Showing 33001 words to 36000 words out of 145961 words

Chapter 12 - ZUCIYA COMPLETE

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

2



2



Mumy ta fito jiki a sanyaye kanta sai sara mata yake yi, a waje ta hango Aneesa ta taho kamar zaki rike da wata zungureriyar waya tana tafe Umma na mata magana amma da alama bata ma jin me ake cemata, Mumy tana tsaye a kofar su Little har An

eesa ta karaso, idanunta sun canza.

Da mamaki Mumy ta kalleta tace " Neesah meye hakan? "

Aneesa wacce sai hucci take ta kasa magana sai neman cusa kanta ciki take, Mumy tasa hannu ta riketa tace " Neesa meye hakan wai? "

Umma ce ta kar

aso cikin kinibibi tace" Yauwa gwara da kika riketa wai Nafi zataje ta zane. "

Mumy takaici ya kamata tace " in kuma Ashraf d'in yajiki kice me? "

kallan Mumy tai kamar mai shirin kuka tace" Mumy amma kina ganin..... "

Mumy tace " Laifinkine

, in har Nafi ta fiki sanin meke damun Ashraf, ke da zai zama mijinki amma ace ba kece ke kula da shi ba. "

Umma tace " wace irin magana kikeyi haka? Haba Amina ya zakisa yarinya a gaba wacce ranta yake a b'ace ki kara b'ata mata."

Mumy ta k

alli Umma sai dai takaicin abinda yake faruwa yasa ta kasa tanka mata.

Umma ta juya kai tace " haba Amina _wace irin zuciya gareki?_ace ke kawai d'anki kika sani? "



Mumy ta juya batare da ta sake magana ba.

Aneesa ta kara zuwa wuya gani

take kamar saboda Nafi itama Mumyn take mata haka.

Hannunta ta fizge daga gun Umma tai ciki a zuciye.

Nafi kam ta d'auro alwala isha'i kenan, ta zauna a bakin gado ta rasa abinda ke mata dadi, taji an banko kofa da karfi kamar za'a b'ala, da s

auri ta kalli kofar.

Little dake zaune akan kujera ma ta d'ago da sauri.

Aneesa a zuciya ta shigo d'akin, Nafi dake tsaye ta shiga kallanta cikin tsananin tsoro, Little ta mike tace " Ya Neesa meye kuma hakan? "

Aneesa ta buga mata wata mu

guwar harara sannan ta nufi kan Nafi gadan gadan Umma kuma ko kunya tana tsaye a baya.

Da karfi Little tace " Wlh Ya Neesa kika daketa sai na fadaki da Yaya. "

Cikin kuluwa Aneesa ta wurga mata kallo, Little ta kalleta tare da d'aukan wayarta t

ace " Wlh kika daketa yanzu zan kirashi."

Aneesa kam ta kulu fam kamar zata fashe, Umma ta matso ta gaurama Nafi mari iya karfinta sannan ta kalli Little tace" ni ki tabbatar kin fadamai inyaso ya zo ya rama mata. "

Tana kai nan ta fizgi hannun

Aneesa tai gaba.

Nafi kam ko kuka batai ba dan ganin zabgegiyar bulalar dake hannun Aneesa yasa batama ji zafin marin sosai ba.

¤¤¤¤¤

Mumy kam ana idar da sallah tai b'angaren Ashraf, a hanya suka had'u da Mumy baice mata komai ba sai

dai yasan gunsa tazo, nan ya bud'e ya shiga tare da kunna kwan wuta.

A bud'e ya bar kofar hakan yasa Mumy ta shiga.

Shikam d'aki kawai ya wuce, ya d'au ruwan da Nafi ta gasa mai gun ciwon ya zubar a toilett, sannan ya matse towel d'in ya sha

nya sannan ya fito.

Mumy na zaune hakan yasa yaje d'an nesa kadan da ita ya zauna a kasa, Mumy ta kalleshi jiki a sanyaye tace " Ashraf abinda ya faru d'azu kayi hakuri....."

D'agowa yai ya kalleta idanunsa sunyi jaa jikinta ya kara yin sanyi,

cikin wata irin murya wanda mai sauraro shi kad'ai zai fahimci abinda ke zuciyar me maganar Ashraf yace " Kin taba yadda dani Mumy? Ko me aka fada a kaina tun ina karami kin taba yin bincike kafin kimin fada? "

Mumy idanunta suka cicika da kwalla s

ai dai tsananin tausayin Ashraf dake yawo a ranta.

