Showing 102001 words to 105000 words out of 145961 words

Chapter 35 - ZUCIYA COMPLETE

Ashraf ya fizge zanin gadon da karfinsa.

Nafi tasa hannu ta kankame jikinta.

Kusa da ita ya matso ya d'agata ya sata a

cikin wannan ruwan dumi mai dan zafi sai dai ba zafin dazai kona mutun ba.

Yar kara tai sakamakon zafin dataji a gabanta, Ashraf ya sunkuyo tare da zama a gefen gun yace " raguwa kawai."

Kallansa tai tace " yaya mai kake kai kuma anan?"

Yai

murmushi yace " baki gani ba? Matata zan taimakama tai wanka."

Idanu ta dan zaro tace " zan iya da kaina."

Yace " na sani sai dai banaji zan iya tafiya na barki."

Kanta ta kawar gefe batai auni ba kawai taji soso a bayanta da sauri ta juyo

ta kalleshi sai dai ta kasa magana.

Gira ya d'aga mata yace " kina farin ciki ko? Allah ya baki namiji mai kulawa ko?"

Ta d'an yi murmushi kadan a ranta tace " dama yaya....."

Bata karasa fadar abinda zata fada a ranta ba taji hannunsa yana

wanke mata wuyanta.

Kallansa tai a hankali tasa hannu ta rike masa hannunsa,wani irin kallo ya mata mai sagar da gababuwan jiki, a hankali ta zare hannunta.

Da kashi ya cud'ata sai daya gama sannan ya mike ya ce kiyi wankan tsarki.

Ya juya y

a fita.

Kallo ta bishi dashi, a hankali murmushi ya bayyana a fuskarta.

Shikansa yana fita ya saki murmushi sannan ya kalli kansa a madubin d'akin yace " wai da gaske nine kuwa???"

Zama yai a bakin gado sai a lokacin tunanin Dadyn Habib ya fado

mai, idanu ya runtse cikin kunar zuci yace " wani kuma abin mamakin zan gani nan gaba??? Ya Allah gani gareka."

Motsin Nafi dayajine yasa ya mike ya sa hannu a kugunta ganin tana d'an dingisa kafa kadan, yana kallanta tai sallah bayan ta idar ta dade

tana addu'oi sai dai gaba d'aya addu'oin ta akan mijinta takeyi bayan ta shafa ne ta juyo ta kalleshi cikin shagwaba tace " Yaya mai zancema Little?"

Cikin rashin kulawa da abin yace " akan me kenan?"

Tace " na kwana anan mana."

Kallanta yai

yace " kice mata kin kwana a gun mijinki, menene a ciki? Ni inaji ma kin dawo nan kenan."

Idanu ta zaro tace "bangane na dawo nan kenan ba?"

Ya hade rai tamau yace " kwarai, nima inasan matata a kusa dani."

Kallansa tai cikin mamaki tace " Sai

muzo mu zauna nida yaya nisa ko me?"

Yace " Nisa?" sam yama sha'afa da ita.

Kallan Nafi yai yace " to sai me?"

Baki dan turo tace " ni dai ban yarda ba kabarni a can gaskiya."

Ya mike yace " shikenan da alama zanje bikon matata."

Ga

ni tai ya mike, da sauri ta riko shi.

Juyowa yai ya kalleta ta shagwabe mai fuska ba tare da tace komai ba.

Kallanta yai shima fuska a hade bai ce komai ba, sun dade a haka kafin tace " ni fa ba haka nake nufi ba."

Ya kunshe dariyarsa yace " th

en?"

Fuskar ta tadan sosa tana kallansa, ya zauna a kusa da ita tarecda jawota jikinsa yace " what are u afraid of?"

A hankali tace " Yaya Mumy ba ta....."

Yace " wannan ba uzuri bane a guna."

Tace " 'yan gidan nan duk......"

Yac

e shima ba uzuri bane a guna."

Tace " amma...."

Katseta ya sakeyi yace " we have already become one, ya kamata ko menene yanzu mu ajiyeshi a gefe."

Kara kwantawa tai a jikinsa tare da d'agamai kai...

Tare suka koma bacci lokacin

tashinsa nayi ya mike ya shiga wanka, farkawa tai a hankali take tafiya ta shiga kitchen, tayi mamaki ganin ba komai a ciki na kayan abinci sai kawai kayan shayi.

Tace " 'yan gidan nan sun saba da a aiko musu da abinci kawai."

Ruwan zafi ta hada

tayi tunanin fita taje kitchen sai dai tana tsoron kartaje kafin ta dawo Ashraf ya fita.

