Showing 30001 words to 33000 words out of 145961 words
takaici ya kamashi ya zauna a cell d'in kamar yasa ihu, gashi sunce inya sake musu turancin nan nasa sai sun fasamai kai........
*THE INNOCENT TEAM*
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*I Sincerely Dedicated This Page To You Billy S. Fari and My Samrah.... ILYSM*
1
⃣
9
⃣
Dakyar Ashraf ya iya watsa ruwa a jikinsa, wajen sa kaya kamar yai ihu, haka dai ya daurw yasa riga,
makuli ya d'auka ya nufi hanyar waje da niyyar zuwa asibiti.
Yaje fita Umma ta kirashi hakan yasa ya karasa gunta, falo suka shiga bayan sun gaisa ya kalleta yace "Umma ya akai? "
Ta d'anyi murmushi tace"Dama tun jiya nakesan magana dakai. "
Kallanta yai kawai baice komai ba, ganin haka yasa tace " yanzu saura wata d'aya da sati biyu bikinku da Aneesa shiyasa nake tunanin kamar ya cancanta a bata sakon mahaifinka..... "
Wani kallo ya mata wanda ita kanta batasan ke yake nufi ba, s
annan murmushi ne ya biyo bayan fuskarsa ya kalleta yace " Ashe har na bada sadaki an shaida kenan? "
Umma tace "mene? "
Yai wani murmushin rainin hankali yace "a iya sanina wanda ya bada wasiyyar nan cewa yai matata ta farko, banaji yace matar dan
a kusa aura. "
Ta kalleshi sannan ta motsa baki zatai magana, mik'ewa yai sannan yace " inada abinyi Umma sai anjima. "
Tabishi da kallo cikin maimaita kalamansa, asanda yai maganar sam kwakwalwarta kullewa tai amma yanzu kam datake maimaita kal
aman ta fahimci banda tsananin rainin hankali ba abinda Ashraf ya fad'a mata.
Shikam cikin tsananin b'acin rai ya shiga mota, yayi tunanin zai iya tuki sai dai jin zafin da kafad'arsa take yasa ya na driver d'in mumy magana, ba'a dad'e ba ya karaso
nan ya jashi suka fita.
Kansa ya kwantar akan kujera ya lumshe idanunsa, menene dalilin dayasa mutane suka damu da abinda mahaifinsa ya bari? _Fatiha an d'aura auren Ashraf da Nafisa yar gidan Datti_
Abinda ya fad'o mai a rai kenan, kallan dr
iver yai yace " Adamu kaini wajen malam Yunus "
To abinda driver d'in ya fad'a kenan tare da murd'a kan sitiyari, sunyi tafiya sosai kafin su isa wata katuwar makarantar islamiya, nan yai parkin Ashraf ya fita, wani babban office ya nufa ya kwankwa
sa, daga ciki aka ce shigo, Ashraf ya murd'a kofa ya shiga.
Malamin na ganinsa ya mike cikin tsananin farinciki ya karaso kusa da Ashraf tare da mikamai hannu alamar musabaha, shi kanshi Ashraf d'in ya saki fuskarsa sosai, nan shima ya mikamai suk
a gaisa cikin girmamawa.
Nan ya nunama Ashraf guri ya zauna, sunyi gaisuwa tare da tambayan juna bayan rabuwa, dattijon Malami ya kara washe baki yace "Muhammad sam ka daina ziyartata. "
Ashraf yai murmushi yace " wlh malam uzuri ne ke hanani
zuwa. "
Sunjima suna gaishe gaishen su kafin Ashraf yai gyaran murya yace "Malam ina cikin wata 'yar matsala ne wacce duk duniya ba wanda na sanar ma kuma ba wanda zan sanarwa sai kai. "
Malam yunus ya kalleshi cikin tsananin kulawa, yace" Inajin
ka."
Ashraf yai shiru, yana tunani.
Malam yace "Muhammad karka b'oyemin komai. "
Ashraf yai kasa da kai nan ya zayyane mai kaf abinda ya faru sannan ya d'oramai da wasiyyar mahaifinsa.