Hannu yasa a bugi inda zuciyarsa take da karfinsa wanda kana iya juyo karar dukan ya cigaba " Kinsan ya nakeji a raina? A duk sanda kika zargeni da abinda banyi ba?....."

Kasa karasa kalamansa ya

i saboda wani rad'ad'i da zuciyarsa take mai, Mumy wacce ganin yanayin d'anta da bata taba gani ba yasa hawayen datake b'oyewa suka zubo ta gefen idanta.

Kallansa tai cikin dauriya tace " ba haka bane Ashraf. "

Ya kalleta sannan yai wani murmushin

takaici yace " Nafi zata tafi makarantar kwana a satin nan insha Allah. "

Mumy bata d'auke ido a kanshi ba tace " amma naga kamar ba tada karatu? "

Ya sake yin wani murmushin wanda itakam mumy sam batasan taga yayi saboda bata sani me yake nufi yace

"eh hanya za'a mata ta shiga Js ko 3 ne inyaso sai a dinga mata lesson kuma a makarantar. "

Mumy ta jinjina kai tace " hakan yayi sai dai baka ganin karatun zai mata wahala? "

Ashraf ya d'an tab'e baki yace " wannan kuma ruwanta. "

Mumy tac

e " shikenan in makarantar ta fito sai ka fadamin sai muje a mata shopping Allah ya baka lada ya kuma yi albarka. "

A cikin ransa yace Ameen, ta mike tace " bari inje. "

Bai amsa ba ko ince tasan ma bazai amsa ba, tana fita yabi bayanta da kallo s

annan ya koma d'aki ya d'auko diary d'in mahaifin sa wanda wasiya ce kawai ya barmai.

Shafin farko wanda a kullum sai ya karantashi yau ma shi ya karanta " _Ashraf kada ka kuskura kabar mutane susan abinda ke zuciyarka,_ _ka dinga kokarin b'oye baki

n ciki ko farin cikin dake ranka, kar ka bari

wani yasan sirrinka, wannan ita kadai ce hanyar da zaisa ka kare kanka...ko da kuwa 'yan uwanka ne na jini..._"

Ashraf ya share zufar data keto mai duk da sanyin AC d'in da ke d'akin, Murmushi yai wand

a kana ganin kasan na bakin ciki ne a fili yace " Dad zan iya jure hakan kuwa? I am really lonely."

Ya kwantar da kansa kan gado, kafad'ar sa na masa zugi sai dai zugin dake zuciyarsa tafi karfin wannan.......



¤¤¤¤¤¤

Habib

kam da kansa ya samu Abbansa ya mai bayani, Abban Habib na tsananin san Ashraf a lokacin ya kira wayar abokinsa ya sanar dashi, sunyi rashin sa'a matar tashi an mata transfer zuwa Rumfa Collage sai dai ya sanar dasu ai kanwarta ma principal ce ta FGC na ka

zaure, nan ya sanar musu in suna san can d'in to a yanzu zai kira kanwar matar tasa ya fada mata.

Nan Habib ya ma Abba alama da a yadda, sunyi sallama akan zai kira anjima.

Ba'a dade ba ya kira tare da sanar dasu ba matsala duk sanda suka shi

rya ko gobe ne su kaita.

Nan Habib ya kira Ashraf yamai bayani.

¤¤¤¤¤

A b'angaren D'an litti kuwa yan sanda sun gaji da ajiyarsa gashi abin haushi bashida alamar sanar dasu Inda Ashraf yake, duk kuwa da dukan da sukamai, hakan yasa ha

ushi ya kamasu suka cilloshi waje tare da kwace wukar dake jikinsa.

D'an litti ya sha kuka wiwi gashi ko ficika bashida shi, ga wunya datake damunsa.

Dakyar ya mike ya dingisa ya shiga gari, yayi sa'a ya sami wani mutum ya bashi naira d'ari.



Nan ya gangara yasai wainar gero kan kace me ya cinye, ta gumi ya baza yace " Oh Ni D'an litti haka rayuwata ta koma? Daga boko sai a nemi halakani? Yanzu ni ina zan nufa in nemo Ashaf d'in? "

Ya jingins kansa da bango zafin rana na damunsa.

Nace wayyo

🤦🏻

‍♀

*THE INNOCENT TEAM**ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

*Fatie Shafi'u ina tayaki murnar kammala Jarabawarki. May Almighty Allah help and protect u.... ILYSM*



Washe gari da safe Habib yaje makarantar mahaifinsa yama Nafi takardun karya na primary da kuma Js 1 and 2, sai dai takardun sun nuna sam batada kokari.



