Showing 6001 words to 9000 words out of 145961 words

Chapter 3 - ZUCIYA COMPLETE

Bai jira komai ba yace " Na gode yai gaba. "



Datti ya bishi da kallo kamar kayansa, sai dai ta ina kayansa zaije gun wannann kad'on?

Yayi tafiya mai nisa dan har ya gaji sannan yaga gari, a ransa ya

ce nan ne garin?

Kauye ne sai dai yanada girma sosai ga mutane sunata hada hadarsu, wajen wani mai tabir din rake ya tsaya ya mikamai hannu suka gaisa sannan yace " Dan Allah akwai ATM anan kusa? "

Kallan mamaki mai raken ya masa yace " A me? "

Yadan dafa kansa sannan yace " Banki fa? "

Me raki ya kalleshi sosai kana ganinshi duk da rigar dake jikinsa zaka gane ba daga nan yake ba, ya girgiza mai kai alamar bai sani ba sannan yace " amma kaje can gurin masu mashina akwai Dan liti wanda

yai karatun boko sai ka tambaye shi. "

Yamai godiya sannan ya karasa gun masu mashina, sallama ya musu sannan ya tambayesu waye D'an liti, wanda ke zaune ya sha riga da wando ya wani tsuke shi a dole dan boko ya kalleshi yace " Yes ganinan. "



Kallansa yai ya wani daura kafa d'aya kan d'aya akan mashin, dariya tadan so kamashi ya daure yace " Dan Allah tambaya nake san ma. "

Dan litti ya dan wani rangwad'a kai sannan yace " what is your ansa? . " wai so yake yace "what is your question?

" lol

Dariya ce ta kama Dan binni yai kasa da kansa tareda murmusawa jiyai abokansa sunce " Kai Dan litti ka kure gayu fa. "

Dan litti ya wani sosa keya irin jin dadin nan, Dan binni ya dago sannan yace " So nake in tambayeka ko akwai ATM anan

kusa."

Fuska dan litti ya canza yadan gyara zama sannan yace " AT me? "

Dan binni yai murmushi yace " ka gane mana inda ake cirar kudi ba tare da anshiga banki ba. "

Tafi Dan litti yai yace " Ohhhhhh ATN? Ha ha ha kai ne bakamin bayani ba,

akwai amma gaskiya sai dai muje can gwaram. "

Dan binni yace " inane kenan? "

Dan litti yai murmushi yace " local gommant d'in mu."

Kai ya jinjina alamar gamsuwa sannan yace " Zai kai minti nawa kan mu isa? "

" A kalla minti 40 inaji.

"

Shiru Dan binni yai sannan yace " Muje to Allah yasa mu dawo kan azahar. "

Dan litti yace " Maganar kudina fa?"

" in mun dawo mayi maganar ai tare zamu mu dawo tare. "

Dan litti ya kwama glass dinsa sannan yace " Hau muje. "

Dan

binni ya hau yana tunanin yanda zaiyi tafiyar kusan hour daya da rabi akan mashin shida rabonsa da mashin har ya manta inbadai race suke da 'yan uwansa ba shima race d'in sun dade basuyi ba kasancewar canjin yanayi da suke fuskanta a tsakaninsu.



************

Nafi zuciya d'aya tana gama aiki ta shigo gun D'an binni sai dai me? Ba shi ba alamarsa, tsoro da fargaba ne suka kamata nan ta fito ta shiga nemansa sai dai samm babu shi, idanunta ne suka ciciko da kwalla tace "

Wato

ya warke shine ko sallama baxai min bako? Me yasa mutane suke min haka? Kowa baya sona? Kowa bai damuwa da halin da nake ciki ko wanda zan shiga? Wato shi kuma wannan zuciyarsa mara rama alkairi ce ko????????

*THE INNOCENT TEAM*

*ZUCI

YA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

5



Sun fara tafiya akan Mashin Dan litti yace " Amma da alama kai ba dan garin nan bane ba ko?"

Murmushi yai sannan yace " ni ba dan garin nan bane kuma ya

u nakesa ran barin nan."

Dan litti yadan juyo sannan yace " When are u fom?" Ya fada cikin irin isar nan wai shi a dole kwarare, Dariya Dan binni yasa hakan yasa Dan litti yace " U don't say English? "

Dan binni kam dariya yake yi har ransa

hakan yadan sa ran Dan litti ya soso, yace " Malam menene hakan ka sani a gaba sai dariya kake?"

