ki huta idan
kinji sauqi zamuyi mgn na gde da kyautar dan da kikayimin mai kama dani" bata Kuma ce Masa komai ba suka zauna na kusan 15 minutes a haka kafin ya fita Innah ta shigo ita da su Mai martaba da Abba bude idonta tayi ta saukeshi akan mahaifinta shima Saida ga
bansa ya fadi ganin irin muguwar ramar da tayi, matsawa yayi ya riqota qoqarin hadiye damuwarta takeyi yace “anya babu wani abu a qasan zuciyarki uwar manya nasanki da baqin zurfin ciki menene waye?"
Yana mgnr ne a rikice idanunta ta sauke akan J
a'afar da yake shigowa da kaya a hannunsa yaji tambayar da Abba yakeyi Mata hakan yasast saurin kadanta Kai ko bai haneta ba bazata iya fada ba a ganinta wannan sirrin gidanta ne tsakaninta da mijinta, ganin bazata fadaba yasa Abba furzar da iska yace “shi
kenan uwata banayi Miki dole Allah ya kawo Miki mafita" sakin hannunta yayi ya fice tabisa da kallo gabanta yana faduwa tasan bai gamsu da shirunta ba to Amma ya zatayi sirrin ciki sai hanji tasan babu abinda yàke tabbata a rayuwa dadi ko wuya komai me wuc
cewa ne zata hqr ta jurewa komai akan mijinta musamman da yake uban danta qaddara ta ko Ina ta hadasu batada yanda zatayi dashi bashida yanda zaiyi da ita dole su rufe sirrin juna,
Kwananta uku a asibitin ta samu qwarin jikinta kullum suna tare a
asibitin duk da ta lura har yanzun ba daidai yake ba Basu cika magana ba saidai kallo da ido amma yana kula da ita matuqa ya daukewa likitocin duk wani Abu daya shafeta su kansu suna jinjinawa qwarewarsa tare da mamakin yanda akayi hakan ta faru yana matsa
yin
consultant doctor matarsa ta hadu da irin wannan matsalar me wuyar sha'ani wadda ko mutum ya warke idan ya shiga damuwa take taba tunaninsa.
Ba huruminsu bane shiyasa basu zurfafa ba a fakaice dai suke bashi shawara suka sallamesu kwanaki biyar lkcn y
aron yayi qwari sosai abu na masu abu kamar Wanda aka hurawa iska ya wani cika abinsa jajir dashi qirar ubansa duk Wanda yaganshi sai yace “masha Allah kamar ba bakwaini ba" daganan gdan sarautar akaso wuccewa ya tubure akan cewa shifa bazaa mayar da matar
sa gidannan ba tunda dai ta haihu idanma can dinne baaso ya Gina Mata wani gdan akaita can zai zuba masu kula da ita Hajiya Innah ce ta dage itama akan cewa wlh bazaa kaita gidansa ba a dakinta zata zauna har sai tayi arba'in ita ba lfy ba shima Kuma ba lf
yr ya cika ba kansa na cikin kwartanniya yace akaita can waye zai kula da ita da jaririn"
Daurin gindi ta samu gurin Mai martaba dole ya hqr badon yaso ba suka wucce da ita fada ananma yaso hana kaita part din Hajiya Innah Amma Babu fuska yanaji
yana gani aka wucce da ita bangaren Hajiya Innah daki guda ta ware Mata da parlour aka gyaranta aka zubawa jariri kayan buqatarsa shima wannan da yana ganin gata a gurin wannan family inda yake fuskantar adawar qarqashin qasa ta mafi yawan bangarori,
Sun
ada wata Al'ada a gidan idan aka haifi jikin farko na da namiji qanne mahaifinsa ne zasu siyansa gadon bacci da kayan fitar suna harda bargon dauka a yanda tsarin yake idan baayi yaro hakan ba to qasqancine anayin wannan ne tun kwana biyu da haihuwa ko uku
Amma shi gashi har kwana biyar duk Wanda ya kamata yayi Hajiya Fatsum da Hajiya Kaltume sun hanasu wannan Abu ya damu zuciyar Hajiya Innah da Ja'afar gashi ya siyo gadon anqi kwantar da yaron akai wai banasa akeso ba itakam rafi'ah bata wani damu ba sabod
a batasan zafin al'adar ba sai daren rana ta shidda da Ja'afar ya shigo dakin tana kwance tana feeding din yaronta ya zauna ya zuba musu ido duk ya susuce yace “ina cikin damuwa fah Rafi'ah meye yasa hakan take faruwa dana ya kasa samun gata a dangina idan
har akayi suna baa kawo gadonnan ba shikenan bazai gaji sarautar gidannan ba meyesa komai daya shafeki yake zuwarmin a baibai Meye karfa Rafi'ah dazu Hajiya Kaltume take cemin wai duk matar data haifi Lil Prince aka kasa samun gadon baccinsa daga dangin
ubansa to karface Kuma asalinta jinin bayice harma tana cemin indai akayi suna baa samu ba to wajibine a cireki daga cikin zuri'a domin zaki bata iri meye kalmar karfa take nufi ne....."