Nan ya taho da shi gidansu Ashraf.

Yau gidan an tashi kowa zuciyarsa ba dadi musamm

an ma Umma da Aneesa, Little kam ta fita makaranta.

Itakam Nafi tana kitchen ta zake sai aikin girki take, sunayi suna 'yar hirarsu da Goggo.

Suna gamawa ta fito duk jikinta ya d'an baci Amra ce ta karaso gunta da gudu tace " Wai kizo inji yaya. "

Nafi ta kalleta cikin zak'uwa tace " Ya Ashraf? " kai Amra ta d'aga mata ai kam Nafi da sauri ta nufi b'angarensa tana tafe tana gogee fuskarta da hannu, tun jiya takesan ganinshi sai dai ba yanda zatai.

Fuskarta a sake ta kwankwasa kofar, ta

saba in yana ciki sai dai yace ta shigo in dai har ba makulli yasa ba, sai dai yau gani tai anzo an bud'e da fara'arta ta kalli mai bud'ewa tace " Yaya ina kwa...... "kalamanta ne suka tsaya ganin Habib a tsaye yana mata murmushi.

Jin ta tsaya da ma

gana yad'an kanne ido cikin salonsa yace " Haba Nafi ba ni kika so gani bane? "

Da sauri ta girgiza kai alamar a'a sannan ta d'ora da cewa " ba haka bane Ya Habib. "

Habib ya d'an matso kad'an hakan yasa ta d'an kara matsawa, kara matsowa yai it

ama ta kara matsawa, sam bata kula tazo karshe ba tayi baya zata matsa kawai taji zata fad'i, da sauri yasa hannu a kugunta ya tarota.

Nafi kam har ta runtse idanta kam, jin an riketa yasa ta bud'e ido a hankali, Habib ya sakar mata wani lalausan

murmushi, sannan ya matso da fuskarsa yace " Me yasa kika tsaya da maganar ki to? "

Yawu ta had'iya da karfi sannan ta d'an motsa baki tace " Ya Habib d'an sakeni. "

Jin ta waske bata bashi amsa ba yasa ya d'agota tare da sake cewa " Shikenan n

a hakura da gaisu.... "

Bata jira ya karasa ba tace ina kwana? "

Dariya ya d'anyi sannan yace " Nafi kina burgeni na rasa me yasa. "

Kasa tai da kai dan itakam tasan wasa ne ace tana burge wani.

Ashraf dake zaune a kujera duk yana kallan

me sukeyi kasancewar kofar a bud'e Habib ya bata yaja wani karamin tsaki tare da girgiza kai yace " in kun gama sai ku shigo, dan ni inada abinyi. "

Nafi ta kalli inda Ashraf yake haka kawai taji gabanta ya fad'i tare da tsananin takaicin ganin ta

dayai.

Habib ya matso da niyyar rike mata hannu da sauri ta b'oye hannun a baya kallanta yai fuska a sake sannan ya d'anyi gaba yace " Ki shigo. "

Da sauri ta shige jikinta duk yai sanyi.

Ashraf na zaune yana kallo ta karasa tare da zama a k

asa, Habib ya kalleta yace " zauna a kan kujera mana? "

Ashraf ya bugamai wani mugun kallo yace " Mu sa'aninta ne? Kai meyasa kake kokarin zubar mana da mutunci agurin yara kanana? "

Nafi wacce ko alamar tashi dama batai ba ta d'ago ta kalleshi

sai dai zuciyarta ta d'anji ba dadi.

Ashraf ya d'auke idansa, Habib ma kasa magana yai, Shiru ne ya d'an biyo baya kafin Ashraf yace " Nafisa! "

Gaba d'aya tun daga kan yatsar kafarta har zuwa kanta sai dataji wani abu ya wuce mata, d'agowa ta

i a hankali ta kalleshi.

Ashraf kam ko a jikinsa yace " yau zuwa gobe zakuje da Little da kuma mumy xakuje siyayyar kayan makarantarki. "

Kallonsa tai cikin mamaki batasan sanda tace " naam? "

Ya had'e fuska sosai yace " bakiji me nace ba? "

Tace " Naji kace makaranta. "

Yace " eh, in kun gama siyayya da komai zuwa jibi zaki wuce makarantar kwana dake kazaure. "

Nafi kam idanunta ne suka ciciko, wani irin farin ciki ne wanda ita kanta batasan irinshi ba yake ratsata, Ashraf ya

ce " meye hakan? "

Hawayenta ta goge wanda suka zubo, ta girgiza kai tace ba komai.