Dan binni ya daure yace " A wacce makaranta kau karatu ne haka?" Mazewa dan litti yai yace " Anan makarantar Gomnati ta Gwaram."

Yadan kare hade ra

i yace " what matter?"

Dan binni yace " lalai naga kanata kokari ne wajen yin turanci."

Dan litti yai wani murmushin isa da takama yace " Kaf garin mu ni kadai ne nai karatu hakan yasa mahaifina ke ji dani kamar kwai sannan yan mata suke sona."

Dan binni ya jinjina kai yace " hmmm gaskiya kam a garin Jahilai dama ai......"

Dan litti yace " me kace?"

Kai ya juya batareda yace komai ba.

Inya tuna turancin Dan litti kawai sai ya saki murmushi lalai ana kwab'a a kasar nan.

Tun yanajin dadin tafiya yana kalle kallen kauye har ya gaji kawai ya zauna yai dif.

Yanaji Dan litti nata bashu labarin makaranta, shidai kam jinsa kawai yake fatansa Allah yasa suje su dawo kafin bakin alkalami ya bushe.

Sunyi tafiya s

osai kafin su isa Gwaram, nan Dan litti ya karasa bakin banki ya tsaya, ya kalli Dan binni yace " Gashi mun iso."

Dan binni ya kalli bankin sannan ya kalli ATM din dake gun guda biyu ne a jere saidai mutanen dake tsaye a gun sunfi 20, wata iska ya fu

rzar sannan yace " Dan litti ba wani sai wannan?"

Dan litti ya kalli mutanen gun yace " Kasan karshen wata yayi ko munje wani gun ma hakan ne gwara mu tsaya anan."

Dan binni ya kalli mutanen gun sannan ya tuna Nafi wacce ake neman ruguza mata

rayuwa, takawa yai yaje har ya tsaya a layi yaga abin kamar bazai yiwu ba, hakan yasa ya karasa ya fara neman alfarma, abinda tunda yake arayuwarsa bai tab'a yi ba kenan wai ace shi ne ya rusunar da kai yake neman alfarma gun wasu, ya taso rayuwarsa ba ab

inda ya rasa, haka ya daure yai ta neman alfarma har ya dawo na 8, suna nan tsaye har aka zi kansa, ya zaro wallet dinsa dake aljihun wandansa ya ciro ATM card dinsa ya sa.

Dubu Ashirin ashirn sau biyu ya cira sannan ya ciri dubu goma ya kama hamsin

kenan, ya musu godiya ya karasa gun Dan litti, tafi Dan litti yamai yace " Gaskiya ka birgeni yanzu mu tafi?"

Dan binni ya kalleshi yace " yunwa dai nake dan ji."

Dan litti yace " Ga mai Yam da Egg can muje sai ka siya."

Murmushi yai sann

an yace " Lalai Dan litti dan boko."

Dan litti ya shafa keya yace " Can we went?"

Dan binni ya juya kai sannan suka karasa gun mai doya, kashi biyu yace asa musu wato shida Dan litti, har zasu juya sai ya koma yace a kara samai wani daban, haka ka

wai yaji zuciyarshi ta tuno mai da Nafi.

Dan litti ya shiga godiya nan suka ci sukasha leman kwalba sannan suka mike suka juya.

************

A can rigar Datti kuwa Nafi ce zaune a dakinta banda kuja ba abinda takey

i ga bakin cikin auren da za' a mata gana guduwar dan binni, mamaki ne ya kamata dataji mutane suna sallama, nan ta fito dan tasan su ba baki

suke ba tunda Baffa baso yake ba, turus ta tsaya tana kallan kanwan mamanta, sai dai ta kasa farin cikin ganinta s

am.

Ganin haka yasa ta matso tare da rungume Nafi tace " Nafi shine kina ganina zaki shareni? Bayan har da kawarki Hanne nazo miki da ita? "

Nafi ta maida hawayenta sannan tace " Aunty nayi mamakin ganinki ne."

Tace" ai daga ke har Datti bak

u kyauta mana ba wau sai dazu aka turo mana almajiri wai yau ake auren ki? Haba Nafi ai ko Datti bai sanar damu ba ke kya fada mana ai."

Nafi kam kasa magana tai dan batasan taka maimai mema zata ceba cewa zatai an bada ita biyan bashi ko me?



Hanne ce ta matso kusa da ita tace " Nafi ya naga ba kowa a gidan? Kamar ba biki za'ai ba?"