Malam Yunus hankalinsa ya tashi dajin wannan al'amar
i ya kalli Ashraf yace" Tausayi da Taimako ne yasa ka aureta sai dai Muhammad inasan tunasar dakai aure ko a wasa akayishi indai har anyi auran yanda musulunci yace to fa tabbas wannan auran ya d'auru sannan hakkin matarka na wuyanka. "
Kallan Malam
yai cikin tsananin damuwa yace " da ina tunanin saki..... "
Da sauri Malam yace " kul Muhammad akan me? Ba taimako kakesan yi ba? Meye amfani taimakon kenan? "
Ashraf jiki a sanyaye ya kalli Malam yace " me zanyi da ita? A kauye fa take ko in
ce a riga, yarinyar da banaji sallah cikake ta iya,
batasan komai na rayuwa ba, infact shekarunta ma inaji basufi 16 ba Malam me..... "
Malam yai murmushi yace " naji duk bata iya komai ba, kamin alkawari d'aya nikuma zan taimaka ma. "
Ashraf
yace "Name kenan? "
Malam Yunus yai murmushi yace " Inaso kasa ta a makaranta inma taa kwana ko ta jeka ka dawo ka kula dacinta da shanta da suturarta har ta kai shekara 20 zuwa da d'aya, inhar aka kai lokacin Bakaji komai a tattare da ita ba inaso ka
bata takardarta ita kuma sai ta nemi wani ta aura. "
Cikin rashin damuwa Ashraf yace "nama wannan alkawari. "
Malam yai murmushi sannan yace " game da wasiyar mahaifinka kuma kasan yanda zakai a rabu lafiya dan kuwa wannan wasiya ta matar daka a
urace ba wacce zaka aura ba. "
Shiru Ashraf yai yana tunanin lalai akwai chakwakiya inhar yace bazai ba Aneesa wannan wasiyar ba, Malam yaji yace " zaka iya jinkirtawa zuwa sanda ka rabu da matarka."
Ashraf yai shiru, sai dai yasan wannan shawar
ar itace daidai,sunyi Sallama Ashraf ya ajiye mai kud'in talafi na makaranta sannan ya tafi.
Mota ya koma nan sukai hanyar Asibiti.
*Dan Allah kuyi Hakuri da wannan wallahi rasuwa aka mana shekaran jiya.*
Nagode![5/9, 09:58] Ayusher
✍
🏻
:
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*Dedicated This Page to World of Hausa Novel 1*
And *Taskar Lubie Mai Tafsir*
2
⃣
1
⃣
A tsorace Nafi ta mike gabanta sai fad'uwa yake, shi
kam gogan ko mikewa baiyi ba sai cewa dayai "Little mikomin rigata a kan gado. "
Nafi ta mikomai sannan ta fito daga d'akin da sauri tare da ja mai kofar, dan ta kula kamar bayasan asan bashida lafiya.
Tana fita falo Asim ya karaso tare da jan
hannunta da karfin tsiya, Nafi ta d'an turje sai hawaye da takeyi.
Asim ya haska mata wani wawan mari yace " banza karuwa, a ido kamar bakauyiya ashe kinfi karuwai iya iskanci. "
Nafi ta shiga girgiza kai hawaye na zubo mata.
Kofa aka
bud'e, mamaki ne ya kama Ashraf ganin Nafi, sai dai bai bari mamakin ya fito fili ba cikin isa ya karaso ya sa hannu ya rike hannun da Asim ya rike.
Asim ne ya kalleshi cikin masifa yace " Me kenan? Kazo karema karuwarka ne? "
Nafi kam kanta
na kasa, kunyar Ashraf duk ta gama rufeta ta sani sarai bai san ita bace sai yanzu.
Ashraf ya kalli Asim yace " Saketa ko? "
Nafi kam hannunta sai zugi yake yi, Asim yace " bazan saketa ba sai munje gaban kawu ta sanar mai abinda kai da ita ku
ke aikatawa. "
Ashraf yai wani murmushi ya kalli agogo karfe 6 na yamma, sannan ya kalli Asim yace " ai banaji sai ta bika wajen isar da sakon kai kad'ai ma ya wadatar kaje ka sanar. "
Asim ya kara cika baki da takaici yace " Me kake nufi? "
Ashraf ya kalli Asim ya mai alama da ya sakar mata hannu, cikin takaici Asim ya saketa, Ashraf ya kalleta yace " wuce ko? "
Nafi ta kalleshi idanunta sun cika da kwalla tanasan bashi hakuri sai dai bataga fuska ba, da kai ya mata alama ta wuce mana
, jiki a sanyaye tai gaba tana yi tana waigensa.
Tana fita Ashraf ya kalli Asim yace " D'an sako mai kake jira? "
"d'an sako? Nine d'an sakon? "
Ashraf yai wani murmushi yace " Au na d'auka danace kaje ka sanar ai zaka wuce da sauri ka gur
fana agaban kawu ka sanar mai. "
A zuciye Asim ya kama wuyan Ashraf cikin masifa yace " Ni kake fada ma haka? "
Ashraf yad'an juya ido kad'an yace " inmu uku ne to dana ukun nake."
