Showing 18001 words to 21000 words out of 69481 words

Chapter 7 - MY BESTIE'S HUSBAND COMPLETE

08 Sep 2026

5

gaske tabdi kina ruwa Dan kuwa duk juyin da duniya zatayi indai

manya suka shiga mgnr nan to kuwa saikin aureshi Kinga aminta zata qara qarfi gaku aminai gaku kishiyoyin juna...."

Batason shirmen Nina don sosai zuciyarta take tuquqi har wani daci takeji a saman harshenta itakam ta gamu da alaqàqai ya zatayi

ne Ja'afar ya gane Kuma ya yarda batasonsa zama tayi dabar bisa gado tana jin kanta na wani juyawa yau duk arhar hawayenta ya qafe qaf yaqi zubowa namiji hankaka tabbas namiji buhun qayane namiji ciwon yatsa, tama rasa da wacce kalma zata fassarashi tayi d

aidai dashi Ja'afar ko iya haka yabarta ya gama da ita ya rusa alaqarta da Bestie dinta, wayarta ce ta dauki ruri tayi firgigit ta duba saitaga number Bestie gabanta yabada wani rass tunaninta lbr yaje Mata aikuwa ta kasa daga wayar sai lkcn kuka ya qwace

Mata ta rinqa kuka me shiga rai itakam tana ganin masifa a rayuwarta yanzu badan mutuwa data dauke Mata Yassar ba da tuni ba wannan zancen akeyi ba.

Ji tayi an dafata ta dago ganin Nina yasata sake rushewa da kuka tace “bansan me zance da Ni'imah ta yarda

dani ba a lkcn da wannan qazamin lbrn yaje Mata Nina kaina ya kulle wlh narasa gane mafitar rayuwata sai nakejin kamar na kashe kaina na hut...." Rufe Mata baki tayi tace “subhanallahi wannan ba kalmace ta Muslumci ba Rafi'ah ki daina idan fah Allah ya qa

darta aurenki dashi bakida tsimi bakida dabara idan Kuma bai qaddara ba ko kinaso bazai yuwuba to ki fawwala masa komai duk wani motsinki yana yuwuwane da amincewar lillahi"

Shiru tayi kafin daga baya ta dago tace “amma mijin aminiyata Nina haba abi

n ya wucce tunani yakasa saurarona ya fahimci nufina wlh Koda baya auren Ni'imah ni baimin ba bawai don baikai ba aa halinsa ne baiminba banasonsa Nina ya zanyi ya gane banasonsa" murmushi Nina tayi tace “aa fah qaryane wannan wlh duk inda

namiji ke kaiwa

asoshi JMW yakai kawai dai kice saboda Ni'imah ne bakiji kinasonsa ba kuma ma badan dai mu Mata bamuda lissafi wlh mijinta tunda yaji a ransa batakai masa ba har ya darsa aure aransa to kuwa sai yayi ni sainaga da a auro maka bare da bakasan halinta ba ai

gara wacce kasani tasanka in zata iya cutar dakai kasani idanma bazata iyaba kasani namiji fah idan yasa kansa Abu idonsa rufewa yake kunnensa toshewa yakeyi,

Sannan nifa sai nake ganin kamar itama bazata tashi hankalinta ba tunda tasan ba haramun bane" d

ago idonta tayi tana share hawayenta tace “bakisan Ni'imah ba bantaba baki lbrnta ba Nina Ni'imah qawatace aminiyata tun bamusan kanmu ba tun muna qanana nasani tanada zafin kishi ni da ita Tasha fadamin tsaf zata iya kashe mijinta ta kashe kanta indai yac

e zai qara Mata kishiya saboda bazata iya sharing din miji ba da wata to balle ni da ni kaina nasan indai na yarda na auri mijinta to naci amanar qauna kuma qauna bazata yafemin ba Ina tayata kishin mijinta saboda nasan tanasonsa fiye da yanda kike zato, n

ifa dana auri mijinta gara na mutu babu aure yafimin sauqi wlh ko bansan Ni'imah ba lbrn kishinta aka bani zan guji mijinta domin dawwamar lfyta da kwanciyar hankali na balle ni nice me bada lbrn"

Numfashi Nina ta sauke tace “to ilahi ya kyauta

Amma ki daina kukannan kiyi addu'a ki tashi muje muyi C.A dinnan mu fito sai ki tafi gida nima gda zan tafi tunda anbamu hutun qwaqwalwa hakan zaibaki damar samo bakin zaren domin wannan mutumin da gaske yake wlh" miqewa tayi suka fita sai yamma suka gama

