Showing 48001 words to 51000 words out of 69481 words

Chapter 17 - MY BESTIE'S HUSBAND COMPLETE

08 Sep 2026

17

bata damar mgn ba ya kashe musu fitila sosai ya sanyata nishadi salonsa yana tsaya Mata arai bata iya bijire Masa dadine me rat

sa kwanya yake bata itama tana tayashi Saida suka samu nutsuwa sosai sannan sukayi wanka suka kwanta.

Wayarsa da tun farko fara harkokinsu take ruri ya dauka ganin number Ni'imah yasashi tsaki kawai ya sata a silent ya koma ya kwanta ya sake rungume m

atarsa wayarta ce itama ta fara ruri gashi ya hanata tashi  bacci ne ya sakeyin dama dasu Basu suka tashiba sai asuba sukayi sallah suka sake kwanciya 11:00am suka tashi sukayi break ya fice ita Kuma ta danyi abinda zata iya ta sake kwanciya tare da janyo

wayarta.

Missed calls tagani sunfi hamsin ta fara dubawa kusan duk na Ni'imah ne tayi murmushi tare da latsa layin Kira daya ta daga tace “sai yanzu kikaga damar daga wayar tawa?" Murmushi tayi tace “wlh kinsan dake ba zaman kaina nakeyi ba lkcn da kika K

ira Ina tare da mijina shiyasa..." Wata dariya Ni'imah tayi tace “kaji fah masu miji mijine dake ko farka da akaga dama aka baki aronsa to bari kiji na fada Miki wani abu dole idan Mai fili yazo me trader ya dauke abarsa domin kuwa shi kansa yasan bazaiyi

jayayya dame contenar ba to kamar hakane tsakanin ni dake nice me Ja'afar nice matarsa ta farko saboda haka shidin nawane ko kina da ja?"

Rafi'ah bataso kulata ba Amma idan ta barta haka tabbas zata siyawa kanta raini numfashi ta sauke tace “tabbas hakan

e kece matarsa ta farko bazaa taba canzawa tuwo suna ba saidai kinyi zuqu baki tsaya a iyakar matsayinki ba kinaso ki shiga nawa bawai Ina fada Miki bane dominsa aa Ina fada Miki ne domin ki kiyaye harshenki Ni'imah Ja'afar nawane zuciyarsa da ruhinsa dukk

a mallakinane domin ni aka haliccesa ki riqe wannan aranki akwai ranar da zaki maimaita dakank....."

Katseta tayi da cewa “hhhhh taqamarki waike kinyi ciki ko lallai yarinya to bari kiji wlh sai naso zaki haifesa banza sakarya yar fashin miji kawai"..

... Qit ta kashe wayar murmushi kawai Rafi'ah tayi tace “shashasha kawai" Kiran Anti Raziqa tabi tana dagawa tace “uwar hudu tun jiya nake kiranki baki dagawa saraki ne ya hanaki ko?" Murmushi tayi tace “aa a silent na sata sai yau dana danji qwari naketa

bin Kira kema ya fada Miki kenan"Sun jima suna waya sukayi sallama ta sake Kiran ta Ammi itama

dai murnar samun cikin tayi Mata kunya kamar ta nutse Ja'afar bashida kunya duk ya gama bazata a duniya yanzu kowa yasan meye sukayi har suka samu cikin, sosai A

mmi tayi Mata nasiha akan ta qara kwantar da hankalinta su zauna lafiya da mijinta da abokiyar zamantasannan tace abbanta yana gaisheta shima jiya bayan Ja'afar ya kirashi ya fada masa ya kirata Bai sameta ba, a kunyace suka gama wayar bata qara tsinkewa d

a lamarin Ja'afar ba Saida wata wayar ta shigo ta daga tare da sallama jin muryar babban mutum ya amsa yasata shan jinin jikinta,

Gaisheshi tayi ya amsa da muryar Isa ya jima sannan ya sake jan numfashi yace “Sannu Rafi'atuh dama haka Allah yake iko

nsa Allah ya rabaku lfy yabaki lfyr shayarwa da tarbiyya Allah ya tsareku da tsarewarsa jiya magaji yake fadamin na kirashi ban sameshi ba idan yazo kice nace munason takwara idan namiji ne idan macece Kuma to munason princess dinmu ta zama tayi halin uwar

su Innah saboda haka munason asa Mata Nana Hafsatu" itadai a kunyace take amsawa sosai Mai martaba yayi musu addu'a sukayi sallama Saida ya aje wayar sannan ta kashe tata cike da mamaki Ja'afar yawucce tunaninta.