Ya ja jikinsa ya koma d'aki dan yin alwala.
Asim ya naus
hi iska cikin tsananin takaici yai waje jiyake kamar ya lumama Ashraf wuka hankalinsa ya kwanta.
Ashraf kam alwala yai sannan ya fito waje.
Nafi kam d'aki tai tana kuka, Little ta gani ta fito daga wanka, da sauri Little ta karaso tace "
Nafi menene? Wani abin ya miki? Laifi kikama yayan? "
Kai kawai Nafi take girgizawa, Little tace " to menene?"
Nafi ta kalleta tace" me karuwa yake nufi dan Allah? "
Little da mamaki ta kalleta tace " Yayan ne ya fada miki hakan? "
Kai ta
girgiza alamar a'a sannan tai hanyar ban d'aki da sauri, da alama kalmar bata da dad'i ganin yanda fuskar Little ta canza.
Little ta bita da kallo, sannan ta d'au always d'in da Mumy ta kawo mata ta sa, zama tai jiki a sanyaye, waye yacema Nafi k
aruwa?
Asim kam ana idar da sallah ya tari kawu acikin masallacin ma ya fad'amai, ran kawu yayi dubu gurin b'aci, ganin haka yasa Asim ya saki wani murmushin mugunta.
Kawu ya fito cikin tsananin masifa nan yace Ashraf ya biyoshi, duk da kas
an zuciyarsa yaji ba dadi sai dai bai nuna ba, nan Asim yabi bayan kawu.
A falo Mumy, Umma, Asim da Ashraf ne a zaune sai kawu.
Cikin fada kawu ya kalli Ashraf yace " Ashraf meke faruwa? Wani banzan labari nake ji haka? "
Ashraf ya kalle
su kaf sai dai kafin yai magana Aneesa ta shigo cikin tsananin kishi ta karaso kusa da Ashraf tace " Yaya me kenan? Ni zakaci amana? "
Mumy wacce jikinta duk ya mutu dan ta taba ganinta ta fito daga d'akin, tai shiru yau kam batada halin kare Ashraf
.
Kawu ya daka mata tsawa yace " Aneesa bakida hankali ne? "
Ta kalli kawu cikin tsananin takaici tace " Amma Abba..... "
Hannu ya d'aga mata hakan yasa Umma ta zaunar da ita a kusa da ita.
Ashraf wanda ke zaune sai dai duk masifar mu
tum bazai tab'a gane meke yawo a ransa ba, sam babu b'acin rai ko farin ciki a tattare dashi.
Kawu yace " Asim fad'i me ka gani. "
Hankalin Asim a kwance ya sanar da abinda ya gani har da karin cewa wai suna ganinshi suka tura kofar d'akin suka
rufe, sai daya dade kafin su fito.
Mumy ta runtse ido zuciyarta na wani irin zafi, Umma ta shiga tafa hannu tana salati, itakam Aneesa kafe Ashraf kawai tai da ido jitake kamar zata mutu dan tsananin kishi.
Kawu ya kalli Ashraf rai a b'
ace yace " Wani irin iskanci ne hakan Ashraf? "
Ashraf ya mike daga zaunan da yake ya kallesu ga mamakinsu Murmushi sukaga ya saki, ya jinjina kai sannan yace" tunda maganar Asim itace gaskiya banaji inada abin cewa. "
Yana kai nan ya nemi hanya
r fita, Umma cikin kuluwa tace "lalai kuwa Alhaji yarinyar nan dole ne ta bar gidan nan, inshi ba'a isa dashi ba ai ita kam karya take. "
Ashraf ya juyo ya kalleta sannan ya kalli Aneesa da ta ke zaune kamar gunki ya bud'e baki zaiyi magana yaji Mum
y tace " Gaskiya nima Alhaji yarinyar nan bata kwanta min ba."
Fuskar Ashraf ce ta canza, yanzu kam ransa ya b'aci sosai, bai damu inkowa ya mai abu ba amma ya tsani yaga mahaifiyarsa na goyon bayan masu mai abu.