_More comments_
_More typing_
*_45-46_*
__
___________________________
_____________________________
Duka na sosai kalamansa sukayi Mata Wanda suka sanya zuciyarta lugude itakam wannan abu na wannan fam yana bata ciwon kai ta rasa meye laifinta meye ta tsare musu, shirun da yaji tayine yasa
shi cigaba da cewa “Al'amura sai lalacewa sukeyi gashi wadda zatayimin wannan alfarmar daga Badi'ah sai Karimah to Badi'ah mahaifiyarta ta hanata dazun take fadamin ta siyi gadon Amma Hajiya Kaltume tace idan ta bada Allah ya daidaitata ita Kuma Karimah ba
bu ita a jadawali saboda kasancewarta qarama a gidannan na rasa ta Ina zan bullowa lamarin nan Allah kibani mafita"
Numfashi taja tare da yunqurawa ya taimaka Mata ta tashi zaune ta dubeshi tace “in advise ka cire jinin bayi Kuma karfa daga sashinka haka
n zaisa ka rinqa samun matifa cikin rayuwarka Ja'afar don Allah kayimin wannan alfarmar inaji ajikina idan naci gaba da zama matsayin mata a gareka zamu wanzu cikin rayuwar qunci Koda kasancewar nasan duk wani Abu daya fado rayuwata to yardar sarkin sarkic
e Wanda baa masa dole,
Ja'afar bandamu da nakasance cikin farin ciki ba indai farin cikina zai tafa darajar wani shiyasa a rayuwata bancika damuwa da dole saina rabi wani ba tabbas abinda Hajiya Kaltume ta fada maka gsky ne Koda akasin hakan ne Toni n
a gasqata maka Ni yar bayice Amma ba qasqantattun bayi ba bayin Allah wadanda suke yarda da duk wani hukunci nasa a ban qasa Ina jiran ka yanke duk hukuncin da zaka yanke Allah na roqeka kada bakawa kowa ikon kawo gadon daraja idan hakan ta kasance ku kore
mu daga garin azare...."