Nan ta jera kayan shayin akan dinning yana fitowa ya ganta a falo.

Yai murmushi ya tuna sanda Anisa nanan har ya fitama bata sani ba tana baccinta.

Kara

sowa yai gunta yace " Me yasa kika tashi bayan jikinki ba kwari?"

Hannunta tasa cikin nasa sannan ta mike tace " muje kasha ko tea ne naga ba kayan abinci a kitchen din."

Yai murmushi sannan suka karasa.

Tea ta hadamai mai kauri a hankali yak

e kurba idanunsa na kanta.

Bayan ya gama ne, ya sunkuyo ya sumbaceta sannan ya dau jakarsa yai waje.

Kallo ta bishi dashi harya fita.

Ashraf yana fita suka hadu da Dan litti nan sukai gun mota.

A tsaye sukaga Asim yana ta danna waya d

a alamar wani yake nema bai sameshi ba.

Ashraf ya dauke kai kamar bai ganshi ba, Asim yace " Lala Ashraf wuyanka ya isa yanka dan an karama matsayi shine har zaka iya ganina ka wuce ni?"

Kallansa Ashraf yai ya saki murmushi yace " Ai ban kula da

mutum anan ba, ya dafatan ka fara sabawa da inda aka maida ka Assistant director."

Asim ya kumburo fuska yace " kana tunanin zan yarda da wannan karamin office din?"

Ashraf ya kalli Kawu wanda ya taho ta bayan Asim yai murmushi sannan yace " Ay

ya gashi banaji Kawu zai daukeka daga nan yanzu."

Asim cikin masifa yace " kana tunanin Abban ya isa ya barni anan?"

Ashraf ya kalli Kawu wanda kalaman Asim suka dakarmai kunne.

Asim ya cigaba " in ma kana tunanin Abban ya isa ne to gwara...

...."

"ni kake fadama haka Asim? Kawu yai maganar cikin zafin rai.

A tsorace Asim ya juya yace " Abba!"

Ashraf ya saki wani murmushin ya hade hannayensa biyu yace " Nabarku lafiya da alama akwai maganar da zakuyi."

Yana kaiwa nan ya wuc

e mota Dan litti yana dariya shima ya shiga sukai gaba.



Kawu ya kalli Asim cikin kunar rai, da sauri Asim ya matso yace " Abba abinda ya faru shine....."

Wuceshi kawu yai ya shiga mota shima yai gaba.

Asim a zuciye ya naushi iska da

hannunsa.....

*#ASHRAFEENAH TEAM*

💞

*ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

💡



*62*

Nafi kam yana fita ta gyara d'akin sannan ta fito kamar m

unafuka ta nufi bangarensu, a hankali take tafiya taje kwanar da zata shiga part dinsu taji ance " kan bala'i daga ina kike?"

Gabanta ne ya fadi ta juyo a hankali cikin tsananin tsoro, Umma ta karaso cikin huci tasa hannu ta fizgota Nafi ta fadi a ka

sa.

Umma ta kalleta tace " daga gidan ubanwa kike da safen nan???"

Nafi ta kalleta tace " ba daga inda nake kawai dai na fito ne."

Umma ta nunata da yatsa tace " ke na miki kama da sususu??"

Cikin mamaki Nafi tace " Sususu??"

Umm

a ta kara hasala tace " badai a bangaren Ashraf kika kwana ba?"

Kasa Nafi tai da kanta da sauri.

Cikin tsananin fishi umma tasa hannu ta mangareta da karfinta tace " 'yata tana can ta kasa bacci tabar mijinta saboda ke, ke kuma kinsamu wannan dam

ar kina neman maye gurbinta."

Nafi ta d'ago ta kalleta, Umma tace "me? Zaki ramane?? Uban me kikaje yi a bangaren 'yata?"

Nafi ta ki dauke ido daga kanta bata kuma bata amsa ba, a zahiri bazata juri dukan nan ba haka kawai ba gaira ba dalili.

Umma ta rike haba tace " ke ni kikema wannan kallon??"

Nafi tai shiru.

Umma ta sa hannu ta kara mangareta tace " dauke idanunki daga kaina."

Nafi kam ko gizau idanun nan nakan Umma.

Takaici ya kara rufe Umma tasa hannu biyu zata rufe

Nafi da duka.

Da sauri Nafi ta matsa sannan ta kalleta tace " Umma a matsayina na matar Ashraf banaji zan yarda ki cigaba da dukana kamar wata baiwa."