Kawu ya kalli Asim yace "Ai
ba sai anja da tsauri ba, yanzu nan za'a kirata tabar gidan nan. "
Ashraf ya had'iyi wani abu sannan ya d'auke idansa daga kan Mumy ya maidashi kan kawu, ya kalli Kawu yace " Kawu banasan abu yaji da zafi sai dai in aka kaini bango banajin kowa zaij
i da dadi a gidan nan. "
Yana kai nan yai waje, Mumy ta dafa kanta, tanaji Umma na cewa " Allah wadaran nakaa ya lalace, sam yaran nan yafi karfin kowa a gidan nan? "
Kawu yai shiru shikansa ya kasa magana.
Ashraf kam yana fita ya kira num
ber Habib, bugu biyu Habib ya d'aga yace " Buddy yau kuma soyayyarce ta tashi? "
Ashraf yai tsaki yace " Habib dan Allah makarantar Abbanka wace iri ce? "
Da mamaki Habib yace "lalai Ashraf kana nufin bakama san me Abbana yake ba? "
Ashraf y
ace " Malam dole ne sai na sani? Ba gashi ina tambayarka baa yanzu? "
Habib wanda baiji dadin kalaman Ashraf ba yace " Primaryce da secondary."
Ashraf yace " day ce ko boarding?"
Day ce mana.
Ashraf yad'an shafi kansa sannan yace " Habib
boarding school nakesan asa Nafisa gashi kasan tayi girma ba ilimi na rasa ya zanyi. "
Habib yai shiru can yace " karka damu Aminin Abba matarsa itace principal ta makarantar kwana dake nan minjibir, sai a d'an yi mata ciwa ciwa ko Js3 ne a sakata. "
Ashraf ya d'an saki fuska yace "yauwa Habib hakan yayi."
Habib yai dariya yace " bazaka gode min ba? "
Ashraf yace " in komai ya kammala zan gode ma, but please ka tambayi Abban yanzu dan inasan ta tafi a satin nan. "
Habib yace Shik
enan.
Yana kashe wayar yai ajiyar zuciya sannan ya makama inda ya fito wani mugun kallo na takaici, yai gaba.
¤¤¤¤¤¤¤¤
Su kam a ciki sai tada zancen suke yi, mumy kam duk ranta ya gama da gulewa rai b'ace ta fito daga falon tai
b'angaren su Little.
A zaune taga Little a kan gado ta zuba tagumi, Nafi kuma ta ra kub'e a gefen gado ta cusa kanta cikin cinyoyinta, abu d'aya ke yawo a ranta tajama Ashraf fada ita abinda ke damunta kenan.
Muryar Mumy ce tasata ga d'ago,
mumy ta tsaya a kusa da Little tace " Nafi ta fadamiki abinda ya faru? "
Jikin little a sanyaye tace " Mumy bakisan Nafi bane, kome ke damunta bazata taba fad'amin ba. "
Mumy cikin fada tace " ai kuwa yau dole ta fada tunda gashi can ta jama
Ashraf cin mutunci. "
Nafi wacce jin hakan yasa ta mike cikin tsoro ta matso kusa da Mumy ta tsugunna a gabanta tace " wlh Mumy ba abinda Yaya ya sani, bai ma san nice naje d'akin ba. "
Mumy tace " mene? "
Nan little ta fad'a mata ita yace taj
e ita kuma batada lafiya shine Nafi taje, jikin mumy ne yai sanyi ta kalli Nafi tace " to akace kina d'akinsa? "
Nafi ta share kwalla tace "Mumy bashida lafiya fa? "
Idanu mumy ta zaro ta kalli Nafi jiki a sanyaye, Nafi wacce idanta ya rufe das
an kare Ashraf tacigaba " Mumy wlh tun safe bashida lafiya kuma wlh yana jin jiki, ni a ganina bai kamata ma ace kaf gidan nan ba wanda yasan halin da yake ciki ba........"
Hannu tasa ta rufe bakinta, me take fada? A ranta tace " amma ai Anisa ta s
ani.
Mumy tai shiru a hankali ta juya tai waje batace komai ba, little ta kalleta tace " lalai Nafi dama kin iya zakewa haka? "
Nafi ta kalleta tace " Maryam bakisan halin da yaya yake ciki bane sannan ace dake kanwarsa da mahaifiyarsa ba wanda
ya sani? Na d'auka in bashida lafiya Mumy ya kamata ya fara sanarwa? "
Little tai wani sansanyan murmushi tace " Nafi kenan, bakisan komai ba a kan harkar rayuwar gidan nan. "
Nafi ta mata kallan mamaki, little tace " karki damu zan sajar dak
e komai gobe, in kikaje zaki gane dalilin dayasa Yaya baya shiga harkar Mumy. "
Nafi tai shiru batace komai ba....
*THE INNOCENT TEAM*
*ZUCIYA*