Showing 12001 words to 15000 words out of 69481 words
tare dashi sannan ki
fahimci dandanon mijinki ki daina cika masa magi da yaji a abinci kinji tawan?"
Jinjina Kai Ni'imah tayi tace “na gde Bestie ba komai zan iyaba Amma zanyi qoqari kinsan mazan ne sai a hankali Ja'afar ko kallo idan baqatarsa ce ta tashi ba ban ish
eshi ba yanzu ma yake tambayata wai dama kin iya ashar shine nace masa nidai bantabaji ba don ko wani yayi nasiha kikeyi masa ya Kuma cemin Amma ke masifaffiyace nace sanyinki yafi na ruwan freezer ko lkcn yarinta ni nake tare Miki fada ke mgn ma bata dame
ki ba don wani lkcn idan na dameki da surutu har kuka kikeyi hawayenki yafi komai arha shine yace yanason mace me saurin kuka nace to aikuwa ke sannu ma kuka sakesaki"
Haushine ya cika Rafi'ah tace “kewai bakida hankali ne kike yabon mace a gaban mijinki
?" Dariya Ni'imah tayi tace “haba ai mace kikace ke kuwa jini daya nakejinmu nasanma bazaiji komai ba yasan ni dake Abu dayane balle wannan dan girman kan idanfa ya tambayeni na bashi amsa sai ya tabe baki yace meyesa ban zama kamr ke ba sai nace bansani b
a kawai sai yace Allah ya kyauta yaci gaba da danna system dinsa" murmushin takaici tayi tace “ok ki daina ko Yusrah ki daina yabo a gaban mijinki ki rinqa yabon kanki kinsan zuciya tsokace batada qashi kinji Bestie na ki kiyaye harshenki don Allah ni zan
kwanta kije ki shirya ki dauki littafin nan Zaki samu yanda zakiyi dashi a daren nan"
Ajiye wayarta tayi tana mamakin hali irinna aminiyar tata dole aiki ya sameta zatayi qoqari Koda bataje inda takeba take bata gudummawa domin da alamun da gaske ta
na buqatar kulawa so takeyi dole ta qarfi kamar yanda Ummanta take juya gidansu itama saita juya gidanta Wanda samun hakan da alamun zaiyi wahala.
Wata baquwar number taga an kirata da ita ko kusa ko alama batayi tunanin komai ba ta daga jin ajiyar zuciya
r yasata kasa kunne domin sauraron jin dawa take mgn, a sanyaye cikin muryarsa me cike da kwarjini da qasaita yace “bestie meye ribarki don kinyi block mijinki kinajin na dameki ne? Ashe dai duk halinku daya da qawarki?"
Wani dogon tsaki taja ta kashe wa
yarta yakira yafi so goma taqi dagawa qarshe ma ta kasheta don da gaske ta fahimci akwai alamun tabuwar qwaqwalwa ga mijin aminiyar tata, washegari ta fice da wuri daga Hostel din ta nufi Venue dinsu ta zauna tana nazarin wani littafin biology taji an tsa
ya akanta bata dago ba da farko saboda tunaninta Nina ce dan dago idonta tayi ta cikin farin glass din dake sanye a idon nata ganin takalmi sawu ciki yasata dagowa tunaninta Taheer ne abokin karatunta da yake nacin sonta.
Annurin fuskarta ne ya
dauke ganin JM ne tsaye sanye yake da alqabba irin tasu ta sarakai hannunsa zure cikin aljihun alqabbar sai baza qanshin wani tsadaddan turare yakeyi me kwantar da hankali fuskarsa dauke da murmushin daya fito da siririyar wushiryarsa, sake tsuke fuska ta
yi ta fara tattare kayan karatunta zata fice ya ya dora qafarsa ya tare hanyar tare da cewa.
“Bestie kin tashi lfy?" Rafi'ah akwai Dara daran idanu hakan yasa harara bata Mata wuya aikuwa ta jefeshi da wata zazzafa da tasa zuciyarsa harbawa yayi qasa da i
donsa tare da zama, zare glass din idonsa yayi yace “zauna muyi mgn don Allah meye kikejin tsoro ne nidai nasan babu macen data Isa tace batasona saboda duk inda namiji yake nakai please ki tsaya mu fahimci juna Rafi'ah muyi auren qauna kada wani qaramin d
alili yasa ki bijirewa hukuncin Ubangiji to waima ni meye laifina ne da har kika daga hannu kika mareni kinsan jiya Marin nan ya hanani bacc...." Dafe kuncinsa yayi a karo na biyu data daukeshi da mari ya dade dafe da kuncinsa yanabin Hall din da kallo ya
sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya ganin dagashi sai ita a hall din ta sake maida hankalinta a tattare kayanta kawai taji an ruqo weast dinta ta baya.