Umma tai sototo tana kallan Nafi, cikin hasala tace " in baki tsaya ba me zakiyi?"

Nafi t

ace " ni dai ki daina dukana, sannan ni ba bangaren 'yarki naje ba bangaren mijina naje, ba kuma naji nayi laifi dan naje can."

Tana kaiwa nan ta mike davkyar sakamakon jikinta ta cigaba da dingisawa tai gaba, kallan kafafuwanta Umma tai nan danan ta

fahimci komai, tsoro da fargaba suka kamata.

Itakam Nafi a hankali ta bud'e kofarsu ta shiga, tana dagowa da niyar ganin Little ko tana bacci, taga Little a tsaye a gabanta daure da towel.

Nafi ta zaro ido ta juya da sauri.

Little tace "

da alama nan gaba kadan zaki gudu daga nan tunda yanzu kunfara dan waken zagaye ke da yaya." ta juya tai toilet."

Nafi tadan rufe bakinta sannan ta zauna a gefen gado.

Bayan Little ta dawo Nafi ta kalleta tace " kinga sakon ki?"

"sakon me

kenan?"

Nafi ta nuna mata da hannu tace " Ya Habib."

Da sauri Little ta mike ta zanyo jakar, ta hau bud'ewa, turaruka ne da wani lace mai masifar kyau, sai dan kunne da sakarsa silver.

Little tace " jiya yazo?"

Nafi ta daga kai alamar e

h sannan tace " do u like him that much?"

Little tai murmushi tace " Ni kaina mamakin kaina nakeyi, amma bakya ganin shima yana sona?"

Tausayinta ya kama Nafi, Nafi tai yake tace " kin fadamai tsakanina da yaya?"

Little ta girgiza kai, Nafi ta

ce " ki fada mai, kar yaji a gari." a ranta tace mayb inyaji ya shiga hankalinsa.

Little ta d'aga kai alamar to sannan ta cigaba da shirin makaranta.

***********

Umma kam a zuciye tai bangaren Mumy, ko gaisawa bata bari sunyi ba tace " Ru

ma hankalinki daya kuwa?"

Mumy ta kalleta tace " ban gane wannan banzan zancen ba."

Umma ta kara yin hucci tace " wai danki yagama fin karfinki ne? Ko kuwa kin sallamashine yabi duniya?"

Mumy wacce kalaman Umma suka bata mata rai tace " wani

irin banzan zance ne wannan, taya zakizo har d'akina ki dinga fadar magana irin wannan wacce batada ma'ana."

Umma ta tabe baki tace " a ido ne kike nuna mana bakyasan wannan tsinaniyar yarinya ko kuwa har ranki?"

Mumy cikin kunar rai tace " har r

aina mana kema ai kinsani."

Umma tacigaba " to in bakiyi wasa ba zaki samu jikar daji, wanda rabin asalinsa ya kasance kidahumin bafulatanin da ko hausa bai sani ba."

Mumy tace " banasan kunbiya kunbiya me kike san fada."

Umma tace " yarinya

ta fara kwana a bangaren Ashraf sannan har jiya ya aikata abinda yakeso, ke wai a sunan uwarsa amma bakisan komai ba sai zaman daki kamar wata gumba."

Mumy ta kara hasala tace " inkin gama zaki iya fita ai ko."

Umma ta juya cikin takaici tai w

aje.

Zama Mumy tai a bakin gado ta dafa kanta tace " Ashraf!!!!!!"

*********

Shikam Ashraf yau ya koma sabon office dinsa a matsayinsa na Chief Director, Kawu dan ya nuna ma mutane yanasan Ashraf da kansa yazo wai zai tayashi murna.



Bayan ya shiga ya kalli Ashraf yace " Congratulation d'ana."

Ashraf ya kalli Mutanen gun ciki harda Asim sannan shima ya mikamai cikin fara'a, bayan sun gaisa ne Ashraf ya matso kusa dashi yace " thanks but not yet."

Kawu ya kalleshi yace " wha

t du u mean?"

Ashraf ya sake murmushi sannan ya kara matsowa yace " in naje office din Chairman na Company din nan at that time zan amshi taya murnar ta ka."

Kawu ya zaro ido cikin mamaki, ya kalli Ashraf wanda ya sake hannunsa ya karasa ya cig

aba da gaida mutane Kamar ba'ai komai.

Asim kam a zuciye yai waje ran nan nasa a b'ace.

Shikam Ashraf ko a jikinsa suna fita ya zauna sannan yasa waya ya kira Dan Litti, ba'a dade ba sai ga Dan Litti nan yazo.