C.A din ko hostel bata koma ba ta nufi gida hakanan tunda ta sauka a mota ta tari adaidaita taji gabanta yana faduwa jikinta a mace ta shiga gidan tana jin faduwar gabanta na tsananta,

Ajiyar zuciya tayi ganin parlour babu kowa tayi hayewarta sama tayi w

anka ta canza kaya sannan ta fito,

********

*_Waiwaye adon tafiya_*

Mahaifin Rafi'ah Alh Nuhu mutum me jan iyali a jiki da kyautata musu kwata² su ukune Allah yabashi Yaya Rashid Aunty Raziqa sai ita auta Rafi'atuh inda suka taso cikin gata

saboda mahaifinsu dan bokone Kuma dan siyasa sannan dan kasuwa da arziqi a gdansu bakin gwargwado gashi dason taimakon talakawa.

Don asalin alaqarta ma da Ni'imah cikin taimakon mahaifinta ne shekaru 18 baya lkcn sunada 3 years a duniya mahaifin Ni'ima m

aqocin shagon Abba ne a kasuwa sai karayar arziqi ta sameshi dake harkar gold sukeyi barayi suka shigo kasuwar sukayi barna Abba ma an taba dukiyarsa sosai amma dake yafisu qarfi Kuma shi kayansa ne na kansa yasa bai tozarta ba inda Alh Sabo mahaifin Ni'im

a ya kasance kayansa hadin gwiwa ne don kaso 70% ba nasa bane gashi yana cikin wadanda akafi yiwa barna.

To dake akwai fahimtar juna tsakanin Alh Sabo da Alh Nuhu yasa Alh Sabo yana kuka yake zayyanewa Nuhu halin da yake ciki yana fada masa yasai da gidan

sa ya rage

bashin kudin mutane duk wata kadara tasa ya siyar Amma bai gama biyaba har yanzu da saura 14 million da ake binsa gashi ko abinda zasuci babu a gidansa gidanma sai gdan gado ya koma kuma mahaifiyarsa ta mutu tun yana qarami matar babansa Kuma ba

sa shiri da matarsa don kullum ciki gori takeyi musu.

Sosai Alh Nuhu ya tausaya masa take yayi masa alqawarin bashi gurin zama a gdansa sannan zai biya Masa bashin Kuma zai zuba masa sabon kaya yake juyawa har Allah ya sake dagashi ranar Alh Sabo yayi kuk

an farin ciki hakance ta faru a ranar Sahura ta dawo gdansu Rafi'ah da zama duk wani alqawari da Abba yayiwa Dad ya cikashi ashe kudin na Sarki Muhammad Wakil ne mahaifin Ja'afar da aka Kai masa sai yace yabarshi kawai ya yafe masa wadanda ya karba na baya

ma don banasa bane na abokinsa ne murna ta cika Dad suka taho abin mamaki Abba saiya miqa masa kudin yace yasai gda dasu Amma yaqi karba qarshe suka tsaya a tsakiya kan cewa saidai a sake zubasu a shago ya zamana shima da hannun jarinsa hakance ta faru iy

ayensu na juya kudinsu gidansu na zaune lfy Sahura irin matannan ne masu homa dajin su wasune sai fankama ta qaru sun samu ci gaba a aro domin ko a lkcn gdan Abba ba qarami bane sosai ta rinqa shigewa Ammi har suka zama qawaye inda aka samu akasi ita Sahur

a macece me yawo ita Kuma Ammi batada yawo hakance tasa Sahura tafita mutane gata tun a lkcn da bin malaman masifa itakuma Ammi komai akayi sai tace Allah zai iya mata.

Anan gdansu Rafi'ah aka haifi qanwar Ni'imah Yusrah sai sabon balli ya tashi m

usamman da Sarkin Wakil ya turo matarsa ta tsakiya wato Hajiya Fatsum barka habawa sai firita ita tazama babbar mace har matan sarakai ke zuwa Mata barka to dake hali yazo daya sai Sahura da Fatsum suka dinke duk da Fatsum ta girmi sahura don a lkcn ma yar

onta autan ma yana Cairo yana karatu shikuma babban yana Uganda yana karatun Parmarcy matan Kuma biyu tayi musu aure Salma da Dija wanda sune manya.