Nan ta yini zaune waya ta ko Ina yimata ak

eyi hatta Hajiya Kaltume Saida ta kirata tayi Mata fatan alkhairi kowa a gidan murna yakeyi zasu fara samun jikan da namiji Lil Prince zaizo qasan zuciyar Kaltume baqin cikine fal duk qudurinta ya rushe idan har ta kuskura tayi saken da Ja'afar ya fara hai

huwa shikenan mulki zai koma gurin Zuri'ar Fatsum sukuma sun tashi a tutar babu kenan, tashi tayi tana kaiwa da komowa tabbas dole tayi wani Abu akan Wannan lamari dole zataja Rafi'ah a jikinta ta hakane zata samu cikar burinta Ja'afar ya jima yana bata ba

rkono ya jima yana cizon zuciyarta idan tabarshi yashata bisillah ta cutu batada hanyar ramawa saita hanyar raba tsakaninsa da Rafi'ah domin ta fahimci duk duniya babu abinda yake qauna kamarta Rafi'ah itace jarrabarsa ita kadaice zaa taba duniyarsa ta gir

giza.

Murmushi tayi tace “Kulsum matanadar makirci Ja'afar lkcn daukar fansa yayi tabbas zaka gane ka tabani" mayafinta ta dauka ta fita ta shiga bangaren bayi ta Kira jakadiya tayi Mata ihsani tace Mata lallai yau tanason ganin Mai martaba, dariy

a jakadiya tayi tace “ai kin biya uwar dakina jeki jirani yanzu zan dawo da sakamako" murmushi Hajiya Kaltume tayi ta koma ta zauna tana karkada qafa awa daya bata cika ba saiga Jakadiya Indo tana rawa tana juyi tace.

“Anyi nasara uwar dakina ki shirya ki

je kawai" tafawa sukayi tace “ki jirani gobe zamu tattauna dole wannan aikin sai kin shigo ciki so nake na tarwatsawa Magaji farin cikinsa gabadaya na hanashi samun nutsuwa a duniya kamar yanda ya hanani amaryarsa tanada ciki nasan kin samu lbr don jiya yi

ni akayi ana celebrating a gdannan zanyi duk me yuwuwa na zuge Mai martaba yasashi dawo da ita amaryar gidannan ta hakane zan samu damar janta jikina so nake nayi amfani da ita wajen ganin bayan mijinta"

Jinjina Kai Jakadiya Indo tayi tace “zaki iya uwar

dakina Amma fah ance yarinyar batada sabo naji suna fada"

Murmushi Hajiya Kaltume tayi tace “babu ruwanki da rashin sabonta ki bari na gama aikina sai na baki naki kedai kiyi qoqari kiga kina nadomin abinda waccan makirar take ciki idan nasan abi

nda suke shiryawa shine nima zanyi amfani da hakan nayi nawa cikin sirri" Jinjina Kai Jakadiya tayi sukayi sallama ta tafi.

Itakuma ta fara shirin tafiya gurin me Mai martabaBayan ta gama komai ta hada masa zobo me dadi da sanyi ta nufi turakarsa sai zub

a qamshi takeyi ta qwanqwasa yayi Mata iso ta shiga yana zaune saman sallaya yana lazumi ta samu guri gefensa ta zauna ya dubeta ta sunkuyar dakai yayi murmushi ya ajiye carbin ya dubeta yace “Uwar gida saqonku ya ishemu dazu ta wajen su Jakadiya muna fata

n dai lfy?"