Ashraf yace " Dan Litti inaso

daga yau sunanka ya koma Auwal Max, sannan ka fadama mutane hakan sunanka yake, ni kuma yanzu inka fita inaso kaje inda Kawu yake zansa a kiramin kai."

Dan litti yamai kallan mamaki sai dai bai tambaya ba sai yes sir dayace.

Ashraf yace sainya

kira ka sau uku zaka amsa.

Yana fita ya shiga neman kawu can ya gashi a sama sai ya wayance da aiki a gun.

Shikuma Ashraf dama dan litti na fita ba dadewa ya tura masingansa akan ya nemomai driver dinsa sunan sa Auwal Max in ya ganshi ya kira su

nan da karfi.

Nan masingan ya amsa sannan yai waje.

Dan Litti yana tsaye, gefe kuma kadan Kawu ne tsaye da Asim.

Kawu ya kalli Asim yace " kai wai meke damunka??"

Asim yace " da akai me kenan?"

Kawu ya hade rai yace " ba nace ka

dinga kokarin boye emotion dinka ba? So kake kowa ya gane bakasan matsayin da Ashraf ya samu yanzu?"

Asim ya hade rai yace " Abba wai ni haryanzu bakamin bayani ba akan wani dalili ne zaka ba waccan yaron matsayi haka? Baka tsoron abinda zai aikata?

Ko kuwa yanzu ka dawo kana bin bayansa ne?"

Kawu ya bud'e baki zai magana yaji ance " AUWAL MAX!"

Cikin tsananin firgice har da sakin takardun hannunsa ya fara waiwaigawa.

Masinja ya kara kwalla kira, Kawu ya rikice yana kalle kalle, Dan l

itti ya zubamai ido, shikansa Asim sai daya fahimta yace " Abba lafiya?""

Kawu kam sai dudubawa yakeyi baiga alamun wanda yake zargi ba duk ya gama rikicewa, sako ne ya shigo wayar dan litti.

Yana dubawa yaga sakon Ashraf akan kar ya amsa yaje ku

sa da masinja din kawai su taho.

Haka kuwa akai, Kawu ya duk ya gama rud'ewa dajin wannan suna shikuma Dan litti yaje yaja hannun masinja sukai gaba.

Dan litti ya shiga gun Ashraf ya sanar dashi halin da Kawu ya shiga daga jin sunan.

Ashraf

yai murmushi yace "jeka na gode."

Bayan ya fita Ashraf yai shiru yana tunani kafin ya dauko wayarsa ya danna number Dadyn Habib."

Bayan sun gaisa yace " Dadyn nikam dan Allah tambaya, kasan wani Auwal Max?"

Gaban Dady ne yai mugun faduwa duk

yadda yaso ya daure sai da muryarsa ta canza cikin rawar murya yace "Auwal Max?"

Ashraf yai dan dariya yace " eh wlh, jiya ne akamin sako akan wai anasan magana dani wai driver din Abba ne Auwal Max, shine nikuma nake tunani kar inje karya yake san

nan ni bangama dalilin haduwar mu ba nace bari na kiraka."

Dady yai sauri cewa " Don't meet him."

Ashraf yace ' naam?"

Dady yace " hmm karka yadda Ashraf ku hadu da mutumin da baka sani ba, wayasa me zai maka? Ko mugu ne??"

Ashraf

ya jinjina kai alamar gamsuwa sannan yace " nima abinda nake tunani kenan, shiyasa nace bari na kiraka."

Dady yace " yauwa Ashraf kayi tunani mai kyau."

Nan sukai sallama, Ashraf ya kankance ido tare da yin hucci yace " How can u do this to me???

? Tayaya duk a cikin mutane ace kaii!!! Har da......"

Kasa karasawa yai ya sa hannu ya rufe fuskarsa.

*ASHRAFEENAH TEAM*

💞

*ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIA

TION*

💡



_*MY INTIMATE FRIEND AISHA MUHD UMAR*_

💞

*As it's a special day for My Intimate Friend, i just can't express how happie i am today, It's ur wedding day, the day 5th August have become a memorial day for us.*

*Allah ubangiji ya baku

zaman Lafiya da zuri'a dayiba Ameen suma Ameen*

*63*

Ashraf yana fita ya wuce gidan su Ferry, yayi sa'a kuwa a lokacin Mahaifin su Ferry ya dawo.

Tare suka shiga gidan bayan sun gaisa Isma'il ya kalli Ashraf yace " banyi tsammanin

ganinka da wuri haka ba."

Ashraf ya dago cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa yace "

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login