Haduwarta da Hajiya Fatsum yasata qara kanainaye Dad duk abinda tace shi yakeyi gashi tun a wancan lkcn ba

wata biyayya ta cikaba kwanciyar aure idan zaiyi da ita saiya biyata, Ni'imah kuwa da Rafi'ah Allah ya hada jininsu ko bacci baya rabasu dole duk inda sukayi bacci nan suke kwana tsakanin dakunan iyayen nasu sunada shekara biyar aka sasu makaranta tun a

lkcn Rafi'ah tafi Ni'imah mayar da hankali a karatu ita wasane akanta sai fada da tsokanar masifa ga surutu ita Kuma Rafi'ah irin silent dinnan ce batada hayaniya duk da tsokanar Ni'imah batada qarfi idan tayo tsokana saita gudo gurin Rafi'ah to itamma ba

qarfine da itaba Amma sai ta hana a daki Ni'imah tace a rama akanta.

Haka sukayita tafiya har secondary a jarabawa ne suka raba layi saboda Ni'imah bata samu abinda akesoba sai ta tafi Art ita Kuma Rafi'ah Science Ni'imah taso jan Rafi'ah ta koma art Amma

taqi tace na marasa qoqarine a lkcn ne Kuma wata qauna ta qullu tsakanin Rafi'ah da dan wan babanta Yassar Amma fah soyayyar bada Rafi'an akeyi ba duk wani Abu saidai ya fadawa Ni'imah ita Kuma ta fada mata.

Daidai lkcn ne Dad yagama tamfatsa gdans

a suka tashi suka koma ranar ansha daru dan Ni'imah qin tafiya tayi inda ita Kuma Hajiya Sahura ta nace saita tafi da yarta har wani cewa takeyi ga sabon gida mi zaayi da tsoho ta manta taohon yayi mata Rana

na kusan shekara goma, dukkansu Saida sukayi ras

hin lfy aikuwa Basu rabuwa sai kwanciyar bacci musamman da Abba shima ya Gina wani gidan kusa da unguwar su Ni'imah duk da dadan nisa Amma yafi dayar unguwar kusa don Nan idan bakasa gandaba da qafama zakaje lkcn ne Abba ya qara aure aunty Murja itama me s

anyin hali babu ruwanta, zamansu lfy Lau da Hajiya Amina wato ammi Kuma daidai lkcn ne akayi auren aunty Raziqa shima Yaya Rashid yayi aure gidan ya rage saura Rafi'ah kadai aikuwa itama guduwa tayi sai tayi sati bata gidan tana gdansu Ni'imah wannan amint

a tana burge kowa don ko Yassar yasani idan zaisaiwa Rafi'ah Abu to dole saidai yasai biyu ita da Ni'imah inkuwa ba hakaba bama zata karba ba yasha tsokanar Rafi'ah yace “to waini ko ku biyu zan aurane?"

Dariya takanyi tace “nikam da nafi kowa mu

rna gani ga Bestie na gidanmu daya mijinmu daya kaga shikenan aminta tayi Rana" duk lkcn da ta fadi haka sai Ni'imah ta harareta tace “Allah ya kiyaye nayi sharing miji ke nifa wlh Bestie yanda ban taso naga kishiya a gdanmu ba haka zan rayu babu kishiya d

on wlh yanda nakejin kishin mijina tun kafin nasanshi zan iya kasheshi ns kashe kaina akan batun qara aure" Rafi'ah takanyi murmushi tace “nikam banida matsala akan abinda ubangiji ya halalta Ni'imah kishi kafirci ne shiyasa nake roqon Allah kada ya jarabc

eni da zazzafan kishin da zai hanani yiwa mijina biyayya kishin da zaisani yin shirka kishin da zai hanani haduwa da Allah salin alin Ina roqon Allah indai yayoni a wannan sahun to ya qaddaramin mutuwa kafin nayi aure don bana fatan na zamewa mijina fitina

masifa Kuma bala'in rayuwarsa"

Tsaki Ni'imah takanyi tace “ai saikiyi banza mara sanin ciwon Kai yo akanme zanyi addu'a Allah ya ragemin kishi bayan kishin adone ga ya mace nifa ko akan kishi da Yusrah ma bugawa zamuyi me qarfi ya kwaci kansa Kuma wlh do

n na kashe kishiya bazan taba nadama don nasan itama ba Sona takeyi ba da zata samu dama zata iya kasheni to da ka bari a kasheka gara Kai ka fara kashewa"