Saurin rufe Mata baki yayi yana girgiza Mata Kai ta zabura ta miqe cikin bala'in da baitaba tunanin ta iyaba ta nunashi da yatsa tace masa “saime Ja'afar shine me danka kirani baiwa kuka ka kirani karfa Ina taka baiwar daka halitt
a sannan Ina taka karfar to duk abinda zakace ko a fada maka ka fadamin na shirya karbarsa Allah ya tsinewa Wanda ya fas...." Dauketa yayi da Marin daya sanyata kifewa a gadon daidai lkcn da Hajiya Innah ta shigo ta rafsa salati tace “meye hakan magaji ba
kada hankali zaka Kai hannunka jikinta yarinyar da ba lfy ta isheta ba meye ma ya farune"
Huci yakeyi kamar Wanda ya hadiyi maciji ya sake nunata da yatsa kawai sai ya juya ya fice a fusace Hajiya Innah ta matsa da sauri ta riqo Rafi'ah tace “meye y
a farune kun ninkeni baibai fah" cikin kuka ta rinqa zayyanewa Hajiya Innah abinda ya faru taja fasali tace “to shine zaki tada hankalinki har kina daga muryarki sama da tasa bayan kinsan halin mijinki ko qalau yake ba hqr ya cikaba balle yanzu da kansa ya
ke dawa Rafi'ah dole ke hqr ya Kama domin ke aka cuta"
Sosai ta rinqa kwantar Mata da hankali harda tayi shiru ta dauki jaririn ta fice dashi tunanin duniya ya damu Rafi'ah gabadaya komai ya daukar Mata zafi tanason ta samu wanda zatayi Hira dashi taji da
di babu Hajiya Innah ta saka Mata ido ko yan'uwanta ne sukazo bata barin dakin saboda kada ta fadi wata mgn da zata fallasa sirrin gidan sarautar tayi kuka kamar ranta zai fita ita daya kamata a rarrasa ita
akewa tsawa harda mari saboda gskyrta wannan dare
dukka bangarorin babu Wanda ya rintsa Ja'afar tunanin maganganun da Rafi'ah ta fada masa ne da Kuma mafitarsa da dansa ya hana idonsa rintsawa ita Kuma alhinin wannan jarabar rayuwa ta zaman qasqanci da boranci tun zamanin quruciya sune suka hanata rintsa
wa Hajiya Innah kuwa tunanin ta inda zasu bullowa wannan al'amari da yanda zaayi su samu gadon daraja ne ya hanata bacci inda Hajiya Fatsum Kuma bokanta yace daga ita har Ni'imah su tube tsirara kowacce a bangarenta su tsaya a tsaye su kwana a haka kada su
yi gyangyadi domin sunayin bacci asirin da suka qullo na haukata Rafi'ah kansu zai koma itakuwa Hajiya Kaltume neman ta inda zata fara bullowa Ja'afar da iyalinsa ya hanata rintsawa Abu na farko daya kamata tayi shine tasan yanda zatayi ta qara shiga tsaka
ninsa da Rafi'ah sannan ta sace wannan jariri kafin wayewar gari.
Kiran sallar asubar farko Rafi'ah ta tashi da wani matsanancin ciwon Kai ta riqe kan da sauri tare da fara karanta izaja'a ta dan samu relief daidai lkcn da taji an bude qofar an sh
igo kasancewar da duhu bataga me shigowar ba ana gama shigowa Kuma sai aka haskenta ido da wata fitila me masifar haske ta yunqura zata miqe abinka da mara cikkakiyar lfy sai tashin ya gagara ta rintse idonta daidai lkcn da taji an watsa Mata wani ruwa any
i baya da sauri.
Aikuwa saita wani yi tsalle ta miqe ta qwallah qara tare da damqar jaririn ta qanqame Hajiya Innah da Ja'afar har gware sukeyi wajen shigowa, Hajiya Innah ta kunna glub ta rintse idonta da sauri saboda tashin hankalin data gani inda Ja'af
ar ya nufeta a guje yana fadin “ Innanillahi wa innah ilaihirraji'un Rafi'ah meye hakan lfyrki kuwa tsirara fa kikayi...." Daukeshi tayi da wani mahaukacin mari tana qara matse danta a qirjinta tana wata dariya me hade da kuka tana cewa “ina ruwanku munafu
kai azzalumai algungumai dukkanku saina kasheku duk Wanda yazo gurina saina harbeshi danane ni na haifi abuna babu me rabani dashi daga yau nasa masa suna mai martaba Muhammadu Mahir eh sunansa kenan sunansa kenan Allah sunansa kenan dana sunansa kenan Ja'
afar ya mutu Mahir maraya ne hhhhhhh Ja'afaru ka mutu ka huta nima na mutu na huta kowa ya mutu ya huta..."
Wani baqin tashin hankali da dimuwa Ja'afar ya shiga ya matsa gurinta saikuwa ta rarumi kaskon wuta