Ya dora hannunsa a saitin ask dinta duka biyun ya miqe lkcn da tayi mutuwar tsaye ya hada gabans
a da bayanta qirjinsa yana gugar bayanta ya matseta tare da Dora kansa saman nata yaja fasali tare da sakin wata qaqqarfar ajiyar zuciya, sai lkcn ta samu damar dawowa nutsuwarta ta sanya hannunta domin bambare nasa Amma saima ya qara matseta ya janyo hann
unsa sama daidai tushen qirjinta ya Kama sosai ya riqe yanda yasan duk qarfinta bazata iya motsi ba saboda wata matsiyaciyar kasala daya saka Mata ta bazata ya bude bakinsa muryarsa na shaking yace “ko
kasheni zakiyi bazan fasa cewa inasonki ba Rafi'ah I
really love you wlh tallahi ko zan mutu saina aureki"
Yanayin da takeji tasa ta kasa ko daga hannunta sai tafasa da zuciyarta takeyi dumin hawayenta da yaji a hannunsa yasashi juyota ganin yanda ta rintse idonta Zara zaran eyes lasher's dinta suka
sauka kan beauty face dinta da hawaye yake wankewa yasashi cika da sauqi baisan sanda yakai bakinsa ya fara tande hawayen ba kawai sai shima yaji zuciyarsa ta karye daqyar ya daure ya hadiye nasa hawayen yanajin bugun zuciyarsa na qaruwa tunda yake baitab
a ganin masifa irin wannan ba shekara da shekaru anaso ya nuna waccce yakeso ya kasa lkcn da Allah ya nuna masa abinda ya dade yana nema Kuma sai abin yazo musu a baibai tabbas akwai sarqaqiya cikin lamarin shidai duk juyin da duniya zatayi bazai janye qud
urinsa ba saboda yasan hakan shine kawai zai dawwamar da zuciyarsa cikin fayyataccen farin ciki,
Janyewa tayi daqyar daga jikinsa ta durqusa a qasa ta kama qafarsa cikin kuka tace “don Allahu huwar Rahamanu Ja'afar Wakil ka daina bibiyata ka janye wanna
n mugun nufin naka akaina wlh ka dauko hanyar ruguzamin rayuwata ne please Ja'afar nayi maka alqawarin ko wani lapse kega Bestie na wlh da qarfin buwayar Ubangiji zata gyara nidai ka rabu dani Allah matuqar ace babu wani namiji bayankai daya saura a duniya
to zan aminta na gama rayuwata babu aure...." Murmushi yayi ya durqusa ya sanya hannu ya Kama hancinta yana murmushi yace “nikuma ko duk duniya matane yanzu ke kadai nake muradi matsayin Mata wlh tallahi matuqar baki amsamin buqatata ba to kuwa zakiyiwa B
estienki asarar igiyar aurenta......."
_Vote_
_Share_
_Comments_
_Please_
*_Ummuh Hairan_*
[1/3, 9:08 AM] Mrs AA Fansah: *_My Bestie's Husband_*
*_Oum Hairan_*
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
*_Dedicated to Mom
twins and Ummu Safnah
🤩
_*
*_9-10_*
Da wani irin sauri ta dago ta kalleshi ya miqe tare da daganta gira yace “wannan shine matakin qarshe da zan dauka indai burina ya kasa cika to zan rusa farin cikin kowa Rafi'ah kinsani kinsan nasani auren
a dake ba haramun bane shin bayan Allah da manzonsa wa kikeso ki birge, wa kikeson farantawa da zakiyiwa kanki asarar masoyi?"
Kallonta yayi na dan lkc kafin ya hadiye wani yawu me zafi yace “dole cikin sharrudana idan na kiraki ki daga indan kikaqi na ra
ntse da kadaitar zati saina dawo Miki da qawarki gda domin batada wani amfani a gurina ba ita nake buqataba ke nake buqata haba haba Rafi'ah shin waima kintabajin inda akayiwa namiji dole ne nifa a duniya ke na faraso tayaya zanyi sake damata ta kufcemin?"