Yanayin Rafi'ah bata musu balle jayayya hakan yakansa da taja taga Ni'imah ta kafe akan r

a'ayinta saita qyaleta abinda ta dauka wani abin halitta ce baka Isa canxa mutum ba haka watanni sukayita turawa tafi na tafiya har shekaru saura wata bakwai candynsu akasa auren Rafi'ah da Yassar murna gurinsu baa cewa komai Yassar kusan yanayinsu daya da

Rafi'ah shima sanyine dashi yana nuna Mata madarar qauna me mantar da zuciya damuwa kullum suna tare babu abinda yake rabasu su uku sai bacci wani lkcn suna zaune sai kawai Ni'imah ta Kama kuka idan suka tambayeta sai tace tana tunanin ranar da Bestienta

zata tafi ta barta ta kwana ta yini bata ganta ba, itama Rafi'ah saita Kama kuka abinka da quruciya tasha samun Yassar ita dashi ta roqeshi ya auresu su biyu yakanyi dariya yace.

“Bakida hankali yarinya ni ba mijin mace biyu bane Kuma ko zan qara aure Ni

'imah batayimin ba banason farar mace sannan ta cika son jiki da rakin masifa ke nifah har tausayin mijinta nakeyi" akan haka Wai yana kushe Bestienta akwai lkcn da Saida sukayi sati uku basa mgn har saida manya suka shiga abin saboda ita Rafi'ah tata mats

alar kafiyar masifa indai aka sake ta furta abu to komai wuyarsa sai tayi shiyasa

iyayenta suke takatsantsan da furucinta dama Hausawa sunce muskilin mutum wuyar sha'ani gareshi shiyasa yawa yawan mutane suke cewa ta fiye jin izza kamar wata yar sarki wasu

suce don tana dakyaune take wulaqanta mutane.

Wanda a zahirin rayuwa ma ta gaske tafi Ni'imah sanyi da sauqi hali kowa takaka da me kudi natane saidai in taku batazo daya ba Amma dake bata da magana sai aka fassarata baibai, lkcn da suka gama e

xams sukayi candy ansha shagali iyayensu suka shirya musu party sannan Yassar ya shirya musu wani lkcn bikinsu saura wata biyar.

Ita Rafi'ah ba ma'abociyar son zama babu bawa brain aiki bace hakanne yasata zaqula wata makarantar amare ana koyar da girke²

da kwalliya da tarairayar miji, da murnarta tazo ta fadawa aminiyar tata aikuwa Ni'imah ta sheqe da dariya tace “cabb kina da aiki kice innayi auren ma wahala zanyi da har zantafi wani koyan kula da miji da girki wlh bazan iyaba kema ki zauna ki huta abink

i girki ko kuku yayi ai tarairaya kuwa yanda ya koyan haka zanyi masa" Rafi'ah tosa jan hankalinta Amma taqi jikinta a sanyaye taje gida take fadawa Aunty Murja ta rinqa rarrashinta tace “ance sai hali yazo daya ake abota amma ku taku halin ya bambamta nis

an yayi yawa kamar misalin sama da qasa Kuma kun kasa rabuwa bazaku rabuba abin daga Allah ne kawai ki bari zan fadawa Abbanki ya biya muku idan ya biya ai dole zataje"

Haka kuwa akayi Abba ya biya musu Amma fir Ni'imah taqi zuwa saima ta kwanta tace bata

da lfy itakuwa Rafi'ah ta rinqa zuwa makarantarta tana dauko darasinta, sosai take kwashewa abin gwanin ban sha'awa idan tazo gida tayita practice Ni'imah tana Mata dariya tana cewa “wallahi anma Raina muku hankali yo wannan abin zaa koya mini tab kina ruw

a itadai bata kulata Saida tayi wata uku tana training din sannan aka yayesu aka basu certificate ita harda gift saboda tana cikin dalubai masu hazaqa na shekarar.

Shirye shiryen biki ya kankama sunata tsare²nsu ya rage saura sati shidda tafiya ta Kama Ya

ssar zasuje daurin auren abokinsu Jos da zai tafi yazo sukayi sallama daqyar suka rabu hakanan duk jikinsu a sanyaye, dake yammace lkcn da suka tafi wajen bakwai na dare mahaifin Yassar ya Kira Abba a waya take Abba ya miqe yana salati inda kowa dake parlo

urn ya miqe suna tambayarsa “menene?"