Nafi ta share hawayenta tace " eh kinsan Baffa bayasan mutanene shiyasa."

Baki Hanne ta tab'e tace " amma dai duk da haka, sannan ke ma kalleki kamar b

a Amarya ba ko wanka ma da alama bakiyi ba."

Nafi tadan juya kanta gefe, Nan Maman Hanne tasa Hanne ta debo ruwa, da kanta ta tasata gaba sukaje ta wanketa fes, sannan suka fito, kayan Nafi ta kalla sam bana arziki bare aje ga sabo haushi da tausayi s

uka kamata ta kalli Hanne tace " Hanne da alama ke zaki taimaka ki ciro kayan jikinki ta saka inyaso ke sai kisa nata."

Hanne ta kalli Nafi tace " Allah Nafi shi yasa kike ban haushi ke wai bazaki taba cewa asai miki kaya ba? Ko sanda innarku nanan it

ama banga ta wani damu da miki dinki ba, yanzu dan Allah meye amfanin hakan?"

Nafi tai kasa dakai, Hanne taja wani dogon tsaki tace " sam ita wannan a kidahuman ma ita ta dabance, fa tsinanan kawaici da hakuri, wallahi babu inda zakiji ba'a cuce ki ba

indai haka zaki cigaba."

Maman ta tace " to ya isheni uwar 'yan masifa."

Nan Hanne ta cire kayanta tana masifa.

Nafi ta saka kayan sun amsheta kuwa nan Hanne ta shafa mata hoda tana shirin yi mata ja gira da kwalli Nafi tace " Bashi Hanne

kema kinsan banasan kwalliya."

Hanne ta mike cikin takaici tace " ni dai kam ban taba ganin mutum irin ki ba, gaskiya Nafi kina neman addu'a ni wallahi haushi wannan halayen naki suke bani."

Tana kainan tai hanyar waje, jitai Nafi tace " kiyi hakuri

Hanne ba bata miki rai naso yi ba."

Hanne ta kara had'e rai tace " kinganta ko Goggo? Yanzu me tayi na bada hakuri dan Allah?" Tai waje ba tareda ta jira amsa ba.

Maman Hanne ta kalli Nafi tace " Nafi kiyi hakuri kinsan kawartaki akwai masifa."

Hanne ce ta shigo cikin mamaki tace " Nafi naga sun fara taruwa inaji yanzu za'a daura, ni ko mijin ban gani ba."

Gaban Nafi ne ya fadi tanasan yin kuka ba kuma taso su Hanne da mahaifiyarta susan halin da ake ciki, kasa kawai tai da kanta tan

a karanta Inalilahi a zuciyarta.

Ango kam yasha babbar riga haka kuma ya taho da abokanansa dayawa dama yan uwa da makota, sannan sun taho da liman da maroka, Datti ne yashigo gida fuskarsa a sake wasai ko a jikinsa, ya zura riga babba shima, yan

ajin Mahaifiyar Hanne na gaisheshi ya shareta yai waje.

Ta birma manya aka shimfida musu sannan Ali ya taho da goro nan aka ajiye, Aka dan gagaisa sannan aka zauna.

A ciki kuwa mahaifiyar Hanne ce ta kalli Nafi tace " Nafi amma an miki komai na k

ayan daki ko?"

Nafi ta kalleta tare da kakaro murmushi kawai amma batace komai ba, hakan yasa itama tai shiru.

An gama addu'oi nan aka ce ina Walliyin Alhaji Ali? Wani kanin mahifinsa yace " Ganinan."

Akace walliyin Nafi fa? Datti yace g

ani.

Kallan mamaki suka bishi dashi sukace " Dakanka malam Datti? Ai kyanta wani dan uwanka na kusa zaka wakilta."

Datti ya hade rai yace " wannan damuwarku ce amma nine zan zama walliyi a auren 'yata ehe."

Sunyi shiru, liman ya kalli Ali, kai Ali

ya daga mai akan ba komai a kyaleshi, nan liman yace to shikenan yanzu zamu gabatar da.........

Ji sukai ance " Ba abinda zaku gabatar domin kuwa ni na hana wannan auren."

Gaba daya suka juyo suka kalli inda maganar ke fito wa, ga mamakinsu wani

saurayi ne ya sauka daga kan mashin sannan ya fara takowa gunsu cikin isa da takama, basusan fuskarba sai dai Datti yasanshi dan kuwa bai manta shi ba.