Baijira cewarta ba ya juya Saida yaje qofar hall din ya juyo yace “zan kiraki anjima ki kula da kanki" yana ficewa ta zube a gurin cikin toshewar qwaqwalwa da rashin madafa tabbas tana cikin ha'ula'i tama kasa tuna abinyi sai jujjuya biro da take
yi idonta hawaye nata sitirya tanajin yanda zuciyarta ke bugawa da qarfi kwantar da kanta tayi saman kujerar tanajin wani zazzabi yana sauko mata ita dama bata iya sanya damuwa aranta ba yanzu zata fige ta lalace, tananan zaune kamar hoto batasan sanda hal
l din ya cika da mutane ba saiji tayi an dafata ta dago idanunta da yayi jajir saboda kuka ta saukesu akan Nina.
Nina tace “naga mayenki ya fita dame yazo?" Numfashi ta sauke tace “ya akayi yasan inda nake?" Shafa Kai Nina tayi tace “guy dinne kwarjininsa
ya Isa yanda baka Isa ka Raina masa hankali ba wlh tambayarki yayi akazo aka nemeki baa ganki ba shine yace a samo masa wata da takeda kusanci dake so shine akazo aka kirani Ina zuwa na raina kaina Ashe ma Prince Ja'afar ne tabdi aikuwa kina ruwa don wlh
soyayya da yayan sarauta bala'i ne baqin naci ke garesu indai su suka furta sunasonka Amma idan aka samu akasi Basu sonka ai ka kade har ganyanka"
Fasali ta sauke ta share hawayenta ta miqe saboda ta haqiqance komai ma yauma bazata gane ba wani gard
en ta nufa ta samu guri ta zauna ita kadai qwal kowa yana gurin daukar darasi ita kuma zuciyarta tanata kaiwa da komowa wajen tunanin mafitarta akan wannan sarqaqqen lamari daya tunkarota babu shiri tunda ta zauna ta kasa samawa kanta mafita ji tayi gabada
ya makarantar ta daukar Mata wani masiffafen zafi idan taci gaba da zama komai zai iya faruwa da ita.
Wannan tunanin yasata tashi ta koma daki ta dauki hand bag dinta da kudade ta fice batare da tabari Nina taganta ba ta samu shatar mota har Azare babu za
to kawai Ammi sai ganinta tayi Aunty Murja ta miqe ta tareta tana cewa “subhanallahi uwar manya meye ya sameki a goshinki haka?"
Fadawa tayi jikinta ta rushe da kuka ta kasa furta ka kalma daya hakan yasa tajata suka shiga ciki Ammi ta miqe tabi bayansu k
anta ta dora a saman qafar Ammi tace “Ammi..." Amsawa Ammi tayi tana shafa kanta tare da zame Mata dankwalinta tace “kinasona Ammi?" Mamaki tambayar tabasu suka kalli juna anti Murja tace “to uwar manya waye zaice bayasonki wlh munasonki"
Ajiyar z
uciya tayi tace “meyesa yakeson kasheni da kalamansa?" Abin ya daurensu Kai suka hada baki sukace “waye?" Kuka ta sake sawa tace “my Bestie husband" a razane suka dago dukkansu sukace me yayi miki?" Cikin matsanancin kuka tayi musu bayanin komai Ammi ta ri
nqa sallalami tana tafa hannu inda anti Murja tayi shiru itama tana mamakin wannan tashin hankali.
Dagowa anti Murja tayi tace “no wonder biri yayi Kama da mutum wlh tun ranar da yazo ya kaiki makaranta na fahimci wani Abu gashi kullum sai yazo yagaida ab
banku" Ammi ce tace “tabdi Amma wannan yaro yakai mara kunya to yasaketa Mana ba kansa zaiwa asara ba shashasha ya dauka ke sakarya ce da zaki biye masa kuci amanar aminiyarki har wani da aure aa da uban aure yakesonki" fada Ammi takeyi ta inda tashiga ba
tanan take fitaba kamar ta ari baki tare da yiwa yar tata kashedi me qarfi da nasiha Saida taga hankalinta ya dan kwanta sannan tace “kiramin shi na tsawatar masa" daukar wayar tayi da murnarta zata kirashi Aunty Murja tayi saurin riqe hannunta tace.
“Amma Hajiya kinsan cewa hakan ba haramun bane ko?" Numfashi Hajiya ta sauke tace “nasani qanwa to Amma Kuma ai kunya tanasa kabar halal yanzu idan mukayi sake mgnr nan ta fita da wanne ido zan kalli Hajiya Sahura ita Kuma Rafi'ah da wanne ido zata kal
li Ni'imah haba tofin ala tsinen ma duniya kadai ai ya ishemu balle Kuma ga wannan aminci daya zama zumunci nikam gara a take abin tun anan namiji ba kunyace dashi ba" duk yanda Anti Murja taso hana Hajiya Ammi Kiran Ja'afar taqi ta dauki wayar Rafi'ah ta
dauki number say ta kirashi jin muryar babba ce yasashi saita nutsuwarsa yana kallon Muhseen tace.
“Sunana Hajiya Amina nice mahaifiyar Rafi'atuh yanzu da dawomin a hargitse tana kuka harma da alamun zazzabi a jikinta take fadamin abinda ke faruwa so don
Allah a daina wannan wasan Ja'afar bashida amfani zai taba musu zumunci kasan Mata da kishi" numfashi ya sauke tare da sake saita muryarsa yace “ba wasa bane Ammi iyakar gaskiyata kenan wlh bazan iya hqr da Rafi'ah ba saboda ita nakeso qaddara ce kawai ta
bani qawar....."
Katseshi Ammi tayi da tsawa tace “karna kumaji banason shirme kaima Ashe sakaraine haba Ja'afar ya zakabari shaidan yayi tasiri haka a kanka Ina zakakai haqqin raba zuciyoyi biyu Rafi'ah da Ni'imah abotarsu tun suna qananu girma
da bambamcin ra'ayi da sabawar halaye baisa sun rabu ba saikaine zaka nemi rabasu to indai dama burinka kenan rabawar kafin ka raba ni na raba Rafi'ah tabar matarka har abada...."
Saurin kallonta Rafi'ah tayi tace “Ammi...." Hannu ta dora Mata a baki tac
i gaba da cewa saboda haka ka kiyayarmin yata bakai babu ita har gaban abada soyayya ta haramta gareku ko babu ran Ni'imah balle tana raye...." Yanason yin mgn Amma fir Ammi taqi bashi dama ta kashe wayarta tana tsaki ta dubi Rafi'ah tace “kekuma ki sawa z
uciyarki salama ki janyewa Ni'imah har zuwa lkcn da komai zai daidaita dama bawai son naki yakeba so yake ya rabaku shine ya bullo tanan saboda haka kiyi cooling mind dinki kinji"
Jinjina Kai tayi ta miqe tayi wanka ta dawo ta kwanta wayarta tayi
ring tana dubawa taga sabuwar number da yayita kiranta jiya ce ta kashe wayar gabadaya tayi kwanciyarta bacci ya dauketa ko babu komai zuciyarta ta samu nutsuwa bacci tayi sosai har yamma dake bata sallah ta tashi ta sake wanka ta zari key ta fice ta tafi
gidan yayarta Raziqa acan ta qarasa yininta sai dare ta koma gida taci abinci ta kwanta zuciyarta ta samu nutsuwa tunaninta yana bata mgnr da Ammi tayi masa zaisa ya janye.
Bude wayarta tayi saqon farko da taga yana yawo akan sensor din ta bude shine ya r
ubuta Mata _“wahala zagi duka dauri a gdan yari bazaisa zuciyata ta hqr dakeba Rafi'ah inanan akan bakana inasonki Kuma aurenki zanyi ki haifamin kyakkyawar Baby kamarki"_ bata gama karantawa ba Kiran Bestienta ya shigo gabanta yabada wani rass tadai daure
ta daga ta Kara a kunnenta tace “bestie da darennan haka...." Kuka taji ta fashe dashi tace “na shiga uku Rafi'ah Ja'afar ya sakeni wlh bansan me nayi masa ba..."
Batasan sanda ta hantsilo daga gadon ba tace “wht! Garin yaya?" Kukane ya hana Ni'
imah mgn Saida tayi me isarta tace “wlh bansani ba nidai qalau muka rabu dashi kawai naga ya dawo yana huci ya shiga dakina ya Kama hadamin Kaya na biyosa Ina tambayarsa kawai sai cemin yayi gda zanje na huta idan ya dawo daga Abuja zai nemeni, inata murna
ta muka fito Saida ya kawoni gda ya zaro kudi yabani kinsanni da kudi kamar mejin yunwa da abinci na karba nayi godiya saiya zaro takarda ya miqomin yana murmushi nace tameye budar bakinsa sai cemin yayi nice katangar da nake neman kare mass cikar burinsa
qila idan ya nesanta dani ya samu muradinsa.
Yana fadan haka yaja motarsa ya fice daga gidanmu yabarni tsayi Ina dubawa naga saki daya ya rubutamin wlh yanzu haka Ina asibiti Rafi'ah wai Ashe yanke jiki nayi na fadi, ya zanyi Rafi'ah inason mijina meye ya
sa ya yankemin wannan hukuncin?" Sosai Rafi'ah take kuka tana furta Hasbunallahu wani'imal wakil a ranta tana Jinjina girman rashin mutuncin Ja'afar Ashe da gaske yakeyi zai iya sakin Bestienta to meye laifinta da zai hucce fushinsa akanta ya sawa aurenta
rauni?
Ta tafi wannan tunanin taji Ni'imah tace “Rafi'ah kiyi wani abu don girman Allah yaqi daga wayar kowa na gdanmu qila ke ya daga taki please Rafi'ah ki taimakeni kada
Ja'afar yayimin nisa wlh bazan iya rayuwa da wani namiji bashi ba" numfashi Rafi'a
h ta fusgo tace “ok ki kwantar da hankalinki insha Allahu zanyi qoqarin ganin komai ya daidaita please ki daina kuka haka kada wani ciwon ya shigeki bari naji ko zan sameshi"
Kashe wayar tayi cikin dimuwa da gushewar hankali ta taqarqare ta runtu
ma ihu abinda yaja Ammi da anti Murja suka shigo dakin a guje har suna hardewa suka tarar da ita riqe da Kai tana ganinsu ta tashi tana jifa da abubuwa tana cewa “na shiga uku no Rafi'ah Allah meyesa kayimin haka ya saketa Ja'afar ya saketa akaina meyesa y
a aikata haka...." Riqeta Ammi tayi tace “ya saketa fah kikace?" Dagakai tayi tace “wlh yanzu ta kirani tana kuka take fadamin Ammi ya zanyi ne ni Bestie tanason mijinta shikuma yana sona wlh ko mijina takeso zan iya sallama matashi balle natane ni Ina zan
sa kaina ta Ina zan fara ne?"
Zaunar da ita Ammi tayi tace “kai ni bantaba jin masifa irin wannan ba wannan wanne irin international dan iskane duk wata hanya ta maslaha kulleta yakeyi Kuma yana sane yake kulleta" numfashi anti Murja tayi tace “dama Saida
nace kada ki kirashi Hajiya yanzu gashi an bata goma daya Bata gyaru ba kuma babu me gyara wannan barakar sai Rafi'ah daganan ne zuciyar mutane zata fara rawa a fara tunanin wanne irin matsayine da ita a gurinsa da iyaye zasu kasa sashi Abu ita tasashi Ki
nga sai a shiga komar bincike da an binciko gaskiya shikenan Abu ya lalace"
Kuka Rafi'ah takeyi kamar ranta zai fita itakam Ammi abin ya girmi tunaninta dole ta fice daga dakin anti Murja ce tayita rarrashinta bata gamayin Shiru ba wayarta ta fara
ring ta dauko da sauri number Muhseen ta gani cikin zaquwa ta daga “ya haka suka tambayi juna a tare" taja numfashi tace “meyesa abokinka zaiyimin haka meyesa zai yiwa soyayyar Bestie na irin wannan mugun butulcin meyesa zai sanya rayuwata a kwale²n masif
a wannan wacce irin lukutar jarabace Muhseen ya Ja'afar yakeso nayine wlh kaina ya kulle na rasa Ina zansa kaina ko babu Ni'imah Ja'afar baiyimin ba a matsayin miji balle tana tsakani tayaya yakeso na tunkari wannan gudumar masifar da ya jefani a ciki?"
F
asali Muhseen yaja yace “wlh akwai matsala Rafi'ah duk wata qofar alfarma Prince Ja'afar ya