Habib cikin damuwa yace " Bakyaso ne? "

Kai ta girgiza da sauri tace "a'a ba haka bane. "

Ashraf ya d'an kuraa mata ido kamar yanasan gano wani abun, id

anunta tai saurin yin kasa dasu tace a hankali tace " Yaya babana fa?"

Jiyai ransa ya b'aci ya ce " Bansan inda yake ba, kuma bana fata insani, sannan in har da haka kike tunanin yin karatun to gwarama karkije, dan ni na tsani mutum mai raunanniyar zu

ciya. " ya mike yai ciki.

Kallo ta bishi dashi zuciyarta tana dana sanin tambayar datai, sai dai duk yanda taso da daurewa ai dole ne tai rashin mahaifinta.

A ranta ta maimaita Raunanniyar Zuciya? Me kenan?

Kamar Habib yasan meke ranta yace "

karki damu da fadan Ashraf dan shi yawancin maganarsa haka take. "

Nafi tabi d'akinsa da kallo tanasan ta bashi hakuri ta kuma tambayeshi ciwon sa, daurewa tai ta kalli Habib tace " Ya Habib meye raunanniyar zuciya? Ma dai san me zuciya take nufi"

Dariya yai yace " rauni fa? "

Tace " na sani. "

Ya sake dariya yace " to sai ki had'asu guri d'aya ki gani. "

Tace " Rauni Zuciya? "

Wannan karan dariya sosai Habib yai yace " lalai Nafi inkinje makaranta cikin mutane a hankali zaki fahimt

a. "

Tace to, sannan ta sake kallan d'akin Ashraf sai dai ba yanda zatai, mikewa tai zata fita, Habib yace " aiki kikai ne? Naga kayanyi sun b'aci kamar daga kitchen kika fito. "

A'a kawai tace tai saurin fita.

Tana gaba kad'an sai ga An

eesa wacce tasha kwalliya tana tafe kamar sarauniya.

Idanunsu ne suka had'u, gaban Nafi ne ya fad'i bawai dan tsoro ba a'a sai dan ganin kyan datai, a cikin zuciyarta tace " Dole Ya Ashraf yasoki. "

Tun datazo gidan bata taba ganin Aneesa ta d'au

kwalliya irin haka ba, ba namiji ba ko mace ce ta wuce dole ne ta kalleta dan tayi kyau sosai, Aneesa wacce takura ma Nafi ido cikin tsananin takaici ta karaso.

Kwalliya tai dan taje su shirya da Ashraf amma me take gani haka?

A zuciye ta karas

o tare da kallan Nafi cikin tsananin takaici tace me kike anan? "

Nafi ta kalleta sai dai ta kasa cewa komai, Aneesa ta sake kuluwa tace " ke dan gidan ku ba magana nake miki ba? "

Nafi ta daure kawai jitai ta sami kanta da cewa" Ya Habib ne ya

kirani. "

Aneesa wacce bata gamsu da zancen ba tace " Nafi karkiga jiya nazo da niyyar dukanki ki d'auka wai ko kishi nake dake ko wani abun. "

Ta d'anyi dariyar kissa tace " Tausayi kike bani, kinfi kowa sanin ni dake ba d'aya bane sannan ke da

kanki zaki iya warewa kisan wa ya dace da Ashraf ko ince wa Ashraf yake so, dan haka ina baki shawara in ma da wani shirme ko yarinta akanki gwara tun wuri ki cireta dan kinsan wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, ke ko masu aikin gidan nan sun fiki daraja

. "

Ta bangaje ta tai gaba, jitai ranta yayi sanyi ta tuno maganar Umma datace " ki nuna mata ita ba komai bace ta hakan ne inma da wani munafircin a ranta zai sa ta shiga hankalinta."juyowa tai ta kalli Nafi tana nan a inda ta barta, ta sake dariya s

annan tai gaba.

Nafi kam sai juya kalamun take a ranta, tafi kowa sanin Ashraf yafi karfinta, ta kuma sani ko kata sun kare ba abinda zaiyi da ita sai dai meyasa takejin zuciyarta ba dadi? Wata zuciyar tace kema Nafi kina ganin mai mace kamar Ane

esa me zaiyi dake? Jiki duk a rame? Gaki yar kauye wacce ake neman biyan bashi da ita? "



Da kyar ta karasa d'aki tai wanka sannan tasa abinci a gaba, da kyar takeci ta rasa me yasa batajin dadin abincin sam.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login