Dan binni ya karaso inda suke zaune ya gaida liman sannan ya kalli Ali wanda yasha manyan kaya,

ba shakka ya girmi mahaifin Nafi lalai mutanen nan basuda imani.

Ali ya harareshi yace " Kai menene kakeyi haka? Ba ka gani aure ake shirin daurawa?"

Dan binni yai murmushi yace " Aure? Dama haka ake aure?"

Ali da 'yan koronsa suka mike suka

ce " kai meye hakan? "

Dan binni yasa hannu a aljihu ya ciro dubu ashirin daya waresu tun a banku yace " ungo! Ba bashi kake binsu ba har kake tunanin kwace mutum akan wata banza dubu ashirin dan tsabar rashin imani?"

Ali ya kalli kudin sannan ya

ce " ni na yafe Nafi nakeso a auren."

Dan binni yace " Ai kuwa baka isa ba, yarinya ba sanka take ba kuma baka isa ka aureta ba, kai ko kunya ma bakaji ba kana yayan mahaifinta? Inbanda zuciyarka irin ta yarace ina kai ina neman wace batafi sa'an 'ya'

yanka ba?"

Datti dake zaune ya mike tsaye yace " Kai wai kai waye ne? Menene naka a ciki? "

Dan binni ya kalli Datti cikin takaici yace " nine wanda 'yarka ta taimaka a lokacin da nake kan karagar mutuwa ta."

Mamaki ya kama datti dama

sauran 'yan gun, Datti yace " to naji, daga taimako sai akace ka isa da ita? Ka dubafa kaga yarinyar nan ta girma amma ba miji, in ka korar mata wannan d'in kai ne zaka aureta ko me?"

Gaba daya kallo yakoma kan Dan binni suna jiran amsarsa.

Gaba

nsa ne ya fad'i baiyi tunanin abin zai juye haka ba, me kenan? Daga taimako?"



Ali ya matso kusa dashi shima yace " eh muna jinka kai ne zaka aureta ko me?"

Innalilahi wa ina ilaihi raji'un!!!!

Allahuma Ajirni fi Masibati wa aklifni kairan mi

nha......

Addu'ar da Dan binni ya shiga yi kenan a ransa.

*THE INNOCENT TEAM*

*ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

6



Gaba d'aya hankalinsa yakai kololuwar tashi muryar Ali y

aji yana cewa " Kai yaro dakai muke magana, Kai zaka aureta amaimako na ko me? Yaran yanzu banda tsugudidi basuda aikin yi inbanda munafirci da shiga shara ba shanu dan ta taimakeka meye naka na shiga shirgin rayuwarta?"

Dan binni ya kalleshi cikin b

acin rai yace " kai yanzu in 'yar ka ce zata auri sa'anka ko wanda yafika zakaji dadi?"

Ali ya kwashe da dariya yace " to menene? Baifi karin zumunci ba."

Dan binni zaiyi magana yaji an dafashi, juyawa yai dan ganin waye, ga mamakinsa dan litti

ya gani a tsaye a bayanshi, ya kalli Dan litti cikin wani yanayi.

Dan litti yace " Abokina ka fita harkarnan tun kafin kuzo kuna arment."

Dan binni ya kalleshi yace " meye arment?"

D'an Litti ya wani sosa kai su kuma mutane suka kalleshi da s

ha'awa jin yana turanci.

D'an litti yace " baka gane ba? Kar kuzo kuna musu nake nufi."

Wani kululun takaici ne ya kamashi dama mutanen gun nan sun gama kona mai rai shikuma D'an litti zai so mai da wani sabon takaici wai arguments ne arment?

Kallanshi ya maida kan Liman wanda yake cewa " ni yanzu a wani matsayi nake? Datti yace " Aure za'a daura da Ali yanzun nan."

Ali ya gyara rigarsa, haushi ya kara turnuke dan binni yace " in kuma nace zan aureta fa?"

Gaba d'aya kowa juyawa ya

i ya kalleshi cikin tsananin mamaki, Datti yace " Kana nufin zaka aurenta?"

Gaban D'an Binni ya fad'i ya daure yace " Eh." Abinda kawaj zuciyarshi take rayamai Allah ya kawoshi garin nan ne dan ya taimake ta."

Matsowa D'an litti yai da kansa sai

tin kunnen D'an binni yace " I am Crazy? Kasan me kake kuwa?"

Dan binni ya juya ya kalli D'an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login