Cikin kidimewa Abba yace “Yassar ne sukayi hatsari ya karye a wuya yanzu ma haka suna asibitin garin nan" ai Bai rufe bakiba Ni'imah da Rafi'ah suka saki wata qara itadai Rafi'ah zubewa tayi a gurin matsayin

gawa aka kinkimeta suka fita asibitin da Yassar din yake sukaje aka kaita wani daki suka fice suka nufi Emergency cikin motar su hudune shi kadai Allah ya karbi rayuwarsa wayyoh zokuga kuka gurin Ni'imah na tausayin aminiyar tata da ta dauki so da qaunar d

uniya ta dorawa saurayin nata tana kuka tana cewa.

“Mutuwa! Wayyoh mutuwa meyesa kikayi mana haka meyesa kika daukewa Bestie na mijinta innanillahi wa innah ilaihirraji'un Allahummah ajirnih fih musibati wa'akalifni khairin minha" kuka take me tsayawa ara

i daidai lkcn Rafi'ah ta fito a guje ta nufo gurin ganin yanda kowa yake kuka yasata runtumawa dakin a guje ta nufi inda su Abba suke lkcn an janyo zani zaa rufe masa fuska ta fuzge zanin ta saki wata

qara tare da fadawa jikinsa hawayenta yana malala tana

jijjigashi tana cewa “Yassar ka tashi banason wasannan dama ka saba idan muna Hira ka kwanta kacemin ka mutu na fada maka banaso ni banaso wayyoh Yassar dina kada ka tafi kabarni wlh yau zan fada maka kalmar da ka dade kanacewa na fada maka naqi fadanta in

asonka don Allah ka tashi....."

Likitan ne ya share hawaye yace “baby saidai hqr Allan daya baki ya karbi abins....." Daga gadon ta sulale bata sake sanin inda takeba sai bayan kwanaki uku ta farka taga Ni'imah a kusa da ita sai kuka takeyi ta tashi a fi

rgice tace “mafarki nayi ko Ni'imah Yassar dina yananan ko?"

Kukan Ni'imah ne ya qara tsananta tace “ya zamuyi da wannan qaddarar haka Allah yaso Rafi'ah kinada tawakkali da dangana don Allah kada ki bani kunya ki dauki wannan qaddarar da hannu bi

yu Allah yafimu sanin abinda yake nufi daya dauke Yassar na tabbata zaiyi Miki zabi mafi kyawun kyau mafi alkhairin alkhairai" rungume juna sukayi sukaci kukansu me isarsu baki Rafi'ah ta kasa budewa saboda zuciyarta azalzalarta takeyi abubuwa da yawa suke

tunkudowa daga zuciyarta sunnason bakinta ya furta idan ta furta Kuma zata iya ficewa ma daga muslumci a hankali ta fara furta astagfurullah! Astagfurullah!! Astagfurullah!!!"

Kawai sai tayi dif sai shassheqar kukanta da yake tashi Abba ne ya shigo ya m

atso da sauri yace “subhanallahi kukan kukeyi uwar manya to ya zaayi sai hqr Allah yana tare dake shikam Yassar ai yadace yasamu shaida Kuma yayi mutuwar shahada tasa tayi kyau saura mu Allah yasa muyi kyakkyawan qarshe irin nasa" janyota yayi yana share M

ata hawayen yana bubbuga bayanta daqyar da taimakon Ni'imah suka samu tayi shiru Ni'imah ta hada Mata shayi tasha kadan tabata magungunan tasha Dad da Abba sukazo suka tafi dasu sunata yimata nasiha hakance ta dan sanya zuciyarta sanyi amma tuquqin mutuwar

yana qasan ruhinta wannan dalilin yasa taci alwashin bazata qara son wani namiji ba a rayuwarta balle ya tafi ya barta.......

_Vote_

_Comments_

_Share_

_Please_

*_Ummuh Hairan_*

[1/4, 6:51 PM] Mrs AA Fansah: I think you'd like thi

s story: "MY BESTIE'S HUSBAND" by realfauzahtasiu on Wattpad https://my.w.tt/Mbal0x4hMcb

*_My Bestie's Husband_*

*_Ummuh Hairan_*

*_Wattpad-realfauzahtasiu_*

*_15-16_*

_Ina qara jaddada muku kada wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login