Qasa tayi da kanta ta tsiyaya lemon a Kofi ta miqa Masa ya karba tayi farr da ido tace “lfy ranka ya dade kawai dai inason ganawa dakai ne saboda an kwana biyu baa zauna ba balle a shawarci juna" shanye zobon yayi yace “wannan gaskiya ne Kalt

ume to ai kudin ne kun fiye rigima shiyasa muka rabu daku" dariya tayi tace “to ranka ya dade ai baayi haka ba tunda Allah yabaku amanarmu ai sai kunyi hqr damu"

Murmushi yayi yace “hakane Allah ya qara Mana hqr" Hira sosai ta barke tsakaninsu i

nda cikin hirar ta lura duk Rabin maganarsa akan cikin da matar Magaji ta samu ne ba wani dadin hirar takeji ba Amma haka ta rinqa daurewa tana nuna masa dokinta akan cikin nandanan zuciyarsa tayi wasai saboda duk Wanda ya nuna yanason cikin jikin amaryar

dannasa dadi yakeji, Nan ta samu dama tace “am dama Mai martaba nikam idan ka bani dama na kawo mana wata shawara Mana" dubanta yayi yace.

“To kaltume muna sauraronku" numfashi taja tace “duba da yanayin auren Yarannan Rafi'ah da Ja'afar da Kuma quruciya

ni sai nake ganin tunda muna raye baikamata abarsu a gefe ita dashi suyi rainon cikin nan ba yakamata manya su shiga ciki domin zatafi samun kulawa ita da jikanmu dake cikinta" Jinjina Kai Mai martaba yayi yace “gaskiyane" sake qass tayi dakai tace “Me zai

hana ya dawo da ita cikin gdannan idanma bazai bari taje wani bangaren cikin gidan ba tayi boffi

ɗ

onta acan ba to ta zauna a bangarensa na cikin gidannan kaga yafi kusa Kuma zatafi samun kulawa fiye da can da suke daga ita saishi dai kishiyar tata Kuma ba

zaman lfy sukeyi ba kullum cikin fada suke saboda ita Ni'imah gani takeyi Rafi'ah taci amanarta to kaga ba wani kulawa zata samu ba kuma ma Koda zaman lfyr ai dukkansu yarane ba tabayi sukayi ba ita haihuwa irin wannan sammatsi gareta Allah shine me karewa

saidai sa idon yanada amfani gaya"

Shiru Mai martaba yayi yana nazarin kalamanta can ya dago yace “kinyi tunani me kyau zamu duba sosai" da wannan suka shiga tattaunawa akan abinda ya shafi cikin gida tana qara tura Masa ra'ayin dawo da Rafi'ah

cikin gdan.

Bangare Ni'imah kuwa tunda ta samu lbrn tabbatar cikin Rafi'ah ta tashi hankalinta ita da uwarta da surukarta babu dare babu Rana suna yason bin bokaye duk bokaye sun kasa sama musu mafita sai guda dayane yayi hobbasan yi musu alqawarin yiwa

Ja'afar din kiranye ya dawo gida idan har ya dawo zai sauka a bangaren Ni'imah to

duk abinda ta bashi zaici wannan karon ba asiri zasuyi ba tsafi ne Amma sai Ni'imah ta yarda an zuqi jininta zaa hada laqani dashi.

Wa'iyazubillah Allah kayi mana tsari da s

hirka, aikuwa haka tabada hannunta bokan na dutsen shadan ya zuqi jininta ya hada da wani qarin magani yace taje tayi turaren gabanta dashi ta tabbatar ya kusanceta to daga haka ksda ta qara komai zataga zuwan da zowar Amma kafin turaren ta gauraya ruwan

rubutun daya Bata da abinci ko lemo ta bawa Ja'afar din yaci.

*_MEXICO_*

Yau laraba ce a Maxico 21/3/ wanda yayi daidai da watannin uku a Mexico suna parlour a zube tana kwance saman jikinsa yana shafa cikinta da ya dan fa

ra dago mararta yanajin dadi sosai Wai shima ya kusa zama Dad murmushi yayi yanajin qauna da tausayinta yanda cikin nasa ke wahalar da ita yace “ina tausaya Miki Bestie babie na yana wahalar dake over" lumshe idonta tayi tace “ni baka wani tausayina bayan

baka dagamin qafa"

Rufe Mata baki yayi ya dagata ya shiga da ita ciki yace “ok haka kikace" Nan fa suka rinqa kokawa daqyar yakaita kasa yaja musu bargo yana Mata dariya yace “sabida Kinga jiya na qyaleki shine kika samu bakin mgn" da turje turjen da kom

ai ya rabata da komai sukayi komai ta miqe tana mita ta shiga bathroom tayi wanka shikuma bacci ya daukeshi bayan ta fito ta sanya kayanta itama ta kwanta ta fara bacci taji ya zabura ya miqe da sauri itama miqewa tayi taganshi riqe da kansa yana furta “a'

uzubillahi minasshaidanur'rajim" jikinsa yana rawa duk gashin jikinsa sun miqe riqo hannunsa tayi tace “fatan lfy mijina" wani gwauron numfashi yaja ya zuba Mata idonsa da sukayi ja saboda bacci.

Baice komai ba ya miqe ya fada bathroom yayo wank

a ya fito ya zura kayansa ya zauna kusa da ita yace “kinci abinci?" Dagansa Kai tayi ya Jinjina ya miqe yace “zan Dan fita ki kula da kanki kafin na dawo" itadai batace masa qala ba har ya fice ta sake kwanciya kanta ciwo yake ita dsma a laulayin ciwon Kai

da amai sune sukafi komi damunta, baccinta tayi sosai sai yamma liqis ta tashi tayi wanka ta shirya cikin wasu fitinánnun qananun kaya tayi kyau sosai duk da ramar da tayi ta dawo parlour ta hada madara da Zuma tanasha tana kallo.

Wayarta tayi ring ta da

ga suka gaisa Hajiya Innah ce take tambayarta jiki ta amsa Mata suka dan taba hira sukayi sallama, tananan zaune zaman jiran tsammani Bai shigo ba har saida tayi sallar Isha ta sake kwanciya waje 12:30am ya shigo ganin tana bacci yasashi bai tasheta ba tau

sayi sosai take bashi abinci kawai yaci ya kwanta shima ya janyota ta bude idonta yace “sorry uwar yayana na dade ko?"

Lbr ya fara bata yace “yau na gama komai daya kawoni qasarnan harma naje nayi mana duk abinda ya dace May be Nan da 1 week mu

tashi zuwa gida am jiya Mai martaba ya kirani yake fadamin idan mun dawo Kai tsaye na kawoki nan gdan sarauta Zaki zauna a bangaren Hajiya Innah harsai kin haihu so nadai nemi alfarmar yabarki ki zauna a bangarena Amma bazan iya barikin ki zauna a bangaren

matan gida ba"

Hakanan tunda ya fara bata lbrn taji gabanta na faduwa taso tayi masa garda sai taga rashin dacewar hakan kawai tayi shiru Amma ranta bai kwanta da komawarta gidan sarautar ba" kwanaki uku ya gamayi musu shirye shirye ta lura da gaske zumu

din tafiyar yakeyi itadai batako kulashi tunda babu wani Abu daya fasayi Mata kulawar da yake bata Bai fasa ba sai kawai mayar da hankalinta akan kula da lfyrta.

Ranar da satin kuwa ya zagayo ranar tafiyarsu ta tashi da azababben zazzabi sosai d

a ciwon Kai ganin yanda yaketa rawar jiki yasa ta boye Masa ciwon nata ta shirya suka fito drivern hotel sinne yakaisu airport suka dago sai Abuja shigar talatainin dare sukayi saboda haka a hotel suka kwana da safe bayan sun karya suka fito shatar mota su

ka dauka har Bauchi.

Daya a Azare tayi musu shine ya dauki kayansu ya shiga dasu cikin bangarenta da yake ya fadawa Hajiya Innah dawowar tasu tasa an gyara musu bangarensu na gidan sarautar to Nan dinma an dan gyarashi saboda tasan qila shigowar dare zasu

yi da addu'a ta sauko a motar saboda tsanantar faduwar gabanta tafi fitowa taji wani jiri ya debeta daidai qofar shiga parlournta ta saki qara ji kake yif ta zube a qasa sumammiya jiyo ihunta yasashi sakin jakar daya shiga da ita a guje yayi waje a kwance

ya isheta cikin wani mawuyacin hali jini sai kwarara yakeyi ta qasanta,

Isa yayi da gudu ya dagota yana jijjigata yana Kiran sunanta daidai lkcn Ni'imah ta leqo daga sama ta hangesu gabanta ne ya fadi ta sauko da sauri ta iso ganin yanda ya gigic

e yasata zagayowa ganin jinin da yake zuba a qasan Rafi'ah yasata sakin ihun kirsa tace “meye hakan Ja'afar ka kaita asibiti Mana jini fah take zubarwa"

Sai lkcn ya iya miqewa ya sureta yasata a mota yana tuqin gabansa na faduwa ganin yanda jinin ke mala

la har lkcn suna shiga ya dauketa suka shiga ciki likitoci suka rufu akanta suna iyakar qoqarinsu sun jima basuga tashin hankali irin wannan ba jinin yaqi tsayawa da sun tsaidashi sai wani ya tsinke gashi cikin yaqi fita sunyi sunyi su cireshi ma ko zasu

samu jinin ya tsaya yaqi abun fah ya zama tashin hankali daga kawotan sunsa Mata jini leda uku, Basu suka samu jinin ya tsaya ba sai wajen shidda na yamma Allah ya taimakesu ya tsaya scaining sukayi Mata abin mamaki cikin yananan qalau dashi Ja'afar ya sau

ke ajiyar zuciya gabadaya yayi faca² da jini yayiwa Allah gdy da babu abinda ya samu cikinsa yasan wannan kariyar ubangiji ce kawai.

Hajiya Innah ya Kira ya fada mata halin da suke ciki itace tazo asibitin sannan ya samu ya tafi gda yana zuwa ya

tarar da Hajiya Fatsum da Ni'imah a parlour sai dariya sukeyi yana shigowa kowacce ta shiga hankalinta Hajiya Fatsum ce tayi saurin cewa “ya me jikin yanzu nazo nake jiran Ni'imah tazo mine mu gano jikin" dadi yaji a ransa yadanyi ajiyar zuciya yace “alhm

dllh Allah ya taqaita cikin Bai fita ba Anna tasha wahala Saida akasa Mata jini leda biyar iya yau...."

Miqewa tayi daga zaman da take tace “bai fitaba fah kace ya akayi ya tsaya naji ance faduwa tayi ruf da ciki Kuma ance jinine ya balle Mata" Jinjina ka

i yayi yace “eh haka Allah yaso" saurin saita nutsuwarta tayi tayi murmushin yaqe tace “to ai gara haka" hayewa yayi sama ya tarar dashi yanda ya tafi ya barshi takaici ya cikashi ya sauko ya fice ya nufi bangaren Rafi'ah anan yayi wanka ya canza kaya ya f

ito ya sake komawa yanzu ita kadaice ta rafsa uban tagumi ya jima akanta sannan taji shigowarsa tayi firgigit ta dawo hayyacinta tare da miqewa tace “ya me jikin?"

Zama yayi yace “da sauqi inajin yunwa" murna ce ta kamata ta miqe ta shiga kitchen

ta hado masa abincin da suka cakuda da magunguna ta kawo masa ya sauko qasa ya bude qamshin abincin baiyi masa ba Amma yunwa yakeji ta gaske haka ya rinqa tsakura yanaci kamar dole daqyar ya iya cokali shidda ya ajiye ya tsiyayi lemon juice yasha badon y

a qoshi ba saidon bazai iyacin na arziqi ba qarni yaji abincin yanayi da alamun naman da akasa Bai samu gyara ba.

Dan kishingida yayi yana latsa wayarsa nan danan bacci ya daukeshi hakan yabata damar miqewa ta kunna garwashi tayi turaren da aka bata sanna

n ta sake zuba wani da akace tayi masa akansa idan ya shaqa nagana ta qare haka kuwa akayi cikin saa ta gama komai ta feshe parlourn d room freshner ta koma ya harde, ya jima yana baccin asara har akayi Isha sannan ya farka da salati yaji kansa ya Sara mas

a kamar irin sarawar da yayi masa ranar da yaji yanason dawowa 9ja.

Bude idonsa yayi ya zubawa Ni'imah data hade cikin wani less me tsadar gaske ba wata kwalliya tayi ba Amma sai ya rinqa ganin tana wani glowing miqewa yayi yanaci gaba da kallon

ta yana sauke ajiyar zuciya sama ya haura sabanin dazu yanzun ta gyarashi yayi murmushi yana Shirin shiga bathroom ta bude qofar da sauri saboda tuna cewa bokan shandan yace idan ta kuskura yayi sallah bayan yaci abincin kafin ya kwanta da ita to komai zai

lalace ya juye kanta,

Zubanta ido yayi babu kunya